MAJNOON

Chapter 3

by @fatymasardauna

*MAJNOON!!*

       (The innocentmad)


*Writting By*

Fatymasardauna 

Wattpad 

@fatymasardauna


*Freepage*

         *Chapter 3*


Idanu Dr. Mouhammad ya tsurawa screen din wayar nasa dake ta faman ruri, tamkar me nazartar wani abu.

Duk da cewar yasan Billonaire DAWOUD Saraki. Bazai kirasa haka kawai ba, lallai dole saida wani abu.

Amma yana tsoron ace masa jikin MAJEED ne ya sake tashi. 


Hannunsa ya mik'a da niyar d'aukar wayar, saidai kafun yakai ga d'auka, kiran ya katse. 


D'an Jim yayi yana me tunanin bin kiran, saidai sanin da yayi cewar mai kiran nasa, zai sake kira ne yasa shi sauke ajiyar zuciya, tare da fesar da numfashi.

Anutse ya koma kan kujera ya zauna. 

Yana me tunani acikin zuciyarsa, ta yanda zai sake fuskantar matsalar MAJEED. 


Idanunsa da suka dan kawo ruwa, ya lumshe saboda tunowa da wasu abubuwa da yayi. 


 

Acan waje b'angaren su Soumaya kuwa har yanzu babu wani wanda yayi kyakkyawan motsi, daga cikinsu haka kuma babu wani wanda yake cikin yanayi mai dad'i.

Sai Moudou wacce ta k'osa da komawarta gida, saboda duk tagaji da zaman asibitin, gashi kuma har yanzu basu san awani Hali Abboun yake ciki ba.


"Idan ya mutu ne ai sai sufito suce ya mutu."


Ta fad'i haka acikin ranta tana mejan tsaki kasa kasa, tare da wurgawa Soumaya harara, wacce ta cusa kanta acikin tsakankanin cinyoyinta.


Gaba d'aya jin duniyar takeyi babu dad'i, acikin zuciyarta kuwa, ak'agare take da sanin halin da mahaifinta ke ciki. 


K'aran sautin takun takalmin da taji acikin kunnuwanta ne, yasa ta d'ago kanta, tare da kallon inda takejin sautin takun, da kumburarrun idanunta. 


Ganin Doctor'n d'azu da tayi yana kokarin k'arasowa garesu ne, yasa ta zuba masa ido, domin hakanan taji zuciyarta na bugawa tamkar zata faso kirjinta ta fito.

Bata fatan jin wani mummunan labari daga bakinsa.

Dan tayi imani cewa jin hakan zai iya sa zuciyarta tarwatse wa. 


Ganin da tayi har ya kusa k'arasowa garesu ne kuma, yasa ta sanya hannu ta d'an dafe kirjinta, tare da rumtse idanunta.

Saboda batason ji da ganin wani mummunan abu. 


"Likita ya ake ciki dai, kodai har yanzu bai farfad'o bane? Ko kuma ya rasu ne kuke b'oyewa?"


Moudou ta jefowa likitan tambayar, da yasa zuciyar Soumaya rugurgujewa, sannan yasa jinin jikinta daskarewa.

Saboda tambayar da Moudou'n tayi ne kuma, yasa bisa dole ta ware idanunta tana kallon likitan, zuciyarta cike da fargaban amsar da zai bawa Moudou'n.


Dr. Hafiz wanda shima yana d'aya daga cikin manyan Doctors din dake cikin asibitin, kallon Moudou yayi cike da mamakin irin tambayar da tayi masa.

Saidai kuma rashin sanin wace ce ita awajen marar lafiyan, yasa shi kawar da mamakinsa, kamar kuma yanda yakasance acikin tsarinsu akwai iya tausasa harshe, da kuma samawa mutane nutsuwa hakan yasa shi, girgiza kai kana cikin kulawa yace.


"Calm down patient dinku zai samu lafiya Insha Allah, domin munyi nasarar ceto numfashinsa, sauran bayani kuma zakuji shi ne daga bakin, Dr. Mouhammad, zaku iya zuwa ku sameshi a office yanzu."


Ya kai karshen maganan yana me nuna musu, hanyar office din Dr. Mouhammad Boulama.


K'akk'arfar ajiyar zuciya mai tafiya da k'warin guiwa, da kuma sanyin zuciya Soumaya ta sauk'e.

ahankali kuma siraran hawaye masu sanyi suka Zubo daga cikin idanunta. 


"Alhamdulillah Allah Mungode ma, yanzu kenan DR. zamu iya zuwa mu ganshi?" 


Ta fad'a cikin farincikin daya kasa b'uya akan fuskarta, dan sai takejin tamkar Doctorn cewa yayi Abboun nata ya warke.


Idanu Dr. Hafiz ya zubawa matashiyar yarinyar, da ya hangi abubuwa da yawa atarrare da ita, tabbas ganin farincikinta, yasa shi jin damuwa acikin zuciyarsa, saboda cutar da yasan yana damun mahaifin nata, kwata kwata baisan ya zasu d'auki abun ba. 

Amma gudun kada ya karya mata lagon confidence din daya gani akan fuskarta, yasa shi bayyana murmushi akan nasa fuskarsa, atausashe kuma cikin kulawa yace.


"Don't worry Zaku ganshi amma ba yanzu ba, ki kwantar da hankalinki kinji, yanzu ku fara zuwa wajen Dr. Mouhammad tukunna, dan yace yana buk'atar ganinku." 


Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, najin dadin abunda Doctor'n ya fad'a mata, dan haka cikin fatan samun kyakkyawan labari ta mik'e tsaye.

 Dan tuni Malam Musbahu da Moudou sun jima da mikewa. 


Dr. Hafiz kuwa shi yayi musu jagora, har zuwa dan corridor din dake gaban office na Dr. Mouhammad din. 


Shida kansa ya shige musu gaba, tare dasa hannu ya soma knocking k'ofar office d'in. 


"Yes come in."

Daga ciki Dr. Mouhammad ya amsa yana me gyara zamansa, tare da d'auko wani file dake gefensa ya soma dubawa. 


Jin anbada izinin shigowa ne kuma yasa Dr. Hafiz ya Bud'e musu kofar, tare dayi musu nuni da hannu alaman su shiga. 


Malam Musbahu ne akan gaba, sai kuma Moudou yayinda Soumaya dake bayansu, duk taji jikinta yayi sanyi, hakanan lokaci daya duk yanayinta ya sanja.

Da k'arfi k'arfi takejin kirjinta na bugawa, sab'anin farincikin da taji a y'an mintunonin da suka wuce, fad'uwar gaba ne ya maye gurbin kowanne dakika na bugun zuciyarta. 


 

Dr. Mouhammad ne ya amsa sallamar da Mallam Musbahu yayi, tare da nuna musu wajen zama.


Kan d'aya daga cikin kujerun dake gaban Dr. Mouhammad din, Malam Musbahu ya zauna, haka ma Moudou wacce take ta faman raba idanu, tana karewa tankamemen office din kallo. 


Soumaya kuwa da ita tayi na k'arshen shigowa, abayan Malam Musbahu dake gaisawa da Dr. Muhammad ta tsaya, tare da sunkuyar da kanta k'asa. 

Aranta take amabaton sunan Allah'n da shi yasanya mata, Rauni mai tsanani acikin zuciyarta. 


Dr Mouhammad kuwa

File din dake gabansa ya karasa cikewa, kafun ya d'ago kansa ya kallesu. 


Gyara zaman siririn farin Glass din dake saman idanunsa yayi, kana anutse kuma cikin kulawa yace.


"Acikinku waye shak'ik'i ko Kuma mafi kusa da marar lafiyar?."


Shiru duk sukayi, sai Malam Musbahu wanda duk damuwa ta bayyyana akan fuskarsa ne yace.


"Dukanmu shak'ik'aine agaresa, domin ni nakasance amini ne agaresa, sannan wannan matarsa ce, wannan dake bayana kuma y'arsa ce ta jini, ita kad'ai ya mallaka."


Ya kare maganan yana me nuna Soumaya dake tsaye ta sadda kanta k'asa.


Wanda kuma sai alokacin ne Dr. Mouhammad ya lura da ita, ido ya zubawa yarinyar sosai tamkar mai nazartar wani abu adangane da ita,

Kana daga bisani ya dawo da kallonsa ga Malam Musbahu'n 


Kallon Malam Musbahun yayi na y'an wasu sakanni, kafun daga bisani ya maida kansa ga duba wani file dake gabansa.

Hakan ko shi yasanya zuciyar malam Musbahu karyewa.

Asanyaye cikin fargaba yace.


"Lafiya kuwa Likita, kodai wani mummunan abu ya faru ne?."


Kai Dr. Mouhammad ya girgiza, tare da zare glass din dake idanunsa.


Cikin sassauta murya ta yanda yasan zasu fahimcesa yace.


"Kamar yanda kuka sani kowani bawa yana da irin nasa k'addarar, Allah keda ciwo sannan shike da magani, babu kuma wata cuta aduniya, da bata da magani amma kuma nayi mamaki kwarai ta yanda kuka bari ciwo yayi worst ajikinsa sosai, domin ayanzu yakai wani stage da shawo kan matsalan abune mai matuk'ar wahala...."


D'an Jim yayi tare da soma kallonsu d'aya bayan d'aya, wannan dalilin yasa Soumaya dake tsaye zuba masa ido. 

Zuciyarta cike da fargaban sauran abunda zai fito daga bakinsa. 


Haka shima Malam Musbahu cikin tashin hankali yake kallon Dr. Mouhammad din, duk da cewar yasan hakikanin zancen, amma yana tsoron abunda zaije yazo. 


"Likita kayi shiru meke damunsa ne, wai kodai mun rasa shi ne kuke boyewa?"

Moudou ta jefo masa tambayar, saboda duk ta k'agara dason jin abunda ke damun Abboun. 


Kai Dr. Mouhammad ya girgiza hade da gyara zamansa yace.


"Ko d'aya bai mutu ba, har yanzu yana numfashi, amma saidai cutar dake damunshi zata iya zama sanadiyar rasa shi acikin lokaci kad'an, matukar akayi wasa to tabbas za'a rasa rayuwarsa, saboda yana d'auke da cutar nanne ta BRAIN CANCER, wato Cancer'n kwakwalwa!!"


Hakika Maganansa daidai yake da saukan aradu, acikin kunnuwan Soumaya, haka kuma maganar sa daidai take da tsayawar bugun zuciyarta na y'an wasu sakanni.


Saurin fusgo numfashinta dake kokarin kwacewa zuciyarta tayi, ta hanyar furta kalman.

"Innalillahi Wa Inna Ilaihirraju'un!!!"

da sauri, saurin dake tafiya da gudun bugun zuciyarta. 


"Likita Cancer'n kwakwalwa fa kace?"


Moudou da tasa hannu ta dafe kirji, ta sake tambaya tare da zazzaro idanunta waje. 


Malam Musbahu kuwa hannu yasa ya soma share gumin dake tsatsafo masa, dan duk da cewar yasan tuntuni ABBOU'n na d'auke da cutar Cancer, amma baiyi tunanin abun zai iya kawosu ga haka ba. 


Soumaya kuwa kai ta soma girgizawa, yayinda acikin sakanni kad'an wasu sabin hawaye suka b'alle daga cikin idanunta. 

Hakanan takejin tamkar k'arya kunnuwanta sukayi mata, wannan dalilin yasa.

Araunace ta matso kusa da kujerar Dr. Mouhammad, tare da zubewa akan guiwowinta.

Cikin matsanancin damuwa hadi da sabon tashin hankalin da tasa mu kanta aciki, ta fa she da kuka mai tsuma zuciya.


Kukan da yasa Dr. Mouhammad dasu Malam Musbahu zuba mata idanu.


Ita kanta tsananin tausayin kanta takeji, saboda tasan cewa farinciki bazai cika mata ba, matukar babu mahaifinta, wannan dalilin yasa araunace, kana murya na rawa tace. 


"Kataimakeni Dr Bana da kowa aduniyar nan sai Abbouna, rayuwa bazata yiwu ba idan babu shi, banason rasa shi, dan Allah kayi wani abu Abbouna ya samu lafiya, ka taimakeni, kada kacemin Abbouna bazai tashi ba, kada kacemin bazai sake motsi ba..."


Maganan nata ya sark'e saboda matsanancin kukan daya kwace mata, sanin bazata iya sake cewa komai bane kuma, yasa ta had'e duka hannayenta biyu awaje d'aya, tana kuka mai Alamana roko, da neman taimako. 


Idanu Dr. Mouhammad ya zuba mata cike da tausayawa, dan yasan da ace tasan yanda ciwon mahaifin nata yayi worst, to da tayi kuka fiye da haka. 


Saidai yanda yaga tana yin kukan da duka karfinta ne, yasa shi sauk'e ajiyar zuciya, tare dayi mata alama akan ta tashi.

Then amatsayin sa na Babba kuma wanda yasan aikinsa, yasa murya atausashe yace.


"Stop crying tashi kinji ki daina kukan nan, Insha Allah he will be fine, bashi ne mutum na farko daya fara facing thesame issue ba, akwai mutane masu fama da brain cancer da yawa, kuma suna warkewa matukar akayi musu abunda ya dace, saboda haka ki daina kuka."


Ya kare maganan cikin lallashi, da kuma fatan daina kukan nata, saboda yasan yanda yawan kuka ke illa ga lafiya. 


Bazata tab'a iya daina kuka ba tasani, har abada way'annan idanun nata bazasu daina zubar da hawaye ba, matuk'ar cutar Cancer bata har jikin Abbounta ba, saboda kasancewar ta d'alibar likitan ci, yasa tasanin yanda Cancer ke cutar da duk wanda ta kama. 


"Yanzu Likita meye abunyi?"


Malam Musbahu ya tambaya, cikin matukar damuwa hadi da karyewar da zuciyarsa tayi.


"Babu damuwa insha Allah komai zaiyi daidai, saboda akwai gwajin da zamuyi mishi gobe, daga nan ne kuma zamu tantance abunda ya kamata, yanzu nasa akaishi d'aki na musamman saboda yana tsananin buk'atar kulawa, kasancewar baya iyayin numfashi da kansa, har saida muka sa mishi oxygen kafun nan, baya ga haka kuma akwai na'urorin da muka sa akansa, Wanda suke lura da brain din nasa, ahalin yanzu dai Hutu kawai shine abunda yake buk'ata."


Kai Malam Musbahu ya jinjina, kafun duk gaba d'ayansu sukayi shiru, saboda kowannensu da kalan irin abunda yake sak'awa acikin zuciyarsa. 


Saidai banda Soumaya wanda tunanin ta ya tsaya cak.


K'aran knocking din k'ofar Dr. Mouhammad din da akasoma yi, shine ya dawo da ita hayyacinta.


"Come in."

Dr Mouhammad dake zaune ya bada izinin shigowa.


Ahankali Nurse Estha dake knocking kofar ta bude ta shigo, hannunta rike da wani file.


K'arasowa wajen Dr. Mouhammad din tayi, arusune cikin kuma girmamawan da suka saba baiwa na sama dasu tace.

"Sir komai ya kammala munkai patient din dakin da kace." 


Kai kawai Dr. Mouhammad ya jinjina, 

tare da karban file din hannun nata ya ajiye.

Bayan ya mike tsaye ne kuma ya dawo da kallonsa garesu, murya atausashe yace.


"Zamu iya zuwa ku gansa yanzu, saidai kaman yanda na fad'a yana bukatar hutu, saboda haka dole acikinku zaku bar mutum d'aya wanda zai kwana dashi, domin yawan hayaniya zai iya causing masa wani sabon problem."


Ya kai k'arshen maganan yana me kokarin wucewa gaba, dan tuni dama ya mike tsaye daga zaunen da yake.


Ganin hakanne kuma yasa duk suka mik'e suma, suka rufa masa baya. 


Koda suka fito daga office din nasa,Kaitsaye wani dogon corridor wanda yake acikin part na musamman suka nufa.

Bayan sun d'anyi tafiya mai nisa ne kuma, suka iso wani babban falo, dake d'auke da wasu d'akuna, masu k'ofofi da windows na glass. 


Irin dai kofuna da windunan nan wanda kana daga waje zaka iya hango wanda yake kwance aciki. 


Hannu Dr. Mouhammad yasa ya bud'e d'aya daga cikin k'ofofin, wanda anan cikin dakin Abboun ke kwance.


Bud'ewar kofar kuwa yayi daidai da sauke idanunta akan Abboun da tayi. 


Cak kuwa ta tsaya da tafiyan da takeyi, yayinda atake, wasu irin hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanunta.

hawayen dake bayyana tausayi da kuma Rauni'n da yayi tasiri acikin zuciyarta. 


Idanu ta zuba masa, kasancewar daga inda take tsayen tana iya hango na'urorin da aka jona masa.


Hakan yasa taji sabon kuka na kokarin kwace mata, yayinda zuciyarta kuwa ke sake raunata. 


"Brain Cancer."

Ta maimaita sunan ciwon da Doctor'n ya shaida musu cewar Abboun na dashi.


Kanta ta shiga girgizawa tare da soma takowa ahankali harta k'araso gaban gadon da Abboun ke kwance. 


Tana isowa kuwa kanta ta kifa akan hannunsa, tare da fashewa da wani irin sabon kuka mai tsuma zuciya.


Shiru gaba d'aya d'akin ya d'auka, kowanne daga cikinsu yana sauraran sautin kukan ta. 


Yayinda Kowa da irin tunanin da yakeyi acikin zuciyarsa, saidai banda Dr. Mouhammad wanda tunanin nasa ya banbanta da nasu.


Domin jin kukan yarinyar wani abu yake tuna masa daban, haka kuma wani abu na daban ne ke yawo acikin tunaninsa. 

Duk da bashi da tabbaci amma yanaji ajikinsa cewar hakan dama ce Babba, damar da zata sauya rayukan mutane biyu, damar da zata juya baki izuwa fari, damar da zata maida baya izuwa gaba. 

Duk da yasan hakan abune mai wahala, ko kuma ace abune wanda bazai yiwu ba, amma idan K'addara ta had'a fa?.


"MAJNOON!!"


Ya maimaita sunan da akullum yakeyi masa yawo akan harshensa. 



*10:00 pm*