page 4
_*Typing🤳🏼*_
_*🍏....ZULFAH....🍏*_
Na
_*®UMMU MAHER(MRS GREEN)*🍀_
*TEAM🔥GAWURTATTU 🤟🏻3*
_*AREWABOOK🤳🏼*_
ZULFAH::https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540
_*Page∆4*_
........Wani irin kuka mahaifin Zulfah ya fara,dukkanin ƴan sandan jikinsu ya yi sanyi sosai acikinsu ma sai da wasunsu sukayi kuka,saboda sunfi kowa sanin yadda ya ke matuƙar son ƴarsa wato Zulfah,zai iya sadaukar da komai nasa saboda ƴarsa wacce matarsa mafi soyuwa aransa,baya ɓoye son da ya kewa Zulfah agaban kowa shiyasa da damar mutane idan suna neman wani abu agunsa suke haɗawa da yi masa kirari,Baban Zulfah kuma uba nagari zaki majinginar Zulfah.
ko da a tv ne kuwa wannan kirarin ake yawan yi masa kuma duk yawancin kamfaninsa da sunan Zulfah ya ke buɗewa,ko gajiya da sanya sunan bayayi saboda son ƴarsa da ya keyi,sai gashi rana ɗaya Allah ya aiko musu da wata mummunar ƙaddara,wacce take baraza da rayuwarsa don mutuwar Zulfah tamkar mutuwarsa ce.
¢¢¢¢¢¢¢¢¢¢
a hankali Zulfah ta buɗe idonta wanda ya yi mata wani irin mugun nauyi,babu ciwo ko ƙwarzane ajikinta saboda alokacin da hatsari ya same ta har ta faɗa cikin wannan babban ramin mai mugun hatsari,yadda kasan an cillo ta daga cikin wannan ramin ta riƙe wani ƙarfe ta dinga sauka a hankali har ta koma cikin wani ɗan ƙaramin lungu,tana murnar tsiran da ta samu sai me kuma???wani ƙaton kumurcin miciji ta gani acikin wannan ramin ta kurma wani uban ihu wanda yasa hankalin kowa ya dawo wannan ramin,nan da nan Abee mahaifin Zulfah ya taso tamkar mahaukaci ƴan sandan nan suka riƙe sa,aka kirawo masu agajin gaggawa suka fito da ita a sume tamkar matacciya,amman abinda ya bawa kowa mamaki bai wuce yadda suka ga Zulfan ba,saboda babu ko ƙwarzane ajikinta alamu dai sun nuna ce wa wani abin ta gani ta tsorata.
Abeey da hjy Innah dasu ta fara cin karo,sun rafka uban tagumi suna kallonta dukkanin nutsuwarsu da komai na su yana ga Zulfah,idanun hjy Innah sunyi jajir alamar tasha kuka har ta gaji,ta juya da kallonta kan mahaifinta shima dai kusan halinda Innar ke ciki shima haka ya samu kansa,ammanfa nashi ma har yafi na Innar don shi jijiyoyin kansa sun tashi sunyi raɗa raɗa dasu.
tausayinsu taji ya ɗarsu a zuciyarta,waɗannan mutanen biyu wato Innah da Abinta sune mafi soyuwa arayuwarta,dasu ta tashi ta buɗe ido sune kominta arayuwa sai kuwa Murash-sha ƴar uwarta kuma aminiyarta,ayanzu ma tayi mamakin rashin ganinta amman tasan hakan bazai wuce rashin amincewar mahaifiyarta ba,don sam momin murash-sha ta tsaneta sosai ko gaisuwa bata haɗasu,daman ita Zulfan ba ma'abociyar gaisuwa bace,dona girman kanta sai dai kai babba ka zubar da girmanka ka durƙusa har ƙasa ka gaisheta amman ita tafi ƙarfin gaisuwa.
ahankali na buɗe bakina wanda ya yi min nauyi na ce"Abeey na".da sauri ya juyo yana kallona,ya ƙaraso inda na ke har yana haɗawa da tuntuɓe. ya shafa gashin kaina yana kuka ya ce"Zulfah kin tashi?me yake yi miki ciwo?me kike so"?.duk alokaci ɗaya ya yimin wannan tambayoyin?ita kuwa Hjy Innah ce wa tayi"ƴar nema duk kin sanyamu acikin tunani da zullumi".sai ta fashe da kuka sosai har da majina don tana masifar sona ni da kaina na tabbatar da hakan.
ana ta zuwa dubani duk da babu abinda ya ke damuna yanzu,don na warke baki ɗaya amman sarai Abeey na ya hanani sakat don ko tafiya zanyi sai yace min wai inyi a hankali.har ranar da za'a sallameni Hjy Raihana bata zo ba,rannan muna zaune ni da Murash-sha Hjy Innah kuma tana sallah ta idar tana jan cazbaharta wato carbi,sai mukaji sallamarta kamar daga sama ita da ƴarta Munirat.
tasha wata uwar ƙwalliya tamkar za tazo gidan biki,wani leshi ne ajikinta ɗan ubansu don faɗar kuɗinsa ma ɓata bakine saboda yadda ya tsaru,ya fitar da kyaunsa na asali da zallar zunzurutun kuɗinsa,tayi ɗaurin ture kaga tsiya daman kuma ita wannan ɗaurin shine ainihin ɗaurinta indai ba abaya ta sanya ba.
Munirat ma tayi kyaunta sosai,tana sanye da wasu ƙananun kaya masu shegen kyau wando jeans me ruwan zaiba,da kuma farar tishet wacce tayi bala'in kamata,ga uban atachment da ta sanya akanta wato gashin doki,don su daman gashin uwarsu sukayo.
Kallo ɗayan danayi musu na kauda kaina ina yi wa Murash-sha magana don ta haɗamin ruwan tea babu madara.ina jinsu suna yimin sannu a wata murya a dausashe,tamkar waɗanda aka yi wa dole Hjy Innah tayi musu kunnen uwar shegu,don sam taƙi jini hjy Raihana saboda yadda take son taga bayanta,don ta rabata da ɗanta daman bata gaida Hjy Innah ba saboda haka nima ban amsa sannunta ba,don gani nake duk wanda zai muzantawa Innah sai inda ƙarfina ya ƙare,don haka da suka gaji da zamansu suka nemi hanyar tafiya.
Inajin Hjy Innah tana ce wa"Innah ta gaida ash-sha dama babu wanda ya gayyaci kaza zuwa hanyar rafi,shisshigi da ƙwala kai afaranti kina tafe kamar wata uwar mata sai munafunci fal ciki".
tas taji abinda surukar ta tafaɗa mata amman ta danne,sai dai Munirat taso ta dawo ta zubawa kakarta rashin mutunci,don ita duk wanda zai taɓa mata uwarta sai ta yayyagashi ko wanene kuwa,saboda haka da sauri Raihana ta riƙeta tana ce wa"kul ɗinki Munirat!saboda kinsan halin munafuncinra,sai ubanki ya dawo ta haɗamai munafunci ƙarya da gaskiya ta faɗa masa,shi kuma ya hau kai har ya nemi yin hukunci akan hakan,banda ma yanzu na sanya mlm na zaune ya rufe masa baki da abinda zai faru da yanzu ba'ayi hirar ba,saboda haka barni dasu dukkansu nasan matakin da zan ɗauka akansu,don wannan son da ubanta yake mata take wani kallon mutane ɗai ɗai ba?to ki rubuta ki ajje sai na mayar dashi mummunar ƙiyayyar da zata sanya ma ya cire ta acikin ƴaƴansa baki ɗaya.
dariya suka sanya ita da mahaifiyarta sannan suka wuce.
¢¢¢¢¢¢¢¢¢
*ALIYU*
da ƙer aka samu aka fito da mahaifinsa,saboda sai da ita da kanta ita Zulfan taga dama sannan ta rattaba hannu aka sallami mahaifinsa,abin ya ƙona masa rai ranar yayi kuka sosai har ya gaji ya share hawayensa,ranar yayi kukan rashin babu yanzu saboda talauci aka yi musu haka?gashi abinda ma yafi ƙona masa rai shine.
da ƙer ya samu ɗan sandan daya shige masa gaba sukaje har gidansu Zulfah,sai da suka ɓata wajen awa uku suna zaman jiran zuwan Zulfah sai da akayi musu manya manyan screening sannan suka ga Xulfah yadda kasan zasu ga wani sarki ko shugaban ƙasa,amman don ganin mutum ɗaya akayi musu wannan cin mutuncin,donshi aganinsa babban wulaƙanci ne saboda sam baiga amfanin yin hakan ba?don zasu ga wannan ƴar tayin ƙwailar yarinyar dako hannunsa zai kai faɗin ƙugunta,amman akanta suka fuakanci tozarci me girma wanda ba'a taɓa yi masa ba.
a hankali ta fara takowa har tazo inda suke,ta zauna awata rantstsiyar kujera tana yi musu wani irin banzan kallo wanda ko kashi tagani sai haka.
jin munyi shiru mu dukanmu babu magana,kuma da alamu ba zata tanka mana ba yasa ɗan sandan nan ya ce"ranki ya daɗe dama wannan saurayin na rako wajenki,don ya nemi alfarma kuma ya baki haƙuri akan abinda ya faru da laifin da mahaifinsa yayi miki".
Ƙala bata ce ba,ta cigaba da danna wayarta ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ɗan sandan ya ɗan taɓani ya ce"Aliyu kayi magana mana"?.
da baiyi magana ba da ko zamu ƙwana awajen bai isa na kallesa bama ballantana ma har inyi wata magana,don ɗaura aniya azuciyata akan cewa indai har bata yi magana ba to nima bazance ƙala ba.
da ƙer na fara magana kamar me ciwon baki na ce"kiyi mana alfarma a sake shi".
Da sauri naga ta ɗago don bata zata zan faɗi ƴar gajeriyar magana haka ba,tayi zaton zan tsugunna ina yi mata fadanci tamkar dai yadda sauran mutane suke mata don ƙwaɗayin abin hannunta,ni kuwa ko xata bani dala da gauron dutse bata isa inyi mata hakan ba,don bana neman komai awajenta face wajen Allah sarki gagara misali.
abinda ta faɗa ne yasa nayi saurin kallonta da wani irin mugun kallon da bansan ya fito ba,ta ƙara zaro idonta masu mugun ƙyau da haske ta ce"are u ready or not"?...............✍🏻
MRS GREEN CE.
domin yin chart danj kai tsaye ***
*_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 SEPTRMBER_*
_1-ƘWAI A BAKA...!!!🥚_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA...!!!🫗_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
_ZULFAH_🍏
👇🏽
*Ummu maher(mrs green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
***
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
***
Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number.
***
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa*
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
***
***
***
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼