9
by @autarmanya
*RABO YA RANTSE...!!*🌹
*NA*
*AUTAR MANYA*
ADABI WRITTER'S ASSOCIATION
*009*
Duk da uban raɓar na'urar A'c data ke kaɗawa a office ɗin, Hakan bai hana Gumi wanke musu Jikin suba.
Shema'u ta kalli Farha wadda take ta faman ƙifta ido kamar zata fasa ihu.
Maganar Md ce ta karaɗe Office ɗin.
"Wannan labari zai jawo hankalin Mutane zuwa wannan tashar tamu uwa uba manyan ƴan kasuwa zasu san da zamanta har ma su fara bamu manyan tallika sannan Ƴan hamayyar jam'iyarsu Suma zasu neme mu ƙila ma su ɗauki Nauyin fili na Musamman dan tattaunawa akan Harkar siyasa"
Md ya faɗa hankalinshi kwance.
"Gaskiya nidai bazan iya ba sabida taɓa Babban Mutum irinshi akwai matsala kamar yadda Taj ya faɗa Kuma ma hakan ya zama kamar Ɓata masa suna zamuyi hakan zai janyo mana babbar matsala"
Cewar shema'u wadda ta faɗa kanta tsaye Md ya ɗaga mata hannu.
"Ƙin Amincewar kowacce acikinku shine Tikitin Barinta aiki a wannan tasha kuna nufin zan ɗaukeku na baku Dubu ashirin duk wata a banza ne Jiya ma kaɗai dana tura ku ɗauko rahoto Guduwa kukai sabida haka wannan Labari dana buƙata shi nake so ku watsa Ƙin amincewa kuma kora ce Amincewa kuma Ƙarin albashine tare da Karramawa ta musamman danna san ba ƙaramin alkairi zamu samu ba"
Ya faɗa yana girgiza ƙafafun shi Farha ta bishi da ido Duk yadda Allah ya rufa mai asiri Amman bai godewa ba yake hango abin da zai saka shi acikin matsala, Har ta ɗaga kai zata ce ita ma bazata iyaba sai ta tuna da yadda aurenta zai zo ga hidimar Kayan ɗaki wanda da wannan aikin Ita da umma suka laru domin su rufawa kansu asiri dan tasan kawu ba abin da zai Sannan matan gidansu kowa ya sawa aikinta ido idan har ta daina wannan zai basu ƙofar Yi mata habaici da dariya sannan zata jefa zargi a zuciyar umma na dalilin daya sa aka koreta tasan kota faɗi dalili ba lallai a yadda.
"Yallaɓai zanyi ni zan iya"
Ta faɗa Muryarta na rawa.
Md ya washe baki yana cewa
"Yawwa ƴar gari To shikenan Gobe zamu fitar da tsarin Komai Yau na sallameki da wuri tafi gida ke kuma ga takardun kinan kada ki kuma dawo min Tasha"
Yana faɗin haka ya miƙe ya watsowa shema'u takardunta yabar Office Ɗin Shema'u ta ɗebe su ta zuba a jaka ta Miƙe tana bala'i
"Dama irin kune kuke ɓatawa ƴan jarida suna kuma in sha Allah wannan labari sai ya wargaza maka farin cikin ka, kawai dan biyan buƙatar kanka zaka ɓatawa Bawan Allah suna mutum mai taimako mai tausayi Allah baze baka nasara ba"
Tana gama faɗin haka ta fice Sauran ma'aikata na mata magana suna tambayarta ƙanwar Gali mai ya faru tai musu banza Ta tari Abin hawa da ƙyar Farha ta cimmata suka shiga adaidaita zuwa gida.
"Ke yanzu Farha akan abin da bai taka kara ya karya ba zaki zaɓi abin da zai ja miki matsala dan wallahi ƙarshenta ta rufta dake, Ki zauna ki karatun ta nutsu shi Md mai kuɗi ne ƙila ma ya ɗauke iyalinshi subar ƙasar ke kuwa fa? baki da tsuntsu baki da tarko wagairahun Ai a kano"
Farha tai murmushi.
"Shema'u baza ki gane ba nidai Allah yasa hakan ya zama alkairi Md ya ƙara min kuɗin nan dan na kashe matsalolin gabana"
Shema'u ta mata wani sakaran kallo kafin tace.
"Farha kenan mai yasa mu mutane muke da son kammu ne? kin zaɓi ki ɓatawa wanda nauyin sama da al'umma dubu suke ci a ƙasan shi dan ki kauda matsalar gabanki? kin zaɓi ƙuntata zuciyar wanda yake taimako domin Allah dan ki kauda taki matsalar lallai kin taro faɗan da baki da ƴan wasa Allah ya baki sa'a"
Duk wannan Maganganu na Shema'u basu saka farha taji wata karaya akan Ƙudirinta ba haka ta rufe ido tana Tunanin yadda zata kaya gobe.
Ba yadda shema'u batayi da farha ba akan ta janye amman taƙi daga ƙarshe haka suka rabu baram baram Farha a zuciye ta shiga gida Sabida yadda shema'u ta gaggaya mata magana har tana ce mata Shi mai kuɗi ne zai iya sawa a ɗaure kaf Familyn su Farhan.
Tana shiga cikin gidan ta tarar da su Umma a tsakar gida kowa farin ciki yake ta aje Handbag ɗinta ta nufi randa ta ɗibi ruwa ta kafa kai tana sha.
"Farha kinga Allah ya karɓi addu'ata Yau dai su Halifa sun sami aiki a kamfanin SA ɗin jiya"
Gaban farha ya faɗi tai murmushin dole tai Musu fatan alkairi ta wuce ɗaki.
Yau gidansu Farha gwanin sha'awa su Halifa anƙi fita konan da can suna gida ana taya su Murna Shi Halifa yana ɓangaran gyaran motoci Nura kuma sune masu Duba motocin da suka shigo da waɗanda suka fita dama an gama karatu ba aikin yi Ga zafin talauci ga Samartaka Wannan samun aikin Nasu Yayi wa kowa na gidan Daɗi hatta kawu sai da ya shiwa SA ɗin gwamna Albarka Abin daɗin Kuma shine Kowani ɗan ɗaki ya samu aikin Halifa ɗan ɗakin su Ruƙayya Nura kuma ɗan Ɗakin su Hadiza ita dama Umman Farha bata da ɗa namiji amman harta fi Iyayen yaran murnar samun aikin nasu.
Gaba ɗaya Farha jitai bata da sukuni Taƙi sakin Jikinta a gida sai faman Juyi take a saman gado Ko tsakar gida taƙi fitowa duk Murnar da ake agidan tana ɗaki a ƙunshe har magariba.
"Wai Farha meke damunki kada kija ace kina baƙin cikin samun aikin su Halifa kinsan halin Gidannan ba'a raina magana"
Farha taja Abin da ta rufe Jikinta dashi.
"Umma bana jin daɗin Jikina ne"
Umma ta dube ta da kulawa sosai.
"Allah yasa ba ciwon marar ki bane zai tashi ba, ga ba kuɗi a hannuna"
Farha ta dubi umma
"A,a lokaci bai yiba kuma ina neman sauƙi wajan Allah"
Ranar Ko makarantar dare ma bata jeba Umma kuwa yau hirar tsakar gida ce ta Ruɗe a gidan wanda Halifa ya baje yana ta basu labarin Yadda Mai Kamfanin Madaki Motors ɗin ya karramasu Kuma da kanshi ya Duba takardun kowanne acikinsu ya kuma raba musu aiki da albashi mai tsoka Halifa ya ƙara da cewa.
"Ai wallahi sanda naji labaran jiya ko bacci banyi ba Muna tashi Da asubah muka tafi Sai wajan azahar layi yazo kammu Mutum Ɗari da hamsin ya nema amman Mutum yakai Dubu da sukaje lallai ana zaman banza a garin nan"
Babarsu Ruƙayya tace.
"Allah dai yayi masa albarka yadda ya fitar damu daga takaicin rayuwa shima Allah ya yaye masa dukkan matsalolin shi"
Babarsu Hadiza tai caraf tace.
"Tab su masu kuɗi ina suka ga matsala zasu sha madara suci kaji Kai dai talaka mai neman na masara kaike da matsala"
Halifa yayi dariya sannan yace.
"Tab yadda naji fa ance bai taɓa haihuwa ba Mama ke kin ganshi kamar shi yayi kanshi dan kyau yadda kika ga Tumatur sabida ja wallahi ban taɓa ganin Mutum mai kyau irin nashi ba Kamar ka taɓa jini ya fito"
Ya ƙare yana kallon Babarsu.
Babarsu Ruƙayya tace.
"Lallai duk wadda Allah yasa ta haihu dashi ta girmi talauci Allah ya bashi ɗan kanshi"
Ire iren waɗannan hirar sukai tayi har kawu ya shigo shima ya saka baki ranar gidan dai ya wanzu cikin farin ciki ita kam Farha bata san wainar da suke toyawa ba haka tai kwanciyar bacci mai nauyi yayi gaba da ita.
***********
Ammi ta dubi Aliyu wanda shigowar shi kenan Falon nata dan tunda yazo bai sami damar zuwa wajanta ba, Yaje gidan gwamna yau kuma ya ɗebi ƙananun ma'aikata a kamfanin shi dan ko wajan wasan ƙwallon ƙafar matasan gwale bai jeba sai saƙo ya bawa musa yakai musu.
"Sannu babana mai za'a kawo maka?"
Ammi ta faɗa da kulawa.
"Ammi ni yanzu bazan iya cin komai ba dare yayi adai haɗo min Baƙin shayi kaɗai ma is ok"
Ammi ta kalli Sajeeda da duk ta shiga taitayin ta ganin dodonsu ya shigo falon.
"Auta maza haɗowa Hammanki shayi a ƙananun Kofuna"
Ya turɓune fuska.
"Ammi kinsan bani son yarannan na taɓa abu kina bani"
Ammi ta kama haɓa tana dariya.
"To sarkin tsafta na manta ne ai, Bara na haɗo ma da kaina, Niko nace yaya Kaje ka dubo Mami kuwa? ɗazu na kira yaya tajirar ma bata ɗauka ba ina ga bata kusa da wayar tata ne"
Wanni kallo ya watsawa Sajeeda ba shiri ta Miƙe har tana haɗawa da Gudu tabar falon.
Kafin yaɗan kalli Ammi............
*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya ****