DOGON BURI

DOGON BURI

by @khadijatishaq

✨DOGON BURI ✨

       *_(Not all glitter are gold)_*



      *_ Story_*


          *_And_*


       *_Written_*


             🔽


      *_Mum sayyid 💫💫 💫_*



*Dukkan godiya ya tabata ga Allah subahanahu wata'ala*


  *_Wanan shafin sadaukarwa ne ga dukkan masoyana da wanda na sani da wanda ban sani ba_*





💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖


           

               ﷽


           Bismillah........ ✍️



💋*TITAN'S OF TALENT*💋


*Marubuta masu aiki da fasahar zamani , zalar ilimantarwa,fadakarwa dakuma nishadantarwa*


**(T .O.T)*

**Breathe in courage, breathe outfear, together we stand**


*Alkalaminmu abin alfaharn mu*




Page 2



____Tana bude kofar gidan kawun ta ta gani tsaye fuskarshi a daure kamar bae taba sanin wani abun ba wai fara'a,kallonta yakeyi sama da kasa kamar ya rufeta da duka "Ke dan ubanki ina dankwalinki,zaki fito ki bude qofar gida ba suturar kirki balle dankwali anya Asma'u tana koya miki abun kirki kuwa,dan wanan hanyar ba mai bullewa bace a gareku" Wani irin kallo take mishi tunda ya fara magana har ya gama a lokacin da yake magana bae kula ba sai da ya karasa magana tukkuna ya kalli fuskarta yaga kallon da take masa na raini wayyo duka ya kawo mata ta goce ta fada cikin gida tana kurma ihu tare da zubewa a tsakar gida tana burburwa kamar wacce aka zubawa ruwan zafi sbd makirci,da gudu Ummi ta fito daga daki zaninta a hannu daga ita sai undies ta fito tsakar gida gun Aleena ta dire tana tambayarta "Waye ya miki wani abun daga zuwa bude qofa naji an kwankwasa qofa kin tafi budewa sai dae naji kina wanan ihu da burburwa na shiga uku ni Asma'u " Jijigata ta cigaba dayi tana hawaye itama ilahirin jikinta rawa yakeyi,dakyar ta daidaita nutsuwarta ta ce "Kawu Musa ne ya kwankwasa qofa Ina budewa ya wankeni da mari kafin nayi magana ya Kara min wani ya wurgoni cikin gida Jamar kayan wanki"cikin sheshekar Kuka take magana kirginta nata sama da kasa kamar numfashinta zai dauke.


"Mu me??? 


"Musa"ta Kara fada cikin ihun kuka.


"Yana Ina yau zai ga rashin mutunci mai wasali wlh"tashi tayi ta daura zaninta gam kamar me shirin ruwa dambe ko gudu,fuskarta ba annuri akanta Sam.


"Yana qofar gi....! Ko karasawa batayi ba ta nufi qofar gida jiki ta na rawa,tana Isa ko gaisawa basuyi ba ta ce "Yanzu Kai Musa! Abinda kayi mun da safiyar nan ka kyauta kenan,kai a rayuwar ka kafi so ka zo ka tada mun hankali shine kawai abinda kafiso yarinyar yanzu me tayi maka daga bude qofa zaka rufeta da duka ba gaira babu dalili, toh kaje Allah ya Isa bamu yafe maka ba shege mai bakin hali, bakayi halin dan uwanka ba murgayi"cikin fada da rawar jiki take masa magana tana nunashi da yatsa kamar zata rufeshi da duka,bakinta sai kumfa yakeyi.


Shi kuwa da mamaki ya kasheshi a tsaye kasa ce wa komai yayi sai idon daya zuba mata tana ta zaginshi har ta gama bai ce mata kalla ba,tana yin shuru ya ce "Hajiya ta ce a sanar dake satin nan ne bikin Jamila"a takaice yayi maganar ya kama gabansa ya barta a nan tsaye tana binshi da zagi da mugun alkaba'i,ko juyowa ya kalleta baiyi ba har bacewa ganinta,abinda ya Kara hasala ta kenan ji takeyi kamar ta bishi da gudu ta rufeshi da duka fiye da wanda yayi wa yarta Aleena,sosai take cin takaice kamar taci tsunma,ta dade tana sufa zagi kafin ta koma cikin gida ta samu Aleena a zaune da farko dariya takeyi ganin Ummi ta nufo cikin gidan ne yasata shuru tana jan shesheka,hakuri ta sake bata tare da bata yakinin sai ta daukar mata fansar Marin da yayi mata kafin tayi shuru da goge hawayenta ta saki murmushi duk a tare.


Gidan da yake kusa da suke Katanga daya ta hannu hagu,gidan yarinyar nace ne me yara biyu,sunata Zainab mijinta kuma Salman,yaransu kuwa mace da namiji ne Amira da Amir, duk suna Jin motsin junansu dasu Aleena,Kuma duk anguwar da ita suke shiri ba wanda suke kulawa sai ita dan tasu ta zo daya dasu,tun lokacin da Aleena ta kurma ihu take son shigowa taji abinda yake faruwa sai dae mijinta na gida ta matsu ya fita ta fada gidan sai dae yaki yin sauri,ji takeyi kamar ta rufeshi da duka dan akwai ta da Jin kwakwaf da son a Yi komai a gabanta,abinci ta zuba masa a lokaci da suka fara Jin muryar Ummi tana surfa fada "Wai meyasa wanan matar takeda son bala'i ne ita,bana son matar nan dan halinta baiyi mun ba tanada matsala gashi bata kama girmanta sam,ke Kuma kin shige mata dayawa Ina guje miki ranar da zata dira akanki,zanyi kamar bansani ba ranar dan Ina hanaki alaqa da ita kinki,in kaki ji bakaki gani ba"Cikin kosawa da halin Ummi yake magana,ita kuwa sadda kanta tayi kamar wata ta Allah jikinta duk yayi sanyi da maganar da yakeyi a kullum indae irin haka ya faru"Haba Bbn Amira meyasa kake mun fata tsiya kullum,insha Allahu ba abinda zai hadani da Ummi a matsayin uwa na dauketa,Kai dae ka bimu da addu'a da fata nagari kaji"ta fada tana langwabar da wuya kamar zatayi kuka,shi kuwa kwafa yayi ya cigaba da cin abincin shi kala bae kara cewa ba ita keta surutunta gashi ta zaku ya gama ya fita taje taga abinda ke faru kar a gama ba'ayi a gabanta,sbd ta tsani labari tafiso a yi komai a gabanta da a bata labari "Yauwa zanje kitso dan Allah anjima idan na gama aikin gidana,ka taimaka ka bani kudin kitson"ta tambayi kitson ne dan kar taje gidan Ummi ya dawo bata nan yayi fada duk da tasan da wuya ya dawo gida in dae ba mantuwa yayi ba,sai da ya gama tsaf ya bika mata dari 500 ya fice ta bishi har qofar gida tayi mishi addu'ar dawowa lfy kafin ta dawo ta kwashe kwanukan daya ci abincin ta kai kitchen ta dauraye cikin sauri kamar zata tashi sama,dama tayi wanka da shiri yaranta kuwa suna makaranta sai karfe 6 zasu taso,hijjab ta shiga dakinta zata dauko ta kara Jin muryar Ummi tana sababi a tsakar gida, wardrobe ta bude garin janyo hijjab daya duka kayan da suke sama wanda ta janyo suka zubo kasa,sbd tsabar sauri haka ta barsu a wajen qofar wardrobe din na a bude ta fito har da dan gudunta ta suri keys din dake kan table din palour tayi waje,dakyar ta iya karasa rufe qofar dake gefen baban gate din gidan,har wani mazari jikinta keyi sbd gulma.


Tana gama rufewa ta afka cikin gidan da sallama a tsakar gida ta samu Ummi da Aleena suna shirin shiga palour,amsa sallamar Ummi tayi ta ce "Mmn Amira karaso mana kin tsaya anan" cikin dane bacin ranta tayi magana tare da hadiye haushin da take ciki, palour suka shige gabaki dayansu,guri ta samu ta zauna tare da gaishe da Ummi cikin ladabi "Ummi Ina kwana Kun tashi lfy ygda" Mmn Amira ta fada "Lfy Lau yasu Amira da Amir fatan Kun tashi lfy" "Alhamdulillah! Ummi lfy kuwa,tun dazu nake Jin muryarki hala wani ne ya zo ya bata miki rai da safiyar Allah nan? Mutane basa kyauta wa baka da lokacin mutum amma sai an kaika bango dan dae kawai aji ta bakinka idan ka fara naka kuma a ga laifinka a dinga yawo dakai ana cewa bakada hakuri,Allah dae ya rabamu da yan wahala masu kaimu bango muyi magana suyi yawo damu" Tayi maganar da fuskar tausayi,tana dafe goshinta, Ummi ce ta amshe maganar da ce wa "Mutum ya dade baiyi yawo dani ba dan kutumar ubansa,ba wanda zai tabani nakiyin magana tunda ba tsoronsa nakeji ba,ke dae yar albarka Musa ne kanin Bbn Aleena ya zo dan wulakanci har qofar gidana ya dakar mu ya sbd ya raina wa kanshi hankali ae sai da na masa zagin kare dangi ya dauka tsoronshi nakeji,abinda ya hada ya Riga ya raba kowa yaji da kanshi bana son shishigin dangin miji wlh tun mijina na raye balle yanzu da kasa ta rufe masa ido,duk su zauna inda Allah ya ajiyesu bana son jaraba da rainin wayyo bazan dauka ba wlh" ta fada kamar yanzu abin ke faruwa haka takeji a ranta don takaici "Sai hakuri dangin miji wlh haka nima nake fama da nawa kamar sai hakuri dadin abun ma ba gari daya muke da su ba shine sauki na Kinga duk randa mukaje ganin gida ji suke kamar su dauke mun numfashi na sbd kiyaya" Mmn Amira ta fada tare da jimami a fuskarta, "Allah ya kyauta ke suke damunki ni Kuma ni ke damun su Kuma ba yadda suka iya dani wlh,ni tun farkon aurena ba dauki wanan rainin ba,balle su bani wahala" fita daga hirar Ummi tayi suka cigaba da hirar duniya sai da azahar tayi sukayi sallah da cin abinci suna hira Aleena tana gefe rike da wayarta tana dannawa ko motsi batayi balle kasan tana palour sai kusan azahar taje ta dora musu farar shinkafa a bisa umarnin Ummi Dan sunada stew tana gamawa tayi sallah a nan wajen ta gyara kwanciyarta ta soma bacci,ita a duniya taki jinin Mmn Amira sam jininsu bae hadu ba yadda Ummi ke sakewa da ita ma haushi yake bata da zata iya da ta dade da yanke alaqar,matsala itace Ummi taki fahmitarta dan ita a nata ce wa take kowa ma Aleena taki jininshi ba ita kadai ba dan haka bazata biye mata ta daina alaqa da mutane ba,duk wanda bata so bata sata dole sai ta saki jiki dashi ba kowa yayi da wanda yayi masa,karfe 2 na rana kafin Mmn Amira tayi wa Ummi sallama akan zataje tayi kitso kafin la'asr,gidan kitson a kasan layinsu yake,sai da Ummi ta rakota har kofar gida kafin sukayi sallama ta juya cikin gida Ita Kuma ta nufi inda zataje,gidan kitso taje akayi mata ba da sauri dan ba kanana tayi ba, cikin mintuna kadan a ka gama mata ta bata kudinta ta fito daga gidan,tunawa da wayarta tayi takaici ya isheta tsabar saurin da takeyi da safe taje taji gulma yasa bata dauki wayarta ba,tana bari gidan kitso ta kamo har yar gida har ta kai qofar gidanta zata kube ta shiga sai Kuma ta juya ta shiga gidan dake kusada nata ta hannu dama,a tsakar gidan ta samu matar gidan tana deban ruwa zata kai kitchen tayi sallama "wslm Mmn Amira kece da yamman nan ygda ya yaran bari na karawa tuwo na ruwa in zo mu gaisa"Cikin kitchen din ta shiga da ruwan sai data gama abinda ya dace ta rage wutar abincin kafin ta dawo tsakar gidan "A'a baki shiga palour ba zaki tsaya waje kamar wata bakuwa haba Dan Allah,mu shiga ciki" Bin bayanta tayi tare da ce wa "Wai dama nufina ki karasa sai mu shiga cikin a tare" Suna zuwa suka zauna suka Kara gaisawa da tambayar yara,kitso naje wlh har zan shiga gida nace bari na leko mu gaisa kwana 2 bamu hadu ba" ta fada tana dariya "Ae kuwa yau nake maganarki a raina nace gobe in na fita zan shiga mu gaisa,ashe ke ce Zaki Riga zuwa" "Eh bari kedai ae ku fita na muku wahala kullum suna kunshe a gida bakwa ko leka makota,kin kuwa ji hayani yau da safe kuwa? Ta fada da salon bugun ciki "A'a gaskiya wani abun ya faru a anguwar ne? Ta tambaya dan Jin Karin bayani "Yanzu zaki ce duk masifar da Mmn Aleena tayi a anguwar nan da sasafe bakiji ba,sai a gaisheku hala bacci kikeyi wajen karfe 10 ko 11 ne" .


"Walahi kuwa! Allah bae sa naji ba,a wanan lokacin kema kinsan ae bana bacci Ina aikin gida ne,da yake ma yau kwalema nayi a chan uwar dakina duk kayana sunyi kura,na cire komai na share na goge har kasan gado,bayan fitar Yara da Bbnsu inaga shiyassa banji ba tunda bana tsakar gida bazan ji ba,Allah ya kyauta ya kiyaye gaba" ta fada cikin kosawa da halin Mmn Amira na gulmace gulmace kar wata rana ta hadasa wa kanta bala'i dan duk randa Ummi tasan abinda take mata na munafurci ranar za'a kwashi Yan Kallo a layin nan "Ashe aiki kika sha shiyasa baki ji ba,kinsan ma nice a tsakiyar ku sai nafi jiyowa,ae kuwa dae wai kanin mijinta ne ta dinga yiwa bala'i dan ya mari Aleena kinsan in kina son shiga tarkon ta to ki taba yar gaban goshinta a lokacin zaka raina kanka dan sai ta Shata maka layin rashi mutunci taga Kuma uban daya tsaya Maka,ni fa na tsani halinta kawai Ina binta ne dan tana shishige mun in badan haka ba ko kallo basu isheni ba,ayi mutum bashida Kara balle kunya zaka Iya taka kowa baka ragawa kowa dan kawai ka iya wulakanci" Tunda ta fara magana Mmn Sumayyah ke kallon ko kiftawa ta kasa yi,tana Kuma mamakin furucinta dan tasan ita ke musu shishigi ba su ke mata ba,Dan Ummi duk unguwar nan ba wanda ya isheta kallo balle tayi masa shishigi harkar gabanta takeyi tsakaninta da yan anguwa shine in ka haihu ta zo maka barka ta baka abinda zata baka sai ranar suna ta leko da yamma shima in kayi sa'a kenan,kawai Dan sharri zata zauna tana ce mata suke mata shishigi ita Kuma ta yadda da yake yarinya ce ita,har ta gama surutun ta kala bata ce mata ba,a lokacin magrib ya kawo kai "Bari na shiga gida ko abinci ban dora ba gashi su Amir sun kusa dawowa" ta fada tana mikewa tsaye,sukayi sallama ta komawarta kitchen ko rakiya bakin kofa bata mata ba dan gulmar data kawo ba karamin kular da ita yayi.


Tana fita ta bude gidanta ta shiga tun safe data fita tana wajen yawo bata ma dora abinci ba sai yanzu data shigo hankalinta ya tashi ta fara guje gujen dorawa,abinci mai sauki take tunanin dafawa amma ta rasa daga karshe dae ta yanke ta dora taliya da miyar jajage na attaruhu,albasa da kifi,ruwan ta dora ta koma daki ta fara linke kayan data zubar da safe garin sauri,kusan rabin kayan wajen ne ya zubo,muryar yaranta taji suna mata sannu da gida ta amsa ta cigaba da aikin da takeyi kar Bbnsu ya dawo bata karasa ba, tanayi tana girki Allah ya taimake ta ana iddar da magrib har ta gama ta gyara ko Ina na gidan yadda ya kamata yaran ta zubawa ita Kuma taje dakinta tayi sallah bata fito ba sai datayi isha'i lokacinta yayi,yaran har sun kamalla cin abinci sun fara bacci saboda gajiyar da sukayi ta wuni guda a makaranta,dakinsu ta gyara musu ta tada su tayi musu wanka da ruwan dumi suka Saka kayan bacci tare da kwanciya ta daura musu gidan sauro sukayi addu'a ta dawo Palour daidai nan Bbnsu ya shigo da sallama,sanin yara sun kwanta ne yasa ta fada jikinshi tana masa sannu da zuwa,dariya yayi ya amsa tare da ce wa "Fatan na sameku lfy Ina yaran suke? "Ka shigo ka huta mana tun daga bakin qofa kake tambayar yara kamar ni ba mutum bace" ta fada tana turo bakinta gaba,cike da shagwaba "Tuba nake uwar Amira da Amir kaina bisa wuya,kar anjima na kawo kukana ayi mun tawaye naje naga duhu dan yau a shirye nake,ayi mun afuwa"ya fada yana shafa mazaunenta,ita kuwa Jin haka ta Kara girgiza bayan nata cike da kwarewa tana tafiya zuwa daki yana biye da ita a bayan ruwa ta hada masa ya shiga yayi wanka kafin ya fito ta kawo masa abinci cikin dakin ta jera masa akan karamin table din dake dakin yana fitowa ya goge jikin shi,wajen abincin ya nufa direct ya soma aikawa cikinsa sauri sauri kamar wanda ya wuni bae ci ba sai da yayi katt,ya ture table din yana sauke numfashi tare da jingina bayanshi a kujerar dake dakin inda yake zaune,kwashe komai tayi ta kai kitchen ta dauraye kafin ta dawo ta fada toilet tayi wanka ta wanke lungu da sako na jikin ta,ta fito zaunawa tayi gaban madubi tayi shafe shafen mata kafin ta gangara wajen turare ta shafe ko Ina shi kuwa Yana kwance kamar soko yana binta da ido jira yakeyi kawai ta gama abinda takeyi dan a matse yake,Abokinshi ne ya kawo musu maganin basir dana maza wajen aiki suka Sha abinda yake tambayarsa kenan,tana gamawa rigar bacci ta zura ko gama daurewa bata yi ba ya fincike rigar yayi kan gado da ita,nan fah alamari ya sauya,rufo qofar sukayi.



**********


Baccin kusan 2hr Aleena tayi kafin ta farka dalilin wayarta da tayi ringing ne ma ya tasheta,lalubo wayar tayi tare da kallon screen din da fararen idonta, "Noorlkalbi" ne ya fito baro baro a screen din,kallon abinda Ummi takeyi tayi ganin tana kallo ne Kuma tasan indae ta dauka ta fara magana sai ta gane da wa take magana ne yasa ta mike tana sakin tsaki marar sauti ta nufi dakin a lokacin Kiran ya katse har wani ya fara shigowa,sai da ya kusa katsewa ta dauka tare da yin shuru daga chan bangaren yayi mata sallama sai da ta dauki yan mintuna har yana tsamanin ko ta katse ne ya dauke wayar a kunneshi ya kalli screen yaga tana still connecting kafin ya mayar ya ji muryarta ta amsa sallamar tashi,sauke numfashi yayi tare da ce wa "Babe are you ok! Ko bakida lfy ne? Ya fada duk a tare cike da dakuwar rashin walwalar da baiji a muryarta ba "Am fine ok daga bacci na tashi kiran ka ne ya tasheni yanzu, that's why am sounding dull ok am fine chill" cikin dariya tayi maganar dan ta kwantar masa da hankali,in ba haka ba yanzu zai birkice mata ya hanata sukuni da kiranshi da baya karewa,sanin halinshi ne yasa tayi dariyar yasan she's ok before he starts, "Ok Alhamdulillah" ya fada yana sauke ajiyar zuciya,Dan hankalinshi har ya fara tashi a lokacin Jin muryarta ba walwala "I just want to inform you that am traveling today at this minute,tafiyar ta zo min cikin gagawa ne Baba ne ya aikeni neighboring state dinmu akan wani daurin auren yaron Amininshi da za'ayi gobe juma'a so yau zamu tafi sai jibi zan dawo Insha Allah,Kuma bazan iya tafiya ban ganki ba,kina gida ne ba biyo yanzu muyi sallama?


"Oooooh travel again! Nifa bana son yawan shiga motar nan da kakeyi,last week kayi and even this week ma kana so ka tafi i just hate hearing this travel matter i swear,am home ka taho sai muyi sallama ok" bata jira amsar sa ba ta kashe wayar dan tafiyar ta bata mata rai sosai,ita a rayuwarta ta tsani tafiye tafiye duk rayuwarta a cikin Kano takeyinsa bata damuwa da zuwa ko Ina ba, ko Ummi zatayi tafiya bata binta sai dae ta tafi gidan kawarta ta jirata in ta dawo sai itama ta dawo,ko lokacin da tayi service aka tura Kaduna daqyar ta Karasa a wanan lokacin sai da Ummi ta zare mata ido kafin ta zauna a ta gama a ranar ta kamo hanyar Kano bata Kara kwana ba a garin,shi Kuma bashi da aiki sai zuwa biki da sauransu,tsaki tayi "Shi ya sani ya tafi bangon duniya ma inya ga dama"Toilet ta shiga tayi alwala Jin ana Kiran sallah tayi sallah ta Saka kwalli kayan jikinta ta chanza zuwa doguwar rigar lace blue da orange ta yafa mayafi orange da flat slippers orange ta fito palour ta ce wa Ummi "Zanje gidansu faizah zamu hadu a chan da sauran magana zamu tatauna" Ta shiryo mata karya,kasan ranta tana istigifari "A dawo lfy ki gaida Mmn nata,Allah yasa ki gane ki dauki shawararsu dan yaran albarka ne masu sonki da gaskiya da so ki samu alkhairi ba tsiyar da kikewa kanki fata ba" Ko karasa magana Ummi batayi ba ta fice daga gidan Jin wayarta na vibrate tasan shine ya iso,gashi Kuma bata son Jin maganar da Ummi ke yi saboda haushi kalaman ke bata a cikin zuciyarta,ko Meye laifin Arif da Ummi ke gani kullum kawai dan bashida shi yau ba shi ke nufin bazai samu ba har abada,kullum ayi ta magana daya kamar wanda ya kashe mata wani a danginta "Ina sonshi zan cigaba da sonshi ruwa da iska,Babu mai rabani dashi ko da kuwa zan rasa raina Ina tare dashi mu mutu tare" Har ta fito qofar gidan tana zancen zuci hangoshi tayi gefen gidansu akan wani dakali yana wasa da yatsun hannushi kallonshi ta tsaya yi tare da ce wa "Meye aibun guy din nan da Ummi keta kusheshi,rashin tsayawa ta kalleshi ne yasa ta kasa gane kyakyawa ne ajin farko,ga class da ilimi abinda ya kawo masa cikas a rayuwa shine kudi shima nasan yana daf da samu Insha Allah" Kara zuba masa ido tayi tana so ta Kara tantance kamaninshi da kullum idan sun hadu sai tayi hakan kafin hankalinta ya Kara kwanciya.


Arif dogo ne mai tsakacin kiba,ba Kato bane Kuma ba ramame bane jikinshi a murde yake,gashi da cikar damtsen hannu fari be tass dan a kallo da zaka masa bazaka taba ce wa cikin gidan talauci ya fito ba fatarshi tana nuna hutu wanda ba hakan bane a zahiri,gashin kanshi baki ne sai tsansi da cika kana ganinsa kaga bafulatani cikake fuskarsa madaidaciya ce mai dauke da dogon hanci da karamin baki ga kayatacen saje dake zagaye da fuskarshi baki sidik,sajen ba karamin kawata fuskarshi tayi ba,Yana sanye ne da yadi baki shine ya Kara fitowa da hasken fatarshi,ba karamin kyau sukayi masa ba duk da ba masu tsada bane sai dae yayi masa mugun kyaun da bazaka dauka kayan mai arha bane,hannushi daure yake da agogo kafarshi kuwa takalmin flat ne me yatsa na maza a kafarshi,hannushi mai daure da agogo dashi ya talabe fuskar shi ya zubawa kofar gidansu ido dan ganin ta inda zata fito, tana fitowa sukayi ido hudu nan take idonsu ya tsake da juna sai kallon junansu suke cike da shaukin so da kauna shimfide a kwayar idon junansu,kallon kusan 10 minutes suka yiwa junansu kafin shi ya janye idonshi,murmushi ne akan kyakyawar fuskarshi tare da dan Bude murya ya ce "Karaso mana Noorlhayat" cikin takunta na Isa da izza ta fara takowa tana rangwada,tafiya take kamar yanke da iska ke kadawa akan bishiya har ta karaso shi kuwa yayi mutuwar zaune baisan ta iso bama sai data hura masa iska akan fuskarshi kafin ya dawo hayacinshi ya kyalkyale da dariyar har kumatunshi na lotsawa ta gefe da gefe,itama dariyar tayi sai dae ita nata lotsawar kumatun gefe daya ne na hannu dama,sai da sukayi mai isar su kafin ta fara tsayawa da dariyar tana kallonshi yadda komai nashi ke burgeta,bae ankara ba sai Jin idonta yayi na yawo a jikinshi dariyar ya tsayar Yana kallonta shima haka dae suka lallace da kallon junansu daqyar suka samu suka hakura tare da gaisawa "Barka da yamma Noorlkalbina,fatan kan cikin koshin lfy? Well I can see you are fine and healthy" Da murmushi akan fuskarta take maganar "Yes of course,as I can see you are too,Allah ya kara mana lfy da nisan kwana mai amfani,dama na zo ne muyi sallama duk da mun fasa tafiyar a yau saboda kinsan kidnapping yayi yawa,kuma katsina zamuje wajen Kusada local government wani kauye akan hanya dae yake gashi yamma tayi zama bari da safe mu tafi karfe 7 ko 8 na safe tunda daurin auren sai bayan an sako juma'a,Kinga zamu shiga da wuri ae har mu huta ma kafin lokaci yayi" Yana kallonta yake maganar har ya karasa "Nifa dah fushi nakeyi amma ganinka yasa na huce,ba damuwa Allah ya kaiku lfy ya kuma dawo mun da kai lfy,Wani hanzari ba gudu ba, don't look at any girl duk wacce ta kalle ban yafe mata ba ehe " idon ta cike da kwalla take maganar kamar zata fashe da kuka dan Aleena akwai kishi sosai,"Kayi mun alkawari ko na hanaka tafiya" turo baki gaba tayi tana jiran amsarshi,idonta cikin nasa "Insha Allah nayi miki alkawari bazan kalle kowa ba duk wacce ta kalleni Allah yasa ta tashi da ciwon ido da safe" Dariya ta saki mai sauti sai da tayi mai isarta kafin ta ce "Yauwa ko kaifa Allah ya tsare ya dawo mun da Kai lfy Hasken zuc......." Tsakin da sukaji a sama kansu ne yasa bata karasa abinda zata fada ba.




Share fissabillah 🙏🙏🙏🙏