7
by @autarmanya
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*007*
Washe gari Farha da wuri ta shirya cikin riga da skirt na atamfa ja ta yafa baƙin mayafi ta fesa turare ta ɗauki handbag ɗinta ta dubi Umma wadda ta zuba mata ido tana kallon ta.
"Umma ni zan tafi ai min addu'a"
Umma ta dube ta da kulawa.
"Allah ya bada nasara, yau ma baki karya É—in ba zaki tafi?"
Tai murmushi mai ƙayatarwa.
"Umma sai na dawo zan karya É—in"
Acikin kuÉ—in da Salim ya bata jiya umma ta É—auki dubu É—aya ta bata tana mata fatan alkairi.
Ta fita tsakar gidansu batare data kalli matan gidan dake hada hadar É—umaman tuwo da dama koko ba.
"Manyan ma'aikata sai ina?"
Cewar Babarsu Hadiza cikin sigar zolaya.
Farha data sa kanta a soro ta É—aga murya sosai tace mata.
"Gidan nasara da sa'a na nufa in Allah Ya yarda"
Daga haka tafita daga gidan titi taje ta sami abin hawa sai da ta biya ta É—auki shema'u sannan suka wuce.
Suna tafe suna hira inda shema'u take bata labarin da ya gali ya bata jiya na cewa ashe Gidan rediyon na wannan mutumin ne anan ya galin su ya fara aiki kafin ya bari wai kuma in dai zaka samo wa md rahoto tofa zai ta ƙara maka albashi.
Farha tai zuru kafin tace.
"Ya Allah kasa mudai muna da rabo"
Haka suka ƙarasa bakin gate ɗin bayan sun sallami mai Adaidata sahun daya ɗauko su, Suka shiga cikin gidan Rediyon zaman jiran Md ɗin sukai har wajan takwas da rabi kafin ya ƙaraso.
Da far'a ya dube su.
"A,a su fatima ne da wuri haka, Ah lallai ba zamu dinga samun matsala daku ba ku biyoni ciki"
Suka miƙe suka shiga office ɗinsa.
Zama sukai a saman kujerun office É—in shima ya zauna sannan suka soma gaishe dashi.
Ya dube su Yana É—aga takardun su.
"To Alhamdulillahi duk abin da nake buƙata a tare daku na samu, sai dokar gidan rediyon nan da zan faɗa muku, Bana son fashi sannan labarai na hausa da turanci ko wanne ya faɗo kanku zaku iyayi"
Duk suka bashi nutsuwar su sannan ya É—ora.
"Ni dai fatana duk inda labari yake mai daɗi wanda zai ja hankalin jama'a ina maraba dashi ku kawo mana Mu watsa tashar mu ta sami karɓuwa, Albashin ku dubu ashirin ne a wata, sannan babu taka maiman lokacin tashi ya danganta da yadda duty yazo muku wanda ake kafewa a waje kowa ya duba lokacin shi"
Farha a wannan karon ma sai da ta zube ƙasa tai masa godiya ya umarce su dasu tashi ya rakasu su zaga wajan da yakamata haka suka bishi ya nuna musu ko ina hatta ɗakin yaɗa labarai da sauran su Ma'aitan tashar basu da yawa abin har ya bawa su farha mamaki, Haka suka gaggaisa da sauran ma'aikatan sannan ya baro su anan domin suga yadda ake gudanar da aikin.
Ranar su Farha basu tashi ba sai wajan la'asar kuma ba komai sukai ba kawai ganin yadda ake labarai ne da yadda ake É—auka da yadda ake yaÉ—awa Wanda kafin kace me Farha harda daÉ—a ganewa sosai.
A gajiye liƙis ta shiga gida wanda tana zuwa ɗakin umma ta zube Fa'iza sai dariya take mata wadda tazo gidan ta wuni Da ƙyar Farha ta miƙe tayo wanka taci abinci dama sunyi sallar su acan Da gayya ta fita tsakar gida ta leƙa ko wani ɗaki ta shaida musu ta sami aiki Sai dariyar yaƙe suke mata Haka ita dai ta koma ɗaki tana bawa su umma labari.
**********
Sadiƙ bayan ya shirya Ya nufi Ɗakin Ammi har ƙasa ya tsugunna ya gaishe da ita sannan yace mata zai je ya Dubo Mami sai ya wuce lagos dan jirgin sha biyun rana yake son yabi Ammi tayi masa fatan alkairi sukai sallama ya shiga mota drivern gidan ya kaishi asibitin da aka kwantar da Mami.
Da sallama ya shiga ÆŠakin da mami take Hajiya Tajira maman mami ta saki fuska sosai tana cewa.
"Wa nake gani a cikin asibitinnan kamar Abubakar sannu da zuwa"
Sadiƙ ya zube har ƙasa yana gaida maman mami kafin ya tashi ya zauna kujerar da take kallon Mami wadda take zaune ta miƙe ƙafa tana shan tea fuskarta fayau duk ta rame.
"Sannu Mami yaya jikin ashe haka Allah ya aiko?"
SadiÆ™ ya faÉ—a cikin jajantawa.
Mami tai ƙasa da kanta tana kallon Ƙarfen gado bata ce komai ba.
"Kiyi haƙuri kada ki sanya tunanin komai aranki In sha Allahu zaki sami wani ingantacce"
Maman mami ta karɓe zancen cikin kwantar da murya.
"Haka ne fa Abubakar nima haka nake ta gaya mata, Amman daga ita har Alin sun ɗaga wa kansu hankali musamman ma shi daya ce ya ƙagu yaga magajin shi"
Sadiƙ ya cije leɓe yana murmushi yasan wannan faɗi ne Ba yadda za'ai Aliyu ya faɗi haka amman sabida kada ya ƙaryata ta yasa yace.
"Dama ai haihuwa ita ce ribar aure Mama muma fatan da muke Allah ya bashi É—an kanshi"
Daga haka ya miƙe ya zaro 20k daga aljihun sa ya direwa Mami yayi mata fatan Allah ya bata lafiya ya fita yana ƙoƙarin Fita daga ward ɗin su Sajeeda suka shigo hannun su ɗauke da ƙaton Basket na Kayan Break fast ya dube su.
"Ku yanzu dan sakarci kun san zaku zo amman baku bari mun tawo tare ba?"
Dariya sukai a tare suka gaishe dashi sannan yayi musu sallama driver ya nufi airport dashi dan yayi jiran jirgin daze bi bai bari maganar Maman mami ta sami gurbi a zuciyar shiba sabida yasan mata basa rabo da kace nace shiyasa ya kawar da maganar bayan yayi wa É—an uwan shi zato mai kyau.
Su Safna sun gaisa da Maman mami sannan sukaiwa mami sannu suka dire mata Basket É—in sabida sauri suke suna da lecture suka bar É—akin Mami ta bisu da harara tana jan tsaki.
"Wallahi Mama na tsani sadiƙ ɗinnan inna ganshi kamar na shaƙe shi sabida a duniya ba maganar wanda Aliyu yake ji sama data sadiƙ komai nashi ya ɗora shi akai"
Hajiya tajira tace.
"Ina sane ai na yaɓa masa magana kuma nasan ya fahimta kedai sha kurumin ki wallahi ba zamu barsu haka ba dole ma mu raba wannan alaƙar"
Mami ta kuma jan tsaki.
"Suma waÉ—annan Æ´an iskan yaran sai iyayi da girman kan tsiya wancan satin fa wayoyi ya sai musu masu uban tsada sannan yace wai ana fara visar umarar azumi zasu tafi Wallahi mama saura kaÉ—an na faÉ—i sabida takaici kuma bara na koma nima sai an tafi dasu Hassana"
Haka suka lalace a wajan suna ƙulla sharrin su kafin Likita tazo taga jikin mami jim kaɗan tazo ta basu sallama da yake da driver nan da nan sukai Gida a maimakon ya wuce da ita gidanta sai Hajiya tajira tace su wuce Fagge inta ƙara jin ƙwari sai ta koma Basu bi takan Aliyu ba Bare a tambayi izininshi.
******
Ranar Farha ta wuni ta kwana cikin farin ciki kuma washe gari babu sanya ta fita wajan aikin ta Alhamdulillahi ta sami wani daga cikin ma'aikatan yana ƙara nuna mata komai Taji daɗin Wajan aikin nata Haka ta cigaba da Fita aikin wanda tuni ta goge har tana ƙoƙarin shiga ɗakin watsa labarai Babban Burin Farha ya cika a sati ɗayan datai a Garkuwa Radio Duk inda ka zaga Muryarta ce raurau ke fita cikin labaran Yammaci wanda duk wanda ya kunna Radiyo ya kamo tashar garkuwa zaici Karo da Muryar Fatimah Ɗandago dan sam batai amfani da Abubakar ɗin ba Dole tasa Salim ya ƙara ɗaga mata ƙafar kawo kuɗin sabida da kanta tace yaje ya bawa kawu haƙuri ta roƙe shi daya bari tai kamar wata guda da fara aikin sai ai maganar auren nasu kuma Salim bai musa ba sabida yana sonta haka yaje wajan kawu da batun wanda kawu yay faɗa amman ya ce daga wannan lokacin baze kuma ƙarawa ba damma daga wajan salim ɗinne aka sami tsaikon.
Cikin rufin asiri farha take aikin ta sabida bama kowa ne yasan ita ce fatima É—andago ba sabida yawanci da farha aka santa Wani bin haka zataji kawu na sauraron labaranta taita dariya tana jin farin ciki sam bata da matsala a wajan aikin ta kuÉ—in mota kuwa wannan dubu biyar É—in umma tace ta aje ta dinga É—auka tana fita aikin Abu É—aya ne ta kula a wajan aikin shine Md babu ruwan shi da ingancin labari shidai kawai a kawo masa ya É—ora a kafarshi dan Rediyon shi tai farin jini sam ba ruwan shi sabida Allah ya bashi jarabar son kuÉ—in tsiya sabida yasan In dai Radion shi tai suna da talla ma kaÉ—ai zai iya biyan ma'aikatan shi.
Tana jin ƴan uwanta ma'aikata na ƙorafi da wannan matsala don zata iya jawo wa gidan rediyon barazana Ita dai da yake Allah bai sa taci karo da wata matsala ba yasa ta saki ranta Shema'u tana sashin labaran wasanni na safe ita kuma tana sashen watsa labarai na yamma wannan tasa sam bama sa haɗuwa da shema'u sabida lokacin da shema'u zata tashi ita kuma lokacin take zuwa Daga gidansu ma bata da lokacin kowa kullum tana ɗaki tana Rubuce rubucenta na labarin da aka bata wanda zata watsa shiyasa wani bin ma sai kaji Ana cigiyarta acikin gidan.
*ABUJA*
*****