Chapter 3
*PART OF OUR DESTINY*
*CHAPTER 3*
Saboda girman kalmar, wacce koda sau d'aya bayason jin wani abu daya dangance ta, domin acikin yan kwanakin nan, gaba d'aya irin wannan cases din suke samu.
Jim ya d'anyi na wani lokaci, kafun ya tattare file d'in dake gabansa, had'i da folder'n nata ya tura acikin drawer'n sa, jikinsa amace haka ya mik'e tsaye hannunsa rike da wayarsa ya fice daga office din.
Kasancewar 1 pm ta cika harda wasu yan mintuna.
Direct parking space d’in hospital d’in ya nufa, domin yasan zuwa lokacin Sa'id Driver na nan yana jiransa.
Kamar yanda ya tsammata kuwa hakanne ta kasance domin Sa'id d’in ya jima da zuwa, wanda hangosa da yayi ne yasa shi tashi cikin sauri ya bud'e masa murfin mortar.
"Barka da fitowa Sir."
Sa'id driver ya fad'a alokacin da Dr. Emraan din ya k'araso.
"Yawwa."
Ya amsa masa agajarce had'i da shigewa cikin motar, wanda ganin hakan yasa Sa'id d'in shima shiga ahanzarce yaja motar suka fice daga cikin asibitin.
Kaitsaye shumfud'add'iyar hanyar da zata sadasu da Annor Mosque suka nufa, domin abune da Sa’id din yasani, kusan ko wacce jumma'a anan Dr. Emraan din keyin sallah, duk da cewa yau d’in sun d'an makara, wanda hakan yasa Sa'id na gama daidaita parking din motar, ya fito da hanzari hannunsa rike da bottle water, dashi yayi alwala tare da wucewa cikin masallacin kaitsaye.
Bayan an idar da sallan addu'o'i yayi kamar yanda ya saba, har na tsawon wasu mintuna kafun ya fito daga cikin masallacin, anan waje ya samu Sa'id tsaye ajikin mota, wanda already ya riga daya idar da nashi sallan.
"Mu tafi ko.”
Ya fad'a yana me shigewa cikin motar, daga haka Sa'id yaja suka tafi.
Tafiyar wasu y'an mintuna sukayi, kafun suka iso cikin rantsatstsiyar unguwar Asokoro, wacce ta k'unshi kyawawan gidaje na gani na fad'a.
Anan cikin unguwar ta Asokoro, gaban wani rantsattsen mansion, daya amsa sunansa motar tasu ta tsaya, tare da soma danna horn, cikin y'an mintuna kad'an aka wangale musu gate d'in, wanda shi kad'ansa ma kan iya d'aukar hankalin mai kallo.
Atsanake Sa'id driver ya tura hancin motar cikin katafaren gidan, da kyau da had'uwarsa ya wuce tunanin mutum, domin kuwa babban gida ne me d'auke da dogon ginin zamani, me matuk'ar k'ayatarwa, wanda yake d’auke da babban compound had’i da babban lambu, uwa uba babban Parking space da cikinsa ke cike da tarin tsadaddun motoci, tamkar wani karamin wajen saida motoci, daga can gefen dama kuwa wani tabkeken swimming pool ne, da aka k'awatasa da flowers had'i da kyakkyawan ruwa me burgewa, after swimming pool din kuwa wasu flat part ne guda biyu manya manya, da akayi musu ginin zamani.
Komai na cikin gidan ya tsaru iya tsaruwa, domin an cikasa da kyawawan shuke shuken, flowers kala daban daban da suka k'ara bayyana tsananin kyau'n gidan.
Acikin babban rumfar Parking Space d'in, Sa'id yayi parking motar.
Batare da wani b’ata lokaci ba Dr. Emraan d’in ya bud’e murfin motar ya fito.
Hannunsa rik'e da rigar suit d'insa da kuma wayarsa, ya nufi dogon ginin gidan nasu.
Tafiya me dan tsawo yayi kafun ya iso, babban balcony d'in da zai sada shi da babban falon gidan, hannunsa ya daura akan handle din k'ofar ya murd’a ahankali, Bakinsa d'auke da sassanyar sallama yasa kansa acikin, babban palor'n tare da ajiye k'afansa akan lallausan sofa'n da y'an yatsun k’afafun nasa suka lume acikinsu.
Ya ilahi na fad'a saboda ganin tsananin kyaun babban parlorn daya samu kansa aciki, wanda aka k'awata shi cikin Original Royal Sofa, masu matuk'ar kyau, da tsadar gaske, kyaun falon tamkar ba a Nigeria ba, bayan kuma babban tv plasma din dake ta aiki shi kad’ai babu kowa a falon.
K'arasowa cikin falon yayi, da yanayin dake nuna gajiya warsa, ahankali ya zube akan royal sofa'n, yana maida numfashi tamkar wanda yayi wasan tsere.
Idanunsa ya d’an lumshe, tare da bud’esu yana k’iran sunan.
"Aamma!”
“Aamma!!”
Da sassanyar muryarsa, had’i da maida kallonsa ga matattakalan dake cikin falon, domin yasan ba lallai wacce yake k'ira d'in ta jiyoshi ba, sanin hakan yasa shi mik'ewa tsaye da niyar haurawa saman.
"Ah Emraan ka dawo ne?”
Sassanyar muryar matar dake tsaye abayansa ta fad’a, wanda jin hakan yasa shi juyowa.
"Aamma na!!”
Ya fad'a fuskarsa d'auke da murmushi yana me kallon, kyakkyawan matar da ak'alla bazata d'arawa 50 years ba, wacce take tsaye sanye cikin rigar Turkish abaya, inda ta yane kanta da mayafin abayar, Matar farace sol, domin saboda tsabar haskenta har wani jaja jaja fatar ta tayi, Idan ka kalleta kaitsaye zaka bata matsayin mahaifiyarsa, saboda yanda yake kama da ita sosai, ga kuma kamanninta da suffarta da suka bayyana cewa ita d'in cikakkiyar Lebanese ce, uwa uba huta da jin dadi sun gama bayyana ajikinta, ta yanda baka isa bata 50 years d’in da take dashi ba, saboda yanda fatar jikinta yake, y’ar gayu ce sosai, komai nata walwali yake kamar yanda tsadaddun gold rings din dake yatsun hannayenta keyi, ita d’in ma’abociyar kyau da ado ce, domin duk da shekarunta bai hanata sakin dogon gashin kanta ya sauk’o har kan gadon bayanta ba.
"Ka dawo?"
Ta tambaya adaidai lokacin da take k'arasowa inda yake tsaye.
"Yeah I'm back Aamma, i came back with hungry."
Ya fad’a yana me kwab’e fuska, tare da soma kokarin cire socks d'in dake k'afarsa.
Murmushi Aamma'n tayi, domin dama tasan za’ayi haka, batare da ta tankashi ba ta nufi dining table d'in dake cikin falon, da yasha kujeru na alfarma.
Fuskarta asake tace.
“Sai kazo kaci abinci ai, acici, kaidai baka tab’a gajiya dacin abinci.”
Murmushi yayi, had’i da rufa mata baya, anutse yaja d'aya daga cikin kujerun ya zauna, Aamma'n ce tayi saving d'insu duka, domin dama itama abincin zata ci.
Hakan yasa su zama akujeran dake facing juna.
Loman farko na abincin daya kai bakinsa, yasa shi lumshe idanunsa, saboda jin dadin abincin Mahaifiyar tasa, kansa ya jinjina cike da gamsuwa yake tauna lamb chops d'in da dad'insa ke ratsa shi.
Daidai lokacin wani kyakkyawan farin dattijo me Kamala ya shigo cikin falon, fuskarsa d'auke da yalwatacciyar murmushin da ta k'ara bayyana kyawunsa dake b'oye acikin tarin farin sajen dake fuskarsa, dattijo ne wanda ak'alla ya rufawa 50 years baya, amma saboda yanayinsa na zama d’an boko, yasa bazaka ce yakai hakan ba, domin yana da kwarjini had’i da tsarin jiki me kyau, ga kuma tarin dukiya dajin dadin da yake ciki, da suka taimaka wajen b'oye shekarunsa.
ENGINEER ASSISIQUE ATTOM EL-FAROUQ kenan, babban d'an kwangilan da ake ji dashi acikin Nigeria, mutumin da sunansa ke yawo ta kota ina acikin k'asar dama wajenta, kasancewarsa k'wararre Kuma lamba d'aya wajen iya tsara manya manyan kwangiloli, domin duk wata babban kwangilan gine gine, daga wajensa yake fitowa, yayi shura akan sana'arsa, duk da cewa yana tab'a wani kasuwancin na daban bawai iya Kwangilan yakeyi ba, mutum ne shi me dattako da kammalalliyar zuciya.
"Assalamu Alaikum."
Yayi sallaman da yasa dukkaninsu d'agowa, atare suka amsa sallaman nasa, kowannensu fuska cike da fari'a.
"Barka da dawowa Abbou."
Emraan ya fad'a cikin girmamawa kamar yanda ya saba yiwa mahaifin nasa akoda yaushe.
"Yawwa Emraan barka, har ka dawo kenan ya Hospital din?"
Abboun ya amsa, adaidai lokacin da ya k'araso dinning area d'in, ya zauna batare kuma daya jirayi amsan Emraan din ba yace.
"Wato ku dai baruwanku dani ko, ko dani ko babu ni zaku iya fara lunch batare da kun jira ni ba."
Yayi maganar cikin wasa da raha, lokaci d’aya yana me kallon Aamma da take cin abincin ta anutse, jin abunda yaceyasa ta dubansa, cikin raha itama tace.
"Toya zamuyi, dama tura abincin kawai mukeyi bawai dan munajin dadinsa ba, kasan idan babu kai akusa abincin baya dad’i ko ba haka ba Emraan?"
Tayi maganar tana me kallon Emraan, da akaron farko yayi dariya, cike dajin dadin ganin farincikin iyayen nasa yace.
"A a kam ke kad'aice kawai kikejin haka Aamma, nidai da yazo ma ji nayi abincin gaba d'aya no taste."
Dariya suka sa su dukansu, daga haka kuwa babu Wanda ya sakeyin magana, sai Aamma da ta tashi tayi saving Abboun, nan suka shiga cin abincin atare.
Wanda ganin yanda suke cin abincin yasa, Emraan kallon Aamman nasa, cikin nutsuwa da kuma santi yace.
"Gaskiya bana jin aduniya za a samu wata mace da takai Ammana Iya girki."
Harararsa Aamman tayi, kamar yanda ta sabayi idan zatayi mishi magana awasu lokutan, batare dayin wani tunani ba tace.
"Zama a samu ne, domin nima ka kusa daina cin abincina kwata kwata, dan da kayi AURE girkin matarka zaka na ci ba nawa ba.”
Cak ya tsaya da cin abincin nasa, domin har yakai loman abinci bakinsa ta furta kalmar da ta sanya zuciyarsa wani irin mummunan bugawa, tare da sanya masa wani irin matsanancin tsoron, daya sashi maida idanunsa k'asa, cike da fargaba ya had'iyi abincin dake bakinsa, wanda daga d'and'ano me dad'i ya koma masa me d'acin gaske.
Shiru yayi domin bazai iya tankawa ba, saidai ak'asan zuciyarsa yana tsoron kada Aamma'n nasa ta sake d'ago maganar, saboda wannan kalmar itace babbar RAUNI aduk gaba d'aya rayuwarsa.
Shiru ya had’i da basarwa, tare dayin kamar baiji me tace ba.
Daga haka itama Aamma’n bata sake magana ba, har na tsawon wasu y'an mintuna, babu d'aya daga cikinsu daya k'ara cewa wani abu.
ahankali ta d'ago da kanta ta kalli Engineer Attom d'in dake cin abincin sa cikin nutsuwa, d'an jim tayi saboda zuciyarta dake wani irin bugawa, saboda tsananin damuwar dake cikinta, batasan wani irin tarba zaiyiwa maganar dake cike abakinta ba, saidai tana so ta fad’a, ahankali ta ajiye spoon d'in dake hannunta, cikin wata irin murya me sanyi'n, dake bayyana tarin damuwarta tace.
"TAREEQ ya kira waya yau, saidai kuma ina ji ajikina cewa kamar baya lafiya.... bansan meya saba, amma na damu matuk'a, na damu dason sanin sai yaushe? sai yaushe ne duk way'annan abubuwan zasu wuce?"
Ta k'are maganar tana me kallon Engineer din wanda jin abunda ya fito daga bakinta, yasa shi had'iye abincin dake bakinsa, batare Kuma daya d'ago kansa ya kalleta ba, ya ja tissue ya goge bakinsa, gami da mik'ewa tsaye, cikin nuna halin ko in kula had'i da wani irin yanayi me kama da fusata ya bar wajen, batare dako kallo d'aya ya sakeyiwa matar tasa ba, wanda ganin hakan yasa ta lumshe idanunta.
"Aamma..."
Emraan ya k'ira sunanta, cikin danne tarin damuwar dake ransa, tare da kamo hannunta ya rik’e acikin nasa.
Jin haka yasa idanunta dake alumshe ta bud'e ahankali cike da tarin damuwa, batare da ta amsa kiran da Emraan din keyi mata ba, ta juya bayanta a sanyaye ta sauk'e idanunta akan wani babban hoto dake cikin falon nasu, hotone dake d’auke da fuskokin maza guda biyu, wanda ke cikin wani frame me masifar kyau.
Kowanne daga cikinsu fuskarsa d'auke yake da murmushi, duk da cewa fuskar d'ayan tafi kama da wanda yake murmushin dole, wanda kuma shine ab'angaren hagu, yayinda fuskar Dr. Emraan ke ab'angaren dama.
"TAREEQ..."
Ta ambata araunace tana me kafe kyakkyawan matashin saurayin da idanunta, wanda yake sanye cikin Louis Vuitton t-shirt, yayinda kansa ke d'auke da tarin suma irin tasu ta cikakkun Lebanese, kyakkyawane ajin k'arshe wanda kamanninsa ya zamana ya banbanta da nasu, saboda yanayin launin cikin idanunsa, da suka kasance grey color, hakan yasa shi zama na daban.
Shiru tayi tana kallon hoton tsawon lokaci kafun ta janye idanunta, da suka kad'a sukayi ja, abayyane kake iya karanto tarin damuwar dake kwance akan fuskarta, duk da kuwa taso b'oye hakan amma ta kasa, Sam batason Emraan ya karanci komai akan fuskarta, hakan yasa ta mik'ewa tsaye, murya asanyaye cikin b'oye damuwarta tace.
"Idan ka gama kaje AMMABUWA nason ganin ka."
Bata jirayi me zaice ba tabar wajen, da idanunsa ya bita da kallo har sai da ta b'acewa ganinsa, kafun yaja wani irin dogon numfashi, jikinsa amace haka ya mik'e tsaye, da yanayin gajiya ya nufi sama, dan ji yake kansa na wani irin sarawa, tamkar zai fad'o k'asa.
Direct bedroom d'insa dake saman ya nufa, yana shiga kayan jikinsa ya cire ya fad'a toilet, wanka yayi ya shirya kansa cikin wasu kayan na daban.
Sosai yayi kyau cikin sabuwar shigar tasa na T-shirt da wandon black jeans, yana kammala shirin nasa, direct k'asa ya sauk'o, daidai saitin wani k'ofa dake cikin falon ya tsaya, hannunsa ya d’aura akan handle din k'ofar ya murd’a, ahankali ya tura kansa cikin d’akin bakinsa d’auke da sallama yana fad’in.
"Where’s my beautiful granny...."
"Bikir.."
Aka fad’a daga cikin d’akin, cikin yanayin d’an firgitar da tasa aka kasa amsa masa sallaman da yayi, wanda jin hakanne yasa shi tsayawa daga bakin k'ofar yana kallon wacce tayi maganan.
Wata Kyakkyawar farar Dattijuwa ce zaune akan kujera, idanunta sanye cikin medicated glass, sama da 20mn ta kwashe awajen tana bidirinta na ciye ciye, amma ganinsa yanzu yasa tayi gum da baki, ad’an daburce cike da son wayancewa, gudun kada ya gano abunda take yi, yasa ta d'agowa ta kalleshi, da fuskarta irin na marassa gaskiya tace.
"Yo meye ka zubamin ido, ba sai yanzu kaga daman zuwa ba, bayan tun daren jiya na fad'a ma irin yanda nakejin k'afata na rik'ewa, gaba d’aya yau ko tashi kasawa nayi, ta rik’e k’am.”
Murmushin daya k'ara fito da kyaunsa yayi, gami da k'arasowa cikin d'akin, daidai kusa da ita yazo, murya asake yace.
"Sannunki da hutawa, sannunki kuma da aiki, da alama dai kin manta da cewa marar gaskiya ko aruwa gumi yake, wato kina nan kina ta ciye ciyen kayan zaki, k'afafun naki kuma tsoron ki sukeji da baza suyi ciwo ba?"
Yayi maganar yana me sanya hannayensa, ya k'wak'ulo sauran Bounty Chocolate da kuma ferreror rocher d'in dake bakinta.
Hararsa tayi tare da sanya hannu ta buge hannunsa dake bakinta, cike da masifa tace.
"Ni fa banason takura Bikir, banason yawan iyayi, ci wannan ba zakici wancan ba, Allah yayimin baki Kuma ace abunda zanci ma sai an zab’amim, mutum sai shegen iyayi, wai akan ka aka fara zama likita ne? ko Ubanku haka yake gani na kuma ya barni babu yanda ya iya dani, sai kai me jajayen kunnuwa kaman k'osai..."
Ta kai k'arshen maganan tana tunkure masa kai, had'i da watsa masa hararan da yasa shi dariya.
Asanyaye cikin rarrashi yace.
"Haba Ammabuwa, yanzu dan mun nuna damuwarmu akan lafiyarki sai ya zamo matsala? Kinsan muna sonki ne shiyasa, At your age taking shugar will be very dengerous for your health, kinsan kina da diabetes, and look at your feet."
Yayi maganar yana me nuna k'afofinta da suka d'an kumbura.
Kallon k'afan nata tayi, bawai dan taso ba cikin guna guni tace.
"To d'aci zan sha idan ban sha zak'i ba? ko guba zan d'idd'ikawa cikina, gaya min.”
"Duk yanda ya miki, gaskiya ce dama ba kya so, amma nidai ina tsoron ace queen of beauty'n gidan mu ta rasa k'afafunta, but idan kin shirya rayuwa akan wheelchair shikenan."
Idanunta ta zazzaro jin ya ambaci maganar rasa k'afa, amma dan ta b'oye tsoron nata sai ta sake gyara zama, had'i da sanya hannu ta k'ara watsa dogon gashin kanta daya cakud'e da furfura baya, dan hakan take aduk lokacin da Emraan din ya kirata da suna Queen of Beauty, domin bata tab'a manta rayuwarta na baya kafun yanzu, tayi tashen kyau harda na nunawa, kasancewar tasha zama sarauniyar kyau a mabanbanta jami'o'in da tayi karatu, wanda tsananin kyaun nata ne ma yasa Alhaji EL-FAROUQ (Grandpa din su Emraan) d'in aurenta, wannan yasa har kawo yanzu take jin kanta a kyakkyawa, kasancewarta BERBER din da ta fito daga k'asar MOROCCO, ita kanta tasan tana da kyakkyawan jikin dake b’oye tsufanta.
Asanyaye tace.
"Shikenan naji bazan k'ara ba, ni dama idan bansha zak'in bane sai naji kaman ana muntsini na."
Dariya ce ta k'wace wa Emraan amma sai ya dake.
Batare daya k'ara cewa komai ba ya matso kusa da ita ya soma yi mata massaging k'afafun nata.
Daga haka ko shiru duk sukayi babu wanda ya sake cewa komai, har na tsawon wasu mintuna yana ta matsa mata k'afafun, a haka har bacci ya d'auke ta, dan dama da an tab'a ta ita sai bacci.
Wanda ganin tayi baccin ne yasa Dr. Emraan gyara mata kwanciyarta, tare da rage mata gudun A/C’n dake d’akin, ahankali kuma ya d’aura bakinsa adaidai saitin forehead dinta, kiss yayi mata kafun ya fice daga d’akin.
kaitsaye nasa bedroom din ya koma dan yana da abubuwan da zaiyi.
Acan ASSIDIQUE ATTOM EL-FAROUQ CONSOLTANT HOSPITAL kuwa, wata motar taxi ce tayi parking acan gefen asibitin.
Wanda hakan yasa wanda ke cikin taxi d'in fitowa, wata dattijuwar mata ce dake sanye cikin riga da zani na atamfa me sauk'in kud'i, yayinda gefen ta kuwa wani matashin saurayi ne, da bazai haurawa 25 years ba tsaye, yana lalub'a aljihun wandonsa dan neman canjin da zai bawa me taxi din.
"Muje KHALTY."
Ya fad'a yana me rik'o hannun matar, wacce ta riga data manyanta, duk da bata wani tsufa sosai ba, amma duk alamun girma sun bayyana ajikinta.
Yana rik’e da hannunta kaitsaye suka nufi cikin asibitin da girma had’i da kyaunsa ya cika musu idanu.
Ita dai matar da aka kira da suna Khalty da k'yar take iya jan k'afafunta da sukayi nauyi, cike take da tarin damuwa, had'i da fargaban abunda zata je ta tarar acikin asibitin, wani irin buguwa kirjinta keyi na ban tsoro'n, da yasa k'afafunta k'yarma tare da neman gaza d'aukar ta adaidai lokacin da suka k'araso mashigar asibitin.
Tsayawa tayi cak domin tana alhinin shiga gudun kada kunnuwanta su jiye mata mummunan labari.
"Yah Allah Khalty me yasa kika tsaya muje mana."
Matashin saurayin ya fad'a yana me sake rik’e hannayenta k’am.
Kai ta soma girgizawa, cikin muryar kukan daya k'wace mata tace.
"Bazan iya shiga ba Omar, bazan iya jurewa ganin YACINE acikin wani halin tashin hankali ba, tsoro nakeji Omar! wannan wace irin k'addarace? wani irin tashin hankali ne muka samu kanmu aciki...."
Ta k'are maganan tana me fashewa da kuka sosai, tamkar k'aramar yarinya.
Kukan da yasa Omar d'in jin wani irin tausayin kansu me tsanani asanyaye, cikin danne nasa damuwar yace.
"Akwai Allah Khalty, kuma in sha Allah zaiyi mana maganin komai, ki daina kuka dan ayanzu Yacine tafi buk'atar kulawan mu fiye da koke koken mu, tunda yanzu munsamu munshigo har compound din asibitin, ki daure mu k'arasa tun kafun nurses su koremu kamar yanda sukayi mana jiya."
Ya k'are maganar yana jawo hannun Khalty'n suka nufi cikin asibitin, badan taso ba, saboda wani irin tashin hankali takeji na kawar da tunaninta, kaitsaye cikin asibitin suka nufa, duk inda suka gilma kuwa mutane da yawa ne keta hada hada, ahaka suka k'araso saman daidai d'akin da suka ga ankwantar da Yacine din jiya, suka tsaya carko carko, kowannensu zuciyarsa cike da fargaban, abunda idan suka shiga zasu tarar.
Omar ne yayi jarumtar bud'e k'ofar d'akin ya shiga, wanda ganin haka yasa Khalty'n rufa masa baya, atare suka sauk'e idanunsu akan Yacine d'in dake kwance flat kamar gawa.
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajun! Yacine... Yacine!!l
Khalty'n ta fad'a cikin kuka alokacin da take k'arasowa inda Yacine din ke kwance, cikin tashin hankali ta soma girgizata
Tana fad'in
"Yacine bud'e idanunki kinji, bud'e idanunki gamunan munzo, dan Allah karki tafi ki barmu Yacine d'ina...."
"Excuse me."
Muryar wata nurse ya dakatar da Khalty'n daga maganar da take, inda gaba d'ayansu suka juyo suka kalleta.
"Bamason hayaniya akan marar lafiya, kuma ma baku ga anyi mata allurar bacci ba ne, hayaniyar ku zai iya tashin ta, saboda haka dan Allah kuyi hakuri kuje waje."
Nurse din ta fad'i hakan tana me kokarin zarewa Yaccine din drip din dake jikinta daya k'are.
"Ina kuma zamuje yar nan? tun jiya fa muka kawota, amma har yanzu a haka take, dan Allah ku fad'a mana idan ma mutuwa tayi..."
Cewar Khalty dake rik'e da hannun Yacine din tana kuka.
Girgiza kai nurse d'in tayi, kamar kuma zata ce wani abu sai ta fasa, kaitsaye ta fice daga cikin d'akin.
Wanda hakan shiya bawa Khalty daman rera kukanta, kukan da babu me rarrashinta kasancewar Omar dake tsaye, shima kukan yake yi, amma nasa kukan na zuci ne ba wai irin na Khalty da takeyi a fili ba.
Haka sukayi ta kukansu har sai da suka gaji dan kansu suka daina.
Jigum jigum haka suka kasance acikin d'akin har na tsawon wasu lokuta.
Babban abunda ya k'ara d'aga hankalinsu kuwa shine rashin farkawar Yacine din, wanda daga isowarsu asibitin zuwa yanzu sun share sama da awanni 4 amma ko y'ar yatsar k'afarta basu ga ta motsa ba.
Hankalinsu ya tashi k'warai ahaka har magriba ta rufa.
Omar ne ya fita yaje yayi sallah, Khalty kam anan dakin tayi sallah, koda takai sujjadarta ta karshe kuka tasa.
Wanda yayi daidai da farkawar Yacine din wacce ta tashi amatuk'ar razane, had'i da ihun da yasa, Khaltyn tashi da sauri ta nufe ta.
"Yacine.."
"Yacine..."
Khaltyn ta fad'a amatukar tsorace saboda ganin yanda, take ta faman fusge fusge, had'i da ihun, da yasa ta tsayawa tana kallonta.
Atsorace take furta kalmar Innalillahi Wa'inna Ilaihirrajun..
Daidai lokacin Omar ya shigo da saurinsa yayi kansu, saboda Yacine din dake ta wani irin fusga, had'e da wani ihu me ban tsoro, cikin yanayi me kama da sambatu take fad'in wasu kalmomin da bazasu tab'a iya fassarasu ba, kasancewar basu san ma'anarsu ba.
Arud'e Khalty ta kalli Omar jiki da murya na rawa cikin kuka tace.
“Shikenan Omar shikenan ya haukata ta, wayyo Allah Na!"
Idanu Omar ya zazzaro jin abunda Khalty ke cewa, cikin wani irin rud'ewa had'i da tsoro ya juya da gudu ya bar d'akin batare daya tsaya baiwa Khaltyn amsa ba.
Jim kad'an kuwa sai gashi ya dawo, bayansa wata nurse ce da kuma wani likita guda d'aya, da alama kuma shima babban likita ne acikin hospital din.
Dr. Rayyern kenan, Gynecologist doctor'n daya k'ware wajen sanin duk wani abu daya shafi aikin sa.
Wanda ganin yanda patient din keta ihu had'i da kokuwan k'wace jikinta, daga rik'on da Khalty tayi mata ya sashi duban Omar, dake tsaye.
"Ku d'an bamu waje please."
Ya fad'a atausashe, jiki asanyaye Omar ya kamo hannun Khalty dake ta faman rusa kuka suka fice daga d’akin.
Fitar nasu kuwa shi ya bawa Dr. Rayyern din, daman yin aikinsa, atashin farko allura yayi wa Yacine din, na kashe jijiyoyin jiki, tare da narkar da duk wata kuzarinta, domin yasan matukar baiyi hakan ba a yanda take bazata tab'a bari ayi mata gwaje gwajen daya dace ba, domin tun ashigowar da yayi amatsayinsa na babban Gynaecologist yana ganin ta ya fahimci abunda ke damunta, hakan yasa shi sanya nurse din da suka shigo dashi d'in ta duba masa Privet part din yarinyar.
Tana kwance bata iya motsa koda y'ar yatsar hannunta, tana ji nurse din ta bud'e mata k'afafunta.
Wani irin hawaye me tsananin zafi ne suka kwaranyo daga cikin idanunta dake rumtse, sam hawayen nata bawai na azaba da radadin da take ji a sakamakon yi mata hakan bane, a'a na wani azababben ciwo ne da take ji acikin zuciyarta, wanda zafinsa ke tafiya da matsanancin bugun zuciyarta dake neman faso kirjinta.
Saida Nurse din ta gama duba ta tsab, kafun ta d’ago, magana tayi wani kasa kasa yanda Dr. Rayyern dinne kawai zai iya jiyota.
Jin abunda tace yasa Dr. Rayyern,
d'in, bata umarni cikin gaggawa, kan ta kai yarinyar, ayi mata duk wasu gwaje gwajen da suka kamata, idan an kammala ta kawo masa result din Office dinsa.
Bai ji rayi komai ba, ya fice daga d'akin da sauri, yanda yace d'in kuwa haka akayi domin wasu daga cikin abokan aikinta nurses ta kira, akan gadon tura marassa lafiya suka d'auki Yacine din dake mik'e samb'al kamar gawa, domin bayan zuciyarta dake bugawa da Kuma numfashin da take shak'a, babu wani abu dake motsi ajikinta, sai hawaye kawai dake bin gefen fuskarta kamar an kunna famfo, kamar yanda yace din, duk wani abu da suka san ya kamata saida sukayi, bayan sun gama tattara result din komai suka dawo da ita d'akin.
Inda suka samu su Khalty sunyi jigum jigum, wanda zuwa lokacin tuni dare ya rufa, kwantar da ita sukayi suka juya, ganin hakan yasa Khalty matsowa kusa da ita, asanyaye ta kama hannun Yaccine din, cikin matsanancin damuwa tace..
"Allah baya bacci Yacine, anyi miki zalunci kuma Allah Zai saka miki, saboda ancutar da rayuwar ki, an kuma b'ata kyakkyawar k'uruciyarki, Allah zai sakamiki Yacine..."
Khaltyn ta fad'a tana me share hawayen dake zubo mata da hab'ar zaninta, yayinda Omar kuwa yayi tsaye, yana jin wani matsanancin k'una acikin ransa, haka ya k'urawa fuskar Yacine din idanu, wacce tayi jajur, lokaci d'aya duk kamannin fuskar nata ya sauya, sakamakon idanunta da suka kumbura sumtum, agefe guda kuwa ga shatin zanen k'atti k’attin yatsu da suka kwanta rad'au agefen fuskarta, baya ga haka lips din ta duk ya fashe.
Yakasa yarda wai yau Yacine ce agabansa acikin irin wannan yanayin, ya kasa aminta da cewa, hakan gaskiya ne.
Ahankali ya janye idanunsa daga kallonta, saboda sautin kukan Khalty daya fara tashi.
"Khalty ya isa haka, ni zan koma gida amma kafunnan zan biya receiption na asibitin, idan akwai wasu kud'ad'e daya kama ta abiya zan biya, sannan zan biya ta restaurant na saya miki abinci, gobe in sha Allah zan dawo..."
Kai Khaltyn ta girgiza cikin sharce hawaye tace.
"Ni babu abunda zan iyaci Omar matuk'ar Yaccine bata dawo hayyacinta ba, banajin zan iya cin komai, saboda haka kaje kawai..."
D'an jim Omar yayi kamar zaice wani abu Kuma sai ya fasa, jiki asanyaye ya fice daga d'akin.
Anan yabar Khalty nata faman sakin sheshshek'an kuka.
Kukan da ita kanta batasan tsawon awannin da ta d'auka tanayi ba, kasancewar tun asali ita din mutumce mai saurin kuka, shiyasa ko ayanzu kukan baya bata wahala, zatayi koda babu hawaye.
Ahaka bacci b'arawo ya d'auke ta, saidai koda baccin nata yayi nisa, kaman an tsikareta haka ta bud'e idanunta, sakamakon wani irin abu da taji Yacine din nayi kamar me sabon hauka, kuka take hadi da ihun, dake nuna cewa sam bata cikin hayyacinta, awannan dare Khalty ta shiga cikin wani abu da ake kira tashin hankali, saboda, duk yanda taso controlling Yacine din ta kasa, daga k'arshe kuka ta sa, domin ayanzu tana da tabbacin cewa Yacine din ta kamu da ciwon hauka, domin sai mai ciwon hauka ne kad'ai zaiyi irin abunda take yi.
Ahaka suka kasance har wajajen 5 am, kafun Yaccine din ta daina sakin ihun firgita, had'i da tsoron dake lullub'e zuciyarta.
#Fatymasardauna