Chapter 10
*MAJNOON!!*
(The innocentmad)
*Writting By*
Fatymasardauna
*Wattpad*
@fatymasardauna
*CHAPTER 10*
*FREEPAGE*
Dummmmmmm!!!
Haka sauti da amonjinta suka tsaya cak, yayinda zuciyarta tayi wani irin bugawa da k'arfi, wanda har saida hakan ya tilasta mata k'warewa, sanadiyar sweet potatoe'n dake bakinta wanda yayi mata wani irin Shak'a, hakan yasa take ta fara wani irin tari, had'i da furzar da abincin dake bakinta.
"Subahanallahi sannu Soumaya."
Malam Musbahu ya fad'a cikin d'an rud'ewa, tare da mik'o mata ledan ruwan pure water, cikin sauri saboda yanda yaga tana tarin kamar zata shid'e.
da sauri kuma cikin rawan jikin da takeyi ta karb'i ledan pure watern, tare da kaiwa bakinta.
Ci gaba da kakkarwa jikinta yayi, alokacin da ta gama shanye duka ruwan, yayinda k'irjinta ke wani irin bugawa, zuciyarta kuwa tuni dama ta soma wani irin bugu, wanda sautin amonsa ke bayyana.
Yayinda filla filla kalaman da Baffan ya fad'a, ke dawowa cikin kanta.
"AURE!!"
Ta maimaita kalmar da jinta ya matuk'ar hautsuna tunanin ta, haka kuma ya d'aid'aita duk wani nutsuwarta.
Hak'ik'a duk da tasan cewar ta amincewa Auren, amma ko kusa bata tab'a kawowa aranta cewar Auren za'ayisa nan kusa ba, saidai jin hakan ayanzu yasa ta shiga cikin tashin hankali marar misaltuwa.
Lokaci d'aya hawaye suka kwaranyo daga cikin idanunta, kana ahankali ta soma girgiza kanta cikin rawar muryar dake nuna asalin gazawarta tace.
"Bazan iya ba Baffa, Aure gobe batare da Abbouna ya sani ba, makaranta na komai nawa fa? Bansan suwaye suba, bansan tayaya zanyi rayuwa dasu ba, ni ban amince da buk'atarsu, dan suyimin aure cikin gaggawa ba, Baffa bazan iya ba..."
Ta k'are maganan tana me tsurawa Baffan idanu, yayinda hawaye ke d'iga mata tamkar an kunna famfo.
Hawayen nata ne kuma yasa jikin Baffan yin sanyi, wanda hakan ya sashi fesar da numfashi me d'umi, murya araunace yace.
"Bamu da zab'i Soumaya, bamu da wani iko ko daman hana hakan, kin amincewa buk'atarsu tun farko, wannan dalilin yasa bamu da daman, mu sa musu buk'atarsu koda me suka zo, ni kaina fargaba nakeyi, inakuma jin tsoron irin sabuwar rayuwar da zaki fuskanta, ina matuk'ar jin tsoron kasantuwarki acikin wannan ahalin, Wanda girma da matsayinsu ya wuce gaban kwatance, saidai akwai Allah akan komai, kuma ya isar miki, duk da Dr. Mouhammad ya tabbatar min da cewar, zaki ci gaba da karatun ki, amma bansan wasu irin k'alubale ne ke jiranki ba, tabbas nayi kaicon wannan rana, ranar da babu zai jefa ki acikin sauyayyar RAYUWA."
Hawaye masu tsananin zafi ne suka sake kwaranyo wa daga cikin idanunta, araunace ta lumshesu, tare dasa hannu ta dafe kirjinta, Wanda takejin zuciyarta na bugawa fast fast acikinsa.
Tabbas ayanzu a kuma rana irin ta yau, tasan cewar ta rasa duk wani fatanta.
Daga yanzu ne kuma sautin amon bugun zuciyarta zai sanja, k'addara kuwa itace zata tayi mata yawo acikin jininta.
Sabuwar rayuwa sabon k'alubale.
"Soumaya."
Baffa ya k'ira sunanta murya asanyaye, batare daya jira amsawarta ba kuma ya d'ora da cewa.
"Bayin kanki bane, K'addararki ce tazo ahaka, yana kuma daga cikin d'abi'a mai kyau yin imani da k'addara mai kyau ko mummuna, duk wani abu da yake faruwa ko kuwa yake shirin faruwa, rubutaccene, kiyi hakuri kinji, babu wani k'unci da zai d'ore!"
"Wacce irin k'addara ce wannan Baffa? Wace irin k'addara ce haka da take kokarin tarwatsa rayuwata? sannan wacce irin k'addarace haka dake barazana ga rayuwata? K'ADDARAR Auren MAJNOON shine k'addarata? ko kuwa sunan MAJNOON dake sanya bugun zuciyata tsananta, aduk sanda sautin amon sunan ya shiga kunnuwa na? Koda amafarki koda sau d'aya ban tab'a kawowa araina cewar rayuwa ta zata canja haka ba Baffa, ban tab'ajin cewar zanyi nesa da Abbou na ba, bansan damuwa ba, bansan cewa kuka na iya zautar da tunanin mutum ba sai ayanzu, ayanzu da narasa duk wani gata na, na rasa mai sauraran bugun zuciyata, bugawar da take haddasamin tsananin tsoro acikin kowani second na rayuwata, burin Abbou akullum shine na girma, nayi karatu har nazama Likita, burinsa shine ya zab'amin mijin Aure da kansa, amma yau gashi k'addara, tasa na zab'arwa kaina, k'addara ta kawo wani gareni, wani da bansan shi ba, sannan wani wanda ya kasance me nak'asu acikin rayuwarsa, nayi imani duk randa Abbou ya bud'e idanunsa, bazai tab'a yafemin ba, kamar yanda Burukana suka ruguje, haka fatana ya tawaya,!."
"Baffa!!"
Ta kira sunan Baffan, tana me matsowa kusa dashi, tare da sanya hannayenta ta dafe k'afafunsa.
Cikin rauni hadi da kukan dake neman cin k'arfinta murya na rawa tace.
"Idan Abbouna ya bud'e idanunsa, ka fad'a masa cewar na amince ne kawai saboda shi, saboda ina matuk'ar buk'atarsa arayuwata, kamin alk'awarin tafiya atare dashi, ka kulamin dashi, dan Allah Baffa idan ya bud'e idanunsa, kayi mishi albishir da cewa Ina cikin halin lafiya, koda na cutu kada ka sanar dashi Baffa, kada ka sanar dashi hakan....."
Matsanancin kukane ya k'wace mata, Wanda hakan yasa ta kife kanta ta shiga rera kukanta me tsuma zuciya.
Kukan da Malam Musbahu bayajin zai tab'a iya rarrashinta, saboda yayi imani kukane dake tasowa tun daga k'asan zuciyarta, kukan da yinsa yasan zai rage mata rad'ad'i na zafin da zuciyarta keyi.
Hawayen da suka sauk'a akan fuskarsa ya share, tare dasa hannu ya d'agota.
Murya araunane yace.
"Bazaki cutu ba Soumaya, Insha Allah bazaki tawaya ba, burukanki bazasu disashe ba, ke y'a d'aya tilo ce acikin dubu, zama da Nakasashe kuma ba kasawa bace, Zama da MAJNOON bashi ke nuna yankewar farinciki arayuwarki ba, WATARANA Soumaya komai zai sanja,WATARANA Auren MAJNOON zai zamo
katanga kuma kariya agareki, bazaki tab'ayin Danasani ba, ki daina kukan nan kinji, kukan ki yana k'ara karyarmin da zuciya, dan Allah kiyi shiru."
Ya k'are maganan yana me tausasa harshensa, domin har acikin jikinsa yakejin Soumayan tamkar y'ace agaresa.
Jin abunda ya fad'a d'inne kuma yasa ta soma, rage sautin kukan nata, duk da kasancewar sau da yawan lokuta bata iya controlling kanta, amma kamar yanda takejin maganan Abbounta, haka ya zama dole taji na Malam Musbahun ma, dan koba komai yanzu shine take kallo amatsayin Abbounta, shi kad'aine wanda ya damu da lamarinsu.
Ganin hakan kuwa shiyasa Baffan sakin ajiyar zuciya, tare da mikewa tsaye bayan ya rufe jakan da mak'udan kud'ad'en ke ciki.
Tashi muje na tara miki taxi ki koma gida, nasan bazaki rasa y'an wasu abubuwa da zakiyi ba, ni kuma Insha Allah zanyi duk wani abunda ya dace, saboda Dr. Mouhammad ya sanar dani cewa, zaiyi duk wani abu daya kamata, zuwa gobe ko jibi da sassape zamu tafi, saboda acewarsa tunda ansamu kud'in to agaggauta yi masa aikin, amma gobe Insha Allah zanzo da safe."
Baffan ya fad'a yana me lalub'o y'ar wayarsa keypad dake cikin aljihu.
Soumaya kuwa jin abunda yace ne yasa ta tashi tsaye, tare da juyawa ta zubawa fuskar mahaifinnata dake kwance idanu.
Wani irin kallo takeyiwa fuskar tasa na daban, kallon da takejin tamkar bazata sake yi masa irinsa ba.
Wannan dalilin yasa anutse ta soma takawa harta k'arasa jikin gadon da Abboun ke kwance.
Hannunta dake rawa ta d'aga ahankali ta d'aura akan nasa, tare da sunkuyowa ta d'aura bakinta adaidai saitin goshinsa.
Kiss ta manna masa irin wanda ke nuna tsananin soyayyarta a gareshi, kasancewar ta lumshe idanunta ne kuma, yasa hawayen dake tare acikin idanun nata, d'igowa akan fuskarsa.
"Zanyi kewarka Abbouna, fiye da yanda zuciya da gangar jiki suke tunani, zanyi kewarka sosai, magananka, dariya, harma labaranka da komai, duk da haka amma zan zauna zaman jiranka, inafatan sake ganinka arayuwata, inafatan sake jin motsi, da kuma sautin muryarka acikin kunnuwana, Inasonka Abbou, inasonka sosai...!!"
Ta k'are maganan cikin rawar murya, had'i da raunin zuciya, Wanda ke sake cin k'arfinta akowanne second.
Ahankali ta kuma rumtse Idanunta, tare da k'ara matse hannunsa dake cikin nata k'am.
Ji takeyi tamkar karta tafi ta barshi.
Amma babu yanda zatayi, tunda K'addara ta riga da ta fara wasa da rayuwarta.
"Soumayatu!"
Baffa ya kira sunanta, gudun kada ta sake fashewa da wani sabon kukan.
Wanda hakan yasa ahankali ta zare hannunta daga na Abboun, cikin kuma dauriya dason gusar da kukan dake son cin k'arfinta, ta sa hannu ta share hawayenta.
Batare data sake cewa komai ba, kuma ta juya tare da nufan hanyar fita daga cikin d'akin.
Duk yanda taso daurewa kuwa ta kasa, RAUNI takeji acikin zuciyarta sosai, Raunin da yake d'aukewa hawayen dake cikin idanunta control.
Hannu ta d'aura akan handle din k'ofar, tare da juyowa ahankali ta sake sauk'e idanunta akan Abboun.
Hawaye masu dumi ne suka silalo kan k'uncinta, ahankali kuma cikin d'an yanayin sanyin da jikinta yayi, ta bud'e kofan ta fita.
Wanda ganin hakanne kuma yasa Malam Musbahu rufa mata baya.
Yayinda Kaitsaye suka nufi hanyar fita daga cikin asibitin.
Saidai kuma duk da cewar tafiya sukeyi, amma kowannensu da irin tunanin da yake sak'awa acikin zuciyarsa.
Musamman Soumaya.
Ahaka dai har suka fito wajen asibitin, inda suna fitowa cikin sa'a, idanun Malam Musbahu suka sauk'a akan wani mai keke napep da yazo wucewa.
da sauri yasa hannayensa ya tareshi, ganin ya tsaya d'inne kuma, yasa shi juyowa ya kalli Soumaya wacce idanunta ke kallon gefe, da dukkan alama kuma hankali da tunanin ta ya tafi izuwa wani waje ne na daban.
"Soumaya Shiga kuje sai nazo gobe da safen."
Baffan ya fad'a yana me ciro kudi daga cikin aljihunsa ya bawa mai adaidaita sahun.
kamar kuwa yanda duk jikinta ke asanyaye, haka ma yanayinta wannan dalilin yasa asanyaye ta shiga Napep din, bayan ta zauna ne kuma ta jingina kanta ajikin wani karfe, had'i da lumshe idanunta, Wanda har zogi takejin sunayi mata saboda tsabar kukan da tayi, gashi sunyi luhu luhu sunyi k'anana.
Mai Napep din kuwa jin ta shiga ne yasashi jan napep d'in sukayi gaba,
Inda Baffa dake tsaye kuwa har saida yaga sun d'anyi nisa, kafun ya juya ya koma cikin asibitin.
Kasancewar yasan Dr. Mouhammad yana jiransa.
Ab'angaren Soumaya kuwa,tunda ta shiga cikin Nepep din bata bud'e idanunta da suke alumshe ba, kamar yanda kuma har zuwa yanzu zuciyarta bata daina bugawa da k'arfi ba, daga gefe guda kuwa, wani irin ciwon kai da zazzab'i ne suka dirar mata, Wanda yanzu kusan sati kenan da take fama da zazzab'in.
Saidai ko sau d'aya bata sha magani ba.
Gaba d'aya a hargitse kwakwalwarta take, wannan dalilin yasa ta kasa kama tunani d'aya da zatayi.
Tana acikin wannan yanayin nata ne kuma, taji Napep din ya soma kokarin tsayawa, Wanda hakan yasa ta bud'e idanun ta.
"Yauwa anan zan sauk'a."
Ta fad'a asanyaye saboda ganin da tayi mai napep din yana kokarin wuce kofar gidan nasu.
Jin kuma tace anan zata sauk'a ne yasa shi parking napep din.
Wanda hakan yasa Anutse ta fito, sanin cewar Baffa ya biyasa kudin Napep dinne kuma, yasa kaitsaye tana fitowa ta nufi kofar gidan nasu.
Daidai ta kusa iso kofar gidanne kuma, taga wata bak'ar mota na fuskantar ta.
Wanda hakan yasa ta d'an zubawa motar idanu.
Musamman ayanzu da taga an bud'e murfin motar, hakan yasa ta zak'u dason ganin wanda zai fito.
Saidai kuma ganin wacce ta fito daga cikin motar ne, yasa ta sauk'e wani irin sassanyar ajiyar zuciya, had'e da d'an lumshe idanunta.
"Meye haka naga kaman kintsorata ba kiyi expecting gani na bane?."
Noor wacce itace ta fito daga cikin motar ta fad'a tana me k'arasowa inda Soumayan take.
Saidai kuma ganin yanayin fuskar Soumaya'n, yasa ta tsayawa turus tare da kafe Soumayan da idanu, kana cikin yanayi irin na damuwa, murya asanyaye tace.
"Soumaya what's wrong? Dan Allah karki fad'amin cewa jikin Abbou ne ya sakeyin tsanani."
Idanunta da sukayi nauyi kana suke kuma bayyana tsananin damuwar dake kwance acikin zuciyarta ta bud'e.
Kallon Noor din tayi, ahankali kuma ta soma motsa jajayen Labb'an bakinta, dan son furta abunda ke cikin zuciyarta, saidai duk yanda takai ga lank'wasa harshenta donyin magana takasa.
Ganin hakanne kuma yasa Noor, zuba mata ido, tare da soma karantar yanayin fuskar ta.
Atake kuwa ta fahimci yanayin Soumaya'n, Wanda hakan yasa ta kamo hannunta,.
Murya d'auke da damuwa tace.
"Nasani Soumaya you're not okay, but yau yanayinki yayi daban, muje ciki kisanar dani abunda ke damunki."
Noor d'in Ta k'are maganan tana me jawo hannun Soumayan suka nufi cikin gidan su kaitsaye.
Da sallama d'auke abakin Noor suka shiga cikin gidan, Wanda hakan yasa Moudou dake zaune atsakar gidan, tana surfa wake ta amsa, tana me d'ago kanta ta kallesu.
"Ina wuni Moudou."
Noor ta fad'a tana me kawar da kanta gefe, saboda Allah ya sani kwata kwata batason matar, saboda yanda take musgunawa rayuwar Soumaya.
Kamar yanda Noor din batason Moudoun kuwa, itama Moudoun hakane a b'angaren ta, dan yanzu ma harara ta watsa mata, batare kuma da ta amsa ba ta cigaba da aikin da takeyi.
Sam Noor bata damu da hakan ba, domin ita ba bak'uwar gidan bace, halin Moudou kuma babu Wanda bata sani ba, shiyasa batare da ta sake cewa komai ba, kaitsaye tanufi d'akin Soumayan, wacce take biye da ita abaya.
Suna shiga Noor ta tura k'ofar ta rufe, tare da juyawa ta kalli Soumaya'n.
Wacce take kokarin zare hijabin dake jikinta, tare da zama agefen katifarta.
"Ya jikin Abbou'n, wato da nace miki zanzo mu tafi tare, shine kikayi tafiyarki ko."
Noor din ta fad'a itama tana me zama akusa da Soumaya'n, wacce da k'yar labb'anta suka iya furta kalmar "Da sauk'i."
Shiru gaba daya dakin ya d'auka, yayinda Noor ke kallon Soumaya, wacce duk yanayinta ya sanja.
"Soumaya."
Noor ta kira sunanta ahankali, hade dasa hannu ta dafa shoulder dinta, still batare da ta jira amsawarta ba, cikin kulawa tace.
"Shiru baya maganin damuwa kinsani , kuma kowa ya ganki yasan cewa kina cikin damuwa, SouMaya ba haka kikeba, look at your eyes, sunyi ja sunyi k'anana, hakan Kuma alama ce dake nuna cewar kinyi kuka da yawa, why Soumaya? I told you Insha Allah Abbou he will be fine, to meyasa kikesa kanki a damuwa, What happened? Tell me then karki manta I'm your bestie, idan bakiyi sharing damuwarki dani ba, waye zaki gayawa?."
Hawayen dake cikin idanunta ne suka gangaro, yayinda tausayin kanta da kuma rayuwarta, suka sake narkar mata da zuciya.
Hakanne kuma yasa cikin sanyi ta soma motsa jajayen lips dinta, kana araunace tace.
"AURE zanyi,!Gobe za'a d'auramin AURE Noor!!"
Kirjin Noor ne yayi wani irin bugawa, Wanda hakan yasa ta tsurawa Soumayan idanu, tamkar wacce taga bak'uwar halitta.
Gaba d'aya kalaman Soumayan jinsu tayi abaibai, Wanda hakan yasa cikin son tantance abunda kunnuwanta sukajiye mata tace.
"AURE? Are you serious Soumaya Aure fa kikace? Aure, please banason wasa tayaya ma zakiyi Aure ayanzu? bayan haka ma kuma wai gobe? gaskia ina tunanin ba adaidai kike ba Soumaya."
Noor ta k'arasa maganan tana me girgiza kanta, cike da alamun rashin gamsuwa.
"Serious Noor, I'm getting Married, zanyi Aure Noor zan auri wani, wani daban wanda bansani ba, zanyi Aure kamar yanda K'addara ta ta tsaramin...."
Soumayan ta fad'a muryarta na rawa, yayinda takejin wani irin abu na game duk wani sassa na jikinta.
Noor kuwa da mamakin kalaman Soumayan suka kusa cika zuciyarta, kai ta cigaba da girgizawa, kana kuma cikin kuma rashin gamsuwa tace.
"Har yanzu ban fahimci inda kalamanki suka dosa ba Soumaya, tayaya zakice min zakiyi Aure Gobe, meyasa? waye kuma zaki aura? Ni duk ban fahimta ba, ki ganar dani ko ki sanar dani cewa wasa kikemin."
"I'm not joking Noor, I'm telling you truth, Zanyi Aure saboda Abbouna, bani da wani zab'I Noor, bani da zab'in daya wuce wannan, adaidai lokacin da Uba mahaifi ke buk'atar taimako, babu wani abu da zan iya wanda ya wuce wannan, shiya bani farincikin dana ginu akansa, shiya bani k'warin guiwan, dana fara fuskantar rayuwa dashi, shi ya zamemin k'ashin baya, Tayaya zan bari na rasashi alokacin da kasantuwarsa acikin rayuwata yake da matuk'ar muhimmanci?, Tayaya Noor..."
Tayi maganan da muryar dake bayyana Rauninta, muryar da jinta kad'ai ya isa raunta zuciyar mai sauraro.
Idanu Noor ta rumtse da k'arfi, lokaci daya kuma taji zuciyarta ta karye, Wanda hakan yasa ad'imauce tace.
"Kina nufin saboda Abbou zakiyi aure? Saboda kud'in Surgery din da za'ayi masa?, nakasa fahimta Soumaya, dan Allah ki fayyacemin komai cause kinsani a duhu."
Tak'are maganan tana me dafa kafad'an Soumayan,
Wacce ta jinjina mata kai, tare da sa hannu ta share hawayen dake fuskarta.
"Waye zaki Aura?"
Noor ta tambaya hawaye suna me cika idanunta.
"MAJNOON!!"
Labban bakinta suka furta kalman, da jinsa kesa dodon kunnuwanta amsa amo.
Kamar dai yanzu da fad'an kalmar yasa, ta jin fad'uwar gaba, hadi da tsinkewar zuciyar, da yasa ta amsan sak'o daga kowani mashigan iska na jikinta.
Noor kuwa jin abunda Soumayan ta fad'ane yasa ta zazzaro idanunta. Murya na rawa Ta maimaita sunan
"MAJNOON!!"
cike da mamaki had'I da firgici.
"MAJNOON Soumaya? MAD irin wanda na sani? Masu bin shara suna d'aukan Dirty? MAD masu buge buge da duke duke? MAD masu saka yagaggun kaya, masu datti? Masu cin duk wani abu marar kyau? Ki amsa min Soumaya, ki amsamin cewar kunnuwana ne basuji da kyauba, ki amsamin cewar ba mahaukaci zaki aura ba!!"
Noor ta k'are maganan tana me d'an jijjigata.
Wanda hakan yasa ta rumtse Idanunta da k'arfi, tare da fashewa da wani irin kuka mai tab'a zuciya, kukan dake fallasa asirin zuciyarta, jiki na rawa kuma
Cikin muryar kukan tace.
"Bansani ba Noor, I don't know him, I don't know..."
Hawayen da yake cikin idanun Noor ne suka zubo kan k'uncin ta, lokaci d'aya kuma duk jikinta yayi sanyi, Wanda hakan yasa cike da tsananin tausayin Soumayan, ta jawota jikinta.
Lallai ta tabbata k'addarace kad'ai zata had'a Soumaya Aure da MAJNOON.
"I'm so sorry Soumaya, I believe kowa da irin k'addararsa, ke taki k'addarar ahaka tazo, I'm sorry, then stop crying, duk da bansan iya adadin da kika d'auka kina kuka ba, amma hakan ba shine solution ba, karki sawa zuciyarki damuwa, komai mai wucewa ne please Maya"
Tayi maganan tana me shafa bayan Soumaya'n ahankali, Wanda kuma hakanne yasa Soumayan sassauta kukan nata.
Tare da lumshe idanunta ta kwanta ajikin Noor din, zuciyarta na radad'i.
hakan kuwa shi ya sanya d'akin yin shiru, har na tsawon wasu y'an mintuna, kafun ahankali Noor din ta soma jiyo, sautin numfashi da kuma yanda Soumaya'n ke sakin ajiyar zuciya akai akai.
"Soumaya."
Noor Ta kira sunan Soumayan tana me lek'a fuskarta.
Ga mamakin ta kuwa sai taga Soumayan tayi bacci.
Ajiyar zuciya ta sauk'e, tare da d'an muskutawa ta gyarawa Soumayan kwanciya.
Tabbas har cikin zuciyarta take matuk'ar Jin tausayin ta.
Musamman ayanzu da ta ke k'arewa kyakkyawar fuskarta kallo, ita din irin matan nanne na musamman, Wanda ita kanta da take mace tayi imani cewa, Soumaya kyakkyawace ta k'arshe, matsayin kyawunta ya d'arawa wasu daga cikin maza, Soumaya macece da kyau da dirinta suka d'arawa duk wani Namijin da yakejin ya isa, amma kuma sai gashi bisa taimakon k'addara, wannan kyaun nata na kokarin tafiya ta wata hanyar, yayinda Fatan rayuwarta ke shirin rugujewa duk ata dalilin MAJNOON!!.
Ajiyar zuciya ta sauk'e akaro na barkatai, kana kuma cikin sanyi ta mik'e tsaye.
D'an Siririn agogon dake hannunta ta kalla, ganin da tayi lokaci ya tafi ne kuma yasa ta, gyara zaman siririn mayafin dake jikinta, kasancewar tayiwa mahaifiyarta alk'awarin cewa bazata jima ba, wannan yasa ganin Soumayan ta samu bacci, yasa ta juya tare da nufar k'ofar fita daga d'akin.
Cikin sauri Moudou dake lab'e abakin k'ofar tun d'azu ta koma baya, tare da soma sakin wani irin shu'umin murmushi.
Wanda hakan yasa Noor da ta fito juyawa ta kalleta, saidai batare da ta ce komai ba, kaitsaye ta fice daga cikin gidan.
Moudou kuwa murmushinta ta cigaba dayi, kasancewar duk wani maganganu da Soumayan su kayi da Noor acikin kunnenta.
After 2 hours later.
Daidai lokacin da aketa kiraye kirayen sallan azahar, Soumayan ta bud'e idanunta wanda takejin sunyi mata nauyi.
Kamar kuma yanda ta kwanta da k'uncin zuciya haka ta tashi, duk jikinta babu dadi, bayan ciwon da kanta keyi kuwa,zafin fever dinnata ya sake k'aruwa, Wanda hakan yasa adaddafe taje ta yi alwala, tare da dawowa ta tada sallah.
Koda ta idar da sallah'n kuma sake komawa tayi ta kwanta, duk da cewar babu ko d'igon bacci a idanunta.
Amma zazzafan zazzab'in da take fama dashi ya hanata sakat.
Ahaka dai ta k'are wunin nata na yau, wunin da acikinsa babu wani abu na dad'i ko sassauci da taji.
Wunin da tayisa cikin zullumi da fargaba mai tarin yawa.
Koda dare tayi kuwa, tamkar yanda taga rana yau dinma haka taga dare, domin bacci k'auracewa idanunta yayi, duk yanda taso samun nutsuwar zuciya kuwa ta gaza.
Tunanine kala kala acikin Brain dinta, tamkar zasu fasa mata k'wak'walwa.
Yayinda sannu ahankali kuma zazzab'in dake jikinta ya sake hawa, inda jikinta ya d'auki zafi zaauu kamar wuta.
Saidai kuma duk da zafin ciwon da takeji, hakan bai hanata shiga fargaba ba.
Hak'ik'a tsoro takeji, tsoron ruskar safiyan gobe, ranan dake kokarin zamantowa, d'aya daga cikin ranakun da bazata tab'a mantawa dasu ba, acikin gaba d'aya tarihin rayuwarta, Ranar da ta kasance me barazana ga rayuwarta, Ranan da zata nisanta ta da mahaifinta, ranan da zata kaita izuwa wata duniya na daban.
Haka kuma ranar da zata kasance mafarin K'addara.
Yawan tunanin da tayi dinne Kuma, ya haifar mata da k'arin ciwon kai had'i da zazzab'in da take fama dashi.
Wanda hakan yasa har k'arfe 4, idanunta basu ko lumshe ba bare su rimtsa, saidai hawaye kawai dake tsiyaya acikinsu, wanda ita kanta tasan da ace hawaye na k'arewa, To da nata hawayen sun k'are a daren yau.
*Washegari*
Sannu ahankali gari ke sakeyin haske, Wanda hakan yasa hasken rana ke sake wanzuwa asararin samaniya.
Yayinda adaidai wannan lokacinne kuma, zuciyar innocent girl din dake kwance ad'aki cikin zullumi ke barazanar tarwatsewa.
Tsoron yau din take. Domin kuwa yau d'in, shine RANA d'aya tilo da zai sanja rayuwarta, ranar da K'ADDARAR da aka rubuta acikin jininta zai soma motsawa, Ranar da bugun zuciyoyi biyu zasu tsananta.
Tabbas Ayau wani tarihin zai soma.
Kamar yanda yau din ya kasance rana wacce bazata sake maimaituwa ba.
Ranar da ta saka masa suna RANAR K'ADDARA.
RANAR bugun zuciyoyin da aka ginasu akan tushe da abu d'aya.
Zuciyoyin dake nesa da juna.
Wannan ba k'addara bace, Fata ne, sannan mafarkine da kuma BURI.
*(Hey Guys saura one page fa Freepage ya k'are Insha Allah, sai ku zama ready. MAJNOON kuwa yanzu aka fara? Yanzu ne za'a bude Shafin farko labarin, biya payment dan kusha karatu🥂
*9:00 pm*