PART OF OUR DESTINY

Chapter 4

by @fatymasardauna

*PART OF OUR DESTINY*


*CHAPTER 4*


Sai alokacinne Kuma ta samu wani wahalallen bacci ya d'auketa. 

Ab'angaren Khalty kam yanda taga rana haka taga k'arishen daren, domin zama dirshan tayi ta dinga kuka harsai da hawayen nata dan kansu suka gaji suka daina fitowa daga idanunta.


ASOKORO.

Duk da sassanyar iskan safiyar dake kad'awa had'i da sanyin A/C'n dake busawa cikin d'akin, hakan bai hana jikinsa tsattsafowa da gumi ba, kasancewar kuma babu riga ajikinsa shiyasa zufan nasa k'ara yawai ta, cikin wani irin mawuyacin yanayi yake nannad'e jikinsa, had'i da fitar da wani irin numfashi mai kama da nishin wahala, wanda daga jin yanda sautin ke fita, da Kuma yanda yake ta nannad'ewa waje d'aya tamkar maciji, zaka fahimci cewa ciwo yake ji acikin jikinsa, duk yanayin nasa yafi kama dana wanda baya cikin hayyacin sa.

 Yana kwance ahakan ya soma jiyo wani irin

k'ara dake kokarin fasa kunnuwansa, azabure cikin tsoro had'i da firgita ya bud'e idanunsa dake rumtse k'am tare da tashi zaune, yana me k'arewa d'akin nasa kallo cikin matsanancin tashin hankalin daya bayyyana akan kyakkyawar fuskar sa.


Wani irin numfarfashi yake maidawa, tare da sanya hannu ya dafe kansa, ahankali cikin muryar sa da ta disa she ya furta kalmar.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajun!!"

Gami da jan wani dogon numfashin daya ida k'arasa dawowa dashi hayyacinsa.

D'an jim yayi na tsawon wani lokaci, yana jin mummunan mafarkin nasa na dawowa cikin brain dinsa filla filla,kansa dake ci gaba da sarawa ya rik'e, domin ko sau d'aya bayason tuna mafarkin nasa, dake kokarin tuna masa wanene shi, domin aduk lokacin daya tuna da hakan, ya kan samu kansa cikin matsanancin tashin hankalin, dake tafiya da duk wani nutsuwar zuciyar sa, akowacce rana ta duniya daurewa yake, domin tuna yana d'auke da wani rubutaccen k'addara acikin jini da b'argonsa ya kansa shi d'imaucewa. 


Ahankali cikin rashin kuzari ya zuro da k'afafunsa k'asa, tare da mik'ewa tsaye, cikin mummunan yanayin daya samu kansa aciki, kaitsaye ya wuce bathroom dinsa dan yin wankan, daya d'auke shi 30mn kafun ya fito d'aure da towel akan waist dinsa.

Agogon dake sak'ale asaman gadonsa ya kalla, wanda ya nuna masa 7:30 am daidai.

Ajiyar zuciya ya d'an sauk'e tare da soma shirya Kansa, cikin wani dogon wandon Calvin Clein, da kuma t shirt na DIOR.

Yayi kyau k'warai cikin shigar da ta amshi jikinsa. White Sneaker shoe ya sanya ak'afafunsa, had'i da feshe jikinsa da turaruka masu dadin kamshi, agogonsa na companyn GUCCI ya sanya, tare da d'aukar wayarsa dake kan bedside, cikin tafiyarsa dake kama dana isa ya fice daga d'akin.


Ahankali yake sauk'owa daga kan matattakalan falon, inda jin k'aran takun tafiyarsa Yasa Aamma dake zaune acikin falon d'agowa ta kalleshi. 

Fuskarta d'auke da kulawa tace.


"Emraan you're awake." 


Kai ya jinjina adaidai lokacin da yake k'arasowa cikin falon, murya asake yace.

"Yes Aamma na tashi, baccin ne duk ya isheni, am going to the hospital ." 


Da mamaki Aamman ke kallonsa jin yace asibiti zashi, domin asaninta ko wani weekend Yana k'aresa ne gida, baya zuwa asibiti har sai idan abun gaggawa ne ya taso. 

Wannan yasa ta yi masa kallon tsab, da yanayi irin na tuhuma tace.


"What will you go there and do ." 


Bai tab'ajin tambayar Aamman ta haifar masa da fad'uwar gaba ba sai yau, domin shi kansa yasan bashi da wani reason na zuwa hospital din, saidai yasan a can d'inne kawai zaije ya samu relief, had'i da y'ancin da zaiyi watsi da duk wani abu dake ranshi, idanunsa ya d'an lumshe tare da marairaice fuska kana asanyaye yace.


"There is a patient I need to check out, Suraj called me."

Ya shumfud'a k'aryar dashi kansa baisan taya akayi ta fito ba.


"It's okay, but you should have your breakfast first ." 

Aamman ta fad'a atak'aice tana mai meda kanta ga TV series din da take kallo.


Baiso hakan ba amma babu yanda ya iya haka dole ya zauna yaci abincin, bawai dan yanajin dadin abincin ba haka ya tuttura, agurguje ya fice daga falon.

Direct compound din gidan ya fito, wanda ganinsa yasa Said dake zaune acan nesa ya taso da sauri, saidai tun kafun yakai ga k'arasowa Dr. Emraan din ya d'aga masa hannu, cikin maganarsa da sautinta bata cika fita sosai ba yace.


"You should rest today, am driving by myself ." 

Yayi maganar yana me nufan parking space din dake compound din gidan, wata kyakkyawar mota ya bud'e ya shiga, reversing din ta yayi, kasancewar already me gadi ya riga daya wangale masa gate din gidan, kai tsaye ya fice daga gidan, tare da d'aukar hanyar da zata sadashi da hospital din nasu.


Anutse yake driving motar, har ya iso cikin hospital din, yana tafiya yana sauraran k'ira'ar suratul Yusuf, wanda MUHAMMAD AFIF ke rerawa.

Koda ya iso hospital d'in parking motar yayi, kamar kuma yanda ya saba saida ya kwashe lokaci mai tsawo kafun ya fito daga cikin motar.

Da tafiyarsa ta nutsuwa ya nufi cikin asibitin.


Duk Inda ya wuce gaishe sa ake har ya iso office dinsa, baizo daniyar yin wani aiki ba, shiyasa yana shiga cikin office din ya nemi waje ya zauna, had'i da jingina bayansa da jikin kujera ahankali ya lumshe kyawawan idanunsa.

Azahirin gaskiya nutsuwa yake buk'ata sosai, saidai hakan na neman gagararsa, saboda yana zama aka soma knocking k'ofar office din, idanunsa dake a lumshe ya bud'e, da yanayi irin na b'acin rai yace.


"come in.." 


Ahankali Dr. Rayyern ya bud'e k'ofar ya shigo, hannunsa rike da wata farar takarda, azahirin gaskiya da yanayin damuwa ya shigo, amma saidai ganin yanayin Abokin nasa yasa shi sake fuskarsa, cikin d'an yanayin tsokana yace.


"Stop frowning your face, it is me not the nurses." 


Murmushin yak'e Dr. Emraan d'in yayi, had'i da gyara zamansa, cikin yanayi irin na wanda ke nuna k'osawarsa da abu, ahankali yace.


"I'm tired Rayyern, I need to rest , yau banason damuwa kwata kwata." 


Murmushi Rayyern d'in yayi saboda Jin abunda 

Dr. Emraan din yace, hakan yasa cikin yanayin tsokana yace.


"Ka tab'a ganin inda Medical Dr ya huta? ai tunda ka zama Dr sai hakuri Baka da wani sukuni, well ba wannan ba what's wrong, you came early today, and it seems like you are not happy, what's wrong?"


"I'm okay Rayyern." 

Ya amsa atak'aice yana me kawar da Kansa gefe, gudun kada Rayyern din ya hango damuwar dake kwance acikin idanunsa, domin kuwa yasan Rayyern din mutum ne me iya karanto abubuwa da yawa daga cikin idanun mutum.  


"You're not okay Emraan, amma I will not force you on this, ga wannan report ne na wata patient, she needs to be taking care of Emraan, she was raped, she gets so many injuries, because she's young, sannan abun ya d'an tab'a mata brain, ta samu MENTAL HEALTH DIS ORDER, I won't say she will take a long time before she's fully recovered , amma dole akwai buk'atar bata kyakkyawan kulawa, for her to get out of this condition ..." 


Ya k'are maganar yana me mik'awa Dr Emraan takardar dake hannunsa.

Karb'an takardar yayi ahankali ya warwareta tare da zubawa rubutun dake jikin takardar idanun sa baya ko k'yaftawa, raunukan dake jikinta yake karantawa domin kuwa Raunuka shida ne ajikinta, biyu agefen waist dinta, hud'u kuma acikin privet part dinta. 

Abun yayi tsanani sosai, babban munin abun kuwa shine desperation din da yarinyar ke ciki. 


Wani irin numfashi Dr. Emraan ya fesar tare da d'ago idanunsa ya kalli Dr. Rayyern, da yaci gaba da cewa.

"Some people are heartless Emraan, so many things are happening in this country , wanda har yanzu aka kasa sauyawa, raping young girls is very common , na kasa gane sai yaushe za a d'auki tsastsauran mataki ga duk way'anda aka kama da aikata hakan, abun yana min ciwo sosai, ana lalatawa yara gobensu had'i da gurb'ata musu rayuwa, ana cin zarafin yayan talakawa saboda ansan iyayensu bazasu tab'a iya tsayuwa akan k'afafunsu dan nema musu hakk'insu ba, bazasu iya shari'a ba saboda rauni da Kuma halin talaucinsu, things are getting worse , I don't think this girl's parents will be able to take care of her in this condition , bana tunanin suna da kudin da zasu tsaya mata wajen ganin ta dawo daidai, abun yana min ciwo Emraan, imagine ace k'anwarka ce akayiwa haka..."


Idanu Emraan ya runtse cikin danne sabon ciwon da yakeji azuciyarsa, ahankali cikin sanyin murya yace.


"Let's go see the girl ." 


Atare suka mik'e shida Rayyern din, kaitsaye d'akin da Yaccine d'in ke kwance suka nufa, inda Rayyern din ne agaba Emraan na binsa abaya, wanda isowarsu bakin k'ofar d'akin ne yasa Emraan gane cewa itace yarinyar daya duba jiya.

Wani irin abune yaji ya tsaya masa a kirjinsa, adaidai lokacin daya jefa k'afarsa acikin d'akin, domin abu na farko daya fara dira acikin kunnuwansa shine sautin kukanta dake tashi, tamkar zai d'aga d'akin.


Wanda shigowar nasu ne yasa Khalty dake rik'e da ita, sakinta tare da k'arasowa garesu da sauri, batare da tunanin ko shid'in waye ba ta rik'o hannunsa, murya na rawa cike da tsoro tace.

"Ku taimakeni dan Allah, ku duba kuga abunda takeyi, tun jiya take abu d'aya, dan Allah kutaimaka, idan ma haukacewa tayi ku gayamin...." 


Ta k'are maganan tana me kallonsu dukansu biyu, Dr. Rayyern ne ya k'arasa kan yarinyar, yayinda Emraan kuwa sai ayanzu ne ma yake sauk'e idanunsa akanta. 

Kwance take akan gadon duk tayi wujiga wujiga, yayinda yalwataccen gashin kanta ke baje akan filon da akayi mata matashin kai dashi, kamar dai jiya har yau din idanunta dake rufe kirib akumbure suke, haka ma gefen bakinta wanda yake a fashe, aduk rayuwarsa yasha jin kukan mutane da yawa amatsayinsa na likita, amma akaron farko wannan kukan nata yanajinsa har tsakar kansa. 

Ji yakeyi ajikinsa bayason jin sautin kukan nata ko kad'an, ahankali ya janye idanunsa daga gareta, gami da takowa ya k'araso inda take kwancen, lallausan tafin hannunsa ya d'aura akan forehead dinta, zafi zau yaji goshin nata alaman cewa akwai zazzab'i sosai atattare da ita.


Juyowa yayi ya kalli dattijuwar matar da tayi jigum tana kallonsa.


"Meye ake kiranta?"

Ya tambaya.


"Yacine.."

Khalty ta bashi amsa tana sharce hawayen dake zuba a idanunta.


Idanunsa ya d'an lumshe ahankali, tare da yin k'asa da muryarsa, cikin wata irin murya kamar ta meyin rad'a, harshensa ya soma tattara kalmomi 6 din da zai ambata, da yanayin da bai tab'a yiwa wani magana ba, akaron farko ya furta kalmar adaidai saitin fuskarta.


"YACINE."  

Ya kira sunanta, da muryar da ta daki dodon kunnenta, tare da haifar mata da mummunan bugawar zuciya, saboda tun bayan faruwar abun shine Namiji na farko da taji sautin muryarsa, hakan yasa tsoronta sake ninkuwa, afirgice ta sake rumtse idanunta, domin duk abunda zata kalla ayanzu gizo yake mata da fuskar azzalumin daya b'ata mata rayuwa. 

Wanda fahimtar hakan yasa Dr. Emraan sake tausasa muryarsa, anutse kamar yanda suka saba yiwa masu rauni irin nata, magana amatsayinsu na doctors yace.


"Open your eyes, bud'e idanunki kinji, bud'e idanunki kiga, no one will hurt you, no one will hurt you anymore, oya open your eyes.." 


Ya k'are maganar yana me kafeta da idanunsa, yayinda acikin kirjinsa yake jin zuciyarsa na wani irin bugawa, wanda baisan kona menene ba, domin bai tab'ajin irin hakan ba, saidai acikin abu biyu dole akwai d'aya, kodai tana bugawa ne saboda maganar da yayiwa yarinyar, ko kuma tana bugawane adalilin mafarkin da yayi a safiyar yau din.


"Yacine." 

Ya sake kiran sunanta a karo na biyu, still cikin wata murya ta daban, wacce tasa Yacine din dake kwance, had'iyan wani Abu dake mak'oshin ta, tare da soma k'ok'arin bud'e idanunta da suka matuk'ar k'ank'ance, da kad'an kad'an take bud'e idanun, awahalce ta dire su akan fuskarsa da keyi mata dishi dishi, rikitattun idanunta masu d'auke da grey eye balls ta zuba masa, bata ko k'yaftawa, tamkar wacce take karanto wasu abubuwa daga kan fuskar nasa, ahankali take motsa busassun labb'an bakinta. 


Shima Dr. Emraan d'in idanun ya zuba mata, yana me kallon yanda hawaye ke kwaranyowa daga cikin nata idanun ba k'akk'autawa, ba zaice wannan shine karonsa na farko da yake jefa idanunsa acikin na mace ba, amma awannan kallon da yake mata jinsa yake wani na daban, hakan yasa shi janye idanunsa daga nata, lips dinta dake bushe ya kalla, ganin tana motsa su, da alama wani abu take fad'a wanda sautinsa bai iya bayyana, saboda raunin da muryar nata tayi.


Doguwar ajiyar zuciya ya sauke, gami da juyowa ahankali ya kai dubansa ga Dr. Rayyern dake tsaye kusa da Khalty dake kuka. 

"I need water ." 

Ya fad'a yana kallon Rayyern


Kai Rayyern din ya jinjina, cikin sauri ya fita daga d'akin, jim kad'an Kuma sai gashi ya dawo rik'e da bottle water a hannunsa, ahanzarce ya mik'awa Dr. Emraan bayan ya bud'e masa murfin bottle din.


Cikin nutsuwa Dr. Emraan ya karb'a tare da zuba ruwan acikin tafin hannunsa, ahankali yake shafa mata ruwan akan fuskarta. 


Wani irin numfashi me k'arfi taja had'i da yunk'urawa saboda sanyin ruwan da taji akan fuskarta, wanda hakan ya sata k'ara ware idanunta, had'i da bud'e bakinta wanda ya riga ya bushe. 

Ganin haka yasa shi d'aura mata bakin gorar akan nata bakin, ahankali yake tsiyaya mata ruwan, wanda sauk'ansa acikin bakinta, ya haifar mata da sakin wani k'akk'arfan ajiyar zuciyar, da yasa ta soma yunk'urin tashi, lokaci d'aya kuma ta fashe da wani irin kuka, tana kiran sunan Khalty cikin muryar kukan da yasa Khaltyn matsowa kusa da ita sosai, da yanayin rud'ewa tace.


"Gani Yacine, gani akusa dake Yacine dina, kalleni, kalli Khaltyn ki." 

Ta k'are maganan tana me tallafo hab'ar Yaccine din duka biyu.

Duk da cewa bata gama dawowa hayyacinta ba, amma bazata kasa gane muryar Khaltyn ta ba, daya taimaka wajen tsagaitawan kukan ta.


Dr. Emraan ne yayiwa Dr. Rayyern alama akan ya fita da Khaltyn, saboda wasu tambayoyi da yakeson yi wa yarinyar, badan Khalty taso ba haka ta fita, wanda ganin haka yasa Yacine din sake fashewa da kuka, tare da kakkare jikinta dake b'ari, had'i da k'yarma, idanunsa ya zuba mata ganin yanda take b'ari, domin hatta labb'an bakinta karkarwa suke, da dukkan alama zazzabi me zafin gaske ne ya dirar mata lokaci d'aya ba shiri.


Ajiyar zuciya ya d'an sauk'e, tare da gyara tsayuwarsa, murya atausashe yace.

"Stop crying please, or do you want me to give you injection ?" 


Ya k'are maganar batare daya kalleta ba, saboda injection din da yake had'awa. 


Yayinda ita kuwa idanunta ta rumtse, tare da sake k'ank'ame jikinta, domin sam bata ma fahimtar abunda yake cewa, saboda tsoronsa da take ji, ko kyakkyawan motsi ta kasa yi.


"Are you scared ?" 

Ya tambaya alokacin da yake jefa k'wayoyn idanunsa acikin nata, dake cike da sabbin hawaye, bai tsammaci amsa ba domin yasan ba lallai ma tana fahimtar abunda yake fad'i ba, wannan yasa ahankali yace.


"You're safe now saboda haka ba abunda zai sameki, I promise you, no one will hurt you anymore , stop being scared, fad'amin ina ne yake miki ciwo? "


Yanda yayi maganar yana me kafeta da idanunsa, wanda azahirance Idan ka kalli cikinsu zaka fahimci cewa bawai yanajin dadin maganar bane.


Kallon juna sukayi in a few second kafun ahankali ya d'ago hannunta adaidai kan damtsen ta ya soka mata syringe na allurar dake hannunsa.

Da yasa ta saki wani irin k'ara me k'arfi, jin alluran acikin jikinta, yasa ta soma kiciniyar k'wace hannunta amma ta kasa, har sai daya gama kafun ya sake ta.


Jin ya sake ta yasa ta soma kokarin dirowa daga kan gadon, amma saboda rashin k'arfin da take fama dashi sai ta kasa.

Bisa dole haka ta koma ta kwanta hannunta dafe da kanta dake ciwo kaman zai rabe gida biyu. 

Wasu irin sambatu take da babu me iya fahimtar me take cewa.

Saidai saboda allurar da ta fara ratsata cikin wani d'an k'ank'anin lokaci duk jikinta ya farayin sanyi, take idanunta suka shiga lumshewa kamar mejin bacci, asannu sannu take jin duniyar na juya mata, hankalinta na sake gushewa izuwa wata sabuwar duniyar, da ta kasa tantance rayuwa ne acikinta koko mutuwa.


Ahankali Dr. Emraan ya dawo da kallonsa ga Dr.Rayyern wanda ya zubawa yarinyar idanunsa baya ko k'yaftawa.


"Let's go to my office ."

Ya fad'a yana me wucewa gaba, ba musu Dr. Rayyern din ya rufa masa baya.


Khalty kuwa dake zaune a waje, ganin ficewarsu ne yasa ta shigowa cikin d'akin, gaban gadon da Yacine din ke kwance ta k'araso, cike da tarin soyayyar da takeyi mata, ta rik'o hannayenta, cikin kulawa had'i da tsananin tausayawa ta soma shafa lallausan gashin kanta.

Ahankali take tofa mata addu'oi akan fuskarta, bayan ta kammala karanta mata addu'o'in murya atausashe ta soma fad'in. 

"Ba abun da zai sake samunki Yacine, in sha Allah, babu wanda zai cutarmin dake, anci mutumcin maraicinki, an keta miki haddinki, amma Allah Baya bacci, yana tare damu akoda yaushe, Allah Baya bacci Yacine." 

Ta k'are maganar tana sharce hawaye da kuma majinan da suka had'e mata.


Daidai lokacin Dr. Rayyern ya kuma sake dawowa, da wasu nurses biyu dake biye dashi a baya.


Kallon Khalty yayi, yayinda nurse din kuwa ke d'auke Yacine dake kwance suka kwantar da ita a wani gadon na daban.

Murya atausashe cikin son kwantarwa da tsohuwar hankali yace.


"Karki damu, ki kwantar da hankalinki zata ji sauki in sha Allah, yanzu zamuje ayi treating duk wani ciwon dake jikinta, sannan akwai yiwuwar zamu iya canja muku d'aki, saboda yana yin ciwon nata tana buk'atar kulawa sosai, tare kuma da gujewa duk wani Abu dazai tsorata ta, musamman ma hayaniyar mutane, wanda idan tana ji zai na damun brain dinta har ya haifar da wani matsalan na daban, saboda haka dan Allah Akula sosai." 


Kai Khaltyn ta jinjina, still dai tana kukan da ita kanta batasan ranar daina shi ba.


Dr. Rayyern din kuwa yana gama fad'in hakan yayi waje, cikin hanzari nurse din suka rufa masa baya suna me tura gadon da Yacine din ke kwance. 


Kaitsaye wani d'aki na musamman suka nufa da ita, bayan anyi mata alluran da zasu kashe mata zafi, wata nurse tayi mata treating duk inda take da ciwo, harta ciwukan dake p*ssy dinta saida sukayi mata treating. 

Bayan sun kammala suka maida ta d'akin, duk wannan abun kuwa batasan anyi ba, domin ta jima da barin duniyar mu, saboda allurar da Dr. Emraan yayi mata takasa tantance shin tana raye ne ko tana mace.


9:00 daidai na dare motarsa Mercedes Benz ta shigo cikin gidan, kamar ko yaushe a parking space yayi parking motar nasa, tare da fitowa kaitsaye ya nufi cikin gidan, hannunsa na dama rik'e da wata ledar dake d'auke da tambarin sunan asibitinsu.


Kamar ko yaushe bakinsa d'auke da sallama ya turo k'ofar falon ya shiga, kasancewar tun kafun ya k'araso cikin falon yake jiyo sautin maganganu, wanda hakan ke bashi tabbacin cewa akwai mutane acikin falon.

Kamar yanda ya zata kuwa hakanne, domin Ammabuwa ce zaune akan traditional red rug, tayi d'aid'ai da k'afafunta, sai faman surfa bala'i take, wanda baisan kona menene ba, domin agefe Aamma ce hannunta d'auke da littafi tana karantawa, sai kuma Abbou dake gefe kusa da Ammabuwa'n yana aiki a laptop d'insa.


Jin sallamansa yasa su d'agowa suna me amsa masa, Aamma kuwa kallonsa tayi cike da tuhuma tace. 


"A ina katsaya haka har kayi dare?" 


Karab Ammabuwa ta cafe zancen da cewa.

"A ina kikeso ya tsaya dama, tunda shi dai ba mace ba ai dole ne ya tsaya yayi abunda yake so, wato kin fiso ya dawo da wuri kusani agaba kuyi ta hantara ta ko, gaba d'aya kun hanani sakat agidan nan, ci wancan ajiye wannan, ni na haifeku amma kun maidani kamar wata y'ar ku." 


Sassanyar murmushi yayi, domin sai alokacin ya fahimci fad'an me Ammabuwa'n keyi, k'arasowa cikin falon yayi, tare da d'an sunkuyawa daidai wajen k'afafun Ammabuwa'n ya zauna, ahankali cikin lumshe idon dake bayyana gajiyarsa yace.


"Haba Ammabuwa wai duk wannan fad'an na menene?" 


"Yo ba dole nayi fad'a ba Bikir uwarka da Ubanka ke neman hana min rawan gaban hantsi, dama Kai kad'ai ne nake jin dadinsa acikin gidannan, Kuma kaima suna son b'ata ka, dama shi wancan me jajayen kunnuwan tuncan ba shiri mukeyi ba, saboda tsinannun magen da yake rayuwa dasu, baya ga haka kamar shiya kawo miskilanci duniya, ba shiga sha'anina yake ba sai yaga dama, gashi kuma tunda yasa k'afarsa ya tafi k'asar Ubansa na gado ya manta da kowa, yo k'asar Ubansa na gado mana k'asar y'an uwansa masu jajayen kunnuwa da jajayen baki, tunda sun b'oyeshi acan, ya manta da kowa nasa, ace ayi mutum kamar dutse, bashi da d'and'ano ko kad'an, bakasan eh dinsa ba baka kuma san a'an sa ba, kai ni naga rayuwa.." 


Idanunsa dake alumshe ya bud'e jin hirar Ammabuwan na neman sanjawa zuwa wani bigiren daban, cike da son kawar da zancen ya jawo ledan da ya shigo dashi din, ya dire agaban ta.


"Gashi magungunan kine kiyi kokari kina sha akan lokaci please." 

Ya kai k'arshen maganan yana me mik'ewa tsaye, tare da nufan hanyar d'akinsa, har ya fara haura stairs din. 

Aamma dake zaune ta juyo ta kalleshi. tare da fad'in.

"Ba zaka ci abinci bane?." 


"Na k'oshi Aamma."

Ya amsa atak'aice batare daya dakata da tafiyar da yakeyi ba, saboda ayanzun bayajin wani abu zai samu matsuguni acikinsa, haka ya k'arasa cikin babban falon nasu, dake sama wanda cikinsa ke d'auke da kyawawan Fulius Luxury Sofa.

 Shima shirgegen falo ne me zaman kansa, da aka narka millions of naira wajen k'awatasa, domin duk da babu wasu tarkace me yawa acikinsa, komai dake cikinsa expensive ne especially sofas din dake falon.

Gajiyayyun idanunsa ya sauke akan wata k'ofa dake d'an nesa da nasa, ta b'angaren hagu, idanunsa ya zubawa k'ofar baya ko k'yaftawa, wasu abubuwa da yawa yake rayawa acikin zuciyarsa, yana nan tsaye har na tsawon wasu mintuna, kafun ya janye idanunsa, k'afafunsa da duk sukayi sanyi yaja ya nufi bedroom dinsa. 

kamar yanda ya saba matuk'ar ya dawo aiki sai yayi wanka kafun kwanciya, hakanne yanzun ma ya kasance, wanka yayi had'i da shirya kansa cikin kayan bacci, domin already ya riga da yayi sallan isha acikin masallacin dake gefen hospital din nasu. 


Laptop d'insa yake son dannawa kamar ko yaushe, dan ya saba kafun yayi bacci sai ya danna laptop din, amma a yau sai yakeji ya kasa iyayin koma, kwanciya yayi lamo akan tafkeken gadon nasa yana me lumshe idanunsa da sukayi ja.

Baisan me yasa yakejin ranar yau din ta kasance ta daban agaresa ba.

Yanajin zuciyarsa na tsananta bugawa, irin bugawar dake shaida masa, tabbatuwar sabuwar k'addarar da ke kokarin tunkaro rayuwarsa. 



#fatymasardauna

#Sacrifice


Vote please