WAZEER!

Interpolated

by @realsmasher

*From the writer of:*

-ƘADDARA KO SAKACI?

-RAYUWAR WANI

-ƳAR GARUWA

-BAMBANCIN AL'ADU

-INA MAFITA

-ZAƁIN WA ZAN BI?

-WANI AL'AMARIN

-ALƘAWARIN JINI

-ƊAN MACE

- IFZAA

-MAKTOUB 

-MANAR 

-IN-LAWS 

-KALLO YA KOMA SAMA 

-CIWO A JIKIN WANI 

-DAUƊAR GORA 1,2 & 3

   *AND NOW*

 -WAZEER  


              07

 


#Interpolated



     Yammaci ne me daɗi dake bada wani irin sanyayyan yanayi,ko da yake duk inda unguwar masu kuɗi yake akwai yawaitar shuke²,wanda duk safiya da kuma yammaci za ka samu yanayin gurin yai daɗi,ni'imtacciyar iska na kaɗawa sosai. Mugun gudun da motar wacce ta fito babban get ɗin gidan,shi ne yasa matasan samarin da suke jugging cikin line sanye da train suite juyawa suka bita da kallo,a hankali ɗaya ya ɗan yi murmushi yace "Hjy *MUNIBA* kenan,ko ina take shirin zuwa,da yasa take irin gudun nan haka?" Ba tare da damuwa ba ɗayan ya ɗan taɓe baki kafin ya juya yaci gaba da abunda ke gabansa,ta mirror ɗin motar kyakkyawar budurwar ta ɗaga kyawawan roundish almond eyes ɗinta masu jan hankali da haske ta bisu da kallo,daga yanda suka tsaya ta fahimci maganarta suke,a hankali tai ɗan murmushi kafin ta ci gaba da driven ɗinta kamar mai shirin tashi sama,fara ce tas duk da a zaune take bazai wuyar gane doguwa ce ba,kamilalliyar fuskarta ma'abociyar fara'a na ɗauke da dogon hanci da ɗan thin round lips,a tsarin zubin halittar jiki kuwa,Allah bai yita irin masu girman jiki nan ba,da kyakkyawan kallo ɗaya ya wadatar da me kallonta cewar,duk inda ta fito ba ta rasa nasaba da jinin asalin Fulani gaba da baya. Duk inda kake neman kyakkyawa,ka sameta tabbas ta kai koma ace ta zarta,domin irin matan nan ne da ake kira da full option,idan nace full option ina nufin ta ɓangaren kyau/kyawawan halaye,uwa uba kuma cikakkiyar tarbiyya,nasaba da ilimin addini. Muniba kenan kamar yanda samarin suka kirata da shi,asalin mahaifanta dukansu uwa da uba,haifaffun cikin tsakiyar birni ne a nan garin Kano,ƴar gata ce a gurin iyayenta ta gaban kwatance. Sunan mahaifinta Dr Abbas Bashir Mijinyawa,haifaffen ƙaramar hukumar Dala ne cikin unguwar Ƙoƙi,asalin gidansu matan babansu Malam Basiru biyu,Inna Rahila itace uwar gida,aurensu tun na sakun lalle ne,yaran Inna Rahila a gidan 4,3 daga ciki dukansu maza ne,ɗaya ce kawai mace me suna Talatu kuma ta girmewa Abbas da shekaru 7,tun daga kanta Inna Rahila bata sake haihuwa ba,daga baya²n haihuwarta sannan Malam Basiru ya ƙara aure,ya auri mahaifiyarsu me suna Maryam,suna kiranta Gwaggo Mairamu,mahaifiyarsu ta kasance kyakkyawar bafulatanar daji,babu jimawa da shigarta gidan ta haifesu su tak,Abbas shi ne babba,sai ƙaninsa dake bi masa Sulaiman,a gurin haihuwarsa Allah yaiwa Gwaggo Mairamu rasuwa ba tare da ta san abunda ta haifa ba,duk wanda ya san kyaun halitta da halin Gwaggo Mairamu,ya kalli Abbas da Sulaiman zai tabbatar ƴaƴanta ne,domin babu abunda basu ɗauko ba na daga kyaunta da sanyin halinta,har ta rasu bata taɓa tankawa Inna Rahila ba,duk masifar da za tazo tayi mata kuwa,kou da kanta za tazo tana sababi,hakan bazai sa ta taɓa ɗaga kai ta kalleta ba,da yawan lokacima sai dai ta bata haƙuri,daga haka za ta bar gurin tana faɗin "Allah ya huci zuciyarki Yaya,duniyar nanfa ba matabbata bace,idan yau mune gobe bamu bane.." Bayan mutuwar Gwaggo Mairamu,danginta sun so karɓar yaranta,amma sai Malam Basiru ya nuna zai riƙe ƴaƴansa,a cewarsa ya fiso yaransa su tashi a gabansa duka,idan akace an rabasu suna wani guri daban da inda ƴan uwansu suke zumuncinsu zai lalace,haka dangi suka haƙura suka barsu hannun mahaifinsu,shekaru 10 tsakani da rasuwar Gwaggo Mairamu,Allah ya karɓi ran Malam Basiru,kafin rasuwarsa haka ya bar wasiyya akan Inna Rahila ta haɗa yaran da nata dana Mairamu ta riƙe,ta kula masa da marayun ƴaƴansa kamar yanda za ta kula da nata,tai na'am tana kuka,tunda Malam Basiru ya kwanta dama,yanayin rayuwa kasancewar yaranta duka babu wanda yai karatun boko sai kasuwanci,ganin Allah ya ɗaga mata nata ƴaƴan yasa ta zubar da Abbas da ƙaninsa Sulaiman,a hankali zamansu a gidan ya sauya,a da ganin idonsa yakansa Inna Rahila nuna musu so,amma tunda ya bar duniya kullum suna cikin wahala da azabtarwa,da daɗi da babu haka suka rayu,wahalhalun yau daban dana gobe,wannan dalilin yasa Abbas dagewa yai karatu,bisa tallafawar dangin mahaifiyarsu,cikin hukuncin Allah haka shi da ƙaninsa suka fita zakka a gidan,har zuwa lokacin da ya fara aiki a matsayin likita,cikin ƙanƙanin lokaci da kama aikinsa Allah ya ɗaukakashi,kafin kace me sunansa ya kai inda bai taɓa zato ba,a yanzu haka da fara aikinsa ya samu shekaru sama da 30,kuma ba'a dena damawa da shi ba,ƙwararren likita ne da ake ji da shi a garin Kano,sannan shi ne amintaccen likitan gidan gwamnatin jihar,tare da duk wani babban me ji da kansa,yanzu haka kuma shi ne Kwamishinan lafiya (commissioner for health) na garin Kano. Dr. Mijinyawa shi ne sunan da kowa ya sanshi da shi yara da manya tun kafin ai masa muƙami a gwamnati ya zama commissioner,idan sanin makamar aiki ne,sunanshi a kaf cikin Kano zai fara zuwa a lambar farko,ya yi aiki a asibitoci da dama,kamar asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH),Muhammad Abdullahi Wase (Nassarawa hospital),da kuma asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad Specialist Hospital (MMSH). Matarshi ɗaya tak tun auren saurayi da budurwa me suna Aminatu,haifaffiyar ƙaramar hukumar tsakiyar birni ce (Municipal),an haifeta a nan unguwar Kankarofi,su 5 ne a gurin iyayensu,Yaa Taheer shi ne babba,sai Muhammad Taqiuddeen,Hashim,sannan ita,sai autarsu Wahidah,iyayensu ba wasu masu kuɗi bane,amma sun taso cikin gata da tarbiyya,mahaifinsu Malam Imraana mutum ne dake son ganin yaransa sun yi karatun zamani,shi yasa mazansu da matansu duka ya tsaya tsayin daka wajen inganta rayuwarsu,ta yi karatun firamare (primary) a Gidan Makama Special Primary School,daga nan ta tafi makarantar gaba da firamare (secondary) a makarantar kwana ta ƴan mata wato Shekara,sannan tayi karatun jami'a a makarantar Ahmadu Bello dake Zaria (ABU),bayan kammala digiri (degree) ɗinta na farko a ɓangaren abunda ya shafi tattalin arzikin ƙasa (Economics),tana matakin digiri ɗinta na biyu Allah ya haɗata da Dr Abbas Mijinyawa wanda ya kaisu ga yin aure,tana ɗakinta tai Masters,inda ta karanci International Economics a jami'ar Bayero,bayan nan ta kama aiki a matsayin Malamar makaranta a jami'ar,a lokaci ɗaya kuma tana karatun Doctoral degree ɗinta,har zuwa matakin da take a yanzu na Dean,duka a jami'ar ta Bayero dake Kano. Suna da yaransu biyu tak,Imraan wanda yaci sunan mahaifinta shi ne babba,suna kiranshi Khalifa,sai Muniba data ci sunan mahaifiyar Dr Abbas Maryam itace auta. Dr Sulaiman Mijinyawa,ma'ana ƙani a gurin Dr Abbas Mijinyawa,shima Likita ne kamar yayansa,ya yi aiki a asibitin Nassarawa,a yanzu haka shi ke kula da babban hospital ɗinsu da suka buɗe da wasu harkokin kasuwancinsu,kusan duk wasu harkokin yayansa shi ne akai,shi yake wakiltarsa akan duk wasu harkoki da suka shafi dukiya,a yanzu haka suna da yara samari da suke tallafa musu,yana da mata ɗaya kamar yayansa,tsayin lokaci ya so sake yin aure Allah bai nufa,yaranshi 3,babban ɗansa namiji Bashir wanda suje kira Mubasshir,sai Khalidah dake bi masa,sannan auta Maryam da suke kira Baniynah,alhmdllh basu da yawa,sai ƴan uba da suke da su,wanda basu damu da sanin yaya suke ba,sai tarin hassada akan ɗaukakar da Allah yai musu,suna zaune cikin farin ciki da rufin asirin Ubangiji,tare da zumunci mai ƙarfin gaske,duk inda Dr Abbas Mijinyawa zaisa ƙafarsa,idan ka duba kusa da shi ƙaninsa ne Dr Sulaiman Mijinyawa,shi ne PA ɗinsa,shi ne best friend nasa,shi ne special advisor ɗinsa,a duniya ƙaninsa shi ne komai nasa. (Wannan kenan).. 



***


   Zaune kyawawan ƴan matan biyu suke a balcony kowacce da waya a hannunta suna operating,lokaci² suke ɗan magana da junansu ba tare da sun ajiye wayoyin ba,daga dukkan alamun yanda suke zaune zai tabbatar maka akwai wanda suke jira. Around 5 o'clock ɗaya daga ciki ta kalli wayar hannunta ƙiran Galaxy S3 tana sakin siririn tsaki,manyan idanunta ɗayar mai ɗan dark skin ta ɗago ta kalleta tana sakin murmushi,a hankali tana sauke ajiyar zuciya tace "sorry friend.." Kafin tayi adding wani magana,ɗayar da suke zaune ta fara magana kamar a fusace "haba dan Allah *BANIYNAH*,for about 1 hour and half fa muke ta zaune muna jiranta,har yanzun kuma bata ƙaraso ba,if ta fasa zuwa ne sai ta sanar mana mu watse,tafiya da ita sai kace dole? Ko daga birnin sin ta taho ai sai haka.." Murmushi wanda aka kira Baniynah ta sake yi tana lumshe idanuwanta tace "i said sorry.. Ke da kanki kin san Sis *MUNIBA* ba mai nauyin shiri bace,sai dai ko idan akwai uzurin da ya riƙeta,haka kawai she won't keep us waiting.." Tsaki wanda tai maganar faro tayi,a hankali ta ajiye wayar hannunta kusa da ɗan ƙaramin hand bag ɗinta da baifi ya ɗaukar mata phone da wasu ƙananun abubuwa ba tana girgiza ƙafa. Bayan ɗan lokaci suna zaune sun yi shiru kowa da abunda take saƙawa a rai,a fusace ta miƙe tana ɗaukan bag ɗinta da phone tace "Baniynah! Ni kam zan tafi,bazan iya zama ina jiran wata ba kuma.. Idan kun gama kwa sameni a gidanmu" gyaɗa kai Baniyna tayi tace "but *SAFWA* dama fa babu wanda ya maki dole,asalima ke kika fi kowa son ayi fitar nan,sannan yanzu ki kama faɗan magana kuma.." Sakin baki Safwa dake kallon Baniynah tayi cikin ɓacin rai da haniya tace "ohoo! Ai sai yanzu na gane nufinku,dama ba kwa so na biku ne,shisa kuka ƙulla munafurcin tayi zamanta kenan,duk sanda na gaji na tafi gida sai ku zame ku tafi?" Sakin baki Baniynah tayi jin irin maganar da Safwa keyi,da sauri tace "dan Allah Malama kada ki juya min magana,ke dai kin cika son jan magana ne ma,amma kou ke kin san Muniba ba mai son ɓata lokaci bace,musamman idan ta san ana jiranta" tsaki Safwa tayi ta fizgi jakarata,Baniynah ta buɗe baki za tayi magana,kafin ta furta abunda ke bakinta Safwa dake tsaye ta ɗaga mata hannu tace "kada ma ki fara please mu barshi haka nan,dan idan maganar yayi tsayi bazai mana kyau ba" taɓe baki Baniynah tayi tace "alright" daga haka ta kai hannu ta sake ɗaukar phone ɗinta,phone book ta shiga da sauri,,number da tayi saving da "Sweet Sis" ta fara kira,ring biyu aka ɗauka,da sauri tasa wayar a speaker,Safwa da har ta fara sauka steps ɗin gurin,ta taɓe baki tana ci gaba da tafiyarta,a hankali Baniynah tabi bayanta da kallo while saying "hello!" Cikin sanyayyar murya mai cike da ruɗewa wanda ta ɗauka tace "i'm so sorry da ɓata maku lokacin da nayi Sisters" Baniynah dake ɗan dariya tana girgiza kai tace "where are u now Muniba?" Muniba dake a ɗan ruɗe tace "on my way soon Babe,wallahi Uncle Hisham ya tsayar da ni zan fito,amma ga ni ina shigowa line ɗinku ma" Baniynah dake hangen Safwa dake tafiya ta nufi get tace "kin fito da mota ne?" Muniba tace "yeah! Saboda banso naita ɓata maku lokaci ba" Baniynah tana ɗan dariya tace "alright.. Kiyi parking a waje bari mu fito kawai sai mu wuce" Muniba tace "okay Babe.." Dai² lokacin ta danna horn tare da parking dai² babban get ɗin gidan,dake tsakiyar manya²n gidaje wannan yana wane wannan,kana kallo za ka san mazauna gurin sun ci sun tada wuya,Baniynah tayi dariya tace "yeah! Na ji ki,i'm coming" Muniba tayi ɗan murmushi mai sauti tace "ahann! Sai kun fito" suka ajiye wayar a tare. Safwa na buɗe ƙaramar ƙofar get ta fito,Muniba dake cikin mota tana buɗe idanunta ta sakar mata murmushi,sororo Safwa ta tsaya kallonta cike da mamaki,har Baniynah ta ƙaraso gurin,tana sakin murmushi itama ta taɓa shoulder Safwa tare da faɗin "let's go Babe" ta wuce ta nufi motar,front seat ta buɗe ta shiga ta rufe ƙofar,kafin tayi magana Muniba ta rigata tana cewa "hello!" Baniynah tace "Hey! Sweetheart how are u? How is ur day?" Muniba dake murmushi mai kama da dariya tace "fine Babe" Baniynah tace "ya Mami da Yaa Khalifa?" Ɗan taɓe baki Muniba ta fara kafin ta dame face ɗinta,kamar ba ta son magana tace "Mami tana lafiya" kallonta Baniynah tayi tana ɗaga eyebrows ɗinta tace "and Yaa Khalifa?" Ɗauke kai tayi bata ce komai ba,sai can tace "i don't know wether he's fine or not" tayi maganar kamar an mata dole,dariya Baniynah tayi tana kallonta tace "so u mean baki sani ba wai kike nufi?" Muniba tace "yeah that's exactly what i meant" shiru Baniynah dake jin presence ɗin Safwa a back seat tayi da maganar,sai ta canja zancen da cewa "oh! Where are we going now?" Muniba bata kulata ba ta cema Safwa "i'm sorry Babe na ɓata maku lokaci,Uncle ya tsareni da zan fito" ɗan dariya Safwa tayi kamar wani abu bai faru ba tace "oh! U shouldn't worry about it,yanzu ba ga shi kin zo ba" Muniba ta tada motar tana tuƙi da reverse ta sauke ajiyar zuciya tace "thanks" then tana ɗan kallon Baniynah dake danna wayarta tace "think za mu fara zuwa gurin this tailor mara alƙawari muji inda maganar mu ya kwana da shi,super market kuma sai musa another time daya dace,yanzu yamma yayi and nace da Mami baza muyi dare ba" a hankali Baniynah ta gyaɗa kai tace "okay! Allah yasa mu samesa tou" tace "ameen" while driving fast,daga cikin Nassarawa GRA kai tsaye Zoo road Muniba ta nufa,dai² gaban wani babban plaza me shaguna da yawa tai parking gurin da aka tanada domin ajiye motoci,sannan suka sauko suna tafiya zuwa ciki.



*WAZEER*


    Haka nan yau tunda ya tashi yake kallon kanshi a mirror,yanda gashinsa yai bala'in yawa gemunshi ya cika,ga nails ɗinsa da suka fito sun yi zaƙo²,shi ba wani halitta na daji ba amma farce kamar yana shirin yin farauta,shi kansa kallon kansa yake kamar wani mashahurin mahaukacin da yai shekara bai samu kula ba,guraren 5pm ya fito cikin shirinsa na fita,ƙananan kaya ne jikinsa da suka amsheshi,sanda ya fara shiga gurin Daada ya sanar mata ya fita aski,sannan ya bar gidan ya nufi zoo road inda ya taɓa raka Iyaad,sanda suke ɗan fita akai² da shi,yana yin parking ya sauko motar ya wuce cikin gurin,har ya shiga yaga gurin cike da mutane sosai,a hankali ya juya ya fita ba tare da yayi magana ba,a rayuwarsa ba ya son cikowa da hayaniya a gurin da yake,yanzu zasu sa masa ciwon kai,wani yaro ne ya biyoshi yana tambayarshi "Oga what do u want?" A hankali yace "zan jira mutane suyi sauƙi" yaron yace "ok! Ga guri ka zauna tou" ya kawo masa kujera ya ajiye masa a inuwa,zama yayi yana kallon mutane dake shige da fice gurin,har sanda wani mota ƙirar Camry gray color yai parking,ƴan matan 3 suka sauko. Tun daga nesa yake kallon tahowarsu,wani irin ƙasa yayi da idanunsa har sanda suka kusan ƙarasowa inda yake zaune cikin plaza yana jira a sallami wanda suke cikin gurin,ba don aski yake son yi da ƴan sauran su gyaran farce da wankin ƙafa ba,da tuni ya ɓace a gurin,each and every month yake zuwa ayi masa gyaran musamman a California,haka Dad ɗinsa ya sabar masa,yana ta zaune yana jira da kallon agogon dake ɗaure wrist ɗinsa,wata gray color ɗin mota ƙirar Camry tai parking kusa da inda ya ajiye nasa,sai ga ƴan mata sun fito motar,ya yi mamakin ganin har me tuƙin dukansu mata ne. 



*MUNIBA*


 Su 3 ne sanye da arabian gowns,kalar ta kowa daban,ka kallesu ka san duk inda cikakkun ƴan mata masu ji da aji gami da kyau duk sun kai,dukansu kuma farare ne tas,sai dai Safwa haskenta mai irin fauu ɗin nan ne,amma bata kai ka kirata Albino ba,while Baniynah kuma kalarta yai ɗan duhu,but baza'a kirata baƙa ba,sai Muniba da za tazo a tsakiyarsu,binsu Wazeer ya ɗan yi da kallo,sanda za su shiga cikin flaza dake ɗauke da aƙalla 100+ shagunan da ake haya,Muniba da yake ganin dukansu ta fisu kyau,tun daga nesa ya gama karancesu,a hankali ta furta "assalamu alaikum.." Da sanyayyan muryarta me ratsa jini da ɓargo,shi kansa sanda ya ɗago ido ya bita da wani irin full kallo kafin ya amsa can ƙasa da "wa'alaikis salaam" kyakkyawan bayanta yabi da kallo dake ɗauke da wasu irin bottocks mulmulallu da suke juya kansu ta cikin tsadadden Egyptian abayan dake jikinta me kalar ruwan ƙasa,duk lafiyayyen namiji ya kalleta a wannan yanayin zai wahala bai ji ya faɗa komarta ba,saurin janye idanunsa yayi underneath his breath ya furta "a'uzhubillahi minash'shaiɗanir rajiim.." Tunda ya sauke kansa bai kuma marmarin ɗagowa ba saboda yanda gabansa yake faɗuwa,har sun ɗan yi nisa da inda yake yaji fara tas ɗin cikinsu me kama da zabiya tana faɗin *"MUNIBA!* Ki kirasa kiji ina ne gurin nasu,kada muyi ta hawa da sauka a gurin nan" ɗan ja suka yi suka tsaya nesa da shi kaɗan,wacce yaji an kira da Muniba tana kallonsu da sanyayyan yanayinta,cikin wani irin melodious muryarta tace "ha'a! Tou wai sau nawa kuke so na kirasa ne?" Wani irin kunne ne da shi mai ɗan banzan jin magana kamar maciji,ko yaya akayi magana yanzun nan iska zai fizgosa ya kawo masa,daga inda yake zaune ya shaida muryar wanda tai masa sallama ce,ɗago kansa yayi ya bisu da kallo yana maimaita sunan a ransa *"MUNIBA!"* Still ɗaya daga cikin ƴan matan,dan bai sansu ba dukansu,tace "ki sake trying please Sweet Sis.. Muna mata bai ci mu tsaya titi ba,kin san Yaa Khalifa ko Yaa Mubasshir suka sani yau mun banu da faɗansu" gyaɗa kai tayi a hankali tace "ok let me try again.. Amma fa tun ɗazu wayan yaƙi tafiya" a ɗan zafafe ɗayar budurwar dake masa kama da zabiya (albino) ta furta "c'mon Baniynah ki kirasa kiji,kinsan idan za mu biye ta Muniba za mu iya kwana gurin nan" ɗan dariya kawai Baniynah tayi tace "ok!" Ta fito da wayarta daga jaka wani Galaxy Z flip 2 da tayi folding ɗinsa ya koma half,ɗagasa tayi ta shiga ta lalubo number,few minutes ta kai wayar kunnenta,ring ɗin da wayar keyi yasa ta zaro ido while tana amsa maganar da aka mata ta cikin wayar da "ohh yes.. Hello!" Sanda take kallon su,jin tambayan da suke mata yasa ta gyaɗa masu kai tana cewa "Damfo please gamu plaza ɗinku,kou za ka fito ka tafi damu bamu san gurin ba?" A hankali ta sake cewa "alright! Don't keep us waiting please,gamu a titi muna tsaye.. Ok sai ka iso" tana katse kiran tace "ga shi nan fitowa yace.." Safwa ta wani yi murmushi a hankali tace "Muniba u better recharge up ur phone,i think u don't have enough airtime" sororo Muniba da Baniynah sukai suna binta da kallo,Baniynah ta girgiza kai alamun maganar bai mata ba tace "stop please! Don't start *SAFWA..* Ke kanki kin san idan maganan credit card za'ayi a waya,tsakanin mu 3 ko ni ban isa nace na fi Muniba ba bare kuma ke,in fact wani lokaci ita ke tura mana airtime daga ni har ke" shiru Safwa da duk ciki kana kallonta za ka san ta fisu rawar kai tayi tana wani ɗaure face tace "tofa ai an taɓa Muniba dole kiyi magana" Muniba kam murmushi tayi,ba tare da ta ce komai ba taja jikinta ta koma kusa da wani shagon da ake saida kayan electronics,a hankali ta zauna saman ɗan steps da gaba ɗaya shagunan da suka yi layi suke da shi,haka nan Allah yayi ta bata cika son hayaniya ba,ga ta da wani irin kamewa,musamman idan ta fahimci akwai wanda ke adawa da ita a guri,nan za kaga ta koma wata very quiet,baza ka taɓa jin maganarta ba sai ka yi mugun dace,ko kaɗan bata da yawan magana a waje,idan kaga tana hira bai wuce tsakaninta da iyayenta,Yayanta sai cousins ɗinta wato Yaa Mubasshir,Yaa Khalidah da Baniynah,ɗan siririn tsaki Baniynah tayi,a hankali ta dawo kusa da ita,ita kam sai sakin murmushi take kamar babu abunda ya faru,Baniynah data zauna next to her tai ƙasa da murya tana faɗin "don't mind her Sweetheart,i know she have alot of matsala wallahi" still murmushi ta kuma yi bata ce komai ba,suna zaune har kusan minti biyar sannan wani matashi da kansa ke da irin hair cut ɗin nan na zamani ya ƙaraso yana kallonsu fuskarsa da fara'a yace "assalamu alaikum.." Muniba da Baniynah da suke zaune next to each other suka amsa masa,followed by maganar Baniynah tace "Damfo?" Gyaɗa mata kai yayi yana murmushi yace "yeah!" Murmushi tayi tace "wallahi mun sha wahala kafin mu sameka,Sis Muniba tana ta kiranka wayan bai shiga" kafin Baniynah ta kai aya yace "wallahi arean da muke ne babu network sosai sai lokaci² ake samun line idan mun fito" Baniynah tace "Allah sarki amma naga kamar MTN kou?" Yace "ehh wallahi amma na siyi Airtel so ba kowa ya sanni da shi ba,sai a hankali nake bawa mutane" Baniynah tace "eyyahh! Babu matsala muma sai ka bamu saboda gaba" yace "ba ki da matsala hajajju" Safwa dake gefe tana jin maganarsu tace "tou yanzu shagon naku za muje?" Yace "ehh baki da matsala Hjy can za muje" tace "okay!" Damfo yace "za mu iya tafiya?" Baniynah tace "why not? But kayan da muka kawo suna booth,ko za'a samu masu ɗauka?" Yace "ehh muje za'a samu yaron da zai ɗauka.." Ta gabansa suka dawo tare da Damfo zuwa inda suka ajiye motarsu,shi ya ɗauko kayan da suka zo da shi,sannan suka sake wucewa zuwa cikin plazan.



*WAZEER*


     Sunan *SAFWA* da yaji an ambata yasa shi tunanin inda yasan sunan,a fili ya maimaita faɗin *"SAFWA!"* Within seconds ƙwaƙwalwarshi ta tuno yarinyar da sukai magana jiya,daga jiya da suka fara haɗuwa sanadin social media zuwa yau,ta yi masa good night massage,tai masa morning,kuma ya gani har yai mata godiya,sai dai bai tabbatar itace kou wata me irin sunanta ba,wayarshi dake hannunshi ya kalla yana tunanin tafiya,dan ya mugun gaji da zama gurin,duk a tsarge yake da kansa,duk da fuskarsa a rufe yake da maso,amma gani yake kamar kowa yazo wucewa kallonsa yake,dai² lokacin yana tunanin tafiya yaron berber ɗin ɗazu ya fito yana faɗin "Oga! Bismillah" tashi Wazeer yayi idanunsa a ƙasa² kuma akansu dai² suna komawa ciki suma yabi yaron zuwa cikin gurinsu,tas ya zauna akai masa aski da duk abunda yake so,sanda ya kalli kanshi ta cikin mirror har wani ajiyar zuciya yayi ganin ya dawo kamanninsa na asali,akai masa bill ya biya sannan ya fita fuskarshi maƙale cikin mask,inda yai parking motarshi ya ƙarasa ya buɗe ya shiga yana kallon motar dake kusa da nashi yaja ya bar area. Yana isa gida yai parking ya sauka ya wuce part ɗinsu ya buɗe ya shiga,a parlour bayan ya ajiye wayarshi da car keys ya wuce bedroom yai wanka,sanda ya fito har wani special iska yake ji yana ratsashi me cike da rahama,ya kwanta saman lafiyayyen 3 seater royal chair yana ɗan lumshe idanunsa a gajiye,a hankali kuma sai ya juya ya kallo wayarshi kafin yasa hannu ya ɗauka,buɗewa yayi ya shiga whatsapp,number Safwa da bai saving ba ya buɗe yai mata sallama,dake tana kan whatsapp lokacin kafin ya fita ta amsa masa,a hankali yace "kamar na so ganinki somewhere" dariya tayi kafin tace "a ina ka ganni?" Yace "zoo road kunzo wani plaza,i guess ku 3 ne" gwalo masa ido tayi surprisingly tace "and how do u know it's me?" Yace "ni dai na ganki" kiranshi ta fara yi video bai ɗauka ba har kiran ya katse,kafin ya kirata voice call,tana ɗauka tace "why don't u pick my call?" Yace "i don't want u to see my ugly face.. And gurin da nake ina ɗakin bawa dawakai ruwa ne" dariya ta fashe da shi na ƙeta kafin tace "and mene ne haɗinka da dawakai? Are u from royal family? Or do u have relationship da gidan sarauta?" Saurin girgiza kanshi yayi yace "not at all,muna dai aiki gidan da suke da alaƙa da sarauta" tace "ohh! Kuma na yarda da kai?" Yace "why not?" Tace "amma baka yi kala da bayi ba" yace "kin sanni ne dama?" Safwa tace "not at all.. Maganarka dai bai yi kama da na bayi ba" yace "yaya ake gane bayi?" Tace "suna da damar yin karatu ne dama?" Ta dawo masa da tambaya ba tare data amsa nasa ba,yace "of course yes.. Baki san yanzu an ƴantamu ba? Ai muna yin karatu sosai" tace "kou?" Yace "uhumn!" Ta gyaɗa kanta a hankali tace "ohh! I see.. And how do u know it's me wacce ka gani? Baka tunanin kou sunanmu ne iri ɗaya?" A taƙaice yace "ok!" Ɗan dariya tayi tace "ya akai ni ban ganka ba tou?" Yace "i just left the place.." Tace "ohh! Ai da ka tsaya mun gaisa,dama bamu taɓa haɗuwa ba,we don't know each other.." Yace "next time dear.. Ai na ga bake kaɗai bace,kada suyi tunanin biyoku nayi zan ɓata muku lokaci,ni kuma gani ba kowa ba" Safwa tace "don't mind them.. They are my friends,munzo bada ɗinki ne" Wazeer da idanunsa suke lumshe wayar ajiye gefe,a gajiye yace "ohh! Hope kun gama yanzu?" Tace "nope! Mun tsaya ya gama amsan measurement" ɗan shiru yai kamar bazai sake cewa komai ba sai kuma yace "measurement na me?" Safwa na ɗan murmushi tace "muna da biki in the next couple of weeks" yace "ohh! Allah ya sanya alkhairi" Safwa tace "ameen.. But baka tambayi bikin waye ba" yace "ok! Na waye?" Tace "bikina" buɗe lumsassun idanunsa yayi da kyau yace "really?" Dariya ta fashe da shi tana girgiza kanta tace "just kidding.. Na elder sis ɗinsu Muniba ne" ganin za ta jashi da magana,shi kuma har ya gaji kanshi ya fara ciwo slightly yasa shi cewa "ohk! Later!?" A hankali ta gyaɗa kanta tace "ok! Zamu wuce gida yanzu" yace "alright!" Suna yin sallama ya katse wayar yana juya sunan Muniba a ransa... 




     #Afwaan editing yau ya cakar dani,via with this guy's.. Surutun da WAZEER yayi ya bani mamaki gaskiya..




*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*


  _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_

  _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


*Infection*

  _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_


  _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._

*****

*****






#Follow

#Comment 

#Vote

#Share fisabilillah!

#ASLI-SMASHER.