Guilt_ridden
by @realsmasher
*SAFWA* Tana haurawa sama ta cire wayarta daga jakar,sai data fara ajiyewa jikin bag rack,ta ƙarasa gaban wardrobe ta buɗe,tana tsaye ta ninke mayafinta ta ajiye sannan ta mayar da ƙofar ta rufe,juyawa tayi ta bar gurin,a hankali ta kwanta saman madaidaicin gadonta kafin ta janyo wayarta,ko da tayi online bata ga ALEY ba,kamar yanda tai saving number ɗinsa,kawai sai ta fita ta tafi duba groups data san ana posting novels,har wani farin ciki ta dunga ji da taga anyi posting novels,nan ta shiga karatu abunta,tana yi tana sakin murmushi,underneath tana furta "Allah ameen.. Allah kasa muna da rabon shiga arziki da jin daɗi marasa yankewa" idan taji ana maganar wealthy people,har wani ɗaukan kanta take tana sawa a position ɗinsu,abun na mata daɗi fiye da tunani,musamman idan ta hango friends ɗinta Muniba da Baniynah,wani zubin ana maganar yaran masu kuɗi da suke da gata,sai tace "kai kamar su Muniba kenan" ita kaɗai taita haukarta,tana ji akai kiran maghreeb,har aka shiga masjid aka fito bata iya motsawa daga inda take ba,tana ta bautar waya da karatun da iyakarsa duniya,ta manta da lahirarta da duk hanyar da za tabi wajen samun aljannarta,ba ita ta tashi ba sai da wani masallaci a can nesa suka fara kiran ishaa,sannan ta ajiye tana faɗin "kai! Ashe fa banyi maghreeba ba,gashi har an fara kiran ishaa kuma.." Idan da sabo barin sallah ya wuceta ba yau aka fara ba,sam bata damuwa da yin sallah akan lokaci,tou Umma ba wani damuwa tayi da sasu suyi ba tunma suna yara,kou azumi Safwa bata yinsa sai ta ga dama,kuma Umma bata taɓa ce mata danme ba,har sai da ya wajaba akanta sannan take yi,da zaran ance yau ana azumin Ramadan to fa baza ta moru ba,komai Umma ce za tayi na buɗe baki a gidan,girki da duk wani aikin gida na ɗiya mace,Safwa bata sanshi ba,duk budurwar da taga tana aiki a gidansu,kallon wahalalliya take mata,abu ɗaya zuwa biyu da tafi iyawa a rayuwarta,shi ne tai wanka ta saka kaya ta fice gidansu Baniynah ɗaukan hoto da za'ayi updating ma samari,sai kuma taci ta kwanta Umma ta ɗaure mata,yanzu ne da gumu tai gumu,sannan ta fara mata faɗan ta dunga yin aiki kada taje gidan miji bata iya komai ba,tana so ta ɗan samu hutu saboda ƙafafuwanta,amma ƙememe Safwa ta ƙi sauraren khuɗubar da take mata,sosai Umma ke cikin damuwar wasu cikin ɗabi'unta a yanzu,ta ƙarfi tana son tanƙwarata,ita kuma ta fito ta nunawa uwar bafa zai yiwu ba kawai tai haƙuri,ita bata gaji aikin wahala ba,fatarta ma bai son wahala ita kalar hutu ce matar manya,dole Umma take aikinta da kanta kamar dai ko da yaushe,tunda ƴar gwal ɗin ta kafe atafau baza ta iya aikin da take so tayi ba. Safwa na idar da sallan maghreeba,masallacin line aka fara kiran ishaa,shi kam ta yisa a lokacin saboda wayarta data cinye charge tas,tana tashi taja wayarta tasa charge sannan ta fita ɗakin saboda yunwar da take ji,ƙasa ta sauka ta tarar Umma ta musu tuwon semovita da miyar ɗanyen okro (kuɓewa) wanda tasa masa ogbono yai bala'in yauƙi,abunka da yare duk ta san kan sirrin girki,kallon tuwon Safwa ta dunga yi ranta duk babu daɗi,ita a son ranta ta fi so kayan kwaɗayi danginsu pizza and ice cream,ta tsani duk wani abinci dangin tuwo,wucewa tai parlonsu ta zauna tana kallon su Aasim da suke cin tuwon har faɗa suke,kasancewar Umma ba daga nan ba,ta iya sarrafa abinci yai daɗi,kaci sai kai zaton wata hamshaƙiyar chef ce daga wani ƙasar,da kallo ta dunga bisu fuskarta a kyaɓe kamar ana mata magana za ta kece da kuka,Umma bata ɓata lokacinta gurin kallonta ba though ta ga duk reactions ɗinta,Safwa dai na ta zaune wanting Umma ta tambayeta ya dai? Can dai Umma kamar za tai dariya,dan yanda Safwa kewa su Bilal masifa,tace "Safwa meke damunki ne wai za ki kama min yara da faɗa? Laifin me suka miki?" Cikin ƙulewa Safwa tace "Umma kin san fa ba na son tuwo,amma baki tambayi ra'ayina ba kikai" Umma na mata wani kallo tace "toh! Ai sai ki bari idan kinje gidanki sai kici abunda ranki yake so,nan kam gidana ne sai abunda naga damar yi,dukanmu muna son tuwon har Babanku,dan ke kaɗai baza mu fasa ba wallahi.. Kin san hanyar kitchen sai kije ki nemi abunda za kici,ko indomie kije ki bararraka kici kada ki kwana da yunwa,idan kina da kuɗi kuma yanzun nan za ki iya zuwa ki siyo abunda kike so,ko ki kira wani cikin samarinki ya kawo,har muma mu tayaki ci ko Awwal?" Awwal dake kusa da Umma yace "ni ta kawo ma zanje na siyo mata wallahi duk nisan gurin" Safwa ta maka masa wani kallo ta miƙe a ƙule ta wuce sama tana gunguni. Umma ta ɗaga kai ta bita da kallo kafin ta taɓe baki,underneath tunani take tunda har Safwa baza ta gyara halinta ba,kuma duk abunda ya kamata tayi ta yi,amma bata canja zani ba,ta yi faɗan,ta yi lallami duk a banza,yanzu ta gano hanya mafi sauƙi da za tabi da ita,cikin ruwan sanyi ba sai ta buɗe maƙogoro maƙota sun jiyota ba,za tasa tai give up ma duk wani ego ɗinta da take ji da shi,daga yau abincin duk da tasan ba ta so,su za ta dunga yi a gidan,sai dai kada taci. Shawaran Umma Safwa tabi,tana haurawa sama dake ta san kan logics ɗinta,musamman idan tana son wani abu gurin samarinta,sad emoji taje tai status da shi,kafin kace me fiye da ⅔ na samarinta da sukai viewing,sun fara tambayarta mene ne? Meke damunta? Ita da waye? Waye ya ɓata mata rai? Zo kaga yanda ake jan aji da shagwaɓa da kwantar da kai,cike da ƙwarewa ta faɗima da yawansu abunda ke damunta,gwaninta da son burga gurin maza,nan da nan aka fara kiranta ana lallashi,Wazeer ko nace Aley a gurinta kamar yanda tai saving number ɗinsa kawai da bata gani ba,babu alamar kuma ya ga status da tayi,tun safe da sukai chat,sai wayar da sukai ɗazu da yace ya ganta zoo road,dama kuma ita ke shisshige masa,ita ke fara yi masa magana,yanzunma sanda ta shiga contact ɗinsa sad emoji ta tura masa sannan ta fita,ta ci gaba da chat ɗinta.
*MUNIBA*
Kafin ta bar gidan sai data tsaya bakin get taiwa Baba me gadi sallama,ta ciro 1k sabuwa dake jikin condem ɗin wayarta,a hankali ta sauke glass tace "Baba ga wannan babu yawa,yau ban fito da kuɗi ba" ya leƙo tare da sa hannu biyu ya karɓa yana faɗin "na gode Hjy.. Allah ya saka da alkhairi yayi albarka,ubangiji ya baki miji na gari,ya rabaki da iyayenki lafiya" ƙayataccen murmushi tayi tace "ameen Baba,na gode sosai²,sai da safe" daga haka taja motar ta bar gidan dattijon yana tai mata addu'ar sauka lafiya,a rayuwarta tana son yai mata addu'ar nan,tana jin daɗi har cikin zuciyarta,kwaɗayin addu'arshi ne yasa ba ta iya zuwa ta tafi bata gaisheshi kou tayi masa alkhairi ba,5 minutes drive shiga line su dake da haske sosai,horn tayi dai² babban get ɗin gidansu,get keepers ɗinsu police biyu suka buɗe mata ta shige,tana yin parking ƙasan tent a babban parking spot ɗin gidan ta buɗe motar,sai da ta ɗauki ledarta da Mama ta bata,sannan ta sauka ta rufe motar,a nutse take tafiya ta haura balcony,tana buɗe entrance ta shiga bakinta ɗauke da sallama "assalamu alaikum warahmatullah wabarkatuh" babban parlour ne dake nan tsaf²,fari tas ɗin marbles me ratshin gold dake shimfiɗe suna wani irin ɗaukan ido saboda gyaran da suka sha,parlon na fidda sanyayyan iska da wani ƙamshi me sanyaya rai,komai na cikin parlon fari ne da ɗan adon gold,ya bala'in yin kyau,kana kallon tsadaddun kujeru da rugs,za ka san tabbas masu gidan sun wuce a kirasu da masu rufin asiri,sai dai kasa su cikin sahun masu arziki,kyakkyawar matar dake zaune saman lafiyayyun royal chairs na parlon ne,ta ɗago tana kallonta ta amsa "wa'alaikis salaam warahmatullah wabarkatuh" Muniba dake shagwaɓe fuskarta tana zama kusa da ita,bayan ta ajiye ledarta saman couch dake gefenta tace "Mami barka da gida" kwata² basu yi kama da Muniba ba,sai dai na kasancewarta jininta,Mami dake kallon ƴarta with caring tace "yawwa! Ai yanzun nan nake shirin kiranki,ke da kika ce baza kiyi dare ba" zamewa Muniba tayi ta kwantar da kanta saman cinyar Mami tace "aiki muka yiwa Mama,shi yasa ban taho da wuri ba" Mami ta gyaɗa kanta tace "ok! Ya Maman naku? Da su Khalidah?" Muniba tace "suna lafiya,sun ce a gaisheku" Mami tace "muna amsawa.." Muniba na kallon fuskar Mami tace "yawwa! Mama tace wai kawo kayan lefen Yaa Khalidah,maza ne za su kawo,kuma sun ce ranar Friday" Mami tace "maa sha Allah.. Allah ya kaimu" tashi Muniba tayi ta janyo ledarta,Mami na kallonta tace "me kika samo a gurin Maman naku?" Murmushi tayi tace "nima ban san mene ne ba,kawai ta cewa Baniynah ta bani" Mami tace "maganar kayan ankon fa? Bata ce miki komai ba?" Muniba dake kici²n fito da robar dake cikin ledar hannunta tace "laa! Ta ce na faɗa miki an kawo,su muka tayata warewa fa" Mami tace "kuma baki karɓo kin taho min da su ba? Ji shiririta don Allah,sai kika zo kina bani labari?" Muniba tace "a'a cewa tayi za tazo da kanta kuyi magana" Mami tace "ok! Allah ya kawota lafiya" dambun nama ne cike da robar data ciro,ta saki murmushi tana cewa "Mami bismillah kou alhamdulillah?" Hjy Aminat tai mata wani kallo tace "idan baki yi niyyar bani ba kici abunki" dariya tayi da ya bayyana kyawawan haƙoranta tace "kai Mami,yanzu ci za kiyi?" Mami tace "a'a tunda baki yi niyya ba ci,za kiga nawa kizo ai kin san abunda zai faru" dariya ta sake yi tace "tou gashi ki ɗiba" Mami tace "je kitchen ki ɗauko bowl sai ki zuba min da kanki,kada kice na kwashe miki" robar ta ɗorawa Mami a cinya ta tashi,babban kitchen ɗinsu dake nan a tsaftace,sai ƙamshin different spices da yake,kai baza kace an yi amfani da wani abu ba,saboda yanda ake kula da shi,a nutse ta shiga ta buɗe dish rack ta ɗauko ɗan madaidaicin bowl sannan ta fito,inda ta tashi ta koma ta zauna,ta kalli Mami dake taunar dambun nama tace "Mami gashi" Mami tace "a'a zuba min da kanki" Muniba tace "ni dai a'a ki ɗiba" Hjy Aminat ta ƙarbi bowl ɗin,ta jirkice kusan fiye da rabin robar,Muniba ta hangame baki kafin tace "kaiii³! Mami kin juye ai" Hjy Aminat bata san sanda ta fara dariya ba,Muniba ta kalli wanda yake cikin robarta ta kalli na cikin bowl ɗin,kamar za tayi kuka tace "Mami kin fa juye min" Mami tace "sai da nace ƙi ɗibar min kika ce na ɗiba da kaina,kuma na ɗiba sai ace na juye? Idan ba'a so naci sai na mayar miki abunki" turo baki tayi idanunta sun yi rau² kamar za tayi kuka,Hjy Aminat ta ɗauke kai tana sakin murmushi,tana kallon duk reactions ɗin Muniba ta gefen ido,buɗe ƙofar da akayi yasa dukansu suka juya suna kallon kyakkyawan babban mutumin da ya shigo da sallama,kana kallonsa ba sai an maka bayanin waye shi ba saboda tsananin kamar da suke da Muniba,da sauri Muniba dake jiran ƙiris ta ajiye robar dambun namanta ta tashi ta nufeshi tana faɗin "Abba oyoyo" murmushi ne kwance saman fuskarsa ya buɗe mata hannu,da sauri da shige jikinsa fuskarta cike da rikici,yana kallonta yace "Mamana! Yaya akayi? Me akai miki kike fushi?" Hjy Aminat dake dariya tace "barka da shigowa yallaɓai" yace "yawwa! Kuna lafiya?" Tace "lafiya lau alhmdllh" kallon Muniba ya sake yi yana zaunawa saman kujera yace "uhumn! Ke da waye?" Hjy Aminat dake kallon fuskarta tana murmushi tace "babu wanda ya taɓa ta,ni da itane" Alh Abbas Mijinyawa ya kalli matarshi yace "toh! Wani laifin tayi?" Mami tace "kou ɗaya,abune tazo da shi tai min bismillah,nace ta bani da kanta,ta miƙo min tace sai lallai na ɗiba da kaina,kuma na ɗiba tana fushi" Abba ya kalli Muniba yace "a'a Auta baki da gaskiya indai haka akayi" a shagwaɓe Muniba tace "Abba juyemin fa tayi,kalli ɗan wanda ta barmin" ta tafi ta ɗauko masa robar,dai² wani saurayi dake sanye da ƙananan kaya ya shigo da sallama suka amsa,Abba na kallon cikin robar yace "ina wanda Mamin naku ta ɗiba?" Hjy Aminat dake dariya tace "gashi nan ka ganshi fa duka" Abba na kallon cikin bowl ɗin hannunta yace "a'a Minah baki da gaskiya.. Wannan ai kin juye duka,daga ance ki ɗiba aga hankalinki sai ki kwashe ⅔,ai dole tace kin juye" Mami na dariya tace "auu! Haka ma za kace?" Yace "ƙwarai kuwa.. Auta jeki ta rage wanda ta ɗiba" matashin saurayin da ya tsaya bayan kujerar Mami yana leƙa cikin bowl ɗin hannunta yace "Mami sannu da gida.." Mami tace "yawwa! Sannu Khalifa,an dawo lafiya?" Yace "alhmdllh" yana ta tsaye har Muniba tazo gurin,ganin ta ƙi kallonsa bare ta kulashi yasa a hankali yace "Mami mene ne wannan?" Mami tace "me idonka ya gani?" Yace "kamar dambu" ta ɗaga kai tai masa wani kallo,kafin ta rage yawan wanda ta ɗiba cikin robar hannun Muniba da tai kicin² ta ƙi kallonsa,ɗan murmushin tsokana yayi yace "Mami zanci please" Mami bata kalleshi ba tace "tou akwaɗaya,nima sammin akai" ya kalli Muniba zai magana,tai saurin barin gurin tana cewa "bazan sammaka ba dai" buɗe ido yayi yace "auuu! Naki ne dama?" Tace "ehh ɗin" ya taɓe baki yace "sai me dan baki bani ba? Ai dama ke marowaciya ce,sai kinga na mutane ki kama zazzare ido kina jiran ai miki tayi" zama tayi kusa da Abba tana cewa "Abba bismillah" ta ajiye masa duka robar,Abba dake sauraren dramarsu yai murmushi yace "Auta ai sai mu cinye baki ci ba,na gode maza kici abunki" shagwaɓe fuskarta tayi tace "ni dai a'a kaci" yace "a'a Auta ki sanwa Yayanki dai tunda yana so,ni na yafe ba sai na ci ba a bashi" jin haka yasa Khalifa ya taho da sauri yace "tunda Abba yace a bani nashi a bani" ɗaga kai Muniba tayi ta kalli Yayanta,fuskarta ɗaure kamar za tayi kuka tace "ai dai baice bazai ci ba,kuma ni bazan baka abuna ba,ai munyi faɗa da kai" Khalifa na kallonta yace "taɓɓɓ ɗin lallaima yarinyar nan,wai tun abunda ya faru ɗazu ne kike ta fushi har yanzu? Lallai angaisheki sannu da aikin wahala,tou ai ni nama manta munyi faɗa" tai masa wani kallo tana rufe robar ta tura bayanta,Khalifa yace "tou mene ne abun ɓoyewa kuma?" Muniba tace "ai bazan sammaka ba" kafin yayi magana Abba dake musu dariya yace "ɗan sammasa kaɗan Mamana,tunda ransa ya biya kuma ya gani,ido guba" Khalifa yace "ke kuwa ki sammin mana,kina ji Abba yace ki bani" tace "taɓɓɓ ɗin.. Ni dai bazan bayar ba" yai mata wani kallo ganin da gaske take baza ta bashi ba,yace "kada Allah yasa ki bayar ɗin,dan kinga ana son abunki kike yiwa mutane wulaƙanci,abunda ma ba daɗi ne da shi ba" Muniba ta hangame baki ta kasa cewa komai,kusa da Mami Khalifa yaje ya zauna yana cewa "Mami ki sammin please naci naji" Mami tai masa wani kallo tace "kai da kace babu daɗi? Ai nima sammin akayi,kuma na kusa cinyewa,baza ka samin rani ba,kaje ka lallaɓata ta sammaka,tunda kun saba haka" yace "kai Mami,yanzu haɗemin kai za kuyi? Ita ta hanani,kema baza ki bani ba? Kuma kina cewa na lallaɓata?" Mami tace "ai sai kayi,baki shi ke yanka wuya,da bakai furucin babu daɗi ba,da na sammaka ka maida miyaunka" da sauri yace "kai Mami wasa fa nake yi,dan taji haushi ne na faɗi haka,ido guba fa Mami" Mami tace "a'a ido kwaɗayi dai.. Ba dan hali ba kawo hannunka na sammaka" da sauri ya miƙa hannu bibbiyu,Abba sai kallonsa yake yana sakin murmushi,Muniba kam mamaki ya gama kasheta a zaune,Mami ta ɗan sa masa kaɗan a tsakiyar hannu,ya watsa bakinsa yana taunawa,zazzaro idanunsa yayi yace "wow! Yummilicious.. Mami a ina akayi wannan?" Mami tace "bari nasa maka throw pillows su tareka kada ka faɗi" Khalifa yace "Mami ba santi nake ba,wallahi da daɗi sosai,dan Allah ki ƙara min" Mami tace "a'a wannan kuma ka yi ƙarya,jeka gurinta ta sammaka idan ta ga dama,idan bata baka ba halinka ya janyo maka.. Nima da aka sammin har ka zaƙe kace na ƙara maka" Muniba tai kicin² ta ajiye robar a saman cinyar Abba tace "mu cinye Abba" Abba yace "Mamana kin damu sai na ci,bari dai naji daɗin nan da suke faɗa" ya ɗan danƙi dambun yasa a baki,komai perfect babu yaji,Abba ya dunga gyaɗa kanshi,Khalifa ya taho ya durƙusa on his knees yace "please Lil sis,i'm so sorry for my mistake,ki karɓi apology dana kawo miki ba don halina ba" Muniba tai masa wani kallo kamar idonta zai faɗo tace "a'a bazan karɓa ba,ai babu daɗi,me za kayi da shi?" Yace "suɓutar baki nayi,amma kiyi haƙuri,kuskure ne na tuba" Mami tana kallon yanda Khalifa yayi a gaban Muniba tace "girma ya faɗi,yanzu akan abun duniya kake durƙusawa ƙanwarka?" Yace "Mami dan Allah kiyi shiru,so nake mu shirya ai" Abba ya danƙo wani a hannunsa ya miƙa masa yace "tashi ka bamu guri,gashi nan na fansheka" da muryar kuka Muniba tace "Abba shi ne ka bashi?" Abba yace "yi haƙuri ki karɓi girman tunda ya bar miki" Khalifa dake taunar dambu ya gyara zama a ƙasa saman rug yana kallonta ya miƙo hannu yana faɗin "ko hanji ko hanta ko hunhu.. A taimakawa ɗan malam zai soye.." Bai kai ƙarshe ba Muniba ta fashe da dariya,Mami da Abba suka dunga kallonsu suna masa dariya,in dai sukai faɗa kafin dare sai Khalifa ya nemo hanyar shiri da ita ko ta ina ne,shi kam yai fuska kamar ba shi ba,Muniba ta kai minti 3 tana dariya kafin ta tsagaita tace "almajiriii" Khalifa yace "na'am! Iya na kawo kwano?" Muniba ta sake kwashewa da dariya tace "eh kawo" kafin kace me ya ɗauki murfin robar data ajiye ya miƙa,Abba da Mami suka shiga dariya,tsakanin Muniba da Khalifa sai Allah,ya bata shekara gurin 5,amma idan basu yi faɗa a rana ba tou basu bane,faɗan sako da sako kullum sai sun yi kuma su shirya,ta zuba masa tana ta dariya,Khalifa ya daddage ya shiga rafka godiya kamar almajirin gaske,kafin ya tashi ya koma kusa da Mami ya zauna ya shiga afawa bakinsa,kiran sallar ishaa ne yasa Abba kallonsa yace "toh! Almajiri idan ka gama ƙwalamar ka tashi muje masjid.." Da sauri Khalifa yace "to Abba" suna haɗa ido da Muniba yai mata murmushi yace "na yi miki wayo yarinya" tana dariya non-stop tace "a wajen iya bara ko?" Yai murmushi ba tare da ya sake cewa komai ba har ya gama suka fita masjid da Abba.
*WAZEER*
Yana zaune parlour zuciyarsa da tunani iri²,wayarsa dake jikinsa ciro ya buɗe ya shiga WhatsApp,Mimi yake son sanarwa ba zai samu damar zuwa yau ba,maybe sai zuwa gobe da safe,yana kallon saƙon Safwa ya shigo amma ya kasa buɗewa,bai da niyyar kulata sam,dan bai son damuwa da surutu a yanayin da yake ciki,har lokacin kuma yana zaune tare da Dad,bayan da ya gama yi masa maganar service ɗinsa,gane yana online da Safwa tayi yasa ta sake tura masa sad emoji,lokaci ɗaya ya buɗe yai mata sallama,kamar bai son tambayarta wata zuciyar tasa shi cewa "hey! Why are u sad?" Safwa bata iya haƙurin jiran tai masa bayani ba ta fara kiransa,a hankali ya kalli wayar kafin yai silencing kiran ya tashi ya wuce hanyar bedroom,Dad ya ɗaga kansa ya bishi da kallo cike da mamakinsa,tuna maganar da yai masa kafin shigowarsu yasa shi taɓe baki. Wazeer na shiga bedroom ɗinsa yasa wayar speaker bayan yai answering kiran,a rayuwarsa saka waya a kunne ya daɗe yana sauraren mutum,ciwon kai yake bashi,shi yasa da yawan lokaci yana amsawa,indai ya san za ka wuce 1 minute kana masa magana yake buɗe abun sauraron wayar ya ajiyeta gefensa,Safwa da ƴar siririyar muryarta data sirantar tace "hello!" Maimakon ya amsa sai yai mata sallama ta amsa,kusan minti ɗaya ya ɗauka kafin yace "so how are u?" Tace "i am not good" yana cire rigar dake jikinsa yace "so me akai miki?" Cikin kwantar da murya tace "ba ni da lafiya" shiru yayi,kafin a hankali yace "meke damunki?" Tace "nima ban sani ba,kawai bani da lafiya" yace "ok! Kinje hospital?" Tace "um'um" yace "me yasa?" Kamar baza tace komai ba,sai kuma tace "ina jiran Baba ya dawo na sanar masa" yana gyaɗa kansa yace "ok! Allah ya ƙara lafiya,idan kinje sai ki sanar min,yanzu ina uzuri,za muyi magana anjima?" A hankali tace "ok!" Yace "bye.. Take care of urself please" ta gyaɗa kanta kamar marainiya tace "ok bye" shi ya fara katse kiran ya duba Mimi ya tura mata saƙon da zai tura mata sannan yayi offline,kafin ya ajiye wayar a gefe yayi shiru yana tunanin abubuwa da yawa wanda Dad ke faɗa masa da can a lokacin da suke California akan Mimi da sauran mata,shi kuma a karatunsa na nazarin halayyar ɗan adam da yayi ya ga saɓanin haka,ya ga mata,ya sansu,kuma ya karancesu tas,ya ga abubuwa da yawa da suka kurkurewa abunda Dad yake ce masa,shin mene ne matsalar data sa Dad yake kallon duk wata mace a siffar da ya sanar masa? Me yasa yace mata mugaye ne? Me ya haɗa shi da Mimi da har kawo wannan lokacin ya kasa mantawa? He want to know abubuwa da yawa da suka shafi iyayensa,kuma ba da nisa ba a ɗan taƙaitaccen lokaci,yana son gano matsalar data sa iyayen nasa suka rabu,tambayar kansa yayi "ta ina zan fara? Mimi ko Dad? Waye me gaskiya a tsakaninsu? Waye yaiwa wani laifi? Akan waye alhakin mutuwar mutuwar Mysha yake? Me yasa Dad yake cewa Mimi ce ta kasheta?" Kiran da ya shigowar wayarsa ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya tafi,special ringtone da yasa mata ne ya sanar da shi ko waye me kiransa,katse kiran yayi sannan ya shiga kiranta back,tana ɗauka tai masa sallama,wayar na hannunsa yace "good evening Mimi" Mimi tace "evening.. How are u?" Idanunsa a ɗan lumshe yace "i am good" Mimi tace "me yasa ka fasa zuwa yau? Is everything ok?" Gyaɗa kansa yayi kamar yana gabanta yace "yeah! Wani uzuri yasa bazan samu zuwa ba" Mimi tace "alright! Allah ya kaimu goben,guraren karfe nawa za ka zo?" Yace "around 11am" Mimi tace "ok! Allah ya kaimu" ya amsa,sai da sukai sallama ta katse kiran daga gefenta,kafin ya ajiye wayar,ya sake dulmiya duniyar tunani. Da safe around 11am ya fito cikin shirinsa,ƙananan kaya ne jikinsa,polo shirt maroon color sai black jean,fuskarsa kamar kullum sanye cikin face mask tamkar mara gaskiya,ko ɓangaren Daada bai shiga ba ya bar gidan,motarsa dake waje ya ƙarasa ya buɗe ya shiga,cikin few minutes ya bar unguwar Tudun wuzirci ya ɗauki hanyar da zai kaishi gidansu Mimi,15 minutes drive ya iso dai² get ɗin gidan,yana yin horn get keeper ya buɗe masa yana yi masa barka da zuwa,a hankali ya wuce ciki ya samu guri yai parking sannan ya sauko,entrance ɗin gidan ya nufa yana tafiya cike da kuzarinshi,yana yin knocking aka buɗe ƙofar,Mimi dake ta jiran zuwansa ta saki murmushi,mask ɗin fuskarsa ya cire idanunsa a kanta ya shiga da sallama a ciki² ta amsa,Mama dake zaune suna hira da Mimi ta kalleshi lokacin da ya durƙusa gabanta yana gaisheta,fuskarta a sake tace "lafiya kau Abuu Turab,ya mutanen gidan naku? Da kakanninka?" Yace "alhmdllh! Suna lafiya" Mama tace "maa sha Allah.. Ya mahaifin naka?" Yace "he's good,alhmdllh" Mimi ya juya ya gaisar,kafin ya koma sama kan kujera ya zauna,me aiki ta fito ta kawo masa ruwa da drink. Nan ya yini bai cewa komai sai idan Mimi tai masa magana,sallah kawai ke fitar da shi,har akai maghreeba ya dawo masjid yai shirin tafiya bai iya sanarwa Mimi zancen shigarsa camp ba,sai da suka fito lokacin ya yi sallama da Mama,suna tsaye compound tana kallonsa,ganin kamar akwai damuwa a fuskarsa kuma ya kasa sanar mata,tana kallonshi tai ɗan murmushi tace "Abuu Turab! Meke damunka?" Kallonta yayi idanunsa a narke ya girgiza kai,sai kuma ya kasa cewa nothing ɗin da yayi niyya,gyara tsaiwarsa yayi yana kallon mahaifiyarsa da kyau ya buɗe bakinsa yace "Mimi can i ask u?" Gyaɗa masa kai tayi tace "yeah! U can,what's happening?" Shiru yayi kamar bazai ce komai ba,yana juya key ɗin motarsa dake hannunsa yace "me ya faru tsakaninku? I mean me yasa kuka rabu ke da Dad?" Kallonsa ta dunga yi na kusan 3 minutes ta kasa cewa komai,a hankali ya ɗaga kansa ya kalleta,ganin kamar tambayar yasa mood ɗinta sauyawa,yasa shi cewa "i'm sorry Mimi.. I never know tambayata zai ɓata miki rai,i'm so sorry.." Daga haka bai sake cewa komai ba ya buɗe motarsa zai shiga...
_#Afwaan! Jiya ban samu kaina ba shi yasa baku ga update ba,but don't forget to follow my account on arewabooks @Realsmasher or https://www.arewabooks.com/u/realsmasher.._
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
*Infection*
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*****
*****
#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#ASLI-SMASHER.