RABO YA RANTSE...!

4

by @autarmanya

*RABO YA RANTSE...!!*🌹

      

      *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


           *004*


Baƙa ce sosai irin baƙin nan mai ɗaukar ido dan fuskarta har maiƙo take yi ga wasu ƙuraje da suka cika fuskar tata ƙananu Tana da Ƙananun ido marasa girma da gajeran hanci ba zaka sanya ta cikin Mata masu tsananin kyawu ba Bata da tsayi sosai ƴar ƙarama ce kamar zaka hureta ta faɗi sabida ƙanƙantarta sai dai daga samanta acike take dam haka zalika ƙasanta ma ta wajan hips ɗinta a cike yake dam amman tafarar ɗaya ba zaka hango hakan ba har sai ka ƙura mata ido Tana da wani irin jiki Wanda ake ce masa karuwan Jiki mai ɓoye halittar jikin mutum, Yanayin jikinta shiya ɓoye mata shekarunta wanda tana cikin shekaru Ashirin da huɗu da haihuwa amman in ka dube ta sai kace ƴar shekaru goma sha shidda zuwa sha bakwai ce, sabida ƙanƙantarta yawanci Ƙawayenta basa kiran sunanta sai dai suce mata bakwaini wannan suna In taji sun gaya mata shi faɗa ake da ita sosai sabida kowa yasanta bata barin kota kwana ƴar hayaniya ce FARHA kenan wadda sunan ta na Asali shine Fatimah Ƴar gidan Malam Abubakar Mai Bulo dake Ɗandago wanda jama'a kewa gidan laƙani da gidan Cida kai ko gidan yawa sabida tsabar yawan ƴaƴan babansu Malam Abubakar mai Bulo shine tasa kowa a gidan yake fafutukar abin da zai ci dan tuni Mahaifin nasu ya sallamawa kowa ce mace nauyin kanta ita da ƴaƴanta sabida tsabar yadda nauyi da rashi yayi masa yawa Mata uku ne agidan su Farha Babar su Hadiza Nada Ƴaƴa Goma Babar su Ruƙayyah nada ƴaƴa Goma babarsu farha nada Ƴaƴa Biyar Gaba ɗaya ƴaƴan gidan su ashirin da biyar ne cif.

Malam Abubakar mai bulo mutum ne mai son ya kyautatawa iyalinshi ada sanda yana dashi anji daÉ—i agidanshi dan wadatar sa ma ita ce ta saka ya tara mata har uku da Æ´aÆ´a batare daya ji wata shakka ba, sai dai yau da gobe ga girma ga nauyi yasa abubuwan suka caÉ“e masa hakan tasa yaja tagumi ya zubawa matan sa ido yanzu haka suke buga buga dan asirinsu ya rufu wani bin inya sa mu yakan Æ™oÆ™arin wajan yaga ya kawo gida mai girki ta sarrafa sai dai akan Shinkafa Rabin kwano ana iya bawa hammata iska acikin gidan Musamman da Farha wadda ita bataÆ™i tai dambe da É—an Æ™aramin yaro akan shinkafa loma É—aya ba, in suna faÉ—a akan abinci agidan tamkar basu taÉ“a cin abincin ba haka suke cika gidan da hayaniyar su har maÆ™ota sai sun shigo rabo ga matan ko wacce ba haÆ™uri daga ana faÉ—an kowacce É—anta take tare wa Malam Abubakar mai bulo ( kawu ) mutum ne mai zafi manyan Æ´aÆ´an sa da ike mata ne suna gama primary ya aurar dasu suma sauran Æ´ammatan sabida yadda zamani yazo ne da Æ™yar aka shawo kanshi ya barsu suke karatun bokon waÉ—anda suke duk Æ™annen farha ne Don ita farha ma ta kammala karatun ta a F.c.e kano inda ta sami diploma a É“angaran mass communication kuma Cikin ikon Allah ta sami nasarar amsar result É—inta wanda bata da wata matsala sabida tana da hazaÆ™a sosai, amman in kaga Æ™annen farha sai ka rantse Yayinta ne.


Ƴaƴan ɗakin su farha Yaya sadiya tai aure Yaya Nafisa tai aure Fa'iza tai aure wadda farha take bi yanzu haka daga farha sai ƴar ƙaramar ƙanwarta mai suna ikram wadda ita ce autar umman su farha.

Suma Æ´aÆ´an É—akin Babarsu Hadiza wadda take itace uwar gida matanta takwas ta aurar da uku saura biyar hadiza ce Babba yanzu a Æ´ammatan tana shekarar Æ™arshe a secondry sai Æ™annanenta mata da suke tawosa sai maza samari guda biyu waÉ—anda suka girmewa Farha sai Æ´aÆ´an babarsu RuÆ™ayya itama ta aurar da biyu yanzu haka akwai shida agabanta RuÆ™ayya ce Babba a Æ´ammatan gabanta sai sauran sai maza biyu suma samari ÆŠaya Æ™anin farha É—aya yayanta Umma mahaifiyar farha bata kai sauran matan gidan jin jiki ba sabida bata da nauyi da yawa sosai tana kuma sana'arta ta wankau sai dai yawanci kuÉ—in basa zama daga an samu ake kashewa Musamman Lokacin da Farha na makaranta sabida umma ce ke hidimar taimakon farha akan karatun nata wanda ta Æ™wallafa rai akan sai ta karanci aikin jarida, Haka Umma ta tsaya akan karatun farha da taimakon Salim saurayin farha É—an Abokin kawu wanda tun kafin farha ta taso Salim ke hidima da ita suna son junan su sosai Salim yana kashewa farha kuÉ—i sabida É—an kwari ne anan yake sayar da atamfofi Yayi nacin ya kawo kuÉ—i Gidansu farha Lokacin da tagama karatu tace ya bari ta sami aiki sabida taga yadda Iyayenta mata ke shan wahala agidan su akan neman abinda zasu ci ba ason ran kawu farha ke zaune ba aure ba ga zabga zabgan Æ™annenta nan duk sun taso sun cika gida yafi son ya soma aurar da ita kafin ya aurar dasu RuÆ´ayya waÉ—anda zasu kammala karatun su na secondry a wannan shekarar Kawu mutum ne mai zafi abu Æ™anÆ™ani in yaji É—ansa yayi yakan iya kullo Æ™ofar gida ya zane shi tas ya huce dukkan baÆ™in cikin talaucin sa akan É—a bai Æ™i ya karya É—a ya aje uwar sa tai jinya ba shiyasa duk hayaniyar Æ´aÆ´an gidan daga kawu ya shigo zakaji sunyi tsit kamar Ba Wani É—an adam dake rayuwa acikin gidan.


Ta shirya cikin baƙar doguwar riga wadda ta yane kanta da baƙin mayafin doguwar rigar ta ɗauki jakarta bayan ta dubi ƙanwarta Ikram wadda bata fi shekaru goma ba tana zaune a saman tabarma tana shan koko.

"Ikram jeki É—akin kawu kiwa ummammu magana ni zan fita"

Ikram ta tura baki gaba tana hararar Farha.

"Kutss ni kike harara Auta? dan ubanki ni sa'arki ce dan wa nake fafutukar fita neman aikin, idan danni da Umma ne sai mu sha ruwa mu kwanta jiya ina ba haka kikai ta mana kukan yunwa ba"


Ikram ta miƙe aguje ta fita daga ɗakin sanin halin farha na rashin haƙuri yanzu sai ta hau jibgarta.

Ummah dake É—akin kawu taje kai masa kokon karin kumallo ita ta dubi Ikram wadda ta faÉ—o É—akin tana nishi.

"Auta meye haka zaki shigo É—akin Kawunku da gudu?"

Ikram data san halin kawu wanda ta haÉ—a ido dashi yana zaune saman darduma da sauri ta koma da baya tana cewa.

"Ummah wai yaya ce zata fita shine tace in gaya miki"

Ummah ta dube ta.

"To kuma sai kin yi gudu daga É—akin zuwa nan"

Ikram ta koma bata bawa umma amsa ba sabida yadda taga kawu na zabga mata harara.

"Nifa Hasiya na gaji har ga Allah, lamarin ku keda Æ´arki ya isheni haka tace candy na barta tace cigaba da karatu na barta wai mai kuke nufi da Salim ne?"

Bai jira amsar ummah ba ya cigaba da cewa.

"Maganganu ko ina nata tashi a cikin unguwa ance cin kuɗin sa muke alhalin ba bashi ƴarmu zamuyi ba, To ni Allah ya gani kuma shaida ne ban taɓa amsar ƙwandalar yaron nan akan Fatimah ba, Hasalima sanin danai wa mahaifinsa a matsayin sa na aminina yasa naji yaron ya ƙara shiga raina amman kun kafe sai tai karatu ta gama kunce sai ta kama aiki to nikam na gaji wallahi kuna kaini bango sai dai ta nemi wani uban bani ba dan nagaji inji dana gabana ma mana haba jama'a"

Umma tai ƙasa da murya sabida ƴan laɓe dan sana'ar matan gidan ne.

"Kayi haƙuri ka ƙara mana lokaci in sha Allah daga lokacin da zaka ƙara ba zamu haura ba"

Kawu yace.

"To kice mata na bata wata guda salim ya aiko na aurar da ita inta ƙara haura hakan to ta nemi wani uban ba Habubakar ba"

Daga haka yaja rediyon shi ya kunna yabar umma riƙe da haɓa.

Tashi tai ta fita tsakar gida cin karo tai da Babarsu Hadiza wadda tai saurin Komawa da baya tana sosa kai Umma tasan labe tai musu anjima kaÉ—an kawu na fita zata kwaza maganar a tsakar gida yanzu shakkar kawun ce ta hana tai mata habaici.


Umma ta ƙarasa ɗakin.

"Umma ni fita zanyi sabida na gaya miki wannan Æ™awar tawa tace yau yayansu yace zamu ga mutumin nan mai gidan rediyon kin san sabuwa ce tashar ana buÆ™atar sabbin ma'aikata"

Ummah ta bita da kallo.

"Ke ko ɗan man leɓe da hoda ba zaki saka ba? gaki baƙa kin ɗauki baƙaƙen kaya kin lafta babu wani armashi a shigar taki..................

***