RABO YA RANTSE...!

13

by @autarmanya

*RABO YA RANTSE...!!*🌹

      

      *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


           *13*


luuu ta tafi zata faɗi Aliyu yayi saurin tarota jikinsa da faffaɗan hannunshi Ya wani rungumeta a cikin ƙirjinshi Ƙifta idanu Farha take tana Ƙoƙarin zamewa gaba ɗaya Jikinta rawa yake sosai tunda take a rayuwa ba namijin daya taɓa raɓata da jikinshi sai wannan bawan Allah da bata san kowa ye shiba.

Cikin Nutsuwa ya zamar da ita daga jikinsa yana sakar mata mayaudarin Murmushi.

Da sauri ta tattare Ƙasan skirt ɗinta zata Koma gida da gudu Aliyu ya kuma saka hannunshi a karo na biyu ya janyota gabanshi.

Ko Rabin tsayin shi bata kai ba ganinta yayi ƴar ƙarama a gaban shi Ya Sunkuyo sosai gabanta ya rage tsayin shi ya ƙura mata idanunshi waɗanda ya lura Suke mata kwarjini a tare dashi fiye da komai.

Lumshe idanu Farha tai Jikinta yana rawa ƙirjinta yana bugawa bata taɓa Ganin Halitta Mai kyau kamar ta wannan Bawan Allah ba, Dan ko kaɗan bata ɗauka ma bahaushe bane.

"Amincin Allah da rahmar sa su tabbata agare ki My princess"

Muryar Aliyu mai taushi ta doki dodon kunnen Farha.

Ƙara raÉ“ewa tai Duk jikinta yayi sanyi atake anan wani irin BAƘON LAMARI Ya ziyarci zuciyarta.

"Nasan zaki mamakin yaya akai nazo har gidanku? Ba mamaki abin da kake so shi kake bibiya Naje har gidan Radio ɗin da kike aiki wanda anan hanyar na ganki amman Naga gidan Radio ɗin a Ƙone mai ya faru da shi?"

Gaban Farha ya faÉ—i waige take Ko wani zai zo wuce wa daga cikin Æ´an gidansu ganin babu kowa yasa taja ajiyar zuciya.

"Bawan Allah kayi haƙuri dan Allah, Nima ban san mai ya faru da gidan Radio ɗin ba, Kuma kabar Ƙofar Gidannan sabida Kawun mu in yazo ya tarar dani da wani raina zai ɓaci"

Aliyu ya zubawa ɗan ƙaramin bakinta ido wanda take sarrafa shi wajan yi masa magana dashi ya wani Lumshe ido tare da warasu akanta Kana yace.

"Ina son ki kuma ni da maganar auren ki nazo in baba ma ya ganni zan sanar masa Naga matar aure agidan shi"

Farha ta firfito da idanunta waje cike da tsaro.

"Dama ana aure batare daka san Mutum ba Bawan Allah?"

Aliyu yayi Murmushi yana danne Abin da ke taso masa a ƙasan ranshi.

"Sunana Bawan Allah anan cikin gari nake nagaya miki in zaki fita aiki nake ganin wucewar ki gashi ma baki gayan dalilin Ƙona gidan Radion naku ba"

Farha ta dafe ƙirjinta dake barazanar faɗowa ƙasa dan tsabar yadda yake Luguden duka.

"Kayi haƙuri Dan Allah, Ina da wanda zan aura in Babana yazo ya ganka sai ya halaka ni"

Aliyu ya wani zaro ido wanda ya ƙara haska zatin kyansa wanda ya kuma ruɗa farha.

Yace.

"Nima ai mijin aure ne serious ina sonki kuma da gaske in da hali zan maye gurbin wancan"

A wannan karon muryar farha da É—an tsiwa tace.

"Zaka biya dukkan hidimar daya ɗauka shekara da shekaru yana mini Idan har na Rabu dashi ai naci amanarshi na yaudare shi Kuma zan sanya Ƴan uwana da iyayena cikin damuwa"

Aliyu ya cije leɓe.

A zuciyar shi yana Cewa Ni kuma silar labarin ki ɗaya a jiya ya cillah dukkan ahalina cikin matsala ya sanya Mahaifiyata zubar hawaye Wallahi bama zan barki ba sai nai amfani da ƙarfin soyayyata na ruguza dukkan farin cikin ki yadda kika min.


Gani yaƙi cewa komai yasa ta juya zata shiga gida, Hannun shi ya ɗora a saman ƙafaɗunta ya juyo da ita tana kallon Fuskar shi.

Ya matso gabanta har yana fesa mata Hucin Numfashin sa


"Ni ina son ki, Kuma auren ki zanyi ina son ki min list na duk abin da yayi Miki ni zan ninka masa"

Daga haka ya turata soron gidan da ƙarfi ya juya yana tafiyarsa mai cike da burgewa.

Zubewa tai a wajan tana Mayar da Numfashi wata sabuwa!

Da ƙyar ta shiga cikin Gida duk maganar da Umma kewa Farha sam taƙi bata amsa gado ta haye tana tunanin anya ba aljani bane ba Ita dai bata san shiba sannan kuma bata taɓa ganin Mutum mai kyanshi ba ɗan gayu ga ƙamshinsa ya cika mata hancinta Tsintar kanta tayi da Lulluɓe Jikinta duk rufe idanun da zatai hoton shine ke yawo acikin idanunta tashi tai ta Zabga tagumi Ganin hakan baze fishsheta ba ta miƙe ta fita tsakar Gida ta ɗauro alwala ta soma nafila.


********

Yana murmushin samun nasara ya shiga Motar Ko kaɗan batai masa ba hasalima bata burge shiba kawai zai aure tane dan ya ƙuntata mata ya kuma sanya takaicin ta acikin zuciyar mahaifanta ya fahimci daga ita har mahaifanta suna bala'in son wannan saurayin nata sabida haka zai amfani da ƙarfin Soyayyar shi wadda zai cusa mata ta ƙarfin tsiya dan ya wargaza dukkan farin cikinta ita da mahaifanta kamar yadda tai jagaba wajan Yaɗa sharrin sa.

Sam baze miƙata ga Hukuma ba aurenta kaɗai da zeyi shine dorinar dukan dukkan laifi kan data masa Sabida ta yaya ma zai tsaya yana shari'a da mace.

Gumi ya share sanda ya tuno da Ammi yasan ko yasha giyar wake baze tari Ammi da batun zai auri yarinyar nan sabida Hukunci ga laifin data masa ba to meye mafita zai boyewa Ammi auren sane Girgiza kai ya shigayi ammi bata cancan ci haka daga gareshi ba Sannan kuma yasan inta sani bazata yarda ya auri yarinyar ba Shi kuma ta hanyar aure kaɗai ya zaɓi Ƙuntata mata dan shi ba mazinaci bane bare yay amfani da wata dama dan ya tarwatsa mata Farin cikinta Kuma shi ya tabbatar wa zuciyar shi cewa baze taɓa barin Wannan yarinya ba wallahi sai ya ɗauki fansar Abin da ta masa.

Har suka ƙarasa gidan shi bai sami mafita ba sallama sukai da Musa wanda bai san yadda Aliyu Yayi da yarinyar ba kuma bai sami fuskar tambaya ba bare ya tambaye shi.

Part ɗin Ammi ya nufa ta tirsasa shi akan dole sai yaci abinci yana ci tana masa Bayanin Maman Mami tazo da Ƴaƴanta Dan su masa jaje, Sannan ta buƙaci Daya Musu alfarma Mami zata ɗan kwana biyu agida ta huta.

Taɓe baki yayi tare da cewa.

"Nifa Ammi cikin satin nan ma zanje chaina dan zan shigo da sabbin Motoci kamfanina dake lagos sabida haka bani da matsala da zamanta agidan nasu"

Daga haka ya tashi yayi mata sallama yabar part É—in.

Kwanciya yayi akan gadon shi yana hasko fuskar yarinyar Ƙaramar yarinya ce sosai Shi dariya ma ta bashi yadda yaga duk ta tsorata in banda Abin shiri na zuciyar mace ina ita ina shi Ya kuma gyara kwanciya yana hasko ƙanƙantar ta Lallai wannan ma in yace zai haɗa ƙirji da ita tabbas Mutuwa zatai dan yayi mata girma shi bai ma taɓa ganin Halitta ƙarama kamar ta wannan yarinya ba komai nata ƙarami hatta yatsun hannunta daya kalla ƙananu ne.

ALIYU KENAN.

Yaja Bargon shi ba jimawa bacci yay awon gaba dashi.

Da safe ya fita kamfanin shi tuni ya watsar ma da batun wannan yarinyar ya shiga sabga da ma'aikatan shi wanda yawanci Jaje ne suke masa akan abin da ya faru Dan nacin Ƴan jarida har can suka bishi akan suna son jin ta bakin shi fafur ya hana ma'aikatan shi barin ƴan jaridar su shigo masa haka ya wuni a office yana saka hannun a takardun Motocin da aka tura wasu jahohin bai tashi ba sai wajan Magariba ƙofar Gidan shi ma ba masaka tsinke tun yana magana muryarshi tana fita har muryar tashi sai da ta dashe sabida amsa gaisuwar jama'a bai shiga gida ba sai wajan 12 na dare Yana mai jin farin cikin yadda al'umma suka nuna rashin jin daɗin su na abin da ya same shi lallai ya yarda jama'a rahma ce Kuma alkairi Daɗi gare shi wanka yayi ya kwanta jikinsa fal gajiya Hutu kaɗai yake buƙata..........

*RABO YA RANTSE! littafin kuÉ—i ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a É—auka a turo,shaidar biya ****