PART OF OUR DESTINY

Chapter 13

by @fatymasardauna

@fatymasardauna


*PART OF OUR DESTINY*


(Don't forgot to follow me on ArewaBooks @fatymasardauna)


*Free page*

*Chapter 13*


Dogon numfashi yaja, tare da sauk'e k'akk'arfar ajiyar zuciya, ahankali cikin rashin kuzarin daya samu kansa aciki, ya sake bud'e idanunsa, da niyar sake zura mata su, amma akasin hakan a wannan karon ido cikin ido sukayi, domin dama ba bacci take yi ba, wanda jin alamun mutum ya shigo ne yasa ta bud'e idanun nata.

Sassanyan numfashi ya fesar, tare da d'an k'alalo Murmushi ya d'aura akan kyakkyawar fuskar sa, ahankali ya nufo inda take kwancen, kana cikin sanyin murya yace.


"Ashe ba bacci kike yi ba, likimo kikayi kamar me bacci, so ya jikin naki?" 


Shiru tayi tana me tsura masa idanunta, batare da tace komai ba, wanda hakan yasa shi juyowa shima ya kalleta, da idanunsa wanda suka tilasta mata janye nata idanun, lokaci d'aya saiga hawaye sun biyo kan k'uncinta. 

Idanunsa ya d'an tsura mata na wasu y'an seconds, abayyane yake iya hango damuwar dake zuciyarta, wanda hakan yasa shi, d'an sunkuyowa, ahankali ya zauna akusa da k'afafunta, tare da jingina bayansa da wata y'ar k'aramar kujerar dake gaban Console, wanda akan console dinne Amma ta ajiye mata plate din, chicken penne Alfredo, da kuma wani karamin bowl wanda yake d'auke da Dynamite shrimp aciki, kallon plate din yayi, ahankali yana me kuma sake kallonta, dan baiga alaman taci abincin ba ko kad'an.


Hakan yasa shi gyara zama, atausashe yace.

"Har yanzu kina jin ciwo ajikin ki ne?"

Yayi mata tambayar yana me tsare ta da idanunsa, da suka sata sake duk'unk'une jikinta, ahankali ta d'aga masa kanta alaman "Eh."

Duk da kuwa bawai ciwon sosai take ji ba, saboda sanyata acikin ruwan d'umi da Amma keyi yana matukar rage mata pain din da take ji. 


"Okay tell me inane ke miki ciwo? nunamin sai na miki allura awajen ko zai daina ciwo."

Yayi maganan yana me juyowa sukayi facing juna.

Wanda hakan yasa da sauri ta zabura ta tashi, cike da tsoro ta fara girgiza masa kai, kana murya araunace cikin yanayin yarinta had'i da tsantsar shagwab'an daya zame mata jiki tace.


"Nifa banason allura, dan Allah Karka min."


"Da gaske?"

Ya tambaya.

"Eh."

Ta amsa tana me karyar da wuyanta gefe.


"Okay indai da gaske ne bakya son allura to kici abinci, idan ba haka ba kuma allura ya zama dole." 

Ya fad'a yana me jawo plate da bowl din abincin ya ajiye agabanta.

"Eat."

Kai ta girgiza, yayinda sabin hawayen da suka cika idanunta suka soma gangarowa, sunan 

"Khalty." 

Ta fad'a ahankali tana me yin raurau da idanunta. 


Wanda hakan yasa shi fesar da numfashi, anutse yace.

"Yau bata zo bane?"


Kai ta jinjina masa alaman "Eh" 


"Okay don't worry zata zo gobe in sha Allah, Amma sai in kina cin abinci, idan baki cin abinci ba zata zo ba."

Yayi maganan yana me sake matso da plate din abincin gabanta.

"Maza ci." 

Ya fad'a cikin kulawa, tare da komawa Dr.Emraan dinsa na asali.

Bisa dole ahankali bawai dan tana so ba, ta jefa hannunta acikin abincin, nasu wanda ita sam bawai ta saba cin irinsu bane, duk kallon wani iri takewa abincin, amma takan rasa dalilin tsoron yi masa musu, atunaninta ko tsananin tsoron alluran da take yi ne ya jawo mata hakan, abincin ta soma ci ahankali da hannayenta wanda ke rawa, saidai kamar ko yaushe bata wani ci sosai ba ta zare hannunta, idanunsa ya d'ago ya kalleta, da sauri ta girgiza masa kai alaman ta koshi.


Bottle din ruwa ya kawo mata tasha, tare da komawa ta duk'unk'une, kallonta yayi na d'an wasu sakanni kafun ahankali, cikin had'iyan abunda ke ransa, da danne tsananin ciwon dake fame zuciyarsa yace.


"Waye wanda ya miki fyad'e? zaki iya shaida ko gane fuskarsa?"


Jin tambayar tasa tayi tamkar dirar aradu acikin kunnuwanta, daya masifar har gitsa tunaninta, domin lokaci d'aya abubuwan da suka faru, suka fara dawo mata sabbi fil, kanta da lokaci d'aya ya soma Juyawa ta rik'e da k'arfi, lokaci d'aya kuma duk jikinta ya d'au tsuma.

Kalaman nasa ne suka soma yi mata kuwa acikin kunnuwanta, wanda hakan yasa agigice ta saki wani irin k'ara had'i da kukan da yasa Dr. Emraan d'in sunkuyowa kanta da sauri, murya araunace yace.


"Is Okay Yacine, is okay karkiyi kuka please." 

Ya fad'a yana me d'aura hannunsa dake karkarwa akan nata hannun, kana cikin wata irin dak'usashshiyar muryarsa da ta disa she, cikin sigar lallashi yace. 


"I'm sorry bazan sake tambayar ki ba kinji".

Yayi maganar yana me had'e tafukan hannayensa da nata, da wani irin karfi ta fauce hannun nata tare da jan jikinta baya daga garesa, hannayen nata duka tasa ta k'ank'ame jikin ta.


Wanda hakan yayi daidai da shigowar Aamma, wacce ta turo k'ofar d'akin ahankali ta shigo, saidai ganinsu a haka da tayi ya sata k'arasowa da sauri kasancewar tun kafun ta k'araso take jiyo kukan Yacine din.


Tana k'arasowa ta kamo hannun Yacine din.

"Meya faru? Me kayi mata Emraan, Meye kuma ya sake sata kuka?"

Tayi tambayar tana me tsare Emraan din da ido, saboda ganin yanda ya kasa d'ago idanunsa ya kalleta.

Sai kansa kawai daya girgiza, batare daya ce komai ba kuma ya mik'e cikin sanyin jiki ya fice daga cikin d'akin.

Wanda ganin hakan yasa Aamma jawo Yacine din jikinta ta rungume ta, tare da soma shafa mata bayan da yanayin rarrashi. 


Dr. Emraan kuwa yana fita direct bedroom dinsa ya wuce, duk da yanda yakejin kansa na matukar sarawa kuwa, haka ya daure ya rage kayan jikinsa, tare da fad'awa toilet yayi wanka, koda ya fito black jallabiya ya sanya, tare da tada sallan isha, kasancewar lokacin sallan ya shiga, sam bai jin zai iya zuwa masallaci, hakan yasa shi yin sallarsa agida.

Yana idarwa kuwa ya lumshe idanunsa tare da jingina bayansa ajikin drawer, sakamakon wani irin sarawa da yake ji kansa nayi.

Ahankali ya fesar da sassanyan numfashi, had'i da bud'e rinannun idanunsa da sukai ja, suke kuma bayyana wani irin ruwa daya kwanta acikin su.

Y'an yatsun hannunsa da suka rik'e nata hannun ya tsurawa ido baya ko k'yaftawa, yayinda zuciyarsa ke raya masa abubuwa da yawa.

Sam bai tab'a tunanin haka rayuwar zata sauya masa da wurwuri ba, bai tab'a zaton zai samu kansa acikin k'aton rauni irin haka ba, a karon farko kenan a duk rayuwarsa da ya fara jin ciwon, wannan tabon me muni da wahalar gogewa dake d'awainiya da rayuwarsa, ada yana tunanin zai iya ci gaba da rayuwa a haka, cike da aminta da k'addararsa, amma sai gashi ayanzu zuciyarsa tana son kaisa inda bai cancanta ba, k'warai mutum kamar shi bai cancanta da wannan yanayin ba, ba kuma ya fata hakan ya zamanto sabuwar k'addarar rayuwarsa.

Hak'ik'a da ace yana da dama daya dakatar da zuciyarsa daga abunda take kokarin kamuwa dashi, wanda yafi yi masa kama da matsanancin SO.

Idanunsa ya sake lumshewa akaro na biyu, yana me nazartar tsananin duhun da yake gani acikin idanun nasa, wanda yana da tabbacin cewa duhun dake cikin rayuwarsa tafi wannan tsanani.


Yayinda acan k'asan parlorn nasu kuwa, Fad'ime ne zaune a gaban Ammabuwa ta tura baki, cikin rashin isashshiyar tarbiyar da suka samu tace.


"Wai ni Ammabuwa me kike nufi ne, kince muzo zai zab'i d'aya acikin mu, amma fa ko kallon kirki bai mana ba, ki duba fa kiga kalan kallon daya min, kamar wanda bata hadu ba, bayan kuma kowa yasan ina da kyau, yanzu kenan munyi zuwan banza, babu wacce zai aura acikin mu."


"Yama isa, ai dolen sa ne ya auri d'aya daga cikin ku, ai indai aure zaiyi to dole bazai wuce ku ba, yo dama ba budurwa ne dashi ba, ke dai ki barni dashi, yanzu sai na fara sawa anyi masa maganin Aljanar da ta auresa tukun kafun mu samu kanshi, dan bana raba dayan biyu Aljana ce ta aure shi."


"Aljana kuma? taya aljana zata auri mutum?" 

Hanayi ta tambaya cike da mamaki.


"Ta yanda akeyi, idan ba Aljana ba ku kuntab'a kallon inda mutum yakai shekara 34 zuwa 35 ba aure? ace dai lafiyarsa lau, kuma baya y'an biye biyen mata, sannan baya shiga sha'anin mata, yana kuma da cikakkiyar lafiya, da rufin asirin Allah, to indai kuka ga baya shiga sha'anin mata aljanace ta aure shi, shi yasa nake da tabbacin akwai aljanar da ta aure shi shima, kuma ko y'ar sarkin aljanu ce saita fita daga jikinsa." 

Ammabuwan ta fad'a tana me sake mimmik'e k'afafunta, tare da duban Fad'ime dake zaune, alama tayi mata akan ta matsa mata k'afafun. 


Kai Fadimen ta girgiza, cikin halin ko in kula tace.

"Gaskiya bazan iya ba, chat zanyi da kawayena na school, hakanan kawai ke ba dama azo inda kike sai kice a matsa miki k'afa."


"Eyyeee uwar marassa kunya, da shegen jan fuska kamar kose, to karki matsa min k'afafun, wallahi kya nemi me aurenki badai Jikana Bikir ba."

Ta fad'a tana sakin k'wafa.

Wanda jin hakan yasa da sauri Fad'ime ta cafki k'afafun nata ta soma matsawa, tana mulun mulun da baki.

Yayinda acan sama kuwa, da k'yar da rarrashi Aamma ta lallab'i Yacine ta daina kukan, saidai duk da haka bata daina sakin sheshshek'a ba.


A tausashe Aamma'n tace.

"Ko wani bawa da irin k'addararsa arayuwa Yacine, duk da nasan har yanzu ke yarinya ce, amma tabbas kinajin ciwon abunda ya faru dake, saidai nasan kinsan babu wanda ya isa sauya k'addararsa, abunda Allah ya tsara ako yaushe shi yake faruwa, sau dayawa abubuwan rashin dad'i na faruwa damu, amma mukanyi hakuri domin Ubangijin da yasa hakan ya faru yafi kowa iya tsari, koda munajin kuka mukan had'iye domin bamuso Ubangiji yaga kamar mun butulce masa mun kasa hakuri, tun ina k'aramar yarinya mahaifiyata ke nusar dani zama jajirtacciyar mace, strong woman, tayanda ba komai ne idan ya faru dani, zan yi saurin karaya ba, domin ako yaushe zama jajirtacce me tsananin juriya shine matakin nasara, nasarar da idan ka cimma kowa sai ya sani a duniya, abu d'aya dake jagoran fad'uwar rayuwa kuwa shine sarewa akan komai, cire rai tare da janye fata da burikan ka, saboda wani nakasu ko mummunar k'addara da ta shigo cikin rayuwar ka, rayuwa na d'auke mana da abubuwa da yawa Yacine, acikinsu akwai abu biyu, shine nasara da kuma fad'uwa, amma saidai koda mun fad'i kada mu tab'a sarewa, never give up, kada mubar wani abu marar dad'i ya b'ata mana kyawawan mafarkan mu, akullum kina tuna cewa kafun ke an b'ata rayuwar wasu y'an matan da yawa, shin kina so ki zamo mace me juriya had'i da cimma mafarkanta na rayuwa?" 


Kanta ta d'ago akaron farko ta kalli Aamman tare da jinjina mata kai alaman "Eh."


Hannunta Aamman ta rik'o, cike da k'arfafawa tace.


"Ki d'auke ni amatsayin Uwa mahaifiya, ki d'auke ni amatsayin uwar da kikasani tunda jimawa, nasani Yacine fyad'e wani abune me ciwon dake ruguza rayuwa da b'ata goben y'a mace, akwai tsananin ciwo, amma saidai zaki iya shanye wannan ciwon, za kuma ki iya gina gobenki me kyau, zan saki a makaranta, sannan zan kasance dake amatsayin uwa akoda yaushe, amma sai kinyimin alkawarin bazaki sake yin kuka ba, za kuma ki zauna atare dani, Yacine ina jinki tamkar y'ar da na haifa aciki na, ina ji ina kuma da tabbacin zamanki atare damu zai inganta rayuwar ki, ki zamo y'a agareni Yacine ni kuma zan baki kyakkyawar rayuwa."

Aamman ta k'are maganar cikin tausasawar, da yasa Yacine d'in k'ank'ame ta sosai tare da fashewa da sabon kuka me tsuma zuciyar me sauraro.

Kuka take sosai ahankali Aamma ke shafa bayanta, har na tsawon wasu mintuna suna ahaka, kafun d'aga bisani Aamman ta soma jiyo sauk'an k'akk'arfan ajiyar zuciyar Yacine din, wanda hakan ke tabbatar mata da cewa bacci ne ya d'auke ta.

Gyara mata kwanciya Aamman tayi, tare da rufe ta da tattausan blanket.

Fuskarta da tayi cab'a cab'a da hawaye Amman ta tsurawa ido, saidai acikin zuciyarta ta kasa tantance me takeji adangane da yarinyar.


Idanunta ta lumshe ahankali, tare da jan dogon numfashi, daidai lokacin wayarta dake kan bedside ta soma ringing.


Saidai kasancewar bata tsammanin kira daga wajen kowa, wannan yasa akasalance ta jawo wayar, numbern dake yawo akan screen din wayar nata ta tsurawa ido, domin bak'uwar number ce da ba'a tab'a kiranta dashi ba, 10 digits ne numbers din, wanda farkonsu ya fara da +33, hakan yasa ta gane cewa number'n k'asar France ne, ahankali ta kara wayar akan kunnenta, batare da tayi magana ba.

Daga inda aka kiratan ma shiru akayi ba ayi magana ba har na tsawon minti d'aya, ba wanda yayi magana, jin hakanne yasa Aamman lumshe idanunta, asanyaye da wani irin matsanancin rauni tace.


"Ka kira ne kawai saboda kayi shiru, ko kuma ka kirane saboda kaji kalan tarin damuwan da nake ciki, saboda idan kaji hakan zaka ji dad'i?"


Daga can inda yake kwance ya lumshe kyawawan idanunsa, tare da gyara zaman kansa akan pillow'n da yayi matashin kai dashi.

Cikin sihirtacciyar muryarsa, wacce ko yaushe take fita cikin wani irin sound na musamman, can k'asan mak'oshinsa, ya had'a kalmomin sannan ya furtasu. 


"I'm missing you Aamma."


Wani irin hawaye ne taji sun taru acikin idanunta, amma saita shanye tare da maye gurbinsu da murmushi, saidai batare da ta bari ya fahimci hakan ba, murya acushe tace.


"Idan kayi kewata zaka so kazo ka ganni, amma tsawon shekaru 4 kenan yanzu ban saka a idanuna ba, ka manta dani TAREEQ ka manta da mahaifiyar da ta haifeka, ka zab'i kalar rayuwar da kake so, kayi nesa damu, shikenan kaje ka ci gaba da zama acan, idan na mutu sai kazo kaga gawata."


Tana gama fad'in hakan ta kashe wayan, tana me share hawayen da suka gangaro daga cikin idanunta, na tsananin kewarsa da tayi.


Yayinda ab'angaren sa kuwa jin ta kashe wayanne yasa shi, zare wayan daga kunnensa, cikin yanayi na kasalan daya san yashi lumshe idanunsa, Ariana dake kwance ajikinsa kuwa idanu ta zuba masa, idanunta da sukayi jajur alaman kuka tayi, kallon tsananin so me zafi dake gauraye da zallan sha'awa ta keyi masa, cike da muradi da fatan kasancewa dashi ako yaushe.

Aduniya ba zata iya bin wani namiji ba bayan shi, domin yana da Qualities din da maza da yawa basu dashi, shi d'in Namiji ne cikakke daya tara abubuwa da yawa.

Bakinta dake manne akan fatar saman mararsa ta bud'e tare da zaro tongue dinta, ahankali ta soma lasan fatar cikinsa.

Yana jin duk abunda take yi masa amma bai daina abunda yake yi ba, har saida ya gama kafun ya sanya hannunsa ya jawo ta kusa dashi, idanunsa ya zuba mata tare da soma zagaye round face dinta da hannunsa, har zuwa kan kirjinta, atsakiyar space din dake kirjin nata ya tsaida yatsun hannun nasa yana meyi mata wani irin abu daya gigita tunaninta, cikin sauri ta kama hannun nasa ta d'aura akan breast d'inta

"Suck."

Ta fad'a cikin lumshewar ido. 


Yayinda awajen Aamma kuwa tunda ta kashe kiran nasa, numbern daya kirata dashi din ta tsurawa ido, ana cikin hakan taji k'aran shigowar sak'o, saurin duba message din tayi, saboda ganin da numbern daya kirata dashi aka turo text din.


"Ina dawowa nan da kwana biyu."


 Wannan shine abunda aka rubuta acikin sak'on, wanda hakan yasanya zuciyarta yin wani irin sanyi, take fari'a ya bayyana akan fuskarta, tsawon shekaru tayi tana jiran wannan ranan, hakan yasa ta mik'ewa, bayan ta sake gyarawa Yacine kwanciyarta, wacce take ta sharar bacci, kaitsaye ta fice daga cikin d'akin, tana fitowa daga bedroom din nata kuwa, direct side d'in su Emraan din ta wuce, tura k'ofar parlorn nasu tayi a hankali, kamar yanda ta tsammata kuwa ba kowa aciki, saboda dama tasan Emraan bai iya zaman parlor ba.


D'akin dake can gefe dana Emraan din ta nufa, tana zuwa ta sanya key din dake hannunta ta bud'e k'ofar d'akin, ahankali ta murd'a handle din k'ofar tare da tura kanta ciki, wani irin k'akk'arfan k'amshine ya bugi hancinta, alokacin da tasa kanta acikin, tabkeken bedroom din, da yaji white Turkish furniture masu tsananin kyau da d'aukar ido, komai dake cikin d'akin white ne, kama daga bed, drawer, bedsides, har zuwa kan beautiful plain cutton din da suka sake k'awata d'akin, yayinda atsakiyar d'akin aka shumfud'e wani kyakkyawan Turkish carpet, me kalan grey, wanda girmansa ya kusan cika dakin.

Ba wani tarkace ne me yawa acikin d'akin ba, saidai amma duk da haka yayi kyau sosai, domin an k'awatasa da abubuwa masu tsada da Qualities na gaske, ciki kuwa harda zanen hoton wani kyakkyawan doki, wanda aka k'awatasa sosai, dake kafe ajikin bango, wanda da gani kasan kud'ad'e masu tarin yawa akasa wajen sayen sa. 

Komai dake cikin d'akin very neat, ta yanda bazaka tab'a cewa mamallakin d'akin ya shafe shekaru baya nan ba, kasancewar duk bayan 2 days Aamma nasa meyi musu share share na shiga tana sharewa, shiyasa babu wani abu na datti acikin d'akin. 

Ajiyar zuciya ta sauk'e bayan ta gama k'arewa d'akin kallo, tare da bud'e had'add'en toilet din dake cikin d'akin, komai yana nan tsab tsab, amma saidai duk da haka gobe zata sa asake gyara d'akin, domin tafi kowa sanin cewa mamallakin d'akin sam bayason k'azanta ko kad'an.


Jawo k'ofar d'akin tayi ta rufe ahankali, har ta juya zata tafi kuma, saita dawo da kallonta ga d'akin Dr. Emraan, k'ofar d'akin ta zubawa ido na d'an wani lokaci kamar me nazartar wani abu, ahankali ta k'arasa jikin k'ofar tare da soma knocking door din.


Knocking tayi har sau 3 amma ba amsa, gashi kuma tana hango wutar d'akin a kunne, wannan yasa ta murd'a handle din k'ofar, bakinta d'auke da sallama ta kutsa kanta ciki. 

Kwance ta hangosa akan lallausan sallayan da yayi sallah, yayi matashin kai da hannunsa na dama, bayan ya duk'unk'une jikinsa da alama bacci yake yi.


"Emraan!"

Ta kira sunanshi ahankali cike da mamakin ganinsa kwance ak'asa da tayi, saidai jin shiru bai amsata ba yasa ta k'arasowa dab dashi ta lek'a kyakkyawar fuskarsa, idanunsa a lumshe suke kirib, yayinda ahankali yake sauke numfashi alaman cewar bacci ya jima da d'aukarsa.

Murmushi tayi tare da d'an rank'wafowa hannunta tasa ta shafa lallausan sumar kansa.


A tausashe tace.

"Duk girman bed dinka ka rasa inda zaka kwanta kayi bacci sai a k'asa, wato gajiya ba dad'i ko."


Tayi maganar tana me jawo had'add'en blanket din dake gefen gadon nasa ta rufa masa, tare da sanya masa pillow madadin hannunsa daya kwanta akai.

Idanunta ta zuba masa na d'an wasu mintuna, aranta take raya cewar kodan irin wannan ya kamata ace yayi aure, ayanzu shiba yaro bane dole yana buk'atar tsayayyar macen da zata kula da rayuwarsa sosai, yana buk'atar wacce zata kula da ci shansa da kuma baccin sa, aduk rayuwarta burinta shine taga y'ay'an nata acikin farinciki, amma when? sai yaushe hakan zata kasance? 

Ayanda ta lura dashi tsoron mata yake, domin sam bayason wata mu'amala ta had'a shi da mace, aduk rayuwarta bata tab'a jin yayi koda maganar wata mace ba, saidai a yau ta hango wani killataccen abu acikin k'wayar idanunsa alokacin da yake zaune a gaban Yacine, duk da ya kaucewa had'a idanu da ita, amma ta riga taga abunda yake gudun ta gani. 


Wani tunani zuciyarta ke bata daban, duk da tanaji kamar akaron farko hasashenta ya sab'awa tunaninta.

Ajiyar zuciya ta sauk'e tare da mik'ewa daga durk'ushen da take, wutan d'akin ta sauya masa izuwa na bacci, ahankali kuma cikin gudun kada ta tashe sa daga baccin da yake din, ta fice daga d'akin tare da jawo masa k'ofar ta rufe. 


Jin alamun fitanta yasa shi bud'e idanunsa da sukai jajur tamkar garwashin wuta, numfashi me zafin gaske ya fesar, tare da sake gyara kwanciyarsa, domin dama bawai bacci yake yi ba, yayi hakanne kawai dan bayaso Aamman nasa ta fahimci wani abu daga cikin damuwarsa, domin idan har ta gane bazai iya yi mata explanation ba.

Taya ma zai iya fara yi mata bayani, akan abun da shi kansa baisan menene gaskiyarsa ba, abu d'aya kawai zai iya tantancewa, shine yana jin kansa a wani mataki na daban, dake k'ara masa fad'uwar gaba had'i da fargaba me tsanani. 


Sai a yanzu yake jin cewa inama da za'a ce duka rayuwar da yake yi d'in mafarki ne, bawai gaske ba, ina ma da ace akwai wani abu najin dad'in rayuwa da zai iya samu koda kad'anne anan gaba.

Idanun nasa ya kuma lumshewa cike da karayar sanin cewa bazai tab'a samun abunda yake so ba, duk da kuwa yana jin yanayi na musamman acikin zuciyarsa, saidai yasan hakan bazai amfanesa da komai ba.

Haka da tunani kala kala acikin zuciyarsa bacci ya d'auke sa, bayan ya shafe tsawon lokaci yana juyi akan darduman sallan nasa. 


Saidai har acikin baccin zuciyarsa bata huta ba, domin wani irin bacci yayi me kama da zahiri, kasancewar duk yanda ya juya, kukan Yacine dinne kawai keyi masa yawo acikin kansa, kamar yanda hoton zanen fuskarta yak'i washewa daga cikin idanunsa. 

Kamar kuwa yanda yayi kwanan rashin dad'i haka itama Yacine d'in, kwana tayi tana b'ari saboda mafarkan da take yi marassa dadi.


Washegari.

Friday tun da sanyin safiya Aamma ta tashe ta tare da taimaka mata tayi wanka, d'aya daga cikin kayan da Dr. Emraan din ya sayo mata ta bata ta sanya, Yasmine Abaya ne me ratsin fari da b'aki, sosai rigar tayi mata kyau musamman ma da ta yane kanta da mayafin abayar daya kasance bak'i, sai hasken fatar ta ya sake bayyana, parlor suka fito ita da Aamman, wanda already ta gama shirya musu breakfast, akan d'aya daga cikin kujerun dinning table din ta zauna ad'ad'are kamar yanda Aamman ta buk'ata.

Tana zama kuwa Abbou na shigowa falon, duk da bata tab'a ganinsa ba, amma tana ganinsa taji ajikinta cewa shine me gidan, wannan yasa ta rusunawa tare da durk'usawa har k'asa ta gaishe shi.


Murmushi Abboun yayi had'i da amsa mata cikin sakin fuska, domin shima sai alokacin ya fara ganinta.


Tambayarta jikinta yayi ahankali tace.


"Da sauki." 

Daidai lokacin Dr. Emraan ya sauk'o daga sama, cikin shigar white Kaftan me ratsin blue, da tayi masa matuk'ar kyau tare da bayyana tsananin kwarjininsa.

Rik'e yake da y'ar k'aramar briefcase dinsa, kaitsaye ya nufo dinning area din.


Saidai tun kafun ya k'araso daddad'an k'amshin turarensa na companyn Louis Vuitton (OMBRE NOMADE) da kuma (OUD ISPAHAN) na companyn Christian Dior, suka cika hancin su, wanda hakan yasa duk suka juyo suna kallonsa, saidai ab'angarenta duk da taji k'amshin amma ta kasa d'agowa ta kalli ko waye.

Jin muryarsa yana gaisawa da Abbou da kuma Aamma dake saving d'insu, yasa ta d'agowa ahankali da idanunta wanda sukayi raurau ta kalleshi.


"Ina kwana."

Ta fad'a cikin rawar muryar, da yasa shi d'ago nasa idanun shima ya kalleta, ido cikin ido sukayi, hakan yasa tayi k'asa da nata idanun.


Yayinda shi kuwa kasa d'auke idanunsa akanta yayi, cike da mamakin yanda ta sauya masa lokaci d'aya.

Idanun nasa ya d'an lumshe, ahankali ya amsa mata da. 

"Lafiya ya jikin ki?"

Ya ida maganar yana mejan d'aya daga cikin kujerun dining table din ya zauna.


"Alhamdulillah..."

Ta fad'a can k'asan mak'oshi, tare da k'ara takure jikinta, domin ganinta acikinsu yasa duk tana jin kanta wani iri.

Abincin da Aamman ta zuba mata ta zurawa ido, tana kallo, yayinda shi kuwa ya zura mata nasa idanun, har na tsawon wani mintuna kafun ahankali ya d'ago hannunsa ya d'aura akan..



#fatymasardauna