Chapter 8
*MAJNOON!!*
(The innocentmad)
*Writting By*
Fatymasardauna
*Wattpad*
@fatymasardauna
*CHAPTER 8*
*FREEPAGE*
Idanuwanta ta zazzaro waje, cike da firgici, kid'ima had'i da tsananin bugawar zuciya.
Yayinda Tamkar sauk'ar araduwa aka,
haka taji sauk'an maganganun Baffan acikin kunnuwanta.
Wanda har saida hakan yasa wani irin gumi ketowa daga cikin kai zuwa goshinta.
Still Cikin yanayin tashin hankali had'i da bugawar zuciyar, daya kusan tsaida fitan numfashinta, murya na rawa tace.
"YARJEJENIYAR AURE? MAJNOON? Ban fahimta ba Baffa, inajin kamar kunnuwana basu jiyemin daidai ba, duk Menenesu? Me nake shirin fuskanta? Katasheni a wannan mafarkin, kasanar dani cewa komai da komai ba gaskiya bane, Baffa kasanar dani cewa mafarki ne dan Allah...."
Ta k'are maganan tana me zubewa akan guiwowinta, tare da zubawa fuskar Baffan idanunta wanda k'iris suke jira su fitar da ruwan hawaye.
Zuciyarta ko bugawa take da k'arfi, yayinda takejin wani irin abu mai nauyi ya to kare kirjinta.
Akan fuskarta kuwa tsananin tsoron maganganun da zasu fito daga bakin Baffan ne bayyane, Wanda tayi imani ba lallai k'wak'walwarta ta iya d'aukarsu ba.
Shikansa Malam Musbahu zuciyarsa araunane take, saidai ya zama dole ya fayyace mata duk wani abu, hakan yasa murya asanyaye, yace.
"Babu dole ko tilas akan hakan Soumaya, kuma nima ban fad'a miki hakan dannayi miki tilas ba, tabbas muna buk'atar kud'i dan ceto rayuwar mahaifinki, amma hakan bashi zaisa ki rushe ginin cigaban rayuwarki ba, hakan bashi zaisa ki auri MAJNOON ba, mu dogara ga Allah ya Isar mana, duk da cewar Dr. Mouhammad yayi hakanne dan taimakon mu, amma wannan abun bamai yiwuwa bane, ki kwantar da hankalinki kuma kisani ban fad'a miki hakan, dan rugujewar rayuwarki ba, hakika tun farkon daya kawomin buk'atar hakan nasan, abune wanda bazai yiwu ba, saboda aikata hakan, daidai yake da sab'awa mahaifinki, da kuma cutar da rayuwarki, ba kuma na fatan nima ki zab'i hakan, bana fatan kashe rayuwarki ta hanyar Aura miki mahaukaci."
Hawayen dake cikin idanunta ne suka samu daman gangarowa, Wanda hakan yasa ta lumshe idanun, a hankali kuma cikin muryarta dake cracking ta ambaci sunan da taji ya tsaya mata arai. Then sunan da taji ya soki k'ahon zuciyarta.
"MAJNOON! (MAD)."
Kalmar tayi mata d'aci har acikin mak'oshinta, Wanda hakan yasa ta soma girgiza kanta.
Cikin kuma bayyana gaskiyar abunda ke zuciyarta tace.
"Bazan iyaba Baffa bazan iya auren MAJNOON ba, Tayaya zan zauna dashi? Tayaya zan iya rayuwa da wani? bansan Aure ba Baffa? bazan iya amincewa da wannan buk'atar tasu ba. Bazan iya ba..."
Ta k'are maganan tana ci gaba da girgiza kanta, tare dasa hannu ta dafe kirjinta, saboda ambatan sunan MAJNOON d'in da ta sakeyi yasa zuciyarta tsananta bugawa.
Hakika Tayi imani cewa kowa da irin k'addararsa amma k'addarar auren Mahaukaci bana ta bane.
"Idan bazaki iyaba zaki bar mahaifinki ya mutu kenan?."
Muryar Moudou wacce tun fara zancen nasu take a lab'e, ya karad'e gaba d'aya cikin kunnuwansu, Wanda hakan yasa su juyawa duk suka kalleta.
Harara ta watsawa Soumaya tare da kama k'ugunta, cikin yanayinta na fad'an da ta saba tace.
"Rashin amincewar auren MAJNOON daidai yake da rasa mahaifin ki, rasashi na har abada, saboda haka ruwanki ne auren mahaukaci, idan kikace ba haka ba kuma nanda kwanaki 5 iwar haka, Ana nan ana zaman makokin Mahaifinki."
Idanunta ta rumtse da k'arfi, lokaci d'aya kuma taji kuka na kokarin kwace mata, tabbas bazata iya jure kalaman Moudou way'anda suke neman tarwatsa mata zuciya ba.
Hakan yasa ta tashi da sauri, tare da wucewa cikin gidan kaitsaye, hannunta rike da takardar yarjejeniyar.
Duk yanda taso jure kukan nata kuwa ta kasa, wannan dalilin yasa taku biyu kacal tayi ta saki kukan da ta kasa controlling d'insa.
Kaitsaye kuma d'akinta ta wuce.
Tana shiga cikin d'akin nata kuwa, kan katifa ta fad'a tare da ci gaba da sakin kuka mai tsuma zuciya.
Kukan da babu mai lallashi, kukan dake d'auke da ciwoka masu tarin yawa.
Acan zaure kuwa ganin ta tafine yasa Malam musbahu tashi shima, bayan ya nannad'e tabarmar da yake zaune akai, ya fita zuciyarsa cike da alhini, had'i da tunanin abunda zai biyo baya, saboda ayanzu ya riga da ya mik'a wuya, kamar yanda yasan cewar basu da wani mafita.
Kuka takeyi sosai, kukan da ayanzu ita kanta batasan dalili d'aya nayinsa ba, kukan rashin lafiyar Abbou'nta, ko kuma kukan sabuwar matsalan da take k'ok'arin kunno kai cikin rayuwarta?
Ada batasan k'unci ba, duk wata damuwa Abbounta ke yaye mata shi, ayanzu kuwa kunci damuwa, had'i da kuka, sune abunda suka cika rayuwarta.
Fargaba ya maye mata gurbin bugawar zuciyarta.
"Ya Allah!!"
Shine abunda ta fad'a tare dasa hannu ta kama kanta, Wanda takejinsa tamkar zai rabe gida biyu, saboda kalmar sunan MAJNOON dake yawo acikin k'wak'walwarta, da kuma kalmar AURE dake neman zautar da tunanin ta. Kalman da bata tab'a kawosa kusa acikin rayuwarta ba, batasan SO ba, bata kuma san menene shi ba, wannan dalilin yasa batasan me Auren kansa ya k'unsa ba.
Almost 20minute.
A hankali sautin kukan nata ke raguwa, saboda k'iraye k'irayen sallan magriba da aka somayi.
Hakan yasa cikin mintuna k'alilan, ta soma sakin ajiyar zuciya da kuma sheshshek'an kuka akai akai.
Asanyaye Kuma cikin rashin kuzarin daya mamaye duk jikinta, ta tashi daga kwancen da take, tare da soma k'ok'arin cire uniform din dake jikinta.
Koda ta cire uniform din wani doguwar rigar atampa mai sauk'i ta sanya ajikinta, tare da wucewa tsakar gidansu ta d'auro alwala.
Bayan ta dawo cikin d'akinnata ne kuma, ta shumfud'a sallaya had'i da ta da sallah.
Kamar kuma yanda ya zama d'abi'arta, lokaci mai tsawo ta b'ata acikin sujjadar ta na k'arshe, tana me kaiwa Allah kukanta.
Hak'ik'a damuwa tayiwa y'ar k'aramar zuciyarta yawa, zuciyar da batasan komai ba, haka kuma zuciyar da batasan kanta ba.
A hankali ta d'an jingina bayanta da jikin d'an drawer'n da takesa kayanta, kana asanyaye ta lumshe idanunta wanda sukayi luhu luhu, saboda kukan da tayi.
Kwarai tanajin bata da nutsuwa atattare da ita, yayinda tunanin Mahaifin nata ke yawo acikin zuciyarta, kasancewar duk yau bataje asibitin ba.
Wannan dalilin yasa duk taji hankalinta ya tafi izuwa gareshi.
Hakan yasa ta k'udurta aranta cewar komai dare sai taje ta ganshi.
Kasancewar tun daga yarintarta har zuwa yanzu, babu wata rana da ta tab'a wanzuwa har ta shud'e batare da ta saka Abboun nata acikin idanunta ba.
Haka kuma tasan koba komai ganinsa zai sanyaya mata zuciya, koda kad'anne haka kuma koda bazaiji sauti da amonta ba, zata sanar dashi abunda ke cikin zuciyarta.
Ahankali ta bud'e idanunta, inda ta sauk'esu, akan takardar y'ar jejeniyar da ta taho dashi batare da saninta ba.
Akaro na barkatai kenan da taji wani irin fad'uwar gaba, me had'e da bugawar zuciya ya rusketa."
Wanda har saida hakan yasa ta, maida idanunta ta lumshe.
Take kuma maganganun Malam Musbahu, suka soma dawo ma.
"Sun amince kan cewar zasu biyaki naira Million 50 idan kika amince da buk'atarsu na Auren MAJNOON!"
Maganganun da suke dawo wa cikin kunnuwanta kenan, Wanda suka kusa sa brain dinta hautsunawa.
"MAJNOON!!!"
Ta maimaita sunan akan labb'anta, sunan da jinsa ke sanya zuciyarta tsananta bugawa, sannan sunan da jinsa ayau yasa duk wani tunanin ta wargajewa.
Sunan da yake tsayar da shiga da fitan numfashinta na y'an wasu sakanni. Then
Sunan da takejinsa tamkar rubutaccen K'ADDARA ne acikin jininta.
Ahankali wasu irin siraran hawaye suka gangaro ta gefen fuskarta.
Yau ga rayuwa tana neman jefata acikin wata duniya ta daban, duniyar da bata tab'a tunani ko hasashen samun kanta aciki ba, K'addara na neman sauya ta, haka kuma gaba na neman juye mata izuwa baya.
Kwarai tana matukar fargaban rashin samun wata mafitar, domin tasan fuskantar hakan na nufin rasa mahaifinta .
Ahankali ta bud'e idanunta da suka d'anyi ja, tare da mik'ewa tsaye.
Kasancewar Kuma ansoma kiraye kirayen Sallah'n isha ne, yasa batare da tajira komai ba ta tada sallah.
Sallan daya d'auketa tsawon mintuna 8 kafun ta idar.
Ganin dare nayi ne kuma yasa batare da tayi doguwar addu'a ba, ta mike tsaye.
Had'e da sake gyaran zaman hijab din dake jikinta.
School bag dinta ta d'uko,
tare da zuge zip d'in, ta zaro 1k daga cikin kud'in da Noor ta bata.
Direct hanyar fita daga cikin d'akin ta nufa,
Saudiya Har takai bakin k'ofar fita, sai kuma ta tuna da takardar yarjejeniyar, da sauri ta dawo ta d'auka.
Dan mayar da ita ga Malam Musbahu, saboda acewarta babu wani amfani da takardar zatayi mata.
Dan bazata tab'a amincewa da buk'atar da zai kashe mata duk wani Fata da Burin rayuwarta ba.
Anutse ta fito daga cikin gidan nasu, tare da nufan babban titin dake shumfud'e agaban gidan.
koda ta iso titin kuwa tayi sa'ar samun taxi, hakan yasa batare da ta tsaya wani jayayya ba ta shiga.
Kaitsaye Nizamiye Hospital suka nufa, Kamar yanda ta fad'awa mai taxi din.
Tafiyar tasu da tayi nisa ne kuma yasa ta, yin kasa da kanta tare ta sauke idanunta akan takardar dake hannunta.
K'urawa takardar idanu tayi tsawon wasu mintuna kafun ta janye kanta gefe, inda ta maida kallonta ga titi, Sam ta ki bawa hawayen dake kwance acikin idanunta, daman zubowa.
Da tunani kala kala acikin zuciyarta, suka iso asibitin.
Yayinda
acan gefe mai taxi din yayi parking motar, wanda hakan yasa koda ta sallameshi saida ta d'anyi tafiya kad'an kafun ta iso mashigan asibitin.
Wanda yake kamar rana saboda wadataccen hasken dake wajen.
Ahankali take taka k'afafunta, yayinda kowanni taku da zatayi, ke tafiya da karfin bugun zuciyarta.
Daidai ta iso b'angaren da aka kwantar da Abboun nata ne kuma, taga gilmawan Dr. Mouhammad cikin sauri.
Hakan kuwa shiya sanya mata jin wani irin fad'uwar gaba.
Da sauri ta nufi hanyar d'akin Abboun, zuciyarta cike da fatan, kada fad'uwar gaban da taji ya zama wani abu na daban.
Cak haka ta tsaya da tafiyan da takeyi d'in saboda hango, Malam Musbahu da tayi, Wanda yake zaune agefen d'akin, ya kife fuskarsa acikin tafin hannunsa.
Duk da tasan cewar tuntuni su din masu damuwa ne, amma ganinsa yanzu da tayi ahakan yasa zuciyarta sake karyewa.
Asanyaye ta k'araso wajen, tare dasa hannu ta murd'a handle k'ofar d'akin da tasan Abboun na ciki.
Da wani irin k'arfi zuciyarta ta buga, wanda har takai ga sautin bugun zuciyar nata ya bayyana.
"Abbou!"
Ta fad'a da d'an k'arfi tare da soma k'arewa d'akin kallo, had'I da wurga idanunta tako ta Ina, ko zata ga Abboun nata, wanda taga babushi ba bu kuma alamarsa a inda tasan yake kwance.
"Abbouuuuu!!"
Ta sake kiran sunansa da k'arfi, tare kuma da juyowa cikin tashin hankali ta kalli Malam Musbahu,Wanda jin sautin muryarta ya sashi d'ago kansa ya kelleta.
"Abbou! Baffa Ina yake? Ina Abbouna?"
Tambayar daya fito daga bakinta kenan, cikin tashin hankalin da yasa duk jikinta fara tsuma.
Tambayar kuma da tasa Malam Musbah'un yin jigum, kana cikin sanyin murya mai dauke da damuwa yace.
"An maidashi ICU Soumaya saboda jikinsa ya k'ara tashi, numfashin da yakeyi ma yanzu ya tsaya, bamu da zab'I Soumaya domin ahalin yanzu muna gab da rasashi, likitoti sun tabbatarmin cewa matuk'ar basu iya ceto numfashinsa ayanzu ba, To saidai muyi hakuri....."
Ya k'are maganan cikin sanyin murya, had'i da gangarowan hawaye daga cikin idanunsa.
Soumaya kuwa Kanta ta soma girgizawa, yayinda duk jikinta ya d'auki rawa, Wanda har hakan yasa ta kasa furta kalman dake bakinta.
Saidai sabbin hawayen da suka tsinko mata tamkar ankunna famfo.
Ahankali ta soma jan jikinta baya, lokaci d'aya batare da tsayawa wani dogon tunani ba kuma ta juya, da yanayin tafiya mai kama da sassarfa, haka ta nufi wani wajen na daban.
Duk da kasa ruwan bata iya ganin inda take jefa k'afafunta, amma bata damu da hakan ba, saboda mai nutsuwa da hankali ne kad'ai, ke damuwa da inda zai sa k'afarsa, da kuma inda ya cire.
Tunani da bugun zuciyarta duk sun tsaya, tamkar yanda tayi imani cewa, ayanzu da za'a tsaga jikinta, baza'a tarar da jini yana gudana ba.
Kamar yanda take fusgar numfashinta kuwa, haka take fusgar k'afafunta, wa y'anda sukeyi mata barazanar Gaza d'aukar ta.
Awajen kuwa mutane da yawa ne ke kallonta. yayinda wasu kuma ke matsawa suna bata hanya, saboda yanda suka ga tana tafiya irin na way'anda babu nutsuwa ajikinsu.
Kaitsaye Office din Dr. Mouhammad ta nufa, yayinda tana isowa ta d'aura hannunta akan handle din kofar, tare da tura kofar ciki.
Da sauri Dr. Mouhammad dake tsaye, yana had'a wasu file dake gabansa, ya juyo tare da zuba mata idanu.
Ita d'inma idanun ta zuba masa, duk da cewar bata iya ganinsa sosai, saboda hawayen dake cikin nata idanun.
Dr.Mouhammad kuwa yanayinta daya kalla ne, yasa shi maida kallonsa ga k'afafunta wanda yaga suna rawa, tamkar wacce aka jonawa shocking.
"Soumaya."
Ya kira sunanta, cikin d'an yanayin mamaki saboda ganin da yayi tamkar bata cikin hayyacinta.
Idanunta ta rumtse saboda kiran sunan nata da yayi ne kuma yasa ta soma takowa zuwa inda yake.
Har saida ya rage bai wuce saura taku biyu atsakaninsu ba.
Kafun ta tsaya, tare da mik'a hannunta a hankali ta d'auki abun rubutu, (pen.) wanda ke gefen table dinsa.
Cikin karkarwan da duka hannayenta keyi, ta soma warware takardar dake duk'unk'une acikin hannunta.
Kasancewar Kuma takardar na left hand dinta ne, yasa ta rike abun rubutun da hannunta na dama.
Hakika ba zata ce tana fahimtar komai ba, saboda duhun daya fara rufe idanunta, yayinda kanta kuwa jinsa take yana wani irin juyawa.
Takardar dake hannun nata ta ajiye akan table din, tare da d'an sunkuyawa.
Sosai hannuwanta ke rawa, Wanda har hakan yasa pen din kasa zama daidai acikin hannun nata.
Ahakan kuwa ta d'aura pen din adaidai wajen signature.
Batare da tsayawa sauraran bugawar da zuciyarta keyi ba, kuwa tayi signing ak'asan takardan.
Kana ahankali ta d'ago da idanunta, Wanda suke aman ruwan hawaye, tamkar duka hawayen cikinsu zai k'are.
Paper'n ta mik'awa Dr. Mouhammad, had'e dayin k'asa da kanta ba tare kuma da ta d'ago ta kalleshi ba.
Cikin muryarta da bata fita da kyau, da kuma matsanancin kuka, had'i da raunin zuciyar da ayanzu yake shirin kaita izuwa wata sabuwar k'addarar.
*"N....A AMI...N..CE!!!!"*
Shine abunda ta fad'a, Wanda fad'ansa yasa ta rumtse idanunta da k'arfi, tare da zubewa k'asa kan guiwowinta.
*(Hmmmm ba'ama fara wasan ba, kamar yanda na fad'a muku a farko, MAJNOON daban yake da saura.)*
*8:00 pm*