DA'IMAN ABADAN ZAZZAFAR KAUNA

ZAZZAFAR KAUNA 1&10

by @jameelarhsadiq6388

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺

_ZAZZAFAR KAUNA_

*~HOT LOVE AND FATE STORY~*


*BOOK THREE*


_STORY AND WRITING BY_

_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_


_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_


_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! ***_


***


*Page na kune masoyana a duk inda kuke ku sani nima Ina sonku kamar yanda kuke sona🥰*


*1-10*


*CIGABAN LABARIN*


Kuka kawai Beauter take ta daura kanta a saman cinyar Ammie tana kuka,komai ya dawo mata sabo fal kamar yanzun komai ya faru haka take ji..tunda Haidar ya fasa aurenta bata taba jin tsanarshi irin yanzun ba tabbas Ahmad ne silar faruwar komai...Amman Haidar shine *SANADI* shine yayi sanadin shigowarta duniya...Da ace bai fasa aurenta ba da yanzun tana gidanshi a kwalkwashin inuwar aurenshi,Amman ya rushe komai yayi sanadin komai ya ruguza komai.


Dago kanta Ammie tayi tana cewa.."kukan ya isa haka Daughter karda kanki yayi ciwo." Share mata hawayen tayi tana cigaba da cewa.."touching heart story! and kuma haka Allah ya qaddara daman haka kika rubuto Daughter in Sha Allah komai yazo karshe ya zama labari...sai dai ba zan matsa maki ba akan aure sai dai inason ki zauna kiyi tunani Daughter ki sani darajar y'a mace dakin mijinta."


Daga kai Beauter tayi bata ce komai ba sai sauke ajiyar zuciya da take..Dad ne ya sauke ajiyar zuciya yana cewa.."Hauwa tashi kije ki kwanta dare yana yi."..To tace tana tashi ta shige room din Ammie tana fadawa wanka,bayan tashin Beauter Dad ya kalli A Kadir yana cewa.


"Kaji dai abunda ya faru da Hauwa'u nasan waye Kai nasan abunda zaka iya da wanda ba zaka iya ba, duk da ba'a yabon d'an yau amman ni nasan waye Kai ka rike wannan yarinyar amana ka sata farinciki ka mantar da ita kuncin da Ahmad da Haidar suka sata nasan zaka iya, abu d'aya zaka yi yanzun ka samu ta anshi soyayyarka shine gaba."


"In Sha Allah Dad,zanyi iyakar kokarina da yardar Allah."


"Allah yasa."


*Nigeria 🥀*


Koda yazo bakin gate danna horn yayi mai gadi ya wangale masu gate yana tura hancin motarshi a cikin babban compound din gidan...da yake babban compound ne wanda zai iya daukar mota saman da goma banda idan kaje dai dai apartment dinka nan ma mota sama da hudu ko biyar za'a parka ta...dai dai apartment dinsu yayi parking din motar yana kashe mota ko kallonta baiyi ba ya balle marfin motar ya ficewarshi ko inda take bai kalla ba.


Da harara ta rakashi tana goge guntayen hawayenta ta fito itama tana tura marfin motar da karfi,duk da yaji yanda ta kulle motar kamar yak'i amman bai ko waigo ba balle ya nuna yasan tana yi,fuuuuu haka take tafiyar sai wani hade fuska take kamar yanda shima yake hadewa bude kofar yayi yana shiga bakinshi dauke da sallama.


Har zata shiga yayi sauri ya riketa yana zabga mata harara da kallon banza yana cewa.." idan kika kuskura kika shigar man gida bakiyi addu'a ba sai nayi ball dake a cikin daren nan stupid marar wayau."


Fisge hannunta tayi daga rikon da yayi mata tana tsayawa tayi addu'a sannan ta shiga ko sallama batayi a fili ba ,sai dai a zuciyarta tayi ko tsayawa kallon tsaruwar parlon batayi ba ta nufi wani room tana murdewa ta shigewarta ta na bango kofar...Tsaye yayi yana kallon kofar da ta shiga can yayi tsaki tana kwafa yace.


"Zan yi maganin wanann rashin kunyar taki soon useless."


Tsaki yayi yana kulle kofar gidan yaje ya ajiye mata leda a bakin kofar da ta shiga ko nocking baiyi ba balle yace fito ki dauki leda, ya juyo ya hayewarshi sama ya samu dakin da yasan nashi ne ya shiga.


Koda ta shiga wanka ta fara yi tana fitowa ta zauna gefen gado ta dan huta tana sauke ajiyar zuciya tace.."zan nuna maka baka iya komai ba a wajen miskilancin wallahi Najeeb a shirye nazo gidan nan dan na gyara maka zama dole nayi maganinka dole na koya maka yanda ake taitala mace dole na koya maka yanda ake susucewa akan mace ba dai ka aureni dan ka kuntata man ba?to dole kaima na kuntata maka wannan alkwarine."


Duba wardrobe din dakin tayi taga ba kaya a ciki haka a gaban mirror din ma babu komai a sama dan tsaki tayi tana daukar hularta ta saka tana bude kofar ta fito,tsayawa tayi tana kallon ledar da ya ajiye mata tsaki tayi tana tsallake ledar tayi wucewarta ko kallon room din da ke gefenta batayi ba dan tasan yana ciki,hararar kofar tayi tana hayewa sama daga ita sai dan karamin towel Wanda iyakacin shi cinya,cinyarma ko rabinta bai rufe ba a hankali take hawa strains din duk da yanda ta saba tafiyarta haka take kayanta sai da fuskarta a tamke take babu fara'a ko d'aya a saman fuskarta.


Tsaye yake da cup din tafataishen black tea a hannunshi kamewa yayi yana kallonta kamar ya samu tv wani irin yarrrr haka jikinshi yake yana jin wata damama haka yake jin tsokar jikinshi tana mashi,take idanunshi suka fara sauya kala hawaye har sun taru a saman eyeballs din shi.


Tsaye tayi a bakin kofar tana kokarin bude kofar amman sai ta jita a kulle ba kamar ta farkon da ta shiga ba,tsaki taja tana tura kofar da karfi amman a kulle take waigawa tayi zata koma kasa idonta ya sauka a kanshi yar razana tayi tana cewa.


"A'uzubillahi! Allah kayi mana tsari aljanu da mugayen mutane, haba mana kurwata kurr wallahi mutun yaci kanshi."


A hankali take maganar yanda ba zai jita ba, amman abunda bata sani ba duk abunda ta fad'a yaji rau a cikin kunnenshi,har ta fara taka step zata bar saman yayi caraf ya kamata yana tsuke fuska yana kallonta daga sama har k'asa.. kokarin ansar kanta daga rikon da yayi mata take tana balla mashi harara tana turo baki can ta cinno baki tana cewa.


"Wai Malan mai haka?bashi ko tara da zaka wani rikeni."


Again baice mata komai ba kuma bai sake ta ba,bai bar kallonta ba,dan kirjinta ya kurema Ido yana kallo kamar zai fiddo su daga cikin towel din haka yaka ji,cizonshi tayi tana kokarin rugawa ko gezau baiji ciwon ba.


Sai ma warce towel din da yayi daga jikinta yana wurgar dashi gefe Kara ta saki tana boye boobs dinta da hannu tana durkushewa k'asa tana kuka.. d'ago ta yayi fuskarshi a turmuke yana mata wani banzan kallo yana cewa.


"Ke har kin kai mace da zan tsaya na kalla?maike gareki wanda zai rudeni har na gigice na kama kallonki.?" Tsaki yaja yana Kai hannunshi a saman boobs dinta yana cewa..."ni nan banga komai ba a shafe nike ganinki ai takamarki kenan nan wajen ko?to ni nan banga komai ba dan baki da banbanci da kirjin yarinya yar shekara 7 mai zanci dake kwaila dake dan haka bari sai kin zama mace sannan zaki girgiza man kirji kina karkada kuhu da zai daukeman hankali haka,never never har abada baki da abunda zai dauke man a hankali."


Tureta yayi yana wulla mata key yayi tsaki yana cewa.."Shashashan Kwaila dake ai taimaka maki nayi da na aureki." durkushewa tayi a wajen tana kuka marar sauti dan bata son yaji sound din kukanta alkwarin da tayi ma kanta kenan.tun kafin ta shigo gidanshi tashi tayi tana goge hawayenta ta dauki towel dinta ta daura tana murmushi tace.


"Wallahi nan gaba sai kayi ma kwaila kuka Najeeb yanzun aka fara wasan kwaila dai ko? dan hakin da ka raina." Daukar key din tayi ta bude room din ta shiga ta kulle kofar ta ciki ta zauna saman stool ta zauna ta shafa cream ta samu halfgown ta sanya tayi addu'a ta tofe jikinta ta kwanta.


★★


Moha ya angonce da amaryarsa Zubaida cikin so da kaunar juna dan ba karamin soyayya ya nuna mata ba a daren,tasha kuka har ta gode Allah.


Dakyal Moha ya samu tayi shuru da kanshi ya had'a mata ruwan wanka dakyal ya samu ta shiga ruwa ta gasa jikinta sosai da sosai sannan tayi wankan tsarki shima bayan ya fito wanka ya sake jallabiya ya gyara gadon ya chanza ma gadon sabon bedsheet...sannan ya daukota suka kanta ya rufesu da blanket sai magana yake mata mai dadi da kwantar da hankali maganarshi ita take saka ta rage jin zafin da jikin yake mata.


Bata san sanda bacci yayi awon gaba da ita ba sai dai taji yana kissing din lips dinta yana shafa k'asan cikinta a hankali ta bude idonta tana saukewa a kanshi, murmushi ya sakar mata yana cewa..


"Darling time for pray."


Lumshe Ido kawai tayi tana murmushi shima murmushin ya sakar mata ya fita dan zuwa sallah sai da ta tabbatar da ya fita ta tashi ta shiga toilet sai da ta k'ara gasa jikinta sosai tayi wanka ta fito tayi sallah,zama tayi tana azkar bata tashi ba sai da gari ya dan fara haske sanann tana cikin linke hijab dinta ya shigo da sauri ya ida karasowa yana ansar hijab din ya linke ya dauketa cak ya direta saman gado yana lublubesu sai da suka gama soyayyarsu sanann bacci ya dauke su.


★★


Koda ya dawo daga massalaci sai da ya shiga kitchen ya hado black tea da yasa lemon a ciki sosai, fitowa yayi yana zama parlo ya kunna news ya fara surber tea din yana kallon tv a hankali kuma yana kallon room din da take ciki.


Sauke ajiyar zuciya yayi yana kure kofar room din da Ido yana jin kamar ya tashi yaje gareta dan jiya shi kadai yasan a yanda ya kwana a gidan,ganin da yayi mata daure da towel ba karamin goge mashi hadda tayi ba,dan ma ya samu yayi tsaye ya kama kanshi da ba karamin raini yarinyar zatayi mashi ba..daman yaga wata tashen balaga da rainin wayau take ji yana sane da ita.


Tsaki ya saki yana cewa.."zanyi maganinki sai na kurje bakin rashin kunyar nan naki zaki zo hannuna kuma da kanki zaki kawo man kanki never nafi karfin na kai kaina wajenki sai dai a dauwama a haka kuwa."(Uhmm nidai ba ruwana anayi muna shan coffee☕)


Haka ya kama balbalama kofa harara har ya gama shan tea din ya kashe kallon ya taitara ya koma room din shi..jallabiyar ya cire ya kwanta haka ya kama juyi har ya samu bacci yayi gaba dashi.


Ita ko Zulaihatu tana tashi tayi sallah bata koma bacci ba bayan ta gama azkar sai ta fara karatun alquri'ani dan daman ita ba gwana bace a wajen baccin safe ta saba da ta tashi ta gama sallah da azkar take fitowa ta fara aikin gida tana gamawa kuma tayi shirin zuwa school.


Tana gama karatu ta tashi ta shiga wanka ta wanke jikinta tas ta fito ta zauna ta shafa cream da lotion masu masifar dadin kamshi sai da ta mulke jikinta da turaruka masu kyau da dadin kamshi da kuma tsada..dan wani sanyaiyen sanyi kamshi take fitarwa har lumshe Ido take tsabar dadin da kamshin yake mata.


Wardrobe ta nufa ta fiddo wani laces marron ta saka ta murza daurin kyallabi dan ba abunda ta shafa ma fuskarta bayan kwali sai cheap da ta shafa sai shinning yake so masha Allah.


Takalmi ta dauko masu kyau flat ta zura ma kafarta ta gyara room dinta tayi ta sakar mashi kamshi sannan ta fito kallon dan karamin parlon sama tayi kujeru ne ash color cushen yan dukus-dukus masu masifar kyau aka jera a sama anyi masu circle sai tv da ke aiki ita d'aya sosai parlon yayi mata kyau sosai bata san sanda murmushi ya subuce mata ba.


A hankali ta ida isa wajen tvn tana kashewa taje ta hado ruwa ta zuba hypo dan kadan ta goge tv din tas sannan kuma ta gyara jeren wajen tv din moping din parlon tayi ta gyara ko Ina need ta jona bona sannan ta sauka k'asa.


Nan ma parlon kasa yayi mata kyau sosai da sosai kujeru biyu ne aka zuba ma parlon duk royal juya kujerun tayi tana gyara parlon ta gyara komai sosai ta baza mashi kamshi kitchen din k'asa ta leka nan taga komai yayi mata shiga tayi ta gyara wajen sannan ta dawo sama.


A hankali take taka upstairs din dan ta gaji sosai saboda aikin da tasha da yake bata saba irin aikin ba duba da girman da gidan yake da shi ba irin nasu gidan bane da cikin minti goma sha biyar ka gama komai har ka zauna.


Bata lura da mutun ba sai ji tayi tana karo da abu tsorata ta yi tana sakin Kara sai ta tafi luuuuu zata fadi,da sauri ya tarota gun ya ida mikar da ita shima ya tafi tangal tangal sai gashi ya zube k'asa tana hayewa kanshi.


Sakala hannu yayi yana rungumaita sosai yana sauke ajiyar zuciya gami da k'ara bude kofofin hancinshi yana shakar kamshinta mai sanyin dadi da kwantar da hankali da kuma saka natsuwa.


Itako Zulaihat har yanzun zuciyarta bata daina bugawa tara tara ba ga hawaye da suka fara wanke mata fuska dan wani irin tsoro ne ya kamata tama sa ta gama karyewa duk da taji laushin fata da kuma kamshi amman har a lokacin kwalwarta bata, bata akan mai take kwance ba dan haka Kara lafewa tayi jikinshi tana sauke ajiyar zuciya sunfi minti biyar a haka sannan ta fara d'ago kanta tana bude ido a hankali a hankali ta sauke a saman fuskar Dr Najeeb da ya kureta da ido.


Turo baki tayi tana kokarin sauka daga samanshi,sakin hannunta yayi yana murtuke fuska ya tureta daga jikinshi har tana bugewa a jikin karfen matakalar benen har sai da ta sakin har Kara a hankali tana cewa.


"Wash Allah! Turo baki tayi tana goge fuskata ta tashi tsaye a hankali tana kallonshi ta balla mashi harara tace.


"Allah ban yafe ba rungumata da akayi da kuma kalleni da akayi sai Allah ya bi man hakina."


Tasowa yayi yana yin kanta da gudu ta balla yana bin ta da sauri kafin ya cinmota ta fad'a daki tana kullewa gam da karfe ta murza key..tsaye yayi a bakin kofar dakin sai huci yake kwafa yayi yana buga kofar da karfi yana cewa.


"Zaki fito ai sai nayi ball dake kwaila kawai dake mai zan runguma a jikinki banda k'ashi sai wari kike kamar dadkwayen kwai."


Tsayawa tayi a bakin kofar tana cewa da karfi yanda zai ji ta.


"Wallahi bani ce ke wari ba sai dai kai,kuma ba komai naji ni kwailarce a haka aka nace aka ce sai kwailar dan naci kuma nan gani nan bari kwaila dai tafi karfinka dan matar manya ce jaruman maza ba irinka lusarai ba."


Zaro Ido tayi tana Kara murza key din jikin kofa sai karma take dan yanda yake buga kofar sai da taji fitsari yana shirin balle mata,kwafa yayi yana cewa..


"Ai da kin fito sai ki maimaita abunda kika fad'a yanzun."


Murguda baki tayi kamar yana ganinta tace.


"Eh din ank'i a fito din."


Tsaki kawai yayi yabar bakin kofar yana sauka k'asa daman abinci aka kawo masu ya sauko zai anso...yana zuwa suka gaisa da gate man yana mika mashi basket din yace.


"Gashi yallabai."


Ansa yayi yana cewa.


"Ina Wanda suka kawo abincin.?"


Nuna mashi part din Moha yayi yana cewa.


"Bangaren yallabai suka shiga sun dan jima basu dade da tafiya ba."


Ansa kawai yayi ya juya yana balla ma part din Moha harara dan ya tuna shakiyancin da yayi mashi yau da asuba bayan sun fito daga sallah.


Yana shiga ya ajiye abincin a saman dinning ya shigewarshi room din shi dan watsa ruwa.


*UKRAINE 🥀*


Shiryawa tayi cikin onion abaya yar dubai tasha stone ba karamin kyau rigar tayi ma Beauter ba zama tayi bisa stool tana kallon fuskarta idanunta sun kumbura tsabar kukan da tasha a jiya...duk da kumburar da idanun sukayi basu sakar ma fuskar muni ba sai ma fayau da fuskar ta Kara yi.


Shafa kwali tayi tana daukar veil din hijab din ta daura ta fesa turare ta sauko k'asa kitchen ta nufa nan ta tadda Ammie ita da Chief din gidan tana gaya masu abunda take so suyi a matsayin breakfast.


Da sallama ta shigo kitchen tana dan daura kanta a saman kafadar Ammie a hankali tace


"Good morning Momy."


Shafa kanta Ammie tayi tana murmushi tace.


"Morning too My Daughter hope kin tashi lafiya.?"


"Lafiya lau Alhamdullahi."


"Masha Allah,Allah yayi maki albarka ya kareki ya albarkaci rayuwarki Jiddah."


Kiss tayi ma hannun Ammie tana cewa.


"Amin Amin Momyna I love you."


Murmushi Ammie tayi tana kama hannunta suka dawo parlo zama sukayi tana kallonta a hankali cikin kwantar da murya Ammie ta fara cewa.


"Jidda."


D'ago kanta tayi tana kallon Ammie tace.


"Na'am Ammie."


Again murmushin Ammie tayi tana cewa.


"Baki jin kewar gida da ta yaranki a ranki?bakijin tausayin a wani hali mamarki take akan tafiyarki Jiddah.?"


Shuru tayi sai kuma tace.


"Duk inaji Ammie Ina tunaninsu a raina nasan tana can a cikin halin damuwa ba ita d'aya ba duka gidanmu ma da kuma kawata Wasi wanda har abada ba zan tab'a mantawa da halincin da tayi man ba."


Girgiza kai Ammie tayi tana cewa.


"Karda kiyi man kuka please share hawayen ki,kukanki yana sani na shiga damuwa ke a matsayin y'ata na daukeki dan haka damuwarki tawace haka tawa damuwar taki ce dan yanzun kece abokiyar shawarata."


Goge hawayen take da bayan hannu tana cewa.


"To Ammie na daina kukan."


Murmushi Ammie tayi tana cewa.


"Allah yayi maki albarka."


Cigaba da cewa Ammie tayi.."wata alfarma zan tambayeki."gyra zamanta tayi tana cewa."wace alfarma ce Ammie Allah ya bani ikon yi maki ita." Murmushi Ammie tayi tana cewa.."This week in shaa Allah zamu koma Nigeria duba da yanayin aikin da suka baro a office ga kuma campanyn Son na motoci yana son yaje yaga ya komai ke tafiya."


Marairaice fuska Beauter tayi tana cewa.."wayyo Allah Ammie yanzun tafiya zakuyi ku barni."


Shafa fuskarta Ammie tayi tana cewa.."idan kina so ba sai ki shirya mu tafi dake ba." Dan b'ata fuska kuma tayi bace komai ba murmushi Ammie tayi tana cewa.."ba zan matsa maki ba akan sai kin koma gidanku ba,amman ai zaki iya zama jigawa ko?amman idan kin daukemu a matsayin da muka daukeki."

Nan ma shuru tayi tana kallon Ammie sai kuma can tace..


"Amman Ammie ni idan har ina zaune a kasar zan dunga tunowa da abubuwa da yawa Ammie."..." Jidda maganar gaskiya baki kyauta ba kuma kin zabi soyayya akan farincikin iyayenki da yan uwanki,Jidda da qaddarar nan ta samaiki iyayenki da yan'uwanki sun dauki qaddara sun rungumaita hannu biyu biyu sun dauki son duniya sun daura ma yaran da kika haifa dan kawai wani wanda bai da Imani kuma bai san ba qaddara tun da yaki yarda da aurenki sai ki watsama iyayenki k'asa a Ido ki bar gida.?"


Cigaba da cewa Ammie tayi."Sam haka bai yi dai dai ba,nasan yanzun Haidar ya manta dake yana can yana rayuwarshi da matar da ya aura and daman can ba sonki yake ba,baa mai sonki tsakani ga Allah sai Auwal sai dai daman ba rabon ki zama matarshi kamar yanda shima Haidar din ke ba matarshi bace."


Hawayenta ta share tana cewa.."Ammie amman ai inason shi ya ki aurena saboda qaddara tahau kaina and Ammie karuwa fa yace man."


D'aga Kai Ammie tayi ta cigaba da cewa.."eh wanann duk bai kyauta ba saboda kishi ne ya rufe mashi Ido za'ace ko kuma daman can ba sonki yake ba tsakani ga Allah,Allah ne masani amman maganar guduwa kibar gida da kikayi baki kyauta ba kuma dole ne ki nemi gafarar mahaifanki dan karda ki mutu da hushinsu a saman kanki and nayi maki alkwarin sai na anso maki hakinki wallahi Ahmad bai keta hadinki a banza ba sai yayi nadama dole hukuma ta hukuntashi dai dai laifinshi."


"Zan kashe ko nawane ganin bayan Ahmad dan wallahi ba za'a barshi a bassila ba and daman barazana yayi maki akan su Meenat da kin fad'i wa yayi maki wanann cin mutuncin da tuni Babanki ya makashi kotu amman kikayi shuru nan ma baki kyauta ba Jidda."


Ita dai Beauter batace komai ba,amman duk jikinta yayi sanyi sosai tabbas tayi kuskure kuskure ma babba da tabar gida tabar iyayenta tabar twins dinta akan laifin mutun d'aya kuma shi yana can yana cin duniyarshi da tsinke da matar da ya aura dan ta tabbata ba zai iya zama babu aure ba har shekara biyar da faruwar lamarin.


Tabbas ta toshe tunaninta kuma tunda tabar gida bata tab'a zama tayi wannan tunanin ba bata tab'a zama ta duba rashin dacewar abunda tayi ba..hakan na nufin tabar point na cewa saurayi tabi kamar yanda Haidar ya fad'a a wajen family meeting,hakan na nuna za'a kama gulma a gari ta shiga yawon duniya ta zama karuwa kalmar da ta tsana a dangantata da ita karuwa kenan.


Kamo hannun Ammie tayi tana cewa.."Ammie zan biku zan biku inason naje gida naga a wani hali Mama take Ina bukatar hakan Ammie."


Murmushi Ammie tayi tana cewa.."Alhamdullahi Jiddah Allah yayi maki albarka dan haka ki fara shiri soon zamu tafi bai wuce Sunday din nan."


Kwantawa tayi tana cewa.."Allah ya kaimu." Bayan angama hada masu breakfast tare suka zauna sukayi nan Ammie ta gaya masu tare da Beauter zasu koma nigeria, sosai hakan yayi ma AK dadi daman yana tunanin yanda zai iya tsaleketa ya barta anan kasar yanajin ba zai iya ba.



*AMATULLAH DATA SERVICES*


*MTN*, *AIRTEL*, *GLO*

500MB-140

1GB-270

2GB-540

3GB-810

4GB-1080

5GB-1350

6GB-1620

7GB-1890

8GB-2160

9GB-2430

10GB-2700


9MOBILE

500MB-150

1GB-300

2GB-600

3GB-900

4GB-1200

5GB-1500

6GB-1800

7GB-2100

8GB-2400

9GB-2700

10GB-3000


VIA✓8160508316

Jamila Bello Abubakar

Opay bank

VIA✓0777512438

Jamila Abubakar Bello

Access bank


*** for call or whatsapp