ZULFAH

page 3

by @rabiattu0444

_*Typing🤳🏼*_





_*🍏....ZULFAH....🍏*_




     Na

_*®UMMU MAHER(MRS GREEN)*🍀_




  *_TEAM🔥GAWURTATTU 🤟🏻3_*



_*AREWABOOK🤳🏼*_

ZULFAH:: https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540




  _*Page∆3*_


_*Zulfah2 pov*_



    da mugun gudu na ƙarasa wajen mahaifiyata,na rirriƙeta ina kuka ina tambayarta waye wannan mutumin?sai kace me hankali nakewa tambayar?kamar yadda kuwa na tsammata shiru tayi min,idanuwanta duj awaje da alama abin ya taɓa zuciyarta nayi saurin rufe idanuwa na,na rufe mata jikinta yadda kai na ke sarawa yadda kasan an sanyashi atukubar tsire tsabar azabar da zuciyata ke yimin,sai naji dama ace mafarki nake bada gaske bane,yanzu mahaifiyata aka yiwa fyaɗe?waye wannan?wani daliline yasanya shi yiwa mahaukaciya fyaɗe?babu me bani waɗannan amsoshin nawa masu kama da kibiyar mashi,don har sunfi mashi tsini da gudu na tashi na arta ana kare tamkar mahaukaciya nayi waje ina kuka,inda bawan Allahn nan nayi da gudu amman babu kowa awajen sai shatin motarsu.

Duƙushewa nayi ƙasa na fara wani irin kuka me cin rai,tabbas rayuwa juyi juyi ce bantaɓa tsintar baƙin cikin daya kai min na yau ba,tabbas ƙaddarar yau ɗin ta dabanne sai na ƙara fashewa da kuka me mugun raɗaɗi da zafi,tabbas rashin gata da rashin galihu ya samu babban bigire aruwarmu,tabbas muna fuskantar rayuwa me tartsatsi tamkar garwashin wuta.




_*ZULFAH1 pov*_



   a hankali na tashi daga nannauyan barcin da ya ƙwasheni ba tare dana sani ba,ɓarin kaina sai ciwo yake na buɗe idona ahankali ina kallon ɗakin tunda dishi disho har na gama buɗe sa tsaf,a hankali naji wani baƙon yanayi na duba hannuna sai naga hannun mutum sarƙe da nawa,gabana yayi mugun faɗuwa a hankalo nakai dubana wajen dana ke tsammanin anan fuskar mamallakin wanda ya gaji wannan hannun.

Sanyayyiyar ajiyar zuciya nayi,ina kallon kyakkyawar fuskat mahaifina tarr akaina yana jeromin sannu,idanuwansa sun faɗa sosai daga gani ma kuka yayi,naji tausayinsa don nasha kamashi akaina yana kuka sosai.

Murmushin dana yi masa yasa ya mayarmin,yana goge hawayensa ya ce"sweet daughter kin tashi?ya jikin naki?babu inda ke miki ciwo?".

Duk alokaci ɗaya yayi min wannan tambayar?nama rasa wacce zan amsa masa sai na ce



 "Fine. . . ."


Tun daga nan ban ƙara koda uffan ba,daman yasan ba lallai ne in cigaba da cewa komai ba,don haka ya tashi ahankali yana kallona yana murmushi har ya fita.

Inason mahaifina sosai,zan iya rasa komai saboda shi duk abinda nakeso mahaifina shi yakeso,ko da kuwa wannan abin shi bai gamsar dashi ba amman ahakan yake haƙura yayi abinda nakeso,dama ni hakan nakeso don duk inda na shiga jin kaina nake tamkar wata giwa kuma nafison kowa na wajen ya bani girma ko da kuwa ya girme ni,ni dai abinda nakeso kowa ya zama ƙasane dani.

Tashi nayi ahankali ina ɗan gyara yalwataccen gashina zuwa dunƙulesa waje ɗaya.

wanka na faɗa,sai danayi kusan awa ɗaya ina wankan ruwan red rose ma nakai kusan minti talatin sannan na fito.

don ni mutum ce me mugun son ƙamshi da gwalli.

Ina fitowa na xauna bakin mirror ina goge lallausar fatata tamkar audiga yadda take wani glowing tamkar ta jariri,saboda tsabar hutu da cin me kyau da kuma shafa me kyau,iya manda nake shafawa a wannan tsadaddiyar fatar tawa sun tasamma guda goma,ko wani bigire na jikina da mansa haka kusurwar jikina ma,ƙamshi kuwa yadda kasan gidan turare aka buɗe don wasu ma namune na shuwa,don ina masifar son turarukanmu na shuwa arab duk wanda yasan shuwa yasansu da bala'in ƙamshi,fintinkau ne su awajen ƙamshi na jiki dana tufafi.


Yau ma kamar kullim t.shirt ce ajikina kalar maroon wacce aka manna hoton mage ajiki fara sol,sai wani wando ɗamamme kalar dark blue,wanda ya kamani sosai sai ɗaukar ido nake,na bazo da gashina ta baya na danna sweet abakina,na saka takalmina ƙirar prado me ɗan tudu sannan na fito ina taku ɗai ɗai,ba iyayi bane a'a haka tafiyata take cikin yauƙi da gwalli.

A falo na haɗu da ƴan dubiya,bance da kowa ƙala ba nayi hanyar fita har hjy Innah wacce keta zuba tamkar makaɗi.

Da sauri ta tashi jikinta na rawa ta nufoni,sai dai gabanta sai faɗuwa yake saboda bata manta azabar da ta sha jiya ba,ta idanuwanta na hango komai amman sai na maze na kalleta kawai.

"Haba haba fisabilillahi,ina zakije kuma baki gama samun lfy ba"?.

Kallon tsaf nayi mata,shima ba kallon rainin hankali bane hakan kallona yake na juya eyes ɗina,masu matuƙar tafiya da ma'abocin kallona sannan na ce"kina da matsalane dani"?.

ina kallon yadda ta tsorata da magana ta,amman da yake Innah tasha miya aduniya sai ta haɗiye tsoronta ta ce"haba masoyiya ta kada ki fita baki gama samun sauƙi ba,kuma kinga fitarki sakaka aƙwai matsala,tunda aƙwai masu harar rayuwarki".

Tunda ta fara magana nake kallonta sannan na ce"to naji matsa zan wuce".

Da mamaki ta matsa amman mamakine fal azuciyarta,don gani take wannan ciwon da nayi jiya da yau sai taga tamkar an ƙara canjani.

Naga hakan ne a idonta lokacin da nake wucewa,sam arayuwata bana son takura ko kaɗan shiyasa sam banso dawowata daga ƙasar Oman ba,kowa rayuwarsa yake babu ruwan kowa da kowa.

Ina fitowa dakaruna suka biyoni a baya,afusace na juyo ina musu wani kallon banza,babu wanda ya kalleni acikinsu saboda yadda suke ƙoƙari wajen yin duk abinda na umarcesu gudun kada su rasa aikinsu.

ni kaɗai na shiga haɗaɗɗiyar motata,wacce faɗin tsaruwarta ma ɓata bakine,tafiya nayi me nisa sannan na gangara ƙasan titi,ahankali na fito da wani hoto aƙasan motar,kallon matar nake sosai don babu abinda ya banbatani da ita,ina da taurin zuciyar daba komai ne yake sanyani kuka ba,zuciyata irinta maza ce mazan ma ba mazare ba,amman ayau kukan na fashe dashi ina rungumar hoton dake saman ƙirjina,kuka nake sosai ina magana da ihu ni kaɗai acikin motar.


 "Why momi me yasa kika mutu kika barni?na saba dake na saba da zama ajikinki,bansan yadda zanyi da rayuwata ba,idan akace haka zan cigaba da rayuwata babu ke adoron ƙasa,ina kewarki Momi!Momiiiiiiiii".!!




*HAJIYA RAIHANA*



    "Momi yanzu kina ganin abinda ke wanzuwa acikin gidan nan?ƙwanan nan nace wa Dady ya canjamin mota,amman cemin yayi sai ƙarshen shekara zai siyomin,amman wannan yarinyar daga dawowarta har an siyo mata fitinanniyar mota,ni ce baragurbi kenan daba za'a canjamin ba?to wallahi abi ahankali dani kafin in fara ɗaukar mummunar fansa akan wannan yarinyar."

 Tana huci ta gama maganarta,tana kallon mahaifiyarta da wani irin duba na ɗaukar fansa ta kowacce hanya.

Hajiya Raihana ta kalli ƴarta Hibba tana jinjina yadda Allah ke ikonsa,tsaf halinta Hibba ta ɗakko babu abinda tabari na halinta yadda kasan kofi ɗinta ce.

Hajiya Raihana ta fara magans fuskarta fayau tamkar babu wani abinda ya faru.

Tsabar sanin takan makirci kenan ta ce"ke Hibba ki dinga iya takunki asannu,ahaka na gama da uwarta cikin ruwan sanyi,don haka ki dinga ɓoye fushinki akanta idan ba haka ba ƙwaɓarki zatayi ruwa,don haka ki ƙwantar da hankalinki,yadda na gama da mahaifiyarta kema itama haka zan gama da ita ta shuɗe baki ɗaya,sai dai labarinta gwara ma uwarta ita ta haifa ana tuno da ita,to ita bazan taɓa bari ta tayi aure bama ballantana har ta haifi ƴaƴan,don haka inason daga yau kibi ahankali mubi komai asannu,indai motace ni zan siya miki tunda nima kaina me arziƙi,masu iya magana sunce kafin ai ɗaran akan ƙwanɗi."

Duk da abin ya yiwa Hibba daɗi amman sai ta tsuke fuska ta haɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya,tana ji azuciyarta dama ta kashe Zulfah ta huta da jaraba.

Wayar Hajiya Raihana aka bugo,ta ɗaga tana ce wa"ok!to ku bita yanzu yanzu kada ku sake ta ƙara tserewa awannan karon don yadda na gama da uwarta itama dole ne tabi sahu."

tana gama wayar ta kalli Hibba,wacce itama kallonta kawai take da mamaki,tana jiran amsar tambayarta sai kuwa Hjy Raihana ta ce"nasan kina da tambayoyi da yawa,amman kuma ayanxu ba zaki samu amsarki ba,har sai burina ya cika don wannan karon so nake ayita taƙare."


Sai danayi kuka na me isata sannan na kamo hanyar gida,ammanfa duk wanda ya ganni yasan tabbas ina cikin matsala,ni daman ba ƙiba ba sai na ƙara figewa tamkar wata figaggiyar kaza.

ahankali nake tafiya acikin motar,amman gabana sai faɗuwa yake ni narasa me yake damuna,amman dai nasan hakan bazai rasa nasaba da kukan dana sha yanzu ba,don rashin uwa babbar ƙaddara ce arayuwa,ni dai yanzu bani da me bani shawara sai benezar,tare mukayi makaranta tun daga matakin farko amman daga baya kowa ya cigaba da karatunsa aƙasar da yake so,don anan burikanmu sun banbanta,ita ƙasar Australia ni kuma Oman don haka kowa ya kama gabansa ammanfa kullum muna manne a waya chart,vedio call da sauransu.

Ahankali na fara fuskantar wata mota na bina abaya,amman ban tsaya ba nayi dauriyar cigaba da tuƙina gabana yana cigaba da faɗuwa.

Tun suna bina ahankali har suka fara yi da ƙarfi,duk yadda nakai da gudu da motata kasawa nayi sai da suka kusa cimmini,Allah ya taimakeni na shige cikin go soluw,abinda na tsana kenan amman awannan karon sai gashi go slow ɗin yayi min amfani awannan lokacin,sai da muka daɗe sannan masu bada hannu suka sallamemu,amman sai na rasa wacce hanya ma zanbi?gashi kuma na rasa yadda zanyi in ɗaga waya in kira dady na.

Wata hanya nabi,ammanfa sai dana bi nake nadamar bin hanyar saboda babu kowa tsit sai ƴan motoci jefi jefi,ai kuwa sai ga motar nan da take bina ta ƙara biyoni,tsoro ya bayyana aruhina da kuma gangar jikina,nayi saurin ɗaukar wayata don kira Dady na,bugu ɗaya ya ɗaga ban bari ya fara magana ba na ce"Dady wasu ne suke bina,don Allah Dady ina kan titin bayan banki wanda kake da hannun jarin nan?"tsit na kashe wayar.

A haukace Malik ya ajje glas cup ɗin da hjy Raihana ta zubo masa sanyayyan zuɓo wanda yasha kayan haɗe haɗe,halastacce da baragurbi don daman ta saba bin bokaye da malamanta.

Tana gani ya tashi afirgice kuma baice mata komai ba yasa tasha gabansa ta magantu.

"haba Dadyn yara ina kuma zaka daga dawowarka?."

fuzgar da wata muguwar iska yayi amman baice mata ƙala ba,ya fice da mugun sauri har yana haɗawa da gudu,saboda ya samu ya buga waya don akaiwa ƴarsa gudum mawar gaggawa saboda ba ƙaramin son ƴar tashi yake ba.

hjy Raihana ta bishi da sauri amman bata cimmasa ba,,ta ɗanyi dariyar yaudara don tasan yau ta ƴar gwal ɗin tasa ta ƙare,sai dai wata Zulfan amman ba wannan ba,yadda ta tsani ahalin Jiddah abin har ya ɓaci,saboda haka ma su kansu iyayan Jidda da ƴan uwanta,sai da tasa aka cire musu tunanin Zulfah baki ɗaya suji su manta da itama adoron ƙasa,saboda haka basu neman Zulfan itama bata nemansu.



Hankalinsa ya tashi sosai,ya shiga goge Zufa yana gani duhu duhu alokacin da komai ya faru,don suna bin bayan waɗannan mutanen kuma gashi da alamar sun kusa cimmata,harbin motarsu akeyi amman tsaf sunƙi tsayawa sai faman harbin iska suke,ita kuwa Zulfah duk iya tserenta yau kasawa tayi,musamman da take tauraruwar ƴar sukuwar doki,amman kuma yau kasawa tayi saboda yau cikr take da nauyin zuciya dana jiki dana ruhi.

Karon farko kenan daya kasa taimakawa ƴarsa,bata neman wani awajensa ta rasa ba musamman asanda ta rasa mahaifiyarta,sai gashi yau yana ganin ƴarsa cikin halaka amman kuma ya kasa taimaka mata ɗin,don duk harbinsu da akeyi baisa sun tsaya ba,sai ƙarawa motocinsu iska da sukeyi su dole sai sun cika burinsu na kashe Zulfah.

Da mugun gudunsu suka kamota,harbin motarta kawai sukeyi sun harbi sama da rabin glashin murfin motar,dauriyarta da jarumtarta duk suka ƙare kawai daga ƙarshe ta gangara cikin rami ne mugun zurfi da kuma duhu,wanda yake nan agefen titi ganin ta faɗa rami yasa sukayi wata muguwar dariya suka wuce da mugun gudu.

Mutuwar zaune Malikh yayi,ya kasa koda motsa ɗan yatsansa don ganin abinda ya faru,kuka da hawaye suka kasa fitowa daga ƙwarmin idanuwansa,ya samu shuɗewa ta wasu awanni ji yake tamkar mafarki yake yi wanda yake shirin farkawa amman ya kasa farkawar saboda tsoron mafarkin.

Ƴan sandan sunyi yunƙurin bin waɗannan mutane amman ganin halinda Alhaji Malikh ya shiga yasa suka kasa aiwatar da komai,don kiran ambaton Allah yake yi jikinsa sai wani irin kyarma yake yi da tsuma,idanuwansa kuwa sunyi wani irin mugun yi ja tamkar idon jini.

Sosai abin ya basu tsoro,da sauri suka tsaya da motarsu dai dai inda abin ya faru.

Amman babbansu ya bada doka akan atsare wannan titin da waɗannan baragurbin suke,don atantance su waye sukayi wannan aika aikar,sannan ya tura musu da nombar motar.

Kasa fitowa yayi daga cikin motar,sai wani irin haki yake yana danne saitin zuciyarsa,sosai ƴan sandan suka tausaya masa suka kasa bashi baki akan wannan babban lamarin,don duk wanda ya ƙwana ya tashi agarin yasan irin bala'in son da Malikh ke yiwa ƴarsa.

Ɗan sanda ɗaya ne yayi ta maza ya matso kusa dashi,ya dafa kafaɗarsa cikin faɗuwar gaba ya ce"mu musulmi ne Alhaji,kuma baza muyi biris da ƙaddararmu ba,kuma daman asali yana can a lauhul mahfuz ka nuna juriya da jarumta azuciyarka,kayi ra kiran sunan buwayi gagara misali,shine ke taimakon mara ƙarfi da kuma mara jarumta,inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,shine abinda ya kamata ka dinga ambato ba riƙe zuciyar da ba tada ƙashi ba,don komai zai iya faruwa da ita daga nan ka mutu ka cewa Allah saboda ƙaddarar daya yi maka ka kashe kanka da ciwon zuciya?,kaga ka zama me butulcewa Allah tunda babu abinda Allah bai yi maka ba,ka taso acikin ahalinka wani kuwa yana can bulayi duniya akufai,baisan iyayensa ba?bai san ƴan uwansa ba?wani kuma babu abinda Allah bai bashi ba,amman a ƙaddararsa sai ya hanashi haihuwa,kuma yana so amman haka yake haƙura,to kai me zai sa baza ka yi wannan haƙurin ba"?.


Sosai Alhaji ya dawo da kafatanin linzamin ganinsa zuwa ga wannan ɗan sandan,sai yaji ya samu wani kyakkyawan hope saboda haka sai ya fara kiran sunan Allah,kawai sai yaji ya samu ƙwarin gwiwar fitowa ahankali,ya fata takawa sannu sannu duk da juriya da dauriyar da yake son arowa amman kana ganinsa zaka gane,maraunaci ne akan abinda yake so ba shida jarumta ko ɗaya ta wannan sashen.

Da sauri ya yi baya ganin har an fara fito da motar Zulfah daga cikin wannan ramin,baki ɗaya motar tayi wani ƙwasa ƙwasa,alamu sun nuna wanda yale cikin motar babu makawa bazai fito da ransa ba,mota ma tayi haka ballan tana mutum?.

Bai san sanda wani mugun jiri ya rinjaye sa ya faɗi awajen ya fad'i tamkar matacce.....✍


MRS GREEN CE.

domin chart dani kai tsaye ***


*_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 SEPTRMBER._*




_1-ƘWAI A BAKA...!!!🥚_

👇🏽

*(Ummu Affan)*



_2-NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA...!!!🫗_

👇🏽

*Badi'at Mrs bukhari*



    _ZULFAH_🍏

👇🏽

*Ummu maher(mrs green)*



_Littafi ɗaya;400_

_Littafi biyu;800_

_Littafi uku;1000_


Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


0037219728

Fatima Rabiu Sunusi

StanbicIBTC Bank


Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽


***


Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽



***


Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number.


***


*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa*

10K ne kacal.

Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽


***

***

***


Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽


2K

sati biyu

3k


idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama

10k kacal.




Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼