RABO YA RANTSE...!

16

by @autarmanya

*RABO YA RANTSE...!!*🌹

      

      *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


           *16*


Tana zuwa gaban shi ta zube a ƙasa tana sakin marayan kuka, Hankalin shi a matiƙar tashe ya tsugunna a gabanta ya sanya hannun shi ya kamo Tattausan hannunta ya zuba mata Girman idanun shi batare daya ce mata ko mai ba sai binta yake da kallo kamar zai cinyeta ɗanya.

Kukan take Babu ƙaƙƙautawa Tuni Kan Aliyu ya fara juyawa in da abin da yafi tsana a duniya bai wuce kukan mace ba sabida tafarar ɗaya yake sanya masa Rauni.

Da ƙarfi ya damƙe hannunta wanda Hakan ya sanya ta sakin wata irin ƙara tana yarfe hannun sabida tun Dukan da umma tayi mata take zaton Hannun nata Ya sami targaɗe.

Kula da yayi hannun na mata zafi ya sanya shi ya sakar mata shi.

"Shiii Be quiet and let's talk"

Ya faɗa yana sakin numfashi mai ƙarfi.

Sannu a hankali take rage sautin kukan nata kamar yadda ya buƙata.

Muryarshi can ƙasan maƙoshi ya furta mata.

"What made you cry?"

Goge idanunta take da hannunta mai lafiya muryar ta a dashe ta soma yi masa magana.

"Kawu ne yace in baka aiko an ɗaura min aure da kai gobe ba, zai ba dani sadaka"

Aliyu ya zare ido with full surprise.

Kafin yayi magana ta cigaba da cewa.

"Tun jiya umammu take dukana har targaɗe tai min"

Tana faɗin haka ta kuma fashe masa da kuka.

Yayi ƙasa da murya kamar mai raɗa Ya ƙara matsowa gaban ta a yadda yake a tsugunnen.

"Duka garin yaya akai haka? dama shi kawu ya sanni ne?"

Ƙunshe fuska tai Cikin jin kunya tace.

"Dan nace bazan auri Salim ba"

Cikin Tattausar Muryar shi yace.

"Dalilin ki? kodai kina sona ne kema?"

Ƙasa tai da kanta ta ɓoye fuskarta da hannunta wanda ya bashi tabbacin zargin dake zuciyarsa na ta bijirewa mahaifan tane akan shi.

Ya saki wani ƙasaitaccen Murmushi ya Leƙa fuskarta data ɓoye.

"Baki sanni ba Fatima, Ko sunana bani tunanin Kin sani bare anguwar mu bare sana'ata kawai tashi ɗaya ki bijirewa wanda da bakin ki kika ce tun kina ƙarama yake miki hidima Why are you doing this, Fatima?"

Ya faɗa mata hakan cike da mamakin ta tare da jinjina girman wauta da ƙuruciyarta.

Muryarta har zuwa lokacin bata Dawo daidai ba may be kukan data sha ne yayi Mata haka da muryar tata.

"Bawan Allah! Koda acikin Bukka kake rayuwa namun daji suna kewaye ka ni zan bika mu rayu tare, Ni dai na san ba zaka cutar dani ba, Kawu yace in baka aure ni ba zai bada ni sadaka kuma kai da bakin ka kace kana sona zaka aure ni"

Shuru Aliyu yayi gaba ɗaya ta gama kashe masa jiki da kalamanta wani irin tausayi yarinyar ta bashi amman daya tuna yadda tai jagora wajan ɓata sunan shi sai ya kawar da tausayin nata a zuciyar shi, Amman kuma mamakin yadda tace tana son shi batare data san koshi waye ba, abin ya bashi mamaki sau da dama yasha Cin karo da ƴammata su tare shi suce suna son shi wanda duk ba domin Allah bane sai dan kawai yana da kuɗi amman ita ta miƙa wiya ko sunan shi bata sani ba amman ta bashi dukkan zuciyarta.


"Kukan ya isa fatima, kawu ɗin gobe yace?"

Da sauri ta ɗaga kanta.

"So nake ki min magana da baki bana son magana da ka"

Ta fahimci yana da son a girmama shi.

"Eh haka yace"

Shuru ya kuma yi gaba ɗaya kanshi ya ɗauki zafi.

"Tom shikenan kice masa zan turo ƙanin mahaifina goben, Amman ni bani da abokai Kuma ni bazan zo wajan ɗaurin auren ba amman zan turo Waliyi na tare da sadaki hakan yayi?"

Ga mamakinsa sai yaga ta saki ranta har tana murmushi batare data tambayi ina zai kaita ba.

"Fatima baki tambayi ina zan kaiki ba inna aure ki?"

Fuskarta cikin farin ciki tace.

"Nina san ba zaka cutar dani ba"

Murmushi ya saki na dole dan ya ɗauki alƙawari mai wiyar cikawa.

"Tashi Muje a gyara maki hannun sai na maido ki gida"

Ta zaro ido wanda hakan ya ƙara fito da kyanta wanda ba kowa ne yake gane hakan ba.

"So kake ai gunduwa gunduwa dani agida"

Ya wani kashe mata ido ɗaya.

"To niba mijin ki bane,Hurry up and let's go back"

Miƙewa tsaye yayi kafin ta tashi har yay tafiyar shi bin bayan shi tayi Allah yasa har suka je bakin layin basu ga kowa ba ya buɗe mata front seat ta shiga shi kuma ya shiga driver seat Lumshe idanu tai Sabida wani mahaukacin sanyin Ac tare da ƙamshi daya cika motar ita sai tace tunda take a rayuwa bata taɓa ganin mota mai kyan wannan mota ba, ( hhh to farha ai masu abu da abun sune da mai kamfanin madaki motors kike tare a rashin sani ) tafiya suke kamar ta kurame shi yana can duniyar tunanin dalar daya ɗaukowa kan shi ba gammo, ita kuma sanyi da ƙamshi da fargabar gida sun sa tai tsuku.

Jifa jifa yake ɗaga wayarshi wanda duk maganar da yake bada hausa yake yiba da turanci yake yinta.


A daidai ƙofar Ɗan agundi Yayi parking ya kashe motar ya ɗauki face mask ya saka wadda ta lura kamar sakata ya zama ƙa'idar shi.

"Muje ko"

Daga haka ya sauka daga cikin Motar.

Yayi gaba tabi bayan shi gidan sarkin Ɗori Suka shiga kai tsaye ɗakin dake soron gidan ya shiga bayan ya tuɓe takalman shi Dattijo suka tarar a zaune yana shan shayi Suka gaisa dashi Aliyu yace.

"Na kawo ta Baba a duba hannun ta"

Dattijon ya aje Kofin shayin.

"Allah sarki yarinyar kace kenan? matso mugani jikata"

Aliyu yayi murmushi yana ayyana lallai ƙanƙantar Yarinyar tayi yawa.

Farha ta ƙarasa gaban Dattijon.

"Ki cire hijabin ki fito da hannun"

Da sauri Aliyu yace.

"A,a zata fito dashi a haka ai yana da hannu, Fatima fito dashi ta cikin hannun shi"

Tayi yadda yace ɗin.

Addu'a Dattijon yayi Kafin ya cafki hannun da sauri yana Matsa shi.

"Wayyo Ummata Washhh zafi"

Ta faɗa tana cije bakin ta.

Kafin a gama Gyaran ta gama Jigata da gumi da hawaye.

Ana gamawa ta sunkuyar da kanta tana Kuka wiwi

Aliyu ya cire kuɗin da bai san adadin yawan suba ya aje wa Dattijon.

Godiya dattijon yayi tare da cewa.

"Wannan yarinyar taka akwai rigima bari na shiga daga ciki Allah ya bata lafiya.

Daga haka ya miƙe ya fita daga ɗakin.

"Ki shuru dare nayi, Ki tashi na kaiki gida"

Kukan take bata kula shi ba.

Ya miƙe tsaye ya nufi hanyar fita.

Da sauri ta miƙe agarin saurin ta take Hijabinta aiko ta faɗi ƙasa tim.

Cikin azama ya juyo ya ɗagota.

"Kema gaki ƙarama kina sanya wannan abun yayta kayar dake"

Hijabin ne ya cukurkuɗe dole ya sanya hannu ya zare mata shi yana warware wa.

Farha tai saurin sanya hannu tana kare Jikinta sabida daga ita sai doguwar rigar atamfa wadda ta kama jikinta sosai Daga saman Ƙirjinta ya bullutso yayo sama dama duk ƙanƙantar ta Allah ya bata sama da ƙasa ba laifi kuma masu fusgar hankali.

Aliyu cikin mamakin Halittar Jikinta wadda ya kalla a rashin sani lokacin daze miƙo mata hijabin Ya bata Hijabin Ya fita daga ɗakin Har ya ƙarasa Cikin mota tana laƙai laƙan tafiya Haka ta shigo Cikin motar duk kunya ta gama kamata.

"Raguwa sarkin raki"

Ya faɗa batare daya kalleta ba yaja motar suka bar wajan, a wani haɗaɗɗan restaurant yay parking.

Ya juyo ya kalleta.

"Wait for me, I'm coming now"

Daga haka ya buɗe motar ya fita.

Minti kusan goma sai gashi nan da Ledoji Manya guda Biyu a hannunshi ya zaga Back Seat ya aje su.

Sannan ya dawo ya shiga motar ya zauna ya tayar da motar suka cigaba da tafiya idanunshi akan kwalta.

"Are you waiting for me? be patient"

Taji muryar shi acikin kunnenta ba tare daya kalle taba.

Har suka Ƙarasa bakin layin su.

Babu wanda yayi magana acikin su.

Ya kashe motar ya Fita ya kwaso ledojin Itama ta fito.

"Muje na rakaki"

Ya faɗa, tana gaba yana binta a baya har suka ƙarasa bakin Ƙofar gidan wanda yayi daidai da lokacin da kawu ya fito daga gidan.

Farha taja da baya ta koma bayan Aliyu cike da tsoro.

"Bawan Allah ga kawu nan na shiga uku"

Ga mamakinta sai taga ya tunkari kawu ba tare da wani tsoro ko fargaba ba.

Ba tada zaɓin daya wuce tabi bayan shi haka tabi bayan shi kamar kazar da ƙwai ya fashewa aciki.

Har ƙasa taga tsugunna yana gaida kawu.

Da gudu tayi cikin gida Kai tsaye ɗaki ta nufa ta haye saman gado.

Jim kaɗan kawu ya shigo yana ƙwala mata kira.

Jiki na rawa ta fito ta tsugunna a gaban shi.

"Allah ya taimake ki, Gobe zasu zo a ɗaura aure amman ki sani duk abin da ya faru dake kada ki nemi gidana"

Daga haka ya juya yabar wajan.

Tana shiga ɗaki Zuhuriyya ta biyota da ledoji.

"Wai gashi inji wani a waje yace wai Allah ya baki lafiya"

Umma ko kallonta batai ba jiki a sanyaye ta ɗebe ledojin ta shige ɗaki.


Aliyu daga wajan Farha gidan Kakannin shi inda ƙannen mahaifin shi suke ya nufa Bayan sun gaisa da baba usman Aliyu ya zaro kuɗi kimanin dubu ɗari ya zube a gaban ƙanin mahaifin shi.

"Baba in Allah ya kaimu Gobe da misalin ƙarfe goma Musa zaizo ya kaiku ɗandago na nemi auren wata yarinya Mahaifinta sadaki kaɗai ya buƙata daga wajena, Amman dan Allah baba wannan magana ta zama sirri bana son Kowa yaji inba sauran kawu naina ba"


Baba usman ya cika da farin ciki addu'a yahau yiwa wannan aure yana saka mai albarka kuma ya tabbatar wa Aliyu da cewa in ba sauran ƙannen shi da zasu je tare ba ko matansu ba zasu ji ba, Aliyu yayi masa godiya yabar Gidan.

Kanshi tsaye gida kuma ya nufa yaje part ɗin Ammi bayan sun gaisa ta kawo masa shayi.

"Ammi nifa gaskiya aure zan ƙara Mami tace sai ta huta zata dawo"

Ya faɗa yana son ya gwada yanayin ta idan har ta amshi maganar sai ya fito fili ya gaya mata gaskiyar shi.

Haɗe ranta tayi kamar yadda ta saba duk lokacin daya zo mata da batun aure.

"Ban amince ba"

Ta faɗa.

"Ammi dalilin ki? shin aurena zai saɓawa shari'a ne ko kuma ƙarin aure haramun ne?"

Ta haɗe ranta kamar bata taɓa dariya ba.

"Ko ɗaya Malam zaka ƙure ni, auren ne kawai banga damar ka ƙara ba ka jira har Allah ya bawa Mami rabonta in ma dan shine kake cewa zaka ƙara aure"

Ganin ta ɗau zafi yasa ya sassauta Murya.

"Allah ya baki haƙuri Ammi ya huci zuciyarki"

Daga haka ya miƙe ya fita daga parlon, Ammi ta bishi da kallon tausayi sai dai ba zata taɓa barin shi yayi aure ba domin tana gudun sharrin matan wannan zamani sannan uwa uba tana taya mami kishi kasancewar ta ƴar yayarta wadda kuma ita ta haɗa auren sabida haka ba zata so ai wa mami kishiya ba.


Daran wannan rana Daga Aliyu har farha sun kwana cikin zulumi.

Washegari gidansu farha ba'a tashi da shirin komai ba kamar ba auren budurwa ba,kawu yace baze gayawa kowa a dangin shiba kuma yace baze kayan ɗaki ba haka umma ma tace ficikarta bazatai ciwon kai ba wajan ƙarfe Goma Baƙin suka ƙaraso Ƙofar Gida Halifa ya kira kawu, Musa sarai ya gane Halifa amman shi Halifa bai gane musa ba dalilin kuwa daya sa Musa ya gane Halifa sabida rabon kuɗin daya yi musu a kamfani, Shi kuma Musa da face mask a fuskar shi wannan tasa Ba kowa zai shaida shiba


Iya maƙota kawu ya kira aka shinfiɗa babbar tabarma a ƙofar gida bayan addu'oi aka ɗaura auren FATIMA ABUBAKAR MAI BULO DA ALIYU AUDU MADAKI, Akan sadaki naira dubu ɗari addu'a akai aka shafa gaba ɗaya mamaki ya cika musa wanda dama tunda Aliyu yayi mishi waya ya sanar masa acikin mamakin yake.


Buhun goro da alawa Baba Usman daya siyo ya miƙawa kawu aka rarraba Musa ya Ɗebi su Baba usman a mota dan ya mayar dasu gida.

Bayan ya cewa kawu zai zo ya ɗauki amarya su wuce kamar yadda Aliyu ya bashi umarni.


Cikin mamakin sunan wanda aka faɗa da angon farha Halifa yake naɗe tabarman da suka zauna, sai dai tunanin da yayi na suna ai da yawa wanda ake cin karo dashi iri ɗaya yasa ya watsar da mamakin nashi ya shigar da tabarmar gida ya shiga sabgar shi.


Kawu yana shiga cikin gida ya watsawa umman farha sadakin farha.

Tare da cewa.

"Burunku ya cika, Ke kuma maza ki haɗe kayan ki yanzu Mijin ki zai zo ya ɗauke ki, kuma koda wasa kada ki zo min gidana da kowace irin matsala"


A wannan karon umma tai magana Sabida ta riga ta saduda da lamarin.

"In sha Allah wannan aure alkairi zai zame mata, Ni mahaifiyarta ce ya Allah ka kare min ita aduk inda take aduk inda ta tsinci kanta Allah ka sawa mijinta son ta da tausayin ta"

Umma ta faɗa tana hawaye dan jiya nasihar umman zage yayarta ta ratsa mata Jiki wanda tace mata kada ta yarda taiwa ƴarta Mugun baki ko fata.


Bayan musa ya kai su baba usman ya aje su Aliyu yayi masa waya sun jima suna magana kafin Musa ya nufi Gidan su farha cike da mamakin maganganun Ubangidan nashi.


Musa ya ƙarasa har ƙofar gidan yasa yara su masa magana da kawu wanda kawun yace ba inda ze fita farha kawai ta ɗauki kayanta tabi shi Farha kuka Umma kuka da sauran ƴan uwanta wanda kawu yace ba mai binta rakiya itama kuma baya neman tazo masa gida haka Su Ikram suka ɗauki jakar kayan farha wadda suka haɗa mata suka fitar mata da ita wajan mota da ƙyar Babarsu Ruƙayya ta ɓamɓare farha daga jikin Umma wadda take kuka kamar ranta zai Fita.

Tana ji tana gani aka saka kayanta cikin Mota itama ta shiga Musa yaja Motar suka Nufi Gidan Mijin nata.


Suna tafe tana kuka har zuwa sanda suka ƙarasa Ƙofar gidan masu gadi suka Wangale Ƙaton Gate Ɗin adaidai nan farha ta ɗaga kanta tana kallon aljannar Duniya.

Musa ya dube ta.

"Alhaji yace a gaya miki, Sunan shi Ali Madaki wanda kikai jagora wajan Yaɗa labarin shi akan ƙarya sannan yace koda wasa kada ki Kuskura ki nuna kina da alaƙa dashi In kina son zaman lafiya acikin Gidannan"

Jikin farha rawa ya kama tsoro nadama fargaba sune suka rufeta Ruf Auren ɗaukar fansa yayi da ita kenan ashe yaudarar ta yayi ya haɗata da iyayenta ya rabata da saurayin ta Kukan ma kasawa tai a wannan Lokacin tasan kuka ma rahma ne, Tana tuna furucin kawu gabanta ya kuma faɗuwa daya ce kada ta nufo masa gida da ko wace matsala, Lallai Bawan Allah.

Ta faɗa a zuciyarta tana Jan ajiyar zuciya ta kalli gabas da yamma ko ina na gidan akwai jami'an tsaro babu damar guduwa to ina ma zata je

"Fito Muje Ciki"

Musa ya faɗa Bata da zaɓi illa sauka tabi bayan shi hannunta ɗauke da jakar kayanta.

Babban parlon daya fi girman Gidan su suka shiga.

Tsayawa faɗin kyan parlon da tsarin shi ɓata Lokacine Musa ya zauna a ƙasan Carpet itama ta zauna.

Ya kalli dattijuwar dake jera kayan abinci dining.

"Hajja dan Allah ki mana magana da Ammi"

Hajja ta juyo da Far'a kana ta nufi wata hanya Jim kaɗan ta dawo tace masa tana zuwa.

Ƙamshinta ne ya fara yi musu sallama Kafin ta ƙaraso Wajansu Kallo ɗaya farha tai mata ta gane itace mahaifiyar Aliyu dan ga kama nan sosai.

Gaban farha ya faɗi haka kawai taji tana Masifar shakkar Ammi.

Musa ya gaishe da Ammi cikin ladabi itama farha tayi yadda yayi Ammi ta dubi Musa da kulawa.

"Musa kwana biyu Ka Ɓuya?"

Ya shafa kanshi.

"Ammi ayyuka ne suka sha kaina, Dama Ammi Nazo da alfarma wajanki ne wannan ƙanwata ce daga ƙauye Ƴar ƙanin mahaifina babanta ya rasu Shine nazo da ita koda aiki a wajanki a bata"

Farha sakin baki tai tana kallon Musa cikin mamaki.

Ammi tai Jimm.

"Ni ina da masu aiki, Amman Naji Aliyu yana cewa Mai girkin part Ɗinsu tayi tafiya jiya, To zata zauna a ɓangarena Ga ɗaki nan a falo ta saka kayanta zata dinga Min gyaran ɗakina dana su Sajeeda, Sannan ta dinga zuwa part Ɗin Aliyu tana musu girki ina fatan ta iya girkin, albashin ta zamiyi magana da ita anjima naji nawa za'a bata"

Musa ya hau godiya kamar zai ari baki.

Sannan ya tashi yayi musu sallama yabar parlon.

Ammi tace.

"Yaya sunan ki?"

Muryar ta tana rawa tace.

"Fatima"

Ammi tayi murmushin ƙasaita.

"To fati saka kayan ki a wancan ɗakin"

Daga haka ta miƙe ta koma in da ta fito.

Farha Kwantar da kanta tayi a saman kayanta tana sakin wani irin Kuka mai Ban tausayi..........

*LAST FREE PAGE*


*RABO YA RANTSE! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank, idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya ****


Wannan shine ƙarshen shafin kyauta base na zauna na rubuto Muku abin da zai faru ba kuma kun san akwai cakwakiya acikin wannan labari In sha Allah duk wanda ya saya zai alfahari da karantawa Nagode masoya sai najiku Allah ya baku ikon siya ya hore muku Amin.