Chapter 6
*MAJNOON!!*
(The innocentmad)
*Writting By*
Fatymasardauna
*Wattpad*
@fatymasardauna
*CHAPTER 6*
*FREEPAGE*
Kanta ta d'an kifa ajikin kulan da abincin ke ciki, yayinda acikin zuciyarta kuwa take tunanin yanda rayuwarsu zata kasance.
"Soumaya bakici abincin ba?"
Malam Musbahu da shigowarsa cikin d'akin kenan, ya tambaya tare da neman waje ya zauna.
"Eh Baffa naji na kasa cin abincinne, tsoro da fargaban abunda zai faru nakeyi, inajin tsoron rasa Abbou Baffa, bansan ya rayuwa ta zata tafi bayan babu shi ba."
D'an Jim Malam Musbahun yayi, kana cikin tausasa murya yace.
"Ki kwantar da hankalinki Soumaya, Insha Allah komai zaiyi daidai, da izinin Ubangiji, bamu ke da cuta ba haka bamu keda maganinta ba, muna namu Allah na nashi, saboda haka dole sai abunda yayi."
Ya k'are maganan cikin son tausasa zuciyarta, yayinda kuma shima har acikin zuciyarsa, tunani yake ta yanda zasu samu muk'udan kud'ad'en da aikin Abboun ke buk'ata, saidai kamar yanda yayi believing cewa Allah zai kawo, Kwarai ya yarda da hakan, saidai daga wani sashi na zuciyarsa, yana fargaban sanin cewa ta wacce hanya ne kudin zasu zo.
Soumaya ko jin kalaman nasa ne yasa ta jingina bayanta da jikin bangon d'akin, tare da lumshe idanunta, Hakika tasan kwakwalwarta bata da quality'n da zata iya warware wannan matsalan, matsalan da ke neman juya rayuwarta, gaba izuwa baya, matsalar dake shirin dakatar da komai nata.
"Baffa idan bamu samu Million 30 zuwa nan da kwana bakwai ba, kamar yanda Dr. ya fad'a kana ganin me zai faru? Zan rasa Abbou kenan?."
Tambayar da ta jefowa Malam Musbahu kenan, Wanda hakan yasa shi yin shiru, tare da fad'awa duniyar tunani.
"Nasani Baffa nasan mezai faru, zan rasa Abbou na tamkar yanda na rasa mahaifiyata, duniya zatamin kunci, zan rasa farinciki...."
Ta fad'a cikin sanyi da kuma raunanniyar muryarta.
Ahankali kuma wasu siraran hawaye suka kwaranyo daga cikin idanunta.
"Cuta lafiya da mutuwa duka na Allah ne Soumaya, tsananin ciwo bashi ke nufin mutuwa ba, haka tsananin tashin hankali bashi ke nuna cewar babu mafita ba, nasani hakika bamu da yanda zamuyi, amma zan fita neman taimako, duk da nasan abune mai wahala kasamu mai taimaka maka azamanin yanzu, wani idan ya taimaka ma, bazai baka ko kwatan kwatan abunda zai biya maka buk'ata ba, gashi kuma kud'in aikin da yawa, saidai mujira hukuncin Ubangiji, idan Allah yasanya da rabon farinciki, zakiyi farinciki Soumaya, kuma ki rik'i hakan amatsayin jarrabawa, wacce babu wanda yafi k'arfinta."
Baffan ya fad'a, yana me kallon Soumaya'n, wacce ta tsaida idanunta akan Abboun, kallo takeyi masa na sosai, yayinda zuciyarta kuwa ke cike da rauni hadi da tausayinsa.
Bazata iya misalta yanda takeji ba, domin yafi karfin hankali da tunani, da kuwa ace zata iya ciro zuciyarta, To da bazata tab'a iya ajuyuwa waje daya ba, saboda yanda take tsalle da kuma bugawar da takeyi akai akai.
K'ofar d'akin akaturo ahankali, Wanda hakan yasa duk suka maida kallonsu jikin k'ofar.
Moudou ce ta shigo fuskar nan nata babu alaman fari'a, ganinsu ahaka da tayi ne kuma yasa ta tsayawa, tare da kama k'ugu cikin d'an yanayin mamaki tace.
"Ikon Allah wai har yanzu bai farfad'o ba, To sai yaushe ne zai dawo hayyacinsa, mutum amik'e haka kamar gawa?."
Ta k'are maganan tana me lek'a fuskar Abboun, Wanda ke sanye da oxygen.
Idanu duk suka zuba mata, yayinda kowannensu yake mamakin halinta, itadai Moudou haka take, har abada kuma bazata canja ba, duk wani abu da yazo bakinta kawai fad'ansa takeyi batare da ta damu ba.
Ganin da tayi cewar duk basu kulata bane kuma, yasa ta kallon Soumaya, wacce ta kawar da kanta gefe.
"Ke wai sai yaushe ne sukace zasu sallameshi? Naga tun jiya ahaka yake, banda numfashi babu wani abu dake motsi ajikinsa, gashi zaman asibiti ba dad'i ne dashi ba, ni duk zirga zirgan nan ba wani sonshi nake ba."
Idanunta da suke kallon k'afafun mahaifin nata ta lumshe, tare da matse lips dinta, saboda batajin akwai wata amsa da zata bawa Moudou'n.
Malam Musbahu dake gefe kuwa, zama ya gyara, batare kuma da ya kalli Moudoun ba yace.
"aiki za'ayi mishi, aikin da yake buk'atar mak'udan kud' har naira million 30, sun kuma ce acikin kwana 7 suke so mu biya kudin, domin rashin yi masa aikin, daidai yake da rasashi na har abada."
"Meye aiki, Naira Million 30??!!!"
Moudoun ta fad'a da k'arfi tare dasa hannu ta dafe kirjinta, dan sai takejin kaman kunnuwanta ma basuji ye mata da kyau ba.
"Aikin naira million 30, haukane abun? Wani irin aiki ne wannan, ko dai shid'in zasu canja, ko kuwa sabon mutum zasu dawo dashi?."
Tayi maganan tana me zazzaro idanunta waje, saboda jin maganan take kaman almara.
Shiru duk d'akin ya amsa, saboda babu Wanda zai iya amsa mata tambayoyin nata, batare da ta damuba kuma ta d'ora da cewa.
"Waima likitotinnan sunsan ko mu suwaye? Anya basa shan k'wayoyi, idan ba haka ba tayaya suke sakaran samun million 30 awajenmu kuma acikin kwana bakwai? Yo ko ashekara bakwai ne bana tunanin za'a had'a way'annan kud'ad'en, tunda dama aishi ba arzikine dashi ba, gashi kuma bai haifi d'a Namijin da zai fafutuko ya kawo ba, irin wannan yarinyar kawai yake dashi, mezata iya yi masa? Wani amfani zatayi masa aduniyar nan?."
Ta k'are maganan tana me nuna Soumaya da hannu.
Daidai lokacin ne kuma aka turo kofar dakin wanda, hakan yasa ta dakatawa da maganganun da takeyi.
Dr.Mouhammad Boulama ne ya shigo, cikin d'akin hannunsa d'auke da wasu takardu, da kuma wasu abubuwan gwaje gwaje.
"Yauwa Likita dan Allah ataimaka asallamemu,ni aganina wannan zaman ya isa haka, ko ba haka ba Malam Musbahu?"
Moudou ta fad'i hakan cikin sauri, tare da kallon Malam Musbahu, Wanda ya kasa bata amsa ya Kuma d'auke kansa daga kallonta.
Kallonta Dr. Mouhammad din yayi na d'an wani lokaci, kafun daga bisani yace.
"Babu sallama har sai anyi masa aiki ya samu sauk'i, idan kuma baku damu da lafiyarsa ba, is okay zaku iya d'aukansa ku tafi."
Ya yi maganan yana me nufan gadon da Abboun ke kwance, saboda yin abunda ya kawosa d'akin.
Aikuwa amsar daya bawa Moudou'nne yasa ta, tsuke bakinta, tare da d'an watsa masa harara k'asa k'asa.
Hararan da kwata kwata baimasan tanayi ba.
Ahankali Dr. Mouhammad din ya gyara zaman oxygen din dake kan fuskar Abboun, tare da d'aukan wani na'uran dayazo dashi ya d'aurawa Abboun akan kirjinsa, har kusan mintuna 5 kafun ya cire na'uran.
Numfashi ya d'an fesar, kana yayi Jim kamar mai nazartar wani abu, Wanda hakan yasa duk suka zuba masa ido.
Almost 7mn kafun ya d'auki wani paper ya d'anyi rubutu ajiki, sannan ya dawo da kallonsa garesu.
"Ku kula sosai bamason hayaniya a inda yake please."
Yayi maganan cikin nuna musu serious akan abun, saidai kuma kasancewar yau din yana da patients da yawa, yasa ba tare, da ya tsaya jin me zasu ceba ya fice Daga cikin d'akin.
Wanda hakan yasa Baffa sauke ajiyar zuciya, tare da kallon Soumaya cikin sanyi yace.
"Soumaya kije gida ki d'an huta, idan yaso kuma sai gobe ki dawo, kinsan koda Abbounki yake da lafiya, baya tab'a bari magriba tayi miki awaje, saboda haka ki d'auki abincin ki tafi dashi gida, ungo wannan saikiyi kud'in mota."
Baffan ya k'are maganan yana me, maida kallonsa ga Soumayan wacce har yanzu idanunta ke kallon gefe, duk tayi zugum ta kuma zama wata iri alokaci guda.
Saidai jin abunda ya fad'a d'inne kuma yasa ta juyowa, tare dasa hannu ta karb'i naira 500 din da yake mik'o mata.
Duk da tanason zama awajen Abboun nata, amma jayayya ba d'abi'arta bane, wannan dalilin yasa tace.
"Nagode sosai Baffa, Allah ya biyaka da gidan aljanna."
Ta ida maganan murya araunace, tare da
sunkuyawa ta d'auki kulan da Inna Hauwa ta kawo musu abinci.
"Babu godiya atsakaninmu Soumaya, ki sani duk abunda Abboun ki zaiyi miki nima shi zanyi miki, Allah dai ya miki albarka."
"Ameen."
Ta amsa tare da juyawa ta nufi hanyar fita daga d'akin, har takai bak'in k'ofar fita kuma sai ta tsaya, had'i da juyowa asanyaye, ta kalli mahaifin nata dake kwance, Wanda idanuwanta ke cike da fatan ganin wani motsi nasa, zuciyarta kuwa keda muradin ganin samun lafiyarsa.
Ahaka ta juya ta fice daga cikin d'akin.
Moudou dake tsaye kuwa, tsaki taja, yayinda acikin zuciyarta kuwa cewa tayi.
"hmmm ni kuma da bana kulawa dashi, sai Allah ya biyani da wuta ko mchewww."
Ta k'are maganan tana me bayyana tsakinta.
Shidai Malam Musbahu ko d'agowa ya kalleta baiyi ba, saboda dama yasan ba koda yaushe ne y'an mutumcin nata sukenan ba.
Soumaya.
Isowarta bakin titi kenan, Wanda hakan yasa ta sanya,
Yatsun hannunta guda biyu ta gyara rik'on da tayiwa y'ar madaidaiciyar kulan dake hannun nata.
Kusan mintuna 8 kenan Yanzu da take tsaye abakin titin, amma kwata kwata bata samu abun hawa ba.
Duk da cewar tana jin wani irin jiri, na d'ibanta amma haka ta daure, domin tasan cewa bakomai ne ke damunta ba, face yunwa kasancewar rabonta da abinci tun jiya da safe, nanma kunune Tasha da k'osai, sai kuma da suka fito sallah amakaranta, Noor ta saya musu hollandia milk suka sha.
To daga nan bata sake cin komai ba, ba Kuma tajin wani abu zai samu gurbi acikinta.
Hango wani mai keke napep da tayi ne kuma, yasa cikin sauri ta soma kokarin tsai dashi.
Saboda tayi imani cewa idan ta k'ara wasu mintuna awajen, babu makawa zata iya yankan jiki ta fad'i.
Cikin sa'a kuwa ta samu mai keke napep din ya tsaya adaidai gabanta.
Wannan dalilin yasa ta fad'a cikin napep din, batare da ko ciniki ta tsaya sunyi ba, bayan ta gaya masa inda zai kaita ne kuma, yaja napep din sukayi gaba.
Tafiya suka somayi akan mik'akk'en titin wanda hakan, yasa ta d'an kwantar da kanta tare da lumshe idanunta, duk jin jikinta takeyi babu k'arfi, sannan kuma har yanzu kanta baidaina yi mata ciwo ba, baya ga haka kuma kasancewar sanyin yammaci ya fara kad'awa ne, ya sa ta sanya hannayenta duka biyu ta matse kirjinta, saboda kwata kwata ita ba mutum bace maison yawan sanyi, dan yana haifar mata da zazzab'i musamman sanyin yammaci irin na yau d'in.
Motoci da kuma ababen hawa dake ta kaiwa da komowa take kallo, amma kuma duk da cewar idanunta akansu suke, saidai hankalinta ya tafine izuwa wani waje na daban.
Ahaka har suka shigo cikin unguwar tasu.
"Anan zan sauk'a."
Ta fad'a asanyaye saboda ganin sun iso daidai kofar gidan.
Tsaida napep din d'an adaidaitan yayi tare da juyowa yana kallonta, kallon da ita Sam batama lura dashi ba.
Kudin dake hannunta ta mik'o masa, batare da ta ko kalleshi ba, saidai ganin bai amsa bane yasa ta d'ago kanta ta kalleshi.
"Malam gashi."
Ta fad'a tana me kallon idanunsa, Wanda ya zuba mata su tamkar yaga wata sabuwar halitta dabai tab'a gani ba.
D'an zabura mai napep din yayi, tare dasa hannu ya amshi kud'in.
Still kuma bai daina kallonta ba.
Kanta ta d'an sunkuyar k'asa batare,kuma da ta damu da irin kallon da yake mata ba, kaitsaye ta juya ta nufi gidan nasu.
Tana shiga kuwa kaitsaye d'akinta ta nufa.
Yayinda tun kafun ta gama shiga ciki, ta zare mayafin rigar abayan dake jikinta, ad'an gajiye ta zauna akan katifarta, tare da bud'e murfin kulan abincin da ta taho dashi.
Idanu ta dan zubawa abincin, batare kuma da tana jin sha'awarsa ba, haka tasa spoon ta diba tare da kaiwa bakinta.
loman farko kuwa na abincin abakinta, kuliyarta wacce tasan bataci komai ba tun safe ta fad'o mata arai.
Wannan dalilin yasa da sauri ta fito, tare da karasawa wajen cutien, akan wani dan plate da take zuba mata abinci ta zuba mata taliyan, kana ta tura mata plate din gabanta.
Da sauri kuwa cutien ta fara cin abincin, Wanda hakan yasa ta komawa d'aki.
Tare da zama ta soma cin abincin itama.
Saidai kuma amma duk yanda taso taci abincin da yawa ta kasa.
Kwata kwata loma 5 kawai tayi, ta ture abincin daga gabanta, saboda duk batajin dadin bakinta, baya ga haka kuma wani zazzafan zazzab'i da ciwon kai ne na lokaci d'aya suka rufe ta, Wanda har saida hakan ya tilasta mata, zamewa ta kwanta.
Hannayenta duka biyu tasa ta rik'e kannata, had'i da takure jikinta waje d'aya.
Tana nan kwance ahaka har aka kira sallan magriba, inda da k'yar ta iya tashi ta d'auro alwala, bayan tayi Sallah'n ne kuma ta sake kwanciya, still 7 da wasu y'an mintuna aka kira sallan isha.
Ayanzu kam adaddafe ta idar da sallan saboda, yanda jikinta keta karkarwa kamar wacce aka watsawa ruwan sanyi.
Gefe guda kuwa Ga kanta dake tayi mata wani irin ciwo, Wanda hakan yasa ta hayewa saman katifarta ta kwanta, bayan ta lullub'e duka jikinta da bargo.
Idanunta wanda sukayi jajur ta lumshe, acikin ranta ta soma ambaton sunan Allah, ahaka har bacci mai nauyi ya d'auketa.
Acan asibiti kuwa Malam Musbahu ne yake zaune da Abboun, yayinda lokaci zuwa lokaci yake kallon tv plasma'n dake cikin d'akin, kasancewar shi yake d'ebe masa kewa.
Domin Moudou kuwa dama Soumayan na tafiya babu jimawa itama ta tafi.
*Washegari (Sunday).*
Kamar dai yanda ta kwanta jiya da zazzafi hadi da ciwon kai haka yau din ma tatashi.
Saidai kuma ayau din ta tashine da fargaban cewar, kwana d'aya daga cikin kwanaki bakwai d'in da Dr. Mouhammad ya fad'a musu ya ragu, yanzu saura kwanaki 6 acikin bakwai din.
Akuma cikin irin wannan yanayin ne, mafarkin da tayi adaren jiyan, ya fad'o mata, Mafarkin daya haddasa mata tsinkewar zuciya, kana kuma ya shiga yawo acikin brain dinta tamkar alokacinne takeyin shi.
Da sauri ta Ware idanunta dake alumshe, saboda mutumin mafarkin da taga yanayi mata gizo acikinsu.
Hannayensa take kallo, Wanda suke d'auke da wani irin Zane ajikinsu, sai kuma jajayen lips dinsa, Wanda taga yana tattaunesu, har takai ga suna zubar da jini.
Saurin dafe zuciyarta dake bugawa tayi, tare da d'an Jan jikinta ta sake duk'unk'unewa, zuciyarta cike da tsoron abunda taga mutumin yanayi amafarkinta, duk da cewar bataga fuskarsa ba, amma hoton zanen dake hannayensa, da kuma yanda yake cizgar lips dinsa ya kasa gogewa acikin idanunta.
Asanyaye ta sake gyara kwanciyarta, tare da kama kanta dake sarawa, duk da cewar tanason tashi, amma tasan babu wani wadataccen k'arfi ajikinta.
Dan karamin agogon bangon dake cikin d'akin ta kalla.
12.30 pm.
Shine abunda ta gani wanda hakan yasa bisa dole ta yunkura ta tashi, saboda tanason zuwa dubo mahaifin nata.
Kasancewar batajin dadi hakan bazai hanata dubo Abboun nata ba.
Hijab dinta ta sa, tare da nufan tsakar gidansu, kamar yanda tayi tunani kuwa, koda ta fito babu kowa a tsakar gidan.
Hakan yasa bayan ta d'ebi ruwa kaitsaye toilet ta wuce tayi wanka.
Koda ta fito daga ban d'akin kuma, kaitsaye d'akinta ta sake komawa, kamar kuma yanda yake al'adarta mai kawai ta shafa, babu ko powder da lipstick.
Riga da skirt na wani atamfa tasa ajikinta, Wanda hakan yasa kyakkyawan surarta bayyana, musamman tsararren hips dinta, Wanda yake da shape mai kyau.
Soumaya kyakkyawace irin ta sosai da sosai, musamman kyakkyawan innocent face dinta, Wanda yake d'auke da manya manyan idanunta masu d'aukar hankali, bakinta kuwa d'an k'arami ne mai d'auke da jajayen labb'a, haka ma hancinta yana da tsawo da kuma shape mai kyau, sai Kuma gashin idanunta wanda suke zara zara masu yawa da Laushi, gashin giranta kuwa d'an dadaine wanda koda yaushe yake kwance, tana da hasken fata sosai, baya ga haka kuma tana da shape din jiki mai kyau, bata da cikan kirji sosai, sannan tana da hips Wanda yake k'arawa jikinta kyau.
Kaitsaye tafi kama da larabawan Yemen 🇾🇪, kasancewarta half Yemenis half Somalia'n shiyasa, take d'auke da wani irin sirrin kyau na musamman.
Numfashi ta d'an fesar cikin kuma rashin k'arfin jikin da take fama dashi, ta zura wani navy blue hijab ajikinta.
Sosai kuwa tayi kyau saidai sam bata damu da hakan ba, hasalima ko kallon madubi batayi ba, haka ta fice daga cikin dakin.
Kasancewar kuma tasan Moudou bata gidan, shiyasa kai tsaye ta nufi hanyar fita.
Da addu'a d'auke abakinta, ta fito daga cikin gidan nasu, tare da soma kokarin rufe kofar gidan, kamar yanda ta saba, bayan ta kammala ne kuma, ta karasa bakin titi inda ta tare napep, Wanda shi ya kaita zuwa asibitin.
Kamar dai yanda aka saba kuma, koda suka iso acan bakin asibitin aka sauk'e ta, inda ta shiga ciki zuciyarta cike da wasu wasin abunda zata tarar.
Ahankali ta tura kofar d'akin ta shiga, bakinta d'auke da sallama.
Saidai duk da cewar bata d'aga murya ba, amma tayi mamaki k'warai saboda ganin Malam Musbahu bai amsa mata ba, kasancewar yayi yayi jigum had'e dayin nisa acikin duniyar tunaninsa.
"Baffa!!"
Ta kira sunansa asanyaye, tare da k'arasowa cikin dakin.
Malam Musbahu wanda kiran sunan nasa da tayi da d'an k'arfi ne, yayi sanadiyar dawo dashi cikin hayyacinsa, d'ago kansa yayi ya kalleta, da fuskarsa wacce ke d'auke da d'an yanayin damuwa yace.
"Soumaya kin iso."
"Umm Baffa yaya jikin Abboun? Har yanzu bai bud'e idanunsa ba ko?."
Tayi tambayan cikin karyewan murya, had'i da langwab'ar da kanta gefe tana kallon Abboun.
"Har yanzu bai dawo hayyacinsa ba Soumaya, yau kwana biyu kenan yana ahaka, banda numfashi babu abunda yakeyi."
Malam Musbahu ya fad'a araunace, cike kuma da tsananin damuwa.
Idanunta da sukayi raurau ta lumshe, tare dasa hannu ta shafa gefen fuskar Abboun nata, tana matukar son taga farkawarsa, tanason ganinsa kamar da, tanason jin muryarsa, tanason sanar dashi damuwar dake kwance acikin zuciyarta, amma babu halin hakan.
Wannan dalilin yasa hawaye suka cika idanunta, saidai sanin dole ta zama mai juriya, yasa ta soma kok'arin shanye hawayen.
Asanyaye ta juyo da kallonta ga Malam Musbahu wanda ke zaune.
"Baffa wani abu ya faru ko? Doctor ya sake cewa wani abu akan Abbou na ko?."
Tayi tambayar tana me kallon Baffan, saboda tsananin damuwa da tun shigowarta ta hango akan fuskarsa.
Nannauyar ajiyar zuciya Ya sauk'e, kana kuma cikin yanayin damuwa yace.
"Ya zamuyi Soumaya, Likita ya sake tabbatarmin da cewa matuk'ar ba'ayi masa aiki nan da kwana kin da suka rage ba tabbas zamu rasashi, Soumaya aikin nanne kad'ai zaisa mahaifinki ya iya dawowa cikin hayyacinsa, shi kad'ai zai iya sawa ya bud'e idanunsa, tayaya ne zamu iya biyan kud'ad'en da suke buk'ata wannan abun shi yake damuna."
Duk yanda taso shanye hawayen dake cikin idanun nata, awannan karon kasawa tayi, wannan dalilin yasa bisa dole saida hawayen suka zubo kan k'uncinta.
Asanyaye kuma cikin rashin kuzarin, daya rage mata ta fad'a kan guiwowinta, tare da kifa kanta ajikin gadon Abboun nata.
Batasan ta yaya ko kuma ta Ina zata fara ba, wannan yana daya daga cikin abun da yake yawan haifar mata da bugun zuciya.
Araunace tace
"Banaso na rasaka Abbou, dan Allah ka tashi, ka bud'e idanunka, ka cireni daga cikin duhun da rayuwa ta take shirin fuskanta, bazan iya jure hakan ba, bazan iya ba Abbouna...."
Ta k'are maganan cikin muryan kukan, dake son k'wace mata Wanda har hakan yasa, ta cusa kanta ajikin hannun Abboun nata.
Adaidai lokacin ne kuma Dr. Mouhammad dake tsaye acikin office dinsa, ya fesar da wani irin numfashi mai d'umi, tare kuma dasa hannu ya gyara zaman medicated glass din dake idanunsa.
Akaro na uku kenan yanzu da yake ta aikin kaiwa da komowa acikin office din nasa.
Kwarai so yake ya yarda da hukuncin da zuciyarsa ke raya masa, hukuncin da yasa adaren jiya ya kusan kwana baiyi bacci ba.
Saidai baisan atayayane zai fad'I sak'on agaresu ba, baisan wani irin fahimta zasuyi masa ba.
K'warai asan zasuyi mishi kallo irin na sonkai, amma bashi da wani zab'i banda hakan.
Idanunsa ya kuma lumshewa yana me tunano abunda ya faru a Daren jiya.
Abunda ya gani shike tayi masa yawo acikin kwakwalwarsa.
Haka kuma maganganun da suka tattauna da BILLIONAIRE DAWOUD SARAKI suke dukan zuciyarsa.
Saboda yasan ba lallaine hakan da suke so, ya yiwu ba.
Kusan mintuna 20 yanzu kenan daya,kwashe yana tunanin yanda abubuwan zasu kasance.
Ajiyar zuciya ya kuma saukewa akaro na barkatai, hade da bud'e idanunsa inda ya sauke ganinsa akan wata farar takardar dake rike ahannunsa.
Farar takarda ce irin wacce tafi kama da takardar later kasancewar ta d'auke acikin envelope.
"Lallai wannan shine hanya guda d'aya, wacce zata warware matsalolin da dukanmu muke k'ok'arin fad'awa cikinta."
*10:00 pm*