Chapter 12
*MAJNOON!!*
(The innocentmad)
*Writting By*
Fatymasardauna
*Wattpad*
@fatymasardauna
*CHAPTER 12*
Fatan rana d'aya tak da sunan MAJNOON zai goge daga cikin rayuwarsu.
Bayan ya gama raba su mintuna da goronne kuma ya, d'ago da kansa ya kalli Baffa, ahankali kuma cikin tausasa murya.
batare daya duba girman matsayi da kuma ikonsa ba yace.
"Alhamdulillah Malam Musbahu,mungode k'warai da irin karramawar da kukayi mana, munji dad'i sosai, saidai kuma kamar yanda yake a al'ada, tunda har an riga da an d'aura aure, To munaso zamu tafi da amarya."
Wani irin duka kirjin Malam Musbahu yayi, Wanda har saida ya haddasa masa jin, fad'uwar gaba.
Saboda sai ayanzunne yakejin wani iri dangane da batun Auren Soumaya'n.
Sai ayanzu yakejin ciwo da kuma zafin abun.
Yayinda yaji wani irin tausayinta ya tsarga mai.
Tabbas yasan cewar ya d'aurawa kansa wani nauyi, nauyin da baisan tayaya ne zai iya sauk'eshi ba.
Nauyin fargaban ranan da zai fuskanci mahaifinta.
Duk da kuwa yasan cewar bashi da zab'i, amma yana jin nauyin abun acikin ransa.
Numfashi ya d'an fesar a hankali, tare da yin shiru, tamkar wanda ya nisa acikin duniyar tunani.
Ganin hakanne kuma yasa, Billionaire Dawoud Saraki, sauk'e numfashi Tare da sake gyara zama ya tankwashe k'afafunsa.
Anutse kuma still
Cikin tausasa murya yace.
"Damuwa mai yawa ta bayyana akan fuskarsa Malam Musbahu, Wanda tasa na fara kokwanton cewa, kodai akwai matsala ne.?"
Kai Baffan ya girgiza da sauri, tare da k'ak'alo murmushin daya fi kama dana dole, ya d'aura akan fuskarsa.
"Ko d'aya billionaires babu wata damuwa, kamar yanda ka buk'ata kuwa bari na shiga ciki sai na gaya musu."
Ya k'are maganan yana me mik'ewa tsaye, tare da nufan cikin gidan kaitsaye, inda yakejin zuciyarsa na bugawa, haka kuma fargabansa na k'ara k'aruwa.
Fargaban d'auke Soumaya'n daga gidan mahaifinta izuwa wani waje na daban.
Wanda baisan meye hakan zai haifar ba.
Da wannan tunanin acikin zuciyarsa ne kuma, ya k'arasa shigowa cikin gidan, bakinsa d'auke da sallama.
Inna Hauwa dake can cikin d'akin Soumayan, tana me harhad'a kayan Soumayan waje d'ayane ta amsa, tare kuma da d'an lek'o kanta waje saboda muryar Mijin nata da taji.
Tana lek'owa kuwa sukayi kicib'us da juna, saidai kuma amma yanayin Ganin fuskar tasa adagule ne, yasa ta sakin labulen d'akin tare da k'arasowa inda yake.
"Malam lafiya kuwa kodai wani abunne ya sake kunno kai?."
Ta fad'a cikin yanayin damuwa.
Wanda hakan yasa Malam Musbahun sauk'e ajiyar zuciya, tare da d'an girgiza kansa, murya ya asanyaye yace.
"Ko d'aya babu wani abu Hauwa, saidai tsananin damuwar dake damuna, dan gane da Auren Soumaya da aka d'aura yanzu, fargaba nakeji Hauwa ta yanda zan mik'a Soumaya ga MAJNOON!, saboda sunce yanzu suke so su tafi da ita, ina cikin damuwar halin da Soumaya zata fuskanta k'warai, duk da nasan cewar wannan auren k'addara ne, amma zuciyarta bazata iya d'auka ba, duk da ba k'aramin gida zata shiga ba, saidai akwai tauye hakki acikin hakan, idan ita ayanda take da k'ananan shekaru ta amince, mu da muke sama da ita bai kamata mu amincewa hakan ba, Aurenta da MAJNOON babban cutarwa ne, inajin tsoro da kuma fargaban, randa Abboun ta zai bud'e idanu ya neme ta, mezance masa Hauwa? Me zance masa? Na aurar da y'arsa shine amsan da zan basa? na aurar da y'arsa ga MAJNOON?."
Shiru ya d'anyi tare da soma girgiza kai, saboda yasan tabbas ranar zata zo, hakan kuwa da yayinne yasa Inna Hauwan, hango hawayen dake kwance acikin idanunsa.
Wannan dalilin yasa asanyaye kuma cikin son kwantar masa da hankali tace.
"Auren Soumaya da MAJNOON ba yin kanmu bane Malam, k'udurar Allah ne, haka kuma k'addarace da aka rubuta ta da manyan bak'i, Wacce bazata tab'a gogewa ba, Insha Allahu kuma rayuwar Soumaya bazata tagayyara ba, Auren MAJNOON bashi zaisa rayuwar ta watsewa ba, Insha Allah, Allah zai kula da lamarinta, dan haka muyi abunda suka buk'ata, bari naje na turo maka ita, kad'an tausheta idan yaso sai su tafi da itadin kamar yanda suka buk'ata."
Ta k'are maganan tana me juyawa, ta nufi cikin d'akin Soumaya'n.
Wacce har yanzu take a kwance, yayinda ayanzu duk jikin nata ke lullub'e da bargo.
"Soumaya!"
Inna Hauwa Ta kira sunanta cikin sanyin murya, tare da d'an lek'a fuskarta, dan tantance ko bacci takeyi.
K'iran sunan daya sanya ta had'iyan wani abu daya tokare mata mak'oshi.
Duk da kuwa cewar taji sauti da amon kiran acikin kunnuwanta, amma sam ta kasa bud'e lumsassun idanunta.
Kamar dai yanda ta kasa iya sarrafa harshenta wajen amsa kiran.
"Soumaya! Soumaya tashi Baffanki ne ke k'iranki."
Inna Hauwan ta fad'a, cikin d'an d'aga sautin muryarta, yanda tasan Soumayan zata jiyota.
Jin hakan da tayi ne kuma, yasa ta jin wani kalan sabon fad'uwar gaba ya shigeta, Wanda har saida hakan yasanya yanayin bugun zuciyarta sanjawa.
Lokaci d'aya kuwa fargaba ya shigeta. sanadin hakan yasa numfashinta soma yankewa.
Akaron farko na rayuwarta da taji fad'uwar gaba dan gane da k'iran Baffa'n.
Wanda dalilin hakan yasa ta bud'e idanunta a hankali.
Cikin kuma tsoro da fargaban Abun da tasan kunnuwanta zasu je, su jiyo daga bakin Baffa'n, murya na cracking tace.
"Inna Hauwa Baffa zai fad'amin cewar anyimin Aure ne ko?, tsoro nakeji Inna, saboda zuciyata bugawa takeyi da k'arfi, inajin tamkar zan fuskanci wani abune na daban acikin rayuwata, kullum haka nakeji, ajikina cewar wani abu zai faru dani..."
Idanun Inna Hauwa ne suka cicciko da hawayen tausayinta.
Saidai kuma gudun kada ta karyar mata da zuciya, yasa ta shanye hawayen hade da tausasa murya, cikin kulawa tace.
"Karki damu Soumaya, komai da yake faruwa dama rubutaccene, Allah kuma baya d'aurawa bawa, abunda bazai iya ba, karkiyi bakinciki kinji, tashi kije yana jiranki azaure karb'a mayafinnan kisa."
Inna Hauwan ta fad'a tana me mik'o mata wani farin mayafi mai d'an kauri.
Yunk'urawa tayi ahankali ta tashi zaune,
Jiki asanyaye kuma ta mik'a hannu ta karb'i mayafin, tare da d'an yafashi ajikinta.
Ahankali ta soma yunk'urin tashi tsaye, saidai kuma kasancewar duk jikinta babu k'arfi ne, yasa dole saida ta dafa bango kafun ta iya tafiya, ahaka harta fice daga cikin d'akin.
Tana me tunanin yanda zata kwatanta iya adadin beating din da heart dinta keyi.
Beating din da akowanne takunta d'aya, yake k'ara tsananta.
Isowarta cikin d'an madaidaicin zauren gidan nasu ne kuma, yasa ta tsayawa, inda ta zubawa Baffan dake tsaye idanu.
Wanda Babu wani alaman kwarin guiwa ko farinciki atattare dashi.
"Baffa!"
Takira sunansa da raunanniyar muryarta, wacce tafi yanayi da muryar kuka.
Ahankali ya d'ago kansa, Wanda hakanan yaji ya kasa iya d'aga idanunsa ya kalleta,
Yayinda azahirin gaskiya kuwa, bayason kallontan ne, saboda gudun kada taga hawayen dake kwance acikin idanunsa.
Domin kamar yanda zuciyarsa ta karye, haka ma duk wani k'warin guiwansa.
"Baffa!!"
Ta sake k'iran sunansa akaro na biyu, kana kuma cikin fad'uwar gaban da takeji, Wanda yake k'ok'arin yin watsi da nutsuwarta.
Baffa ko da duk jikinsa yayi sanyi, sam har zuwa yanzu ya kasa amsa ta, saboda wani irin nauyin Soumayan daya keji.
Ganin hakan da tayinne kuma yasa, ta langwab'ar da kanta, wanda hakan yasa asanyaye hawayen dake cikin idanun nata gangarowa kan k'uncinta.
Duk kuwa da yanda takejin labb'anta nayi mata nauyi, hakan bai hanata, rumtse Idanu, had'e da motsa labb'an bakin nata ba, wanda cikin
sark'ewar murya tace.
"Baffa an d'aura min Aure da MAJNOON ko?"
Tambayar ta kenan data sanya Baffan rumtse Idanunsa, had'e kuma dajin wani irin tausayinta mai tsanani, Wanda kuma sai ayanzu ya iya motsa bakinsa, inda cikin sanyi yace.
"K'addara ta riga fata Soumaya, saboda ayanzu an riga da an d'aura miki aure, Auren MAJNOON k'addararki ce, ki rungumi hakan Insha Allah, Allah bazai bari kiyi kuka ba."
Siraran hawaye masu d'umi ne suka kuma gangarowa daga cikin idanunta.
Wanda hakan yasa ta zamewa ahankali ta zube akan k'afafunta.
Hak'ik'a ajikinta takejin tsananin tausayin kanta, yayinda damuwa had'i da Rauni sukayiwa duk wani tunaninta k'awanya.
Lallai wannan itace k'addara mai iya sauya rayuwar mutum lokaci d'aya.
Tabbas kuwa sunan MAJNOON yazo a k'addarar ta.
K'addarar da ta fara farkonsa cikin tashin hankali, k'addarar da ta d'aid'aita tunaninta, had'e dayin watsi da hankalinta.
Sannan kuma K'addarar da ta juya rayuwarta gaba izuwa baya.
Tayaya zata fuskanci rayuwar da bata sani ba? rayuwar dako amafarki bata tab'a tunaninta ba.
Tayaya ne zata iya zama da mahaukaci amatsayin mijinta?
Lallai Wannan ba mafarki bane, kamar yanda take tunani afarko, tabbatacce ne, tabbataccen al'amarin dake neman tab'a k'wak'walwarta.
Waye zaiji kukanta? Waye zata fad'awa abundake cikin zuciyarta a irin wannan lokacin?
Tabbas ita mai rauni ce akan komai, sannan kuma mai karyayyar zuciya, wannan dalilin yasa ta sakin wani irin sassanyan kuka, me tab'a zuciya, kukan dake bayyana tsananin damuwarta.
Wanda ganin hakanne kuma yasa Baffa, share y'ar k'wallan daya zubo masa, cikin kuma damuwa had'i da sanyin da jikinsa yayi.
yasanya hannu ya kamo kafad'un Soumayan.
Ahankali da muryarsa wacce ke rawa yace.
"Hak'ik'a Soumaya ke amanace a wajena, amanar da nauyin ta ke hanani sukuni, saidai kuma ayau nima zan mik'aki amana ga wasu mutane na daban, ki nutsu Soumaya, kuma ki sani koni da Abbounki bama tare dake ,Allah yana nan, Allah yana tare dake, kamar kuma yanda kikayi jihadi, Allah bazai bari ki wulak'anta ba, Soumaya duk da cewar MAJNOON kika aura, amma inaso kisani Aure ba abun wasa bane, kiyi imani cewar Allah ya zab'eki ne, dan ki kula da mutumin da baisan komaiba arayuwarsa, mutumin da baisan daidai ko rashinsa ba, haka kuma mutumin da fari da bak'i duk d'aya suke awajensa, karkiyi kuka da zab'in Allah Soumaya, haka kuma karkiyi bak'in ciki, domin kowa yana da irin nasa damuwar, haka kuma yana da nasa raunin."
Shiru yayi tare da d'an sauk'e ajiyar zuciya, kana ya maida kallonsa ga, kud'ad'en dake hannunsa, Wanda suka kasance kud'in sadakinta ne.
hannunta ya kamo ahankali ya saka mata kud'ad'en, tare kuma da kwantar da murya cikin sanyi yace.
"Wannan sadakinki ne da suka bayar naira dubu sittin, ki rik'esu domin halal dinki ne, kamar kuma yanda na fad'a miki, Dr. Mouhammad yace zaiyi mana duk wani abunda ya dace, saidai tafiyan mu zaikai jibi, saboda visa'n da za'a samu acikin wata 1 shine zai sama mana acikin kwana hud'u, duk da yin hakan sai ankashe kud'I sosai, amma karki damu duk randa zamu tafi zanzo naganki Soumaya, saboda yanzu suna can suna jiranki, tashi muje na mik'a ki ga iyayen mijinki."
Ya k'are maganan yana me sake sharce hawayen, dake cikin idanunsa.
Tare kuma da mik'ar da Soumayan tsaye, wacce take kuka sosai, mai d'auke da yanayin shid'ewa, kukan kuma da sautinsa ke tashi, har zuwa cikin gidan nasu.
Hak'ik'a ayau tana cikin tashin hankalin, da yake neman gusar da nutsuwarta.
Jin yanda kirjinta ke tsananta bugawa ne kuma, yasa ta soma girgiza kanta, yayinda zuciyarta ke cike da son fad'an abunda ke cikinta, amma saidai labb'anta sun kasa bata daman hakan.
Akowani lungu da sak'o na kirjinta kuwa, damuwa had'i da fargaba ne kawai ke gudana acikinsu.
Wannan dalilin yasa take kuka irin na zautattu.
Yayinda Inna Hauwa kuwa jiyo sautin kukan Soumayan ne, yasa ta k'arasowa cikin zauren, tare da kamo hannun Soumayan.
Ahankali sannan cikin ban baki tace.
"Kiyi hakuri kinji Soumaya, kukan ya isa haka muje na shiryaki, kowanne rayuwa kika gani akwai k'alubale acikinsa, saboda haka Malam kace musu gamunan fitowa."
Kai Malam Musbahu ya jinjina, tare da juyawa ya fice daga cikin zauren.
Yayinda Inna Hauwan kuwa hannun Soumaya'n, ta kamo had'e da janta suka koma zuwa cikin gidan.
Koda suka k'arasa cikin gidan kuwa, direct d'aki suka nufa, inda Inna Hauwan ta zaunar da ita akan katifa, tare da gyara mata zaman mayafin dake jikinta, kana ta fesa mata wani sassanyan turare mai d'ad'in k'amshi.
In banda sheshshek'an kukan Soumayan kuwa, babu wani abu dake tashi acikin d'akin.
yayinda ta zubawa kud'ad'en dake cikin hannayen nata idanu.
Kamar yanda zuciyarta ke tsananin bugawa kuwa, haka ma duk jikinta ke rawa, saboda wani irin kukan da takejin na taso mata, tun daga k'ark'ashin zuciyarta.
Tabbas tunaninta ya hautsune, kamar yarda nutsuwarta ya gushe.
Sau d'aya tak arayuwarta bata tab'a kawowa cewar, zata bar gidansu acikin irin wannan yanayin ba, bata tab'a jin cewar nan kusa zatayi nesa da mahaifinta ba.
Amma sai gashi yau zata koma wani sabuwar duniya, mai d'auke da sabuwar rayuwa.
Hannunta tasa ahankali ta dafe daidai saitin zuciyarta.
Cikin muryarta dake fusga tace.
"Shikenan Inna Hauwa yanzu idan na tafi ya rayuwata zata kasance? Bansan mezai faru dani ba, wannan wace irin k'addarace? waye zai kulamin da Abbouna aduk sanda buk'atar hakan ta taso? Banason tafiya Inna Hauwa, dan Allah kice musu subarni, subarni na rayu da iya fargaban da nake samun kaina acikin ta kowacce rana."
Ta k'are maganan tana me had'e hannayenta waje d'aya, tare kuma da fashewa da matsanancin kuka, irin kukan da duk wani mai imani idan yaji saiya tausaya mata.
Wannan dalilin yasa Inna Hauwa dake d'an harhad'a mata kayanta, soma share hawayen daya zubo mata, Tabbas tasan cewar a irin wannan ranar kowacce amarya tana kukan rabuwa da gida.
Saidai kukan ya banbanta da irin wanda, Soumayan keyi ayanzu, kasancewar Soumayan kuka take irin wanda ke fallasa asirin k'uncin zuciyarta.
Kukan dake sa zuciya narkewa, saboda ita kanta jin kukan takeyi har tsakiyar kanta.
Hakanne kuma yasa cikin sauri ta gama harhad'a kayan, acikin y'ar k'aramar jaka, bayan ta kammala ne kuma, ta juyo tare da rataya jakar a kafad'anta.
Hannun Soumayan ta kamo ahankali, tare da d'agota tsaye.
Cikin kulawa had'i da tausasawa tace.
"Allah zai kula da lamuranki Soumaya, Insha Allah bazakiyi kuka ba, tashi muje."
Ta fad'a tana me dafa kafad'an Soumayan, tare kuma da rik'ota suka nufi hanyar fita waje.
Wanda ganin hakan yasa sautin kukan Soumayan k'ara tsananta.
Musamman ayanzu da kirjinta ke amsa wani irin bugu aduk bayan kowanni taku d'aya da zatayi. Domin ji take ajikinta tamkar tana k'ara kusantar wani abune na daban.
Ahaka suka iso bakin k'ofar fita Daga cikin gidan, nasu Wanda har zuwa yanzun kuma sautin kukanta bai daina tashi ba, saboda kukan ne kuma hatta jikinta yanzu tsuma yakeyi.
Saidai kasancewar fuskarta na lullub'ene, yasa babu Wanda ya ke iya kallon fuskar nata.
Banda Inna Hauwa dake tsaye, wacce sautin kukan Soumayan kesa ta karyewar zuciya.
fitowarsu wajenne kuma yasa, D'aya daga cikin escort din Billionaire Dawoud Saraki karasawa da sauri ya bud'e wata bak'ar Benz, dake cikin d'aya daga cikin motocin da suka zo dashi.
Wanda ganin hakan yasa Inna Hauwa k'arasowa ta sanya Soumayan acikin motar, kana itama da shiga ta zauna.
Tare dasa Hannu ta soma kokarin rufe murfin motar, saidai kafun takai ga cimma hakan, taji an fisgo murfin motar, tare da fad'owa kansu.
"Subahanallah, lafiya kuwa?."
Ta fad'a ad'an tsorace tana me kallon Moudou, Wacce itace ta shigo aguje.
Harara Moudoun ta watsa mata, cike kuma da nuna isa, murya adake tace.
"Bansani ba, ko lafiya ko akasin hakan, zanje ne naga wani irin munafurci kuka k'ulla keda mijin naki, sannan na kuma ga shi Mahaukacin Mijin, ya nasa salon haukan yake, ko akwai me hanani ne?"
"A'a."
Inna Hauwan ta fad'a tana me jawo Soumaya, dake takure a gefe jikinta.
Wanda saboda tsabar Kuka ko wacce gaba dake jikinta rawa yakeyi.
Inda Moudou ganin hakanne yasa ta sakin dogon tsuka, tare da bararrajewa, acikin motar tana me shak'an sanyin A/C'n dake dukan fuskarta.
ahankali kuma sukaji motar ta soma tafiya, cikin wani salo tamkar ba driving dinta akeyi ba.
Wannan dalilin yasa Moudou sake gyara zama, tare da somawa raya abubuwa da yawa acikin zuciyarta.
Soumaya kuwa dake lafe ajikin Inna Hauwa, wani irin kuka takeyi, Lallai ayanzu ta tabbatar da rayuwa ta ruguje mata, buri da mafarkinta sun tsaya.
Sakamakon yin imani da tayi kan cewar tarasa komai.
Yayinda daga can waje kuwa, Baffa ne ya d'an sako kansa, ta jikin murfin motar da Billionaire Dawoud din yake.
Gaba daya duk idanunsa sunyi ja, haka ma muryarsa ta bayyana damuwa.
Komai nasa asanyeye kamar yanda jikinsa ke asanyaye yace.
"Alhaji Dawoud ga amana nan na baka, Soumaya Amanace dazanyi fatan ku rik'eta rik'o mai kyau, duk da cewar yarjejeniya ce atsakaninmu, amma zan roki alfarmar kulawa da Soumaya, Dan Allah ku kula da Soumaya, domin akasin hakan idan ya faru bansan me zan fad'awa mahaifinta ba."
Ya k'are maganan yana me had'e hannayensa biyu, awaje d'aya alaman rok'o.
Wanda ganin hakan yasa Billionaire Dawoud Saraki sauk'e ajiyar zuciya.
Duk da yasan hakan wani nauyi ne,
amma cikin tausasa murya yace.
"Insha Allah Malam Musbahu, na karb'i wannan amanar, Kamar yanda ka buk'ata."
Kai Baffan ya d'an jinjina, tare da janye jikinsa gefe.
Badan wai kuma ya gamsu ba.
Yayinda drivern Billionaire Dawoud din kuwa yaja motar, suka gangara bisa kan titin dake wadace a k'ofar gidan.
"Fatan alkhairi Soumaya."
Abunda Baffan ya iya fad'a kenan, alokacin da yakebin motocin da idanu.
Wanda hakan yasa hawaye gangarowa daga cikin idanunsa.
Zuciyarsa kuwa cike da damuwa, haka yabi motocin da idanu, har saida ya daina hangensu kuwa kafun ya janye idanunsa.
Kasancewar sun riga da sunyi nisa.
Yayinda daga can cikin motar da Soumayan take kuwa, fusga da sheshshek'an numfashinta ne kawai ke tashi, bayan sanyin a/c'n da ke busawa.
Duk yanda Inna Hauwa taso ga rarrashinta kuwa abun yaci tura.
Musamman ayanzu da tayi tamkar wacce bata cikin hayyacinta.
*MAITAMA ESTATE*
Idanu Moudou dake bakin window keta warewa, saboda ganin ta da tayi, acikin wata sabuwar duniya.
Duk da kasancewar kuma motar akwai tint amma hakan bai hanata, Ware idanu tana kallon tsala tsalan gidajen da suke wucewa ba.
Tafiya kad'an sukayi, wanda hakan yasa ta dawowa cikin hayyacinta, saboda ganin kansu da tayi agaban wani irin gida wanda a iya tsawon rayuwarta bata tab'a ganin irinsa ba.
Gidan daya amsa sunansa gida.
Haka kuma gidan da kyawunsa ya d'arawa na gefensa, duk da cewar gidajen wajen na kamanceceniya da juna.
Idanunta ta kara warewa dan tabbatar da cewar, glass din da taga yana bud'ewa da kansa, gate ne kokuwa akasin hakan.
Batare data gama tunanin nata bane kuma, taga motar tasu tabi sauran sun kutsa ciki, Wanda hakan ya tabbatar mata da cewar Lallai gate ne.
*(Wellcome To The Billionaire Dawoud House!)*
Shine abunda ke rubuce asaman babban gidan, wanda yake d'auke da gidan sama mai hawa biyu, bayan wasu had'add'un part d'in dake cikin compound din gidan.
Gidan da aka yi masa wani irin gini, tamkar ak'asar England, ginin daya sa Moudou soma kokuwar bud'e murfin motar ta fito, batare da ta bari motar takai ga tsayuwa ba.
Saidai kuma kasancewar anyi lock na motar, yasa bata samu daman fitowa ba, har saida drivern ya gama daidaita parking din motar.
Duk acikin motocin kuwa itace first d'in fitowa, inda ta bud'e, baki hanci had'i da idanuwa tana kallon gidan.
Tare da mutsutstsuka idanunta, cike da fatan farkawa a mafarkin da takeyi.
Inna Hauwa kuwa, hannun Soumayan ta rik'o, tare da fito da'ita daga cikin motar.
Wanda ayanzu kuma itama hankalinta, bawai akan Soumayan yake ba, tsananin kyawu da had'uwar gidan kawai take kallo.
"Muje ko."
D'aya daga cikin escort d'innan ya fad'a, yana me kokarin wucewa gaba, danyi musu jagora.
Jin hakanne kuma yasa Inna a Hauwa, sake rik'e Soumaya, wacce sam bata masan duniyar da aka kawota ba.
Kamar yanda batasan inda take jefa k'afafunta, dake shirin gaza d'aukarta ba.
Saboda wani irin ciwon kai daya dirar mata, har yasa ta kasa bud'e idanunta.
Badan kuma rik'eta da Inna Hauwan tayi ba, tabbas da tuni ta jima da daina tsayuwa akan k'afafunta.
Duk da kuwa ayanzun bazata iya fad'in ga inda suka nufa ba, amma tasan cewar tafiyane mai d'an tsawo sukayi.
Yayinda Moudou kuwa kebin ko Ina da suka bi da kallo, kasancewar ta kasa samun bakin magana, dan saida suka shigo cikin taga ashe wajen gidan ba komai bane.
Saboda yanda aka tsara cikin da wani irin kayan ky'ale k'yale na kwalliya.
Tabbas zuciyarta ta fara tsinkewa ayanzu.
Yayinda wasu irin tunani ke neman haukata mata k'wakwalwa.
Abu d'aya dake yawo acikin ranta kuwa shine.
Wanne irin MAJNOON ne Soumaya'n ta aura? Wanne irin tarin dukiya ne wannan? ayanda gidan dama masu gidan suke, suna da y'ancin da zasu aurawa mahaukacin d'ansu kowacce irin mace da suke so, tasan kowacce mace zata zauna kodan kud'insu.
Amma meyasa suka zab'i SOUMAYA? Meyasa sai ita?
Hakan na nufin akwai wani b'oyayyen al'amari ne?
Tambayoyin da suke shirin fasa kan Moudou kenan.
Daidai lokacin kuwa suka k'arasa haurowa babban falon saman, inda escort din yasa hannu ya bud'e musu wata k'ofa.
"Anan Oga yace ku ajiyeta, Idan kuma kun gama zaku iya biyoni mutafi, saboda ance kada na sauk'o sai tare daku."
Escort din ya fad'a yana me sake gyara tsayuwarsa a bakin k'ofar, tare kuma da
kallon CCTV camera'n dake lik'e can saman babban falon.
Inna Hauwa kuwa jin abunda ya fad'a d'inne yasa ta.
K'arasawa cikin d'an madaidaicin falon.
Ahankali ta zaunar da Soumayan akan d'aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun falon.
tare kuma da kamo kyawawan yatsun Soumayan ta rik'e acikin nata.
Ahankali kuma cikin tausasa murya tace.
"Wannan itace k'addararki, k'addarar da babu Wanda ya isa canja ta, saboda haka inayi miki fatan alkhairi aduk rayuwarki, ina miki fatan kasancewa cikin farinciki Soumaya, abu na k'arshe kuma da nakeson ki sani shine, babu wani mutum d'aya, da yafi k'arfin irin wannan jarabawar, mu zamu tafi, dan Allah karki zama mai yawan sawa kanki damuwa kinji."
Idanunta dake zubar da hawaye tamkar an kunna famfo ta bud'e ahankali, tare dasa hannu ta zare mayafin dake lullub'e bisa kanta.
Jajayen idanunta ta zubawa Inna Hauwan, Akaron farko kuma kenan da ta soma yunk'urin motsa labb'an bakinta, saidai sam ta kasa furta abunda ke
Cikin zuciyarta.
Wannan dalilin yasa a hankali ta rik'o hannun Inna Hauwan, tare da soma girgiza kanta, cikin muryar kukan da ayanzu yinsa ya zame mata sabo, murya na rawa tace.
"Dan Allah... Inna Hauwa Karku tafi.... Karku tafi ku barni..... dan Allah.... ...."
Ta k'are maganan cikin tsoron bugun zuciyar dake barazana wa kirjinta, saboda tun shigowarta cikin gidan taji bugun zuciyar nata ya tsananta.
Jin hakanne kuma yasa hawaye gangarowa daga cikin idanun Inna Hauwa'n, saidai kuma babu yanda zatayi, wannan dalilin yasa ta zare hannunta daga cikin na Soumaya'n, tare da mik'ewa tsaye, cikin sauri ta juya ta fice daga cikin d'an madaidaicin falon.
Wanda ganin haka yasa Moudou dake tsaye rufa mata baya, cike dason titsiye Inna Hauwan, saboda ayanzu zuciyarta ta gama gamsar mata cewar, Inna Hauwa da Malam Musbahu'n sayar da Soumayan sukayi, bawai Aure suka d'aura mata ba kamar yanda suke fad'a.
Ai kuwa suna fita wannan escort din dake tsaye, ya rufo k'ofar gam, tare da juyawa ya rufa musu baya.
Ganin hakanne kuma yasa Soumaya dake zaune akan kujera, zamowa k'asa ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Kukan da ta sabayinsa alokacin da babu mai rarrashi.
"Yah Allah!!"
Shine abunda ta fad'a acikin zuciyarta, adaidai lokacin da take shirin had'iyan wani busashshen yawu daya tsaya amak'oshinta.
Ahankali kuma ta sake takure jikinta waje d'aya.
Tare da rumtse Idanunta, Wanda sukeyi mata matuk'ar zogi, saboda kukan da tayi.
After some minutes!
Ahankali sautin amon kukan nata ke raguwa.
saboda shid'ewan da tayi. Wanda hakan yasa
Lokaci daya jikinta ya shiga wani irin karkarwa.
Inda hakan yasa ta sake takure kanta waje d'aya.
Tare da soma fitar da wani irin Numfarfashi, dake nuna galaibatan da tayi.
Haka kuma Numfashin dake shigar mata da wani irin yanayi,.
Asanyaye ta lumshe idanunta tare da, sake nutsa kanta cikin Lallausan carpet din dake malale bisa tsakiyan falon.
Wanda azahirin gaskiya tayi hakanne saboda sautin bugun zuciyarta, da takejin yana komawa cikin kunnuwanta.
Hak'ik'a ranar yau d'in wata rana ce ta daban acikin rayuwarta.
Ranar data kawota izuwa wata duniya na daban, ranar da k'addara ta soma gara rayuwarta tamkar gare gare.
Siririn ajiyar zuciya me tafiya da sheshshek'a ta kuma sauk'ewa, alokacin da taji wani bak'on yanayi me kama da bacci, na kokarin fusgar ta.
Duk da yanda taso ta daure wa yanayin kuwa ta kasa.
Domin cikin abunda bai wuce 15mn ba, yanayin baccin ya soma cin karfinta ta hanyar sata bacci.
***
Kanta take juyawa cikin wani irin azababben yanayin daya sanya, kowanni silin gashi dake jikinta mimmik'ewa.
Duk da sanyin A/C'n dake tashi acikin falon kuwa, ita wani irin gumi ne ke ketowa daga kowani sashi na jikinta.
Sautin fitan Numfashi da gurnaninsa takeji nayi mata yawo, har acikin k'wak'walwarta.
Sautin dake neman zautar da ita, ya kuma haukata nutsuwarta.
Wanda hakan yasa ta sanya hannayenta duka biyu ta toshe kunnuwanta.
Had'i da rumtse Idanunta k'am.
Saboda abunda suke gane mata.
Kamar koda yaushe Hannayensa ne ke d'igar da jini, yayinda ayau din takejin sautin gurnanin nasa kusa da kunnuwanta, zuciyarta kuwa sannu ahankali take ci gaba da amsa amon kowanni gurnanin fitan numfashin nasa.
Wani irin yanayi takeji na daban yau d'in.
Wanda tayi imani da cewar matuk'ar b'ata bud'e idanunta ba, To zata iya zaucewa.
Wannan dalilin yasa azabure ta farka, still cikin kuma yanayin kid'ima tasanya duka hannayenta biyu, ta toshe kunnuwanta.
"A'aaaa....a'aaa!!!...."
Shine abunda ta soma fad'a da d'an k'arfi, tare da fara jijjiga kanta, saboda yanda takejin gurnanin numfashin har lau na yawo acikin dodon kunnuwanta.
Duk da kuwa cewar ta bud'e idanunta, Wanda a iya saninta ta kanji hakanne kawai amafarki.
Saidai kuma gashi yau abun yana neman zautar mata da k'wak'walwa, saboda tamkar azahiri haka takejin abun.
Saurin juyawa tayi, saboda wani irin kara da taji ya fito daga bayanta.
K'ara mai kama dana fashewan abu.
Idanunta dake a k'ank'ance ta zubawa, inda taji sautin k'aran ya bayyana.
Yayinda a hankali kuma ta soma jan jikinta baya.
Cikin yanayi mai kama da firgici, take kallon d'an corridor din dake cikin falon.
Tabbas ba mafarki takeyi ba, ba kuma bata cikin hayyacinta ba ne.
Lallaine daga wajen sautin gurnanin numfashin ke fitowa.
Wannan dalilin yasa a firgice ta sanya hannayenta, biyu bisa kan fuskarta ta murza idanunta.
Hak'ik'a acikin zuciyarta fata takeyi, fatan ace mafarki takeyi, bawai gaskiya ba.
Saidai da alamu Kuma bawai mafarkin takeyi ba.
Abunda yake azahiri ne kunnuwanta suke jiye mata.
Wanda hakan yasa gaba d'aya jikinta ya soma b'ari, tamkar wacce aka jonawa igiyar lantarki.
Afirgice take k'warai da jin yanda amon sautin ke k'ara kusanto ta.
Wannan dalilin yasa batare data tsaya tantance tana cikin hayyacinta ko akasin hakan ba, ta mik'e tsaye tare da k'urawa hanyar corridor din idanu.
Ahankali kuma batare data tsaya yin wani tunani ba, ta soma taka k'afafunta dake azabar rawa.
Ta hanyar kusanta kanta ga inda takejin amo da sautin gurnanin na tashi.
Inda daga cikin kirjinta kuwa zuciyarta ne ke wani irin bugawa, tamkar wacce zata faso k'irjinta ta fito.
Saboda tayi imani kamar yanda duk ilahirin jikinta ke rawa, haka ma zuciyarta ke tsalle aduk kowani taku d'aya da zatayi, dan kusanta kanta da wajen.
Yayinda daga cikin jikinta kuwa wani irin gumine ke keto mata, gumin dake bayyana tsannanin tsoron da take ciki.
Ahaka har ta k'araso cikin corridor d'in, Wanda ya kasance library, saboda yawan takardu da kuma littatafan dake cikinsa.
Wani irin fad'uwar gaba taji, alokacin da idanunta suka sauk'a, akan wani labule wanda, yayiwa Library'n k'awanya.
Wanda Kuma daga bayansa ne sautin dake neman haukata mata tunani, da kuma tsayar da bugun zuciyarta ke fitowa.
Kanta take girgizawa.
Cikin kuma rawar da jikinta keyi.
Ahankali ta ci gaba da tafiya, harta k'araso jikin labulen daya kasance fari tas.
Wanda kuma shine yayi mata Katanga da ganin, Wanda sautin numfashi mai kama da gurnanin ke fita daga gareshi.
Lallai Wannan ba mafarki bane, haka ba kuma wasa bane.
abune da yake abayyane, matuk'ar bata dakatar dashi ba, to zuciyarta zata tsaya da bugawa, tsayawa kuwa na har abada.
Wannan yasa ahankali cikin tsuman da jikinta keyi, ta d'aura hannunta akan farin mayafin.
Tare kuma da rumtse Idanunta k'am.
Batare da ita kanta ta shiryawa hakan ba kuwa, taji hannayenta dake rawa, sun yaye labulen gaba d'aya.
Wanda hakan yasa cikin firgici ta bud'e idanunta.
Dammmmmm!!!
haka zuciyarta ta amsa.
Cikin tsananin zabura kuma ta k'ara ware idanunta, tana kallon abunda ke yi mata yawo acikin mafarkinta.
Abunda ke shirin haukata ta, Wanda ayanzun ya d'aid'aita tunaninta.
Agigice tasoma jan jikinta baya baya, saboda idanunta da suka sauk'a akan jinin dake d'iga ahannayensa.
Wanda ganin hakan yasa taji tamkar an buga mata guduma ne atsakiyar kanta.
Cike da kid'ima take kallon hannun nasa, har zuwa kan fuskarsa.
Wacce ta kasa bayyana saboda yawan tarin sumar dake kansa, wanda ya sakko har zuwa kan wuyansa.
*MAJEED*
Adurk'ushe yake akan guiwowinsa, Wanda ya ajiyesu acikin fasassun kwalabe.
Kamar yanda jikinsa ke rawa, kuwa haka kowanne silin gashi dake jikinsa suka mimmik'e,
Kasancewar Kuma babu riga ajikinsa ne, yasa murd'add'iyar surar jikinsa bayyana.
Yana sakin Nishi mai kama da fitar hayyacin ne kuma, saboda dogin faratan hannunsa da yake sawa yana kartan fatar jikinsa, Wanda suke fitar da jini, adalilin tsayin da faratan hannun nasa sukayi.
Wanda kuma ganin hakanne yasa cikin matukar firgita, had'i da d'imaucewa, Soumayan ta soma girgiza kanta.
Tare da kokarin jan jikinta baya.
Cikin zaucewar da take tunanin tayi, murya na rawa, tace.
"MAJ....NOON!!! A'a aa..... Aaaaaaaaaaaaa!!!"
Ta fad'a da k'arfi, cikin tsuman da jikinta keyi.
Bayyanar sautin muryar nata ne kuma yasa, Wanda bata iya kallon fuskar nasa ya d'ago da kanshi.
Wanda hakan yasa atake idanunsu suka fad'a cikin na juna.
Idanunta ta zazzaro cikin yanayin fitar hayyaci, had'i da tashin hankalin ganin fuskar tasa da tayi, yasa numfashinta wani irin fusga, cak kuwa bugun zuciyarta ya tsaya, yayinda lokaci d'aya duk wani abu dake jikinta ya daina motsi.
Wanda hakan yasa a d'imauce ta tafi luuuuuu ta fad'i k'asa sumammiya.
*(Hmmmm yanzu akasoma labarin, wanene MAJNOON? Menene Kuma ya maidashi mahaukaci? Ya rayuwar Soumaya zata kasance acikin, sabuwar duniyar da gaba da bayanta, ke cike da k'alubale had'i da k'addarori kala kala, Tabbas wannan duniyar MAJNOON ne, mutumin da yake daban da kowa, Wanda kasantuwarsa MAJNOON ya zaman to masa wani al'amari na daban. ba iya bugun zuciyarsa ba, har acikin jininsa SOUMAYA k'addararsa ce.)*
*4:00 pm*