WAZEER!

Camp

by @realsmasher

  ```Alhamdulillah alaa kulli halin! I am stepping toward shifa,thanks so much for ur prayers.. Allah ya bar zumunci,na gode³ sosai. Ahabbakum'kthiir..😍🙌❤ Kada kuma a manta aje ai following ɗina a arewabooks @Realsmasher or https://www.arewabooks.com/u/realsmasher.```️



 

                10

 


#Camp



        Hannunsa Mimi da jikinta yayi sanyi ta riƙo,tana kallonsa idanunta cike da hawaye tace "kaima kana tunanin ni na kashe Mysha? Ni ba me kisa bace,ban kashe kowa ba,ta ya ya zan kashe ƴata da na haifa? Me zai sa na kashe jini na? Me tayi min?" Girgiza mata kai yayi jikinsa a ɗan sanyaye yace "i know Mimi,ta ya uwa za ta kashe ɗan data haifa? Ban taɓa yarda za ki kashe ko da kiyashi bane bare ƴarki,na kasa gane dalilin da yasa Dad yake kallonki da laifin nan,me ya faru? Waye behind mutuwarta? Shi ne abunda bai fito ba har yanzu" sanyayyar ajiyar zuciya Mimi tayi tana ɗauke ƙwallar da ya gangaro idonta,cikin sanyin murya tace "koma waye ya aikata laifin nan,da yasa Hamood yake kallona da laifin na kashe masa ƴa,Allah yana kallo kuma yana ji,muddin bai zo ya nemi yafiyata ba,ba zan yafe masa ba" Wazeer dake ta tsaye ya ɗan gyaɗa kansa a hankali yana kallon mahaifiyarsa,da wani calm muryarshi yace "Mimi!" Sai kuma yayi shiru kamar yana tunani,Hoor dake riƙe da hannunsa har lokacin ta kalleshi tace "me kake tunani? Wani abu na damunka ka kasa sanar min ko?" Babu ɓoye² ya gyaɗa kansa a hankali,cikin kame² yace "arghm!" Sai kuma ya sake yin shiru,ya rasa ta ina zai fito ya fara sanar mata,ajiyar zuciya ta sauke tace "speak up Abuu Turab.. What's happening? Mmm?" Ya kasa kallonta saboda nauyin da maganar yayi masa a rai,yace "Dad said that ranan Monday zan shiga camp" maimakon yaga ta nuna damuwa sai murmushin da tayi masa tace "akan wannan kake damuwa?" Gyaɗa kansa yayi ya ɗago idonsa ya kalleta,tace "Allah ya kaimu,ya bada sa'a.." Ya amsa da ameen,tace "in the next couple of days kenan kou?" Ya gyaɗa mata kai a hankali,tana ɗan sakin murmushi tace "ok! Ma yi waya idan ka koma gida,kada dare yai maka a nan" ya sake gyaɗa kansa a hankali cikin wannan kamilalliyar huskey voice ɗin nasa yai mata sallama,tana tsaye ya buɗe motar ya shiga,sai da ya bar gidan kafin ta juya ciki tana tunanin abunda za tai masa,na ta gudunmawar na tafiyarsa,shekaru 20 Hamood ya haramta mata gani da jin daɗin ɗanta a kusa da ita,yanzu da yake kusa tana ganinsa baza tai sake Hamood ya fita kyautata masa ba har yasa masa zargi akanta,tana wannan tunanin ta shiga parlour,zaunawa tayi a kusa da Mama tana sakin kyakkyawan murmushi tace "Mama! Me kike ganin ya kamata na yiwa Abuu Turab da zai tafi Camp da shi?" Mama tayi murmushi irin nasu na manya,cikin sanyin hali da muryarta dake nuna shekarunta sun tura sosai tace "duk abunda kikai niyya Auta kiyi masa" Mimi tayi murmushi tace "Mama da na yi tunanin wai ko zan tura masa kuɗi,sai kuma naga ai bazai buƙaci kuɗi ba saboda Hamood na tare da shi,sai kuma nace kou snacks za'ayi masa da stew haka ko?" Mama ta gyaɗa kanta tace "ehh ayi masa hakan,tunda garin ba nan bane kou?" Mimi tace "ehh can Ƙaraye LGA ne" Mama tace "Allah sarki,ko zai iya rayuwar gurin nan?" Mimi tayi murmushi tace "ko bazai iya ba tunda Allah ya yisa a namiji ai haka zai daure har ya saba" Mimi tayi shiru tana tunani,can kuma sai ta tashi ta tafi store ta duba abunda yake akwai da wanda babu,bayan ra gama dubawa ta fito ta tafi upstairs,bedroom ɗinta dake nan tas a tsare kamar tana gidan mijinta ta shiga,ta ƙarasa gaban rack na tsadaddun bags ɗinta ta buɗe wani Luise votton me bala'i tsada da kyau ƙarama,jotter da biro ta ɗauko sannan tai tai waje,tana saukowa downstairs ta koma kusa da Mama ta zauna tana rubutu,tas tai making list duk abunda take so sai data gama sannan ta kirashi taji yanda ya isa gida. Washe gari Friday kafin ta tafi hospital sai data bayar da list ɗinta a nemo mata komai,sannan ta bar gidan,da yake da wuri take dawowa gida,ana tashi ta tuƙo motarta zuwa gida,sanda ta shigo sai data fara tsayawa suka gaisa da Mama kafin ta wuce sama,wanka da sallah ta fara yi,ta canjo kayan shan iska sannan ta sauko,ko abinci a gaggauce ta iya tsaiwa ta ci,tana gamawa ta wuce kitchen ta kama aiki tare da househelp ɗinsu biyu,aikin da ta daɗe bata yi irinsa ba ta duƙufa yi kamar ba Hoor ba,sai dare ta samu kanta,nan gajiya tace bata san zance ba,gaba ɗaya jikinta ya dunga ciwo,sai data nemi painkiller ta afa,tana yin wanka da ruwa masu zafi tai sallolinta ta kwanta,take wani irin ƙaƙƙarfan bacci yai gaba da ita.



*MUNIBA*



   Guraren zhuhur suka fito lectures,sanye suke da Turkish abaya masu kyau,kana kallon yanda sukai shiru babu me cewa ƴar uwarta komai za ka san a mugun gajiye suke,suna isa carline dake cike da tsadaddun motoci,Baniynah ta buɗe driver side ta shiga,Muniba data rufe mota bayan ta shiga gurin me zaman banza ta kalli agogon CK dake ɗaure wrist ɗinta,a hankali ta lumshe ido ta buɗe tace "ai sun kawo kayan ma tun ɗazu na san" Baniynah tai ajiyar zuciya tana yiwa motar key tace "ai taimakon da Allah yayi mana maza ne za su kawo kayan nan,da yau maybe bamu samu zama gida ba,kuma kinga ga test ɗin nan da yazo bagatatan" Muniba tace "uhmn! Bari dai muje gidan" daga haka suka bar premisses na haɗaɗɗen school ɗin da kamar ba'a Nigeria ba,ko'ina yaran masu kuɗi ne asalin ejeboters da suka tashi cikin gata,suna fita get na MA'AUN (Maryam Abacha American University of Nigeria) Baniynah ta shiga driving kamar za ta tashi motar sama,kai tsaye gidansu Muniba suka wuce,da yake can za'a karɓi kayan kamar yanda Dr Sulaiman ya shaidawa matarsa,jefi² suke hira har suka shigo GRA,dai² babban get ɗin gidan Commissioner Abbas Mijinyawa Baniynah tai horn,police get keeper da suke da su yazo ya buɗe musu,tana yin parking suka sauko,kamar ƴan yara har rige² suke su isa ciki,Muniba data riga Baniynah yin gaba tana dariya ta bude entrance ta shiga da sallama,hayaniyar data ji yasa ta buɗe ido tare da kama kanta,Baniynah ta shigo da sallama tana cewa "shi ne kika gudo kika barni,ashe kin san abunda kika shuka shi yasa kika barni da driving" Mami da suke zaune ita da Mama sai wasu few neighbors da Umma,wacce ta biyo Mama jin cewa a nan gidan Commissioner aka karɓi kayan,sai ɗaga lefen take tana washe baki da faɗin "a'ahh! Wallahi Khalidah ta yi goshi,Allah yasa gidan zamanta ne na har abada" Mami tace "ameen yaa rabbi" sallama suka sake yi sanda suka iso,Umma ta tada kai tana kallonsu,Mama dake murmushi tace "a'a ƴan biyun Mami kun dawo?" Muniba ta tafi kusa da ita ta zauna jikinta tana faɗin "Mama sannu da zuwa.. Ina yini?" Mama tace "yauwa ƴar albarka,ya makarantar?" Muniba tana ɗan yatsina fuska tace "alhmdllh! Babu daɗi" Mama tace "ai dama haka karatu yake,sai nan gaba kun gama za kiga kamar ma baki yi ba" sauran occupants ɗin parlon suka gaisar duka suka amsa,Muniba na kallon tulin boxes ɗin dake ajiye set 5 ga wani traditional boxes kuma da ake cema adudi shima ta jinjina kanta tana murmushi,kaya dai na kece raini akaiwa Khalidah,saboda ɗan Deputy governor ne zai aureta,Baniynah ta waro ido waje ganin uban kayan da aka kawo,Umma sai birkitawa take kamar me lissafawa a rai,lokaci ɗaya ta kalli Muniba sukai murmushi,a hankali Muniba ta waske tana kallon Umma dake ta ɗaga tsadaddun supers ɗin da aka zubo,for about 2 hours da wani abu kenan suke gidan,ko gajiya ta kasa yi tunda aka fito masu da kayan daga parlon Abba,a hankali tace "Umma Safwa bata dawo school ba?" Umma tana washe baki tace "wallahi bata dawo ba har na fito gida,amma ta ce min lakcha 3 ne da ita,tana gamawa za ta taho,za tazo in sha Allah" Muniba ta gyaɗa kai tace "Allah sarki,Allah ya kawota lafiya" Umma tace "ameen²" tana ta washe baki,ji take kamar ace mata kayan nan gidanta aka kawo,tunda take bata taɓa ganin lefe kamar na Khalidah ba,shi yasa ta kasa daina taɓa kayan,su Mami kuma an rasa me cewa ta bari a rufe boxes ɗin haka,tashi Muniba tayi tace "Sweet! Zo muje upstairs" Baniynah ta tashi da sauri kamar ana tsunkulinta,Muniba ta kalli Mami tace "Mami idan Safwa ta zo muna sama" Umma tai caraf ta amshe maganar tace "toh baza ku tsaya kuga kayan ƴar uwar taku ba za ku wuce sama?" Muniba tai murmushi tace "wanka za muyi da sallah,za mu gani anjima idan kun gama" Umma tace "toh shi kenan" suna haurawa sama Baniynah tace "ikon Allah! Ni matar nan ban san meke damunta ba wallahi,ita duk inda taje sai ta nuna halinta,wannan ai sai mutane su tafi da ita a baki ace hassada take yi" Muniba ta taɓe baki tace "idan abun arziki ne ai sai ta ci gaba da yi" suna barin parlon babu jimawa Safwa ta shigo gidan cikin kwalliya,dama ita ba daga nan ba tana son make-up,a parlour ta tsaya ta gaisar da su Mama,Mami ta sanar mata inda su Baniynah suke,ta tashi za ta tafi sama,Umma da bata gaji da kallon kayan ba tace "ki zauna ki kalli kayan mana,ai sun ce wanka za suyi da sallah" Safwa dake ta ɗokin ganin kayan tunda taga tulin akwatuna ta koma ta zauna,Mama dai da Mami wanda yace mata komai,nan ta dunga ɗaga kayan Umma na tayata,ita ba ma kayan ne suka fi tafiya da ita ba,akwatunan kansu dan kallonsu kawai kayi indai ka san kaya masu daraja to za ka gane,tana ta ɗaga kaya babu kunya a tsakiyar iyaye Umma na mata sharhin tsadar kayan,sakkowar Muniba za taje dining ɗebar musu abinci taga Safwa zaune,ta ɗan waro ido tana sakin murmushi tace "ohh Safwa kin iso ashe?" Safwa tayi dariya tace "ehh wallahi na tsaya naga lefen ne kafin na isko ku" Muniba ta gyaɗa kai tace "ohh! Allah sarki,bari naje kitchen na fito,Baniynah na sama ai bamu san kin shigo ba" Daga haka Muniba ta mayar da hankali kan Mami tace "Mami za mu samu abinci?" Mami tace "ai kin sani idan za ku samu ko baza ku sani ba" murmushin yaƙe Muniba tayi sannan ta wuce ta bar gurin,sanda ta fito kitchen da tray a hannunta ta haɗo abincin mutum 3,tana tsaye gaban staircase tace "Safwa taso muje" Safwa dake ta kallon lefe tace "kije kawai idan na gama zan zo" Muniba tace "ok!" Daga haka ta wuce sama,tana shigowa parlon ta samu Baniynah zaune ta ɗora ƙafarta saman center table,wayarta a hannunta tana chat,ajiye tray ɗin Muniba tayi kusa da ƙafarta tace "guess what?" Baniynah tace "uhmn! What?" Muniba na zaunawa tace "ƙawarki ta zo fa" Baniynah tai saurin kallonta tace "Safwa!?" Muniba tace "Yes!" Baniynah ta taɓe baki tace "tana can cikinsu Mami tana kwainane da feleƙe kou?" Muniba ta zaro ido tana dariya tace "a'a babu ruwana ban san me take ba" Baniynah tace "ai ko baki faɗa ba,na san abunda take yi kenan" Muniba tace "ni dai na ce miki ai ban sani ba.. Let's eat kada abincin ya gama yin sanyi" sauka Baniynah tayi ƙasa saman rug,Muniba ta sauke musu tray ɗin suka fara cin abinci,sai da suka kusan gamawa sannan Safwa ta hauro saman da ƴar sallama tana sakin murmushi,tace "hey guys" Muniba tai mata murmushi tace "sai yanzu za ki zo? Muna ta jiranki muci abinci" Safwa tace "ohh! Kada ki damu ai ban jima da dawowa gida ba,sai da naci abinci sannan na fito.. Kuma na san baku daɗe da dawowa ba" Muniba tace "wallahi kam muna shigowa muka yo nan,wanka kawai mukai sai abincin nan da muka ci" Baniynah dai na jinsu bata ce komai ba,Safwa ta kalleta tace "yane Babe? Ko duk gajiya ne yasa kikai shiru?" Baniynah tayi ɗan taƙaitaccen murmushi tace "ke dai ki bari yau na gaji sosai,ga test da mukai" Safwa tace "Allah sarki,semester ɗinku yai nisa ko?" Muniba tace "ai ki bari kawai,addu'ah nake Allah yasa lokacin bikin nan kada yazo mana muna exams" Safwa tai dariya tace "ohh! Ni kuwa ya maganar ɗinkinmu ne? Ko har yanzu tailor ɗinmu bai ce komai ba?" Baniynah tace "ya yi magana sai dai ban samu nutsuwar dubawa ba gaskiya" Safwa tace "ok! How many weeks yanzu ya rage bikin?" Baniynah ta girgiza kai tace "a'a bamu sani ba,mu ko kayanma bamu tsaya gani ba" Safwa tai murmushi tace "ai kuwa kaya sun yi kyau,gaskiya Yaa Khalidah ta more,mijintan nan yana sonta sosai²" Muniba dai bata ce komai ba sai murmushin da take saki,guraren maghreeba sanda Umma za ta tafi,ta aiko househelp tai mata kiran Safwa tazo su wuce gida,tana saukowa ta ɗan tsaya a shagwaɓe tace "Umma za mu taho tare da Baniynah" Umma tace "toh! Nima zanje naima Babanku girki,sai ƙannenki da na bari a gida,shi yasa zan tafi.. Shi kenan sai kun taho" Safwa ta amsa ta koma sama,har gurin ishaa suna gidan,ta yi zaton tare da Baniynah za su wuce,lokacin sun idar da sallah,da yake a cikin mutane tana ƙoƙarin yi idan taga kowa ya tashi,tana kallon Baniynah dake kwance babu alamar za taje wani waje,tace "dear sai yaushe za mu tafi?" Baniynah ta ɗago tana kallonta da manyan idanunta tace "a'a ni ai sai gobe zan koma gida" Safwa tace "alright! Bari nabi Mama to idan bata riga ta tafi ba" Baniynah ta gyaɗa kanta tare da taɓe baki,vail da jakarta Safwa ta ɗauka,tana kallonsu tace "arghm! Kin ce Damfo ya yi miki magana kou?" Baniynah tace "Mmmm!" Safwa tace "ok! Duk yanda kuka yi da shi let me know please" Baniynah tace "zan tura miki number ɗinsa kuyi magana kawai,mun fara haɗa CA a school ba ni da lokaci yanzu sosai gaskiya" Safwa da bata fahimci magana Baniynah ta faɗa mata ba tace "ok!" Tare suka sauko downstairs,suka tarar da Mama ta gama shirin tafiya suna dai ta magana da Mami,boxes ɗin lefe a gefe an rufesu,Mama ta kallesu tace "Baniynah sai yaushe za ku taho ne? Kada dare yayi muku fa,ni yanzu zan wuce gida" Baniynah tace "Mama ni dama ba yau zan taho ba sai gobe" Mama tace "a'ahh! To Safwa tazo mu tafi mu sauketa a gida" Safwa tace "ehh! Dama shi yasa muka sauko tunda ba yau za ta tafi ba" Mama tace "alright!" Tana kallon Mami tace "Dr zan wuce gida,sai mun yi magana dai ta waya" Mami tace "toh shi kenan Hjy" har compound suka rakosu gurin mota,driver ɗin Mama dake jiranta a mota bayan ta kirashi,ya fito ya gaida Mami tare da buɗewa Mama back seat ta shiga,Safwa ta buɗe ɗayan gefen ta shiga itama tana sake yiwa Mami sallama,Baniynah tace "na tura miki number nasa" Safwa tace "ok! Thank uuu dear,duk yanda muka yi da shi zan sanar muku" Muniba tace "ok! Ki gaida gida,a gaida Baba da su Bilal" Safwa tace "za su ji" sai da motarsu ya bar gidan sannan suka koma ciki,Baniynah na cewa "yarinyar nan wallahi ba ta da hankali" Muniba ta fara dariya tace "a'a babu ruwana,ƙawarki ce fa" Baniynah tace "ƙawarki dai,ai banda Allah yasa we are cousins,da ƙawance ne na waje tsakanina dake,wata rana cewa za tayi ita ta haɗa ni dake" Muniba dai dariya kawai take ƙyalƙyalawa,sai sannan suka shiga bubbuɗe boxes ɗin suna kallon kayan,gwal kawai da aka saka a lefen wani danƙareren set ne da idan kaji kuɗinsa sai ka kwana kana mamaki,suna kallon kayan Baniynah tace "Mami kuma how many weeks suka ce? Na ji Mama ta ce za'a iya ƙarawa" Mami dake zaune tana kallon aljazeera tace "3 weeks,sun ƙara 1 week akai,saboda mahaifinsa zai je ganin likita nan da 2 weeks" Muniba tace "ai basu ƙara ma da yawa ba,Allah ya kaimu lokacin" Mami ta amsa da ameen. Shigowar Abba tare da Yaa Khalifa yasa Muniba tashi ta nufi Abba tana dariya tace "Abba sannu da zuwa" ya amsa tare da riƙe hannunta suka ƙarasa ya zauna,Mami da Baniynah sukai masa barka da shigowa ya amsa,idon Khalifa akan Baniynah da taƙi kallonsa,Muniba tace "Yaa Khalifa sannu da zuwa" ya amsa yana ɗauke idonsa ya zauna kusa da Mami yana cewa "Mami barka da gida" ta amsa tana faɗin "ya aikin?" Yace "alhmdllh!" Tace "maa sha Allah.." Abba ya kalli yanda suka baza boxes ɗin yace "wannan ba'a gama gani bane?" Mami tace "su suke gani" Abba yace "toh! Idan kun gama a rufe mana" Muniba ta tashi ta tafi kusa da Baniynah tana cewa "Abba yanzu muke gani" yace "toh! A gani lafiya" daga haka ya tashi ya wuce sama part ɗinsa,Mami ta tafi dining ta haɗa masa abinci ta wuce sama,tana barin gurin Khalifa dake ta kallon Baniynah yace "Muniba kawo min ruwa mara sanyi" sai data kalleshi tayi murmushi kafin ta tashi ta wuce kitchen,tana barin gurin ya sauko daga kujerar da yake ya zauna kusa da Baniynah,a hankali yace "baza ki kulani ba dear?" Baniynah tai saurin tashi kamar a tsorace tana buɗe manyan idanunta tace "Yaa Khalifa please Muniba na nan" yace "ok! Me yasa baki amsa kirana ba?" Tana turo baki tace "muna school fa" yana kallonta da kyau yace "and then?" Tai shiru taƙi cewa komai,ya kalleta ganin Muniba ta fito yace "me ya hana ki kirana bayan nan?" Ƙin cewa komai tayi har Muniba ta bashi ruwan ta koma inda ta tashi ta shiga mayar da kayan da suka fito da,tana gamawa ta tashi ta ɗauki wayarta tai hanyar dining tana cewa "Sweet dinner fa?" Baniynah data ƙi kallon Khalifa ta tashi tabi bayanta da sauri. 



*SAFWA*



   Har ƙofar get ɗinsu Mama tasa driver suka ajiye Safwa,sanda taga shigarta gida sannan ya juya motar suka ƙarasa nasu gidan,Safwa na shigowa parlour tai sallama,Umma dake zaune ta amsa tana kallonta ta saki murmushi tana faɗin "kun dawo?" Safwa tace "eh! Tare da Mama muka taho,su suka sauke ni har ƙofar gida" Umma tace "Baniynar fa? Ba tare kika ce za ku taho ba?" Safwa na girgiza kanta tace "a'a wai ba yau za ta dawo ba,can za ta kwana" Umma tace "aiho! Kuma sunga kayan?" Safwa tace "a'a har na taho basu gani ba gaskiya,sai dai in yanzu bayan na baro gidan" Umma tace "ai an yiwa Khalidah kaya,tunda nake ban taɓa ganin lefe kamar nata ba.. Allah yasa mu a danshinsu" Safwa tace "ameen.. Wallahi ko ni ban taɓa ganin irin kayanta ba" Umma tace "dama ina za kiga haka idan ba gurin irinsu ba,ai shi yasa nake so ki fito a bikin nan,ke da gani kin san baza'a yi harkar ƙaranta ba,bikin manya sai manya.. Idan Allah ya taimakemu sai kiga addu'armu ya faɗa,kin samu miji a ƴan bikin nan,ɗan wani Commissioner ya ganki yace yana so" Safwa tai murmushi tace "Allah yasa" Umma tace "ameen.. Yawwa ni kuwa ina maganar telan naku? Ya yi magana ko har yanzu?" Safwa tace "Baniynah ta tura min number ɗinsa,yau zan yi masa magana naji yanda ake ciki" Umma tace "gara dai kiyi masa magana,ga dai biki na ta matsowa,banda sun ƙara sati ɗaya ya zama 3 weeks,da tuni yanzu saura 2 weeks" Safwa tace "ai kuwa bari na duba number ɗinsa nai masa magana" Umma tace "kiyi da jiki toh,ni na fi so na sallameki gaba ɗaya" Safwa tai ɗan murmushi kafin ta buɗe data ta fara duba number da Baniynah tai mata sending,ko saving bata tsaya tayi ba ta fara masa magana,da taga ba ya online ta bar masa offline messages sannan ta fita duba story ɗin mutanenta,status ɗin Baniynah da Muniba da sukai just now ya ja hankalinta,da sauri ta tafi dubawa,ganin lefen Khalidah ne yasa tai saving itama tai story da shi,nan samari suka fara tambayarta lefen waye? Ita kuma tana faɗa musu na yayarta ne,har da masu tambayar lokaci,duka tana faɗa musu weeks da suka rage,kafin kace me an fara tambayarta account details ana sa mata kuɗin anko,wani ihun datai sai da ya tsorata Umma da su Bilal da suka shigo,rawa Safwa ta tashi ta fara tiƙa a gaban mahaifiyarta da ƙannenta,Umma tace "ke lafiyarki lau kuwa?" Safwa da murna ta gama cikata tace "Umma barni na gama rawan zan baki labari" Umma ta saki baki tana kallonta,Awwal da ya shigo a ƙarshe ya zauna ya kalli Umma yace "ita kuma wannan lafiya take?" Umma ta taɓe baki tace "toh gata nan dai,na tambayeta ta ƙi ce min komai" dan kanta data gaji ta zauna tana haki da mayar da numfashi,tace "Umma albishirinki?" Umma tace "goro" Safwa ta buɗe mata alert da banki sukai mata ta miƙa mata tace "kinga" Umma ta gwalo ido ganin ajejjere an turo mata kuɗin da sukai making almost 200k+,tace "ke a ina kika samu kuɗi haka?" Safwa tace "wallahi story nayi fa kawai da lefen Yaa Khalidah,shi ne ake tamabyata biki za muyi nace ehh,daga tambayar account details na tura,sai alert nake ta ji wai na siya anko" Umma ta washe baki tace "ahh kya yi rawa ƴar nan,nima da da hali ai da na tayaki,Allah ya taimakemu kin samo kuɗin ɗinki da kwalliya" Safwa ta kwanta jikin Umma tace "wallahi komai ma sun isheni nayi" Umma tace "ahh ƙwarai kam,yanzu sai in samu in yiwa ƙannenki ɗikin fita bikin suma,tunda za suke dinner da ɗaurin aure,abu na gida ai bana barsu su fita kamar almaijai ba.." 


      

*WAZEER*



    Sam ka ganshi babu wani alamar dake nuna yana farin ciki da tafiyar nan da zai,tunda ya dawo masjid sallar jumu'ah ya shiga gida,bai kuma marmarin fita ko ina ba,sai da akai kiran la'asar ya fito ya tafi masallaci,ana idar da sallah kuma ya sake komawa gida,ranan sallah kawai ke fitar da shi har dare,wayarshi kuma gaba ɗaya tana off,sanda ya dai²ci lokacin shigowar Dad ya yi ya bar parlon ya wuce bedroom ɗinsa,bai son magana da kowa,kuma bai son zama tare da kowa,haka washe gari ma ya yini a gida. Ranar Sunday can da yamma ya kunna wayar,sai ga Mimi ta kirashi,ya ɗauka jikinsa a sanyaye kamar ba shi ba,suna gaisawa yayi shiru,Mimi tace "idan kana gida kazo ina son ganinka" da yake ya gaji da zaman kaɗaici da shiru yasa yace "toh Mimi" suna yin sallama,ko cikakken minti 5 bai ƙara a gidan ba ya fita ya wuce jambulo,yana yin parking ya sauko motar ya ƙarasa gaban entrance yai knocking,Mimi tasa me aikinsu ta buɗe ƙofar,ganin wanda yake tsaye yasa yarinyar komawa baya ta bashi hanya tana cewa "sannu da zuwa" bai kalleta ba ya shiga ciki da sallama a ciki²,Mimi dake zaune tana jiran zuwansa ta juyo tana sakin murmushi,ya ƙarasa tare da zama kusa da ita,yana kallonta idanunsa a narke kamar yana shirin yi mata kuka yace "ina yini?" Mimi tayi murmushi tace "lafiya lau,ya gida da su Daada?" Yace "suna lafiya" daga haka yai shiru yana juya wayarshi dake hannunsa,Mimi tace "kaje ka gaida Mama,she's upstairs" kallonta yayi kamar zai yi magana sai kuma ya fasa ya tashi ya wuce sama,Mimi ta tashi ta tafi kitchen,duk abubuwan da tayi masa da akasa cikin containers masu kyau,tasa aka fito da su parlour,bai jima ba ya sauko a ɗan hanzarce yana kallonta yace "Mimi zan tafi,Dad yana son ganina" a hankali tai masa murmushi tace "ok! Ga saƙonka nan,Allah ya tsare ya bada sa'a" yana kallon manyan square containers ɗin masu kyau,ya ɗan juyo kalleta yace "Mimi mene ne wannan?" Murmushi ta sake yi masa tace "na ka ne,za ka buƙacesu idan ka shiga camp" ya gyaɗa kansa yana kallonta wani sabon son mahaifiyarsa na huda zuciyarsa,yai ɗan bayyanannen murmushi yace "na gode Mimi,Allah ya saka da alkhairi" Mimi ta girgiza masa kai tace "هذا واجبي.." Ya sake yin ɗan murmushi saboda ya ji me tace,sannan ya sunkuya zai ɗauka,da sauri tace "bari akai maka mota" ya gyaɗa kansa yace "ok" househelp tasa ta ɗiba ta kai masa mota,suka fito tare ta rakashi har gurin motarsa,sai da ya buɗe ya shiga sannan ta ɗora masa ledar hannunta tace "and this is for u also.. Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya" buɗe baki yayi zai magana,ta juya ta bar gurin tana ƴar dariyar farin ciki tace "sai mun yi waya" ya ɗaga kai yana kallonta ya kasa cewa komai saboda mamaki,sai da ta shige ciki sannan yaiwa motar key ya bar gidan. Da ya iso gida ya tarar da Dad a parlour yana jiransa,bai iya sanar da shi komai game da mahaifiyarsa ba,ya zauna suka yi maganar da za suyi,Dad na kallonsa ya miƙa masa ledar sabon uniform ɗinsa biyu da yasa aka sake ɗinka masa,suna zaune kuma yai masa transfer kuɗi masu nauyi,sannan sukai sallama saboda ba lallai su haɗu ba da safen zai je Lagos,Wazeer yai masa godiya ya ɗauki kayan ya wuce bedroom ɗinsa. Da safe around 7am ya fito cikin shirinsa,kasancewar sun yi sallama da Dad tun asubah yasa ya wuce ɓangaren Daada,da sallama ya shigo ya zauna suka gaisa kafin yayi mata sallama,tayi masa addu'ar tsari sai ƴan abubuwan da baza'a rasa ba da tasa akai masa,ya amsa tare da yi mata godiya sannan ya fita gurin Abba,nasiha sosai Abba Waziri yai masa,yai masa addu'o'in kariya daga miyagu sannan yace "akwai driver a waje yana nan za su kaika,Allah ya bada sa'a yasa a dace" ya amsa da ameen sannan ya tashi yaja luggage ɗinsa,da ya fito garage sai da ya buɗe motarsa yasa aka fito da all abubuwan da Mimi ta bashi da bai manta da su ba,akasa booth ɗin babbar jeap ɗin Abba da za'a kaishi camp me ɗauke da lambar *WAZIRI 001*,sai kuma motar fadawa ɗaya da za su rakashi,sanda yai addu'ah kafin ya shiga mota,driver ya rufe ya shiga tare da bafade ɗaya ya tada mota suka bar unguwar Tudun wuzirci,suna hanya sukai waya da Mimi tai masa addu'ah sosai,tunda ya kashe wayar ya ajiye gefensa yai shiru yana tunanin yanda rayuwarsa zai kasance a inda babu wanda ya sani,sai tunanin yanda zai zauna gurin yake,da wasu irin mutane zai rayu,kusan tafiyar 1 hour suka iso close to Kusala Dam dake cikin Ƙaraye LGA,dai² NYSC Permanent Orientation Camp get driver yai horn,military da suke zaune wajen a ƙasan bishiya riƙe da bindigu suka taso ganin motar emirate ga fadawa kuma suna gani...






*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*


  _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'in magungunan gargajiya masu kyau da inganci_

  _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


*Infection*

  _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯*_


  _Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._

*****

*****






#Follow

#Comment 

#Vote

#Share fisabilillah!

#ASLI-SMASHER.