Chapter 4
*MAJNOON!!*
(The innocentmad)
*Writting By*
Fatymasardauna
*Wattpad*
@fatymasardauna
*CHAPTER 4*
*FREE PAGE*
MAJNOON! Ya maimaita sunan da akullum yakeyi masa yawo akan harshensa, haka kuma sunan da yazamo mummunan TABO ga rayuwar wani wanda ya kasance na musamman agaresa.
Shiru gaba d'aya d'akin ya d'auka, yayinda har zuwa yanzu sautin kukan Soumaya ne, ke tashi acikin dakin.
Gaba daya ganin Abboun nata da tayi ahaka ya sake raunata mata zuciya.
"Soumaya."
Malam Musbahu dake tsaye ya kira sunanta, zuciyarsa cike da rauni hadi da damuwar sabuwar rayuwar da suke shirin fuskanta.
"Soumaya!"
Dr.Mouhammad ya maimaita sunan, da yaji ankira yarinyar dashi akan bakinsa.
Tare kuma da maida idanunsa kanta.
Yarinyace k'arama wacce, zuciyarta bata da k'warin d'aukar damuwowi da yawa.
"Soumaya!"
Ya kira sunanta yana me karasa matsowa kusa da gadon da Abboun ke kwance.
Kanta dake kife bisa hannun Abboun nata ta d'ago, had'e da juya jajayen idanunta ta kalli Dr. Mouhammad wanda taji ya kira sunanta.
"Kinason mahaifinki ya samu lafiya?"
Dr. Mouhammad ya tambaya yana me kokarin, daidaita zaman oxygen din da aka sawa Abboun.
Kai ta jinjina masa da sauri tare da tsaida kukan da takeyi din, ta kafe Dr. Mouhammad din da idanunta.
"Good girl to ki daina wannan kukan, domin duk wani sauti ko kuma k'ara zai iya affecting masa wani sabon problem, saboda haka kiyi shiru Insha Allah zai samu lafiya."
Hawayen da suka silalo daga cikin idanunta, ta sanya hannu ta share, tare da d'an Janye jikinta baya.
Duk da cewar tanajin Rauni da kuma losing hope dinta.
Amma hakan bazaisa ta kasa kwararawa kanta guiwa ba.
Ganin ta tsaida kukan nata ne kuma yasa, Dr. Mouhammad sauke ajiyar zuciya.
Tare da juyowa ya kalli su Malam Musbahu, da Moudou wanda tuni idanunta sun fara lumshewa saboda baccin da takeji.
Gyaran murya yayi, cikin yanayin yanda yasan zasu fahimta yace.
"Kamar yanda na fad'a muku bama buk'atar hayaniya a inda yake, saboda haka zaku iya tafiya, Sai zuwa gobe."
Kai Malam Musbahu ya jinjina, cike da gamsuwa ya juyo ya kalli Moudou dake tsaye.
"Ki d'auki Soumaya ku wuce gida, ni zan kwana dashi anan."
Da sauri Moudoun ta amsa masa da "To." domin dama duk ta k'osa ta tafi, bata kuma fatan ace itace zata kwana da Abboun, duk da cewar kuwa taga d'akin ya wadatu da AC amma kwata kwata batason wahala.
"Baffa ni zan kwana da Abbouna, bazan iya tafiya na barshi ba."
Soumaya dake tsaye ta fad'a tana me yin raurau da idanu, wanda da alama wani sabon kukane yake kokarin zuwa mata.
"A'a Soumaya dole zaku tafi gida, ni nan na isa zanyi masa duk wani abunda ya dace, kuma gashi gobe kina da Islamiya, kuje gida ku huta."
Baffan ya fad'a cikin tausasa murya da kuma, lallashin Soumayan.
Tabbas bazatace taso hakan ba, domin akoda yaushe tafiso ta kula da mahaifinta, burinta ne hakan, amma gudun kada Baffan yace tana jayayya dashi shiyasa tayi shiru, dama kuma tun asali ba d'abi'arta bane yin jayayya da na gaba da ita.
Fuskar Abboun nata ta kalla asanyaye, kuma ta juya ta soma tafiya.
Hakanan takejin tamkar tafiyarta zaisa Abboun yayi nisa da ita.
Tamkar bazata dawo ta sameshi ba.
Duk da tanajin k'warin guiwa awani sashin, amma ita Mai Rauni ce akan komai.
"Da Halla ni wuce muje kina tafiya kamar wanda k'wai ya fashewa."
Moudou dake bayanta ta fad'a ad'an fad'ace, saboda tak'osa taga sunbar cikin asibitin.
Asanyaye ta karasa ficewa daga cikin dakin.
tare dabin bayan Moudou wacce tuni ta, matsa mata tayi gaba.
Kaitsaye babban corridor din dazai kaisu compound din asibitin suka nufa, inda take bin bayan Moudou wacce ayanzu ta riga da tayi mata nisa.
Tabbas kallo d'aya zakayi mata kafahimci cewa tana cikin yanayin damuwa, dan ko kad'an babu wani kuzari acikin tafiyan da take.
hasalima ko sanin inda take jefa k'afafunta batayi ba, ita dai tafiya kawai takeyi.
Ahaka har suka iso babban compound din asabitin, wanda yake kamar rana, saboda yalwataccen hasken dake wajen.
Ga kuma mutane dake ta kaiwa da komawa, kamar ba dare ba.
Wajen asibitin suka fito, dan neman abun hawa, saidai kasancewar dare ya fara shiga, yasa kwata kwata babu yalwan masu taxi sai dai Napep, suma Kuma basosai ba.
Kusan mintuna 8 suka kwashe tsaye awajen, kafun suka samu wani napep wanda yazo wucewa empty.
Da sauri Moudou tasa hannu ta tareshi, cikin sa'a kuwa ya tsaya.
"Wuse 2."
Moudou ta fad'a tana me kokarin shiga cikin napep din.
Batare dako ciniki ta tsaya sunyi ba.
Ganin hakan da Soumaya tayi ne, yasa ta shiga itama ta zauna.
Take kuwa mai napep din yaja sukayi gaba.
Ahankali ta d'an jingina kanta da jikin k'arfen napep din, hade da lumshe jajayen idanunta.
Saidai kasancewar napep din bashi da labule ne, yasa duk wani sanyi da iskan dake busawa yake sauk'a akan fuskarta.
Gaba d'aya batajin dad'in yanayin nata.
Yayinda har zuwa yanzu kuma, sunan ciwon dake damun mahaifin nata ke yawo acikin k'wak'walwarta.
Tabbas akwai abunda takeson sani agame da mahaifin nata, tambayoyi da yawa ne suke damun zuciyarta, tambayoyin da babu wani wanda zai iya amsa mata sai Abbounta.
Haka dai da tunani kala kala acikin zuciyarta, har suka iso cikin unguwar tasu.
"Yauwa malam yayi ajiyemu anan."
Maganan moudou kenan da yasa ta bud'e idanunta, Wanda tunda suka d'auko hanya suke alumshe.
Asanyaye ta fito daga cikin napep din, yayinda Moudou kuwa ta mik'awa mai napep din kudin dake hannunta.
"Hajiya d'ari biyu fa kika bani."
Mai napep din ya fad'a yana me jujjuya d'ari biyun da Moudoun ta bashi.
"To da d'ari nawa kakeso na baka?."
Moudou'n ta tambaya cikin d'aure fuska.
"D'ari hud'u zakiban gaskia bazan karb'i naira 200 ba, da kinsan 200 zaki ban, kika shiga napep dina kaitsaye?."
Mai Napep din ya fad'a yana me miko mata d'ari biyun.
"Amma kai kuwa baka tsoron Allah, daga asibitin zuwa nan shine Zan baka d'ari hud'u, b'arawo ne kai? To bazan bayar ba."
Moudou'n ta fad'a tana me kokarin wucewa ta barshi awajen.
"Wallahi Hajiya bazaiyiwu ba, sai kin cika min kud'i na, ai ba aikin banza nakeyi ba."
Mai Napep din ya fad'a yana me k'ok'arin fitowa daga cikin Napep din, don da katar da Moudou'n, wacce ta riga da tayi gaba.
Da sauri Soumaya ta matso inda yake, tare da shan gabansa, idanunta wanda har yanzu suke d'auke da danshin ruwan hawaye ta zuba masa.
Asanyaye kana cikin raunin murya tace.
"Kayi hakuri dan Allah!"
Baya ya d'anja tare da zubawa fuskarta idanu, saboda tun shigarsu napep din bai lura da ita ba sai yanzu, kasancewar wajen daya d'aukesu akwai duhu, shiyasa kwata kwata bai kula da kyawunta ba.
"Innalillahi."
Ya fad'a yana me sake baki, hanci da idanunsa.
"Kayi hakuri dan Allah!!"
Soumayan ta sake fad'a akaro na biyu, yayinda awannan karon ta had'e hannayenta biyu waje d'aya alaman rok'o.
Baki bud'e yace.
"Shikenan taci darajar kyawunki, amma bacin haka wallahi da sai ta biyani sauran kud'ina."
Mai Napep din ya k'are maganan yana me kallon k'afafun Soumayan, saboda tantance da aljana yake magana ko mutum.
"Mungode."
Ta fad'a anutse tare da juyawa ta nufi gidan nasu.
Da kallo Mai Napep din ya bita, har saida ta b'acewa ganinsa kafun ya koma cikin Napep d'insa.
"Hmmm gaskiya akwai mata masu kyau aduniya, amma tunda nake ban tab'a ganin irin wannan yarinyar ba, komai nata kaman madara, wannan ai mai d'aukarki saidai namijin d'awisu"
Yayi maganan yana me kokarin tada napep din, yabar wajen.
Soumaya kuwa tana shiga cikin gidan, ahankali ta maida k'ofar gidan nasu ta rufe.
Cikin yanayin sanyin da ta samu kanta aciki ta, juya ta kalli kofar d'akin Moudou'n, wacce tuntuni ta riga da ta wuce d'aki, kanta kawai ta girgiza tare da dawo da kallonta, ga plate da kuma abincin ta wanda ya zube ak'asa, saboda rudewa da kuma tashin hankalin da ta shiga d'azu.
Sai alokacin ne kuma ta tuno da cewar, yunwa takeji sosai, wanda har zuwa yanzu kuma yunwan takeji.
A hankali tasa hannu ta dafe goshinta, da takejin yayi mata nauyi, batare kuma da ta tsaya wani tunani ba kaitsaye ta nufi d'akinta.
Tana shiga cikin dakin ta zare hijabin dake jikinta, tare da ajiyesa akan gado, daidai saitin inda cutie'nta ke kwance tana bacci.
Hannu tasa ta d'an shafa kan cutien nata.
Ahankali kuma Cikin rashin kuzari ta karasa gaban d'an sip din da take ajiye Kayanta.
Riga da wandon uniform din dake jikinta ta cire, bayan ta zaro wani siririn doguwar riga marar nauyi daga cikin kayanta.
Rigar kawai ta zura ajikinta, kana ta juya ta fice daga cikin d'akin.
Harabar Maidaidaicin tsakar gidan nasu ta fito, inda ta d'auki buta kaitsaye ta wuce ban d'aki.
Mintuna 7 ta d'auka acikin toilet din, kafun ta fito d'aure da alwala.
Kaitsaye dakin nata ta kuma komawa, tana shiga kuwa ta sawa k'ofar sakata, domin haka ta sabayi akoda yaushe.
Dan madaidaicin sallayan da take sallah akai ta shumfud'a, tare da saka babban hijab d'inta ta tada sallah.
Kasancewar Ana binta bashin sallan Magriba dana Isha.
After 12minutes
Idanunta dake cike da hawaye ta lumshe, araunace cikin kukan dake kokarin cimmata ta bud'e baki, da niyar fad' in abunda ke zuciyarta.
Saidai hakan ya gagara saboda kukan ya riga yaci karfinta.
Duk da cewar tana cikin sujjadarta ta k'arshe ne, amma zuciyarta ta rauna na sosai.
Damuwar dake cikin ranta shiyayi tasiri wajen kasa furtawa, Wanda yasan fili da bad'ininta abundake bakinta.
Kusan mintuna 3 takasa furta komai sai kuka, hakan yasa ta d'ago daga sujjadan, tare dayin tahiyya ta sallame Sallah'n.
Ajiyar zuciya ta soma sauk'ewa akai akai, Wanda hakan yasa ahankali ta zame ta kwantar da jikinta akan sallaya'n, bayan ta d'aura kanta asaman katifarta.
Idanunta ta lumshe, tana me sauraran bugun zuciyarta, bugun da bata tab'ajin irinsa ba, bugun da yake sawa takejin tamkar zuciyar tata zata fito waje.
Hakika tanajin damuwa mai yawa acikin ranta, damuwar da takejin ta kasu biyu, na farko dai tasan damuwar rashin lafiyar Abbounta ne, amma na biyun fa menene shi?
" Wata K'addararce."
Wani sashi na zuciyarta ya bata amsar, da tasa hawayen dake cikin idanunta gangarowa bisa gefen fuskarta.
"Yah Allah!!!."
Tafad'a tana me gyara kwanciyarta, tare da kama kanta wanda keyi mata ciwo saboda kukan da tayi.
acikin idanuwanta dake alumshe take kallon fuskar Abbou nata da keyi mata gizo, fuskarsa wacce akullum akuma koda yaushe take d'auke da yalwataccen fari'a.
"Inasonka Abbouna!"
Ta fad'a abayyane tare da sake gyara kwanciyarta, had'i da jawo dan karamin pillow'n dake kan gadon ta rungume shi a kirjinta.
Ahaka har wani bacci mai nauyi ya d'auketa.
Baccin da yake cike da mafarkai kala kala.
*Washegari.*
8:30 am.
"Soumaya!
Soumaya!!"
Muryar Moudou dake kiran Soumayan ta karad'e duk tsakar gidan nasu, Wanda hakan yasa Soumaya dake tsaye agaban sip din kayanta, tayi saurin yafa d'an madaidaicin mayafin doguwar rigar dake Hannunta.
Tare da juyawa ta nufi hanyar fita daga d'akin nata, saboda
Jin yanda Moudou ke k'wala mata kira da tayi.
Tana fitowa kuwa Moudoun ta watsa mata harara, still kuma ckin dan yanayin fada tace.
"Da kika shiga cikin daki kika zauna, uban waye ne zai karasa dama miki kunun da kika fara, koni kikeso na karasa?"
"Aa Moudou nasa kayane."
Ta fad'a tana me sunkuyar da kanta k'asa.
"Ohon miki idan ma fata ki ka sanja ba kaya ba damuwar ki ne, nidai ko tsinke bazan d'aga agidannan ba, kinga ma tafiyana, sai anjima nazo asibitin."
Moudou'n ta fad'a tana me gyara zaman jakar dake kafadanta, batare da tajira cewar Soumayan ba kuma ta juya ta fice daga gidan.
Da Kallo Soumaya ta bita, duk da cewar tasan halin Moudoun, amma bata tab'a tunanin cewa idan Abboun baida lafiya, zata ci gaba da nuna musu halin rashin kulawa har haka ba.
Asanyaye ta juya ta koma kitchine din nasu.
Kunun Kokon da ta fara damawa ta karasa, kana ta juyeshi acikin kofi.
Drawer'n da suke ajiye kayan abinci ta bud'e.
Tare da lek'a cikin drawer'n, abunda idanunta suka gane mata ne Kuma yasa,
Take taji idanun nata sun ciko da hawaye, saboda gani tayi babu komai acikin drawer'n nasu, sai y'ar shinkafan da bata wuce gwangwani biyu ba.
Maida murfin drawer'n tayi ta rufe.
Tare dasa hannu ta d'auki jug din kunun.
Cikin shanye hawayen dake tare acikin idanunta ta fito daga kitchine din.
Sake gyara zaman mayafin dake jikinta tayi, bayan ta shiga d'akinta ta d'auko ragowar canjin taxi d'inta na jiya.
Tsakar gidan nasu ta sake dawowa, tare dasa makulli ta rufe kofar dakin nata, cikin sanyin yanayin da tasamu kanta aciki daga jiya zuwa yau, ta nufi hanyar fita daga gidan hannunta rike da jug din kunun.
Kasancewar gidan nasu abakin titi yake ne, kuma yasa tana fitowa ta
samu kanta ababban titin unguwar tasu.
Saidai kuma yau Abun hawa ko daya babu, kasancewar ranar yau din yakasance weekend, shiyasa ko masu kudin unguwar dake kaiwa da komawa, babu su akan titin saboda ranar hutu ce.
Hannu tasa ta d'an kare ranar dake dukan fuskarta.
Tare da sake lek'a titin ko zata ga abun hawa.
Wata had'addi'yar mota k'irar Benz ce tazo daidai gabanta ta tsaya, wanda hakan yasa ta d'anja jikinta baya, batare da ta tsaya kallon motar ba, ta kawar da kanta gefe.
Ahankali aka zuge bakin glass din motar.
Wani kyakkyawan matashin saurayi ne ya leko da kansa, Wanda akalla bazai haurawa 26 years ba.
"Mai Zafi, ina zakije ne haka, kike tsaye akan titi rana yana dukan fuska da jikin ki mai tsananin tsada?."
Saurayin ya tambaya yana me kallonta daga sama har k'asa.
Kasa amsa mishi tayi, kamar kuma yanda ta kasa juyowa ta kalleshi.
"Oh Maya I'm talking to you fa."
Saurayin matashin yaron ya fad'a, yana me kokarin bude murfin motar da niyar fitowa.
Da sauri tasake Jan baya, still batare da ta d'ago ta kalleshi ba tace.
"Please Saeed leave me alone."
Cak ya tsaya tare da lumshe idanunsa, saboda jin muryarta da yayi, domin yayi imani cewa jin muryarta kad'ai yana sama masa relief.
Ganin kyakkyawan surar jikinta kuwa idan yayi, yana sake haukatar dashi.
Tayaya zata fahimci yanda yakeji akan ta?
"Maya."
Ya kira sunan ta, tare da soma kokarin matsowa kusa da ita.
Da sauri ta matsa gefe, daidai lokacin kuwa wani mai taxi yazo wucewa.
Da Sauri tasa hannayenta duka biyu ta tsaida mai taxi din.
Yana tsayuwa kuwa ko gama daidaita parking baiyi ba, ta bud'e murfin motar tare da fad'awa ciki.
"Malam dan Allah Muje."
Ta fad'a da sauri, tana me rufe murfin taxi din.
Shi kuwa mai taxi kasancewar bai kashe motar ba, jin abunda tace yasa shi Jan motar sukayi gaba.
Da idanu saurayin da takira da suna Saeed yabi motar, har saida ta b'acewa ganinsa kafun ya shiga nasa motar, zuciyarsa cike da sak'e sak'e kala kala ya koma hanyar daya fito.
"Yarinya Ina zamuje ne?"
Muryar mai taxi din ya katse ta, daga shiru hadi da kallon titin da take.
"NIzamiyye hospital zaka kaini."
Ta fad'a tana me gyara zaman jug din dake hannunta, duk da tanajin yanda zafin kunun ke k'ona mata jiki, amma haka ta shanye.
mai taxi din kuwa jin abunda tace ne ya sashi karya akalan motarsa, zuwa hanyar da zata sadashi da asibitin.
*NIzamiyye Hospital*
*Surgery and Scanning room*
K'wararru kuma mayan Doctors din asibitin, kimanin guda hud'u ne ke tsaye akansa.
Cikinsu kuwa harda Dr. Mouhammad Boulama, Wanda yake rike da wani takarda.
Yayinda sauran Doctors din, keta amfani da wasu na'ura dan tabbatar da abunda result din test din da sukayi ya basu.
Sake juya takardar Dr. Mouhammad Boulama yayi, akaro na barkatai, tare dasa hannu ya d'an share gumin dake feso masa.
Sannu ahankali yakejin
Kuka da kuma magiya hadi da rokon da yarinyar keyi masa Adaren jiya, na dawowa cikin tunaninsa.
Wannan dalilin yasa shi jin wani irin karyewan zuciya, duk da kasancewar dama yasan hakan zai iya faruwa, amma baiyi suspecting cewa lallai dole sai irin wannan aikin mahaifin nata ke buk'ata ba.
Numfashi mai zafi ya fesar, tare da maida hankalinsa, ga second result din Abboun.
"Yawwa mun iso"
Cewar mutumi mai taxi din, Wanda yayi parking motar taxi din nasa, agaban asibitin.
Ajiyar zuciya ta d'an sauk'e tare da bud'e, murfin motar ta fito, Mika masa naira 200 dake hannunta tayi.
Saboda tasan tafiyan da sukayin bai wuce na hakan ba.
Babu jayayya kuwa mai taxi din ya amsa, tare da Jan motarsa yayi gaba.
Sake gyara zaman jug din kunun dake hannunta tayi, tare da nufar cikin asibitin kaitsaye.
Tana jefa k'afarta acikin asibitin kuwa, takun farko da tayi taji wani irin fad'uwar gaba, da Kuma bugawar zuciya sun risketa.
Wanda har saida hakan ya tilasta mata tsayawa cak awaje daya.
"Hasbunallahu wani'imal wakeel!"
Shine abunda ta fad'a tana me kokarin controlling nutsuwarta, tare da soma kallon mutanen dake ta zirga zirga acikin asibitin, tamkar wacce ke nazartar wani abu atattare dasu.
Hakanan take gani tamkar dukansu suna yawo ne, dan su jiyar da ita wani labari na daban.
For the second time da ta sakejin fargaba, da tsoron jin wani abu da za'a fad'a dangane da mahaifin nata.
Still Hawaye ne suka sake cika idanunta akaro na barkatai.
Saidai ayanzu sam batason yin kuka, wannan dalilin yasa ta shanye hawayen nata.
Zuciyarta ko d'auke da fargaba, haka ta soma Jan k'afafunta zuwa can cikin asibitin.
Hak'ik'a yaune karo na farko arayuwarta da taji, kwata kwata bata damu da irin kallon da mutane keyi mata ba, duk da kasancewar tanajin yanda idanunsu ke yawo ajikinta, amma bata damu da hakan ba.
Domin fata d'aya ne ke yawo acikin rai da zuciyarta, shine samun Abbounta lafiya.
Kaitsaye babban corridor din da zai sadata da d'akin da aka kwantar da Abboun nata ta nufa.
"Soumaya."
Malam Musbahu dake zaune akan wani benci ya kira sunanta.
"Na'am."
Ta fada da sauri, tare da juyowa, saboda sautin muryan Malam Musbahun da taji, tana juyowa kuwa suka had'a idanu dashi.
"Baffa."
Ta fad'a tana me nufowa inda yake da d'an saurin ta.
"Na'am Soumaya kin iso."
Malam Musbahu'n ya amsa, fuskarsa dauke da yanayin damuwa.
Yanayin daya masifar karyar da zuciyar Soumaya.
Asanyaye tace.
"Baffa meyasa ka zauna anan? Ina Abbou na? Ya farka? Yayi magana?."
Ta jerowa Baffan tambayoyin, tana me zama akusa dashi.
Ajiyar zuciya Malam Musbahu ya sauke, karanto fargaban da yayi akan fuskarta ne kuma yasa shi, aro k'warin guiwa ya dasawa kansa.
Atausashe yace.
"Ki kwantar da hankalinki, Abboun ki yana nan lafiya, yanzu ma an shiga dashi d'akin gwaji ne, Insha Allah kuma zasu fito dashi lafiya."
K'akk'arfar ajiyar zuciya ta sauk'e, tare da had'iyan wani abu daya tsaya mata amakoshinta.
Kwarai tana me fatan hakan.
Wannan yasa asanyaye Ta mikowa Malam Musbahun kofin dake hannunta.
Cikin muryarta dake dauke da damuwa tace.
"Kayi hakuri Baffa shi kad'aine kawai abunda muke dashi, dama Abbou ne....."
Sai kuma ta kasa k'arasa maganan saboda wani irin kuka da taji yana kokarin zuwar mata.
Duk yanda taso ga danneshi kuma, saida hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa kan kuncinta.
"Karki damu Soumaya komai zaiyi daidai wani lokaci, watarana komai zai canja Insha Allah."
Baffan ya fad'a cike dason k'ara mata k'arfin guiwa.
Daidai lokacin Dr. Mouhammad dama sauran Doctors din suka fito daga, wani d'aki dake facing dinsu.
Da sauri Suka mike tsaye ita da Baffan.
Inda ta zubawa d'an dattijon likitan wato DR. Mouhammad idanu.
Harya k'araso inda suke.
"Kusameni a office."
Shine abunda Doctor Mouhammad din ya fad'a, batare daya jira komai ba kuma cikin sauri ya nufi office dinsa.
Wani irin rawa taji k'afafunta nayi, yayinda atake bugawar zuciyarta ya tsananta.
"Muje Soumaya, Allah yasa muji alkhairi."
Cewar Malam Musbahu yana meyin gaba.
Wanda hakan yasa asanyaye ta rufa masa baya zuwa office din Dr. Mouhammad din.
Isowarsu bakin office din Dr. Mouhammad dinne Kuma, yasa ta gane cewa Ashe ma bata fara bugawan zuciya ba tukun.
Malam Musbahu ne ya tura musu kofar suka shiga.
Inda suka samu Dr. Mouhammad din atsaye, yayinda ya juyawa kofar shigowa office din baya.
Jin motsin shigowarsu ne kuma yasa shi, juyowa tare da nuna musu wajen zama.
Kana shima ya koma kan kujerarsa ta musamman ya zauna.
Shirune ya biyo baya atsakaninsu babu Wanda yace k'ala, da kuwa zasu saurara banda karan A/C'n dake tashi, babu wani abu wanda sautinsa ya bayyana sama da bugun zuciyar Soumaya.
Kowannensu fargaba ce fal acikin ransa.
"Likita."
Malam Musbahu ya fada asanyaye, saboda shima ayau din fargaban abunda zaiji yakeyi.
Nannauyan ajiyar zuciya Dr. Mouhammad Boulama ya sauk'e.
Bayan kuma ya zare medicated glass din dake idanunsa ne, ya d'ago ya kallesu dukansu.
"Likita ya sakamakon gwajin nasa?"
Malam Musbahu da yayi karfin Hali ya tambaya.
Takardan dake hannunsa ya mikowa Malam Musbahun.
Kan cikin son kwantar musu da hankali yace.
"Wannan shine result din gwajin kwakwalwa da mukayi masa, amma...."
Shiru yayi tare da d'an sanya hannu ya tallafe habarsa, Wanda kuma yayi hakanne saboda baisan tayaya zasu fahimci abunda yake son fad'a musu ba, baisan maganar a ya zata zo musu ba.
"Amma me likita kayi shiru, akwai matsalane ?"
Malam Musbahu ya tambaya ad'an tsorace.
"K'warai kuwa akwai matsala, saidai kamar yanda kuka sani kowa da irin k'addararsa, babu kuma wata cutar da bata da magani, tabbas ciwon dake damunsa yayi worst, domin yaci karfin jikinsa sosai, kasancewar baya amfani da magungunan da suka dace, saboda haka ya zama dole sai anyi mishi Surgery."
"Innalillahi wa'inna ilahirraju'un Surgery? Aiki fa kenan likita?"
Baffa ya fad'a cikin tashin hankali.
Yayinda Soumaya da zuciyarta ke wani irin tsalle kuwa, idanu kawai ta zubawa Doctor Mouhammad din, takasa motsa komai na jikinta.
D'an jim Dr. Mouhammad yayi, lokaci daya kuma damuwa ta bayyana akan fuskarsa.
Lallai ya zama dole ya fada musu gaskiya koda zasuji babu dadi.
Wannan dalilin yasa murya asanyaye yace.
"Kuyi hakuri da abunda zance, amma ya zama dole sai anyi mishi aiki, ba kuma normal aiki irin wanda kuka sani bane, aikine da kwata kwata ba ayinsa a Nigeria, haka kuma aikine da yake bukatar magudan miliyoyin kud'ad'e, Wanda rashin yi masa aikin kuma daidai yake da rasashi, I mean rasashi na har abada!!!."
*Hmmmm har yanzu ba'a ma fara labarin ba, sharar Fage ne kawai.
Saidai Karku manta Freepage kuke morewa🤗. Biya 300 dinki kacal dan samun daman more, tsananin Soyayya, k'addara da kuma tausayin dake cikin labarin MAJNOON, ko kunsan waye MAJNOON? I can't explain yanda littafinnan yake, shi ba irin SOORAJ ko LAYLERH MALEEK bane, shi na musamman ne, MAJNOON ya zo da wasu irin surprises daban daban domin samun shiga PAID group na MAJNOON zaki tura kudinki ta Account Number ne kamar haka 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz bank, ko kuma kitura MTN Card na 300 ta wannan numbern *** banda VTU.*
*8:00 pm*