SHU'UMAR MASARAUTA 1

Page 7

by @ameeraadam60

*SHU'UMAR MASARAUTA*



    ©AMEERA ADAM


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*


Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.



 SHAFI NA BAKWAI



   Koren macijin da Umaru ya kashe tun kafin haihuwar matar nan suka hango ya sulalo ya kafe su da ido yana kallo tamkar zai far musu da sara, suna nan cikin tsinkewar zuciya suka ga ya ƙarasa wurin jaririyar ya kanannaɗe ta, suna daga wurin da suke a gefen Umaru ya ce. "Mai gado an ya yau mun shigo dawa a sa'a kuwa?" Da sauri ta girgiza masa kai. "Tun wuri mu kama hanyar gida." Cikin sanɗa suka miƙe da niyyar tafiya sai dai bisa ga mamakinsu babu macijin babu alamarsa, don haka suka nufi hanya da niyyar tafiya. 


 Cak Mai gado ta tsaya tana waige. "Tsayawar me kika yi Mai gado?" 


"Mai gida zuciyata ta karaya, ba zan iya tafiya na bar yarinyar can ba. Ka dubi yadda mahaifiyarta ta aminta har ta damƙa mana amanarta. Ba mu sani ba wataƙila samunta babbar rahama ne a tattare da mu, ta wani fannin ma gani nake Allah ne ya azurta mu da samunta ka duba ka gani haihuwata huɗu duk yanzu babu rayayye, idan muka bar ta a wannan ƙungurmin dajin ba mu san wacce irin rayuwa za ta gudanar ba." Jikin Umaru ya yi sanyi ya waiga yana hango jaririyar da ke tsala matsanancin kuka. "Mu je na ɗauko ta In Shaa Allah, Allah zai kare mu tun da ya ga kyakkyawar niyyarmu." Da haka suka rankaya suka wuce har gaban jaririyar suka ɗaukota, Mai gado ta kunto ɗankwalinta ta nannaɗe ta a ciki sannan suka nufi hanyar da za ta sada su da gida. Sai da fargabar da Umaru yake ciki ba wuce irin tarbar da mutanen ƙauyensu za su yi musu ba, musamman idan aka samu akasi wani al'amarin almara ya faru kamar yadda suka gani daga wurin mahaifiyarta. Sai dai sun ɗaukar wa kansu alƙwari babu wanda za su furtawa silar samuwar yarinyar don kada ta taso cikin tsangwama da ƙyara.


Masarautar Huddam


  Ɗan matashin ne mai kimanin shekara goma zaune a cikin fadar Sarki Abdul'aziz a kan shimfiɗaɗɗiyar shimfiɗar alfarma yana sanye da rantsattsiyar alkyabba. Kallon mutane yake yi ɗaiɗai fuska a murtuke babu walwala, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da mulkin gadarsa ya yi ba taka-haye ba. Gajiyar da ya yi da zaman cikin fadar ya sa ya miƙe cike da izza yana taku kamar ba zai taka ƙasar ba.


 "Takawarka lafiya Yariman masarauta, a huta lafiya sarkin gobe da yardar Allah."


 Fadawa suka ɗauka a lokacin da suka lura Muhsin ya miƙe da niyyar fita daga fadar, wasu daga ciki suka ƙarasa suna take masa ba. Hannu ya ɗaga haɗe da tsayawa wuri ɗaya cak, ya kusa minti ɗaya a haka sannan ya furta. "Ba na buƙatar rakiya." Lokaci ɗaya suka ja da baya sannan ya ci gaba da taku, duk hanyar da ya bi haka bayi da fadawa suke zubewa suna kwasar gaisuwa amma ko kallansu ba ya yi ballanta su saka ran zai tanka musu. Yana gab da shiga sashen mahaifiyarsa bisa tsautsayi wata baiwa ta fito da sauri don isar da saƙon Fulani Umaima, a rashin sani ta bangaje shi har sandar hannunsa ta faɗi ƙasa. Jiki na karkarwa ta zube ƙasa.


 "Tuba nake shugabana, a gafarce ni uban gidana ni mai laifi ce ba tare da..." Marin da ya ɗauke kuncinta da shi ya sa haƙoranta suka datse harshenta har sai da bakinta ya fashe, idanunta suka fara zubar da ƙwalla ta sake zube wa a ƙasa tana faɗin. "Godiya nake Sarkin gobe." Ɗaga kansa ya yi ya hango wani Bafade hannunsa ɗauke da murtukekiyar bulala ya furta, "A hora ta na tsawon wuni guda da alama ba ta gama sanin a gidan masarauta take rayuwa ba tun da ba ta san aikinta ba." Yana gama maganar ya wuce ba tare da ya jira cewarsu ba. 


A kishingiɗe ya tarar da mahaifiyarsa tana huatawa, wasu 'yan matan Bayi na tsugunne wurin ƙafarta suna yi mata tausa. Ganin yanayinsa ya sa ta tashi zaune haɗe da sallamarsu.


 "Wa ya ɓata ranka Muhsin?" Fulani Umaima ta tambaye shi. 


Bai tanka mata ba sai da ya zauna. "Wata baiwarki ce ta ɓata mini rai amma komai ya wuce." 


"Wace ce ita na sa a hukuntata?" Muhsin ya fara rage kayan jikinsa. "Na sa a hukuntata, ina Ruƙayya ban ganta ba?" Fulani Umaima ta yamutsa fuska, "Za ta wuce sashen Fulani babba ne, yarinya sai baƙin nacin tsiya kamar tsohuwar mayya." Take idanunsa suka yi jawur rai a matuƙar ɓace ya saki guntun tsaki, ba tare da furta komai ba.


  Ihun da Ruƙayya ke ƙwallawa ne ya ja hankalin Fulani babba da sauran bayin da ke harabar gidan, turus bayin suka yi suna kallon juna duk da ba yau ce rana ta farko da suka ga Abubakar na kama gashin duk wani mutum da ya kusance shi ba ciki kuwa har da mahaifiyarsa. Ruƙayya ƙanwar Muhsin ce ita take binsa shekararta bakwai a duniya, Allah ya haɗa jininta da Abubakar ba ta iya wuni guda cir ba tare da je sashen Fulani babba ta shiga ɗakin Abubakar ta tsaya yana yi mata gwaranci tana mayar masa ba. Babbar matsalar da ke damun Fulani Babba bai wuce yadda Abubakar yake cizgar gashin kansa yana ci ba, idan na kansa ya ƙare kuma duk wanda yake da tsautsayi idan ya damƙe ka haka zai dinga cizga har sai an kwace ka. Abubakar ya shiga shekara ta goma sha ɗaya, sai dai har lokacin a zaune yake ko motsi ba ya iya yi komai sai an yi masa. Fari ne sol kamar mahafiyarsa sai dai kammaninsa sak da Sarki Abdul'aziz, tun da ya taso ba ya iya magana sai dai gwaranci kuma har kawo lokacin yawu na dalala daga bakinsa. Idanunwansa duka biyun a juye suke, hannuwa da ƙafafuwansa suma a shanye suke babu abin da yake iya aikatawa hatta wanka da tsarki yi masa ake yi. 


 Fulani Babba da sauri ta ƙarasa gaban Abubakar ta sa hannu cike da ƙunan rai ta ɗauke fuskarsa da mari, wannan ne karo na farko da ta taɓa sanya hannu a jikinsa da sunan duka. Zafin marin ya ratsa shi hakan ya sa ya ƙarasa cizge kitson kan Ruƙayya da ke bakinsa, sai kuma ya fashe da kuka yana gwara kansa da ƙasa. Cikin azaba ta sake ƙwalla ƙara take numfashinta ya ɗauke ta sume a wurin. Tamkar mayuwancin zakin da ya samu nama haka Abubakar ya tura sillin jelar kitson kan Ruƙayya da ya cizge cikin bakinsa ya fara tauna kafin wani lokaci ya haɗiye shi gabaɗaya. A firgice Fulani Babba ta shiga yayyafa wa Ruƙayya ruwa ta jima a kanta sannan ta sauke ajiyar zuciya a galabaice, ganin ta buɗe ido ya sa Fulani Babba ta ji farinciki har cikin ranta sai dai kuma wurin da ya ɗaye mata kitson tuni gefen kan ya kumbura suntum. Wani irin sara ta ji kan yana yi mata a daddafe ta iya miƙewa ganin haka ya sa Fulani ta ba wa Bayin da ke gefe umarnin su ɗauke ta zuwa cikin turakarta. Duk dauriya irin ta Ruƙayya sai da ta dinga zubda ƙwalla sakamakon yadda take jin kanta na sara mata kamar zai tsage gida biyu. Duk yadda Fulani babba ta so zaman Ruƙayya a ɗakin zuwa lokacin da zugin zai sarara mata fir ta ƙi yarda, don haka ta sake saka Bayi suka ɗauke ta tana gaba suna biye da ita a baya har cikin sashen Fulani Umaima. 


Ganin a halin da aka shiga da Ruƙayya ya sa Fulani Umaima miƙewa zumbur! Bakinta har rawa yake ta furta. "Me ya faru da ita?" 


"Laifi ne yayanta Sadik ya yi mata, wallahi tsatsayi ne Fulani don haka na zo da kaina ba saƙo ba..."


"Dakata Fulani! Hawainiyarki ta kiyayi ramata. Ba tun yau ba na lura da take-takenki dangane da kiranyen da kika yi wa Ruƙayya. Lokaci ɗaya kin sa an lashe kurwar yarinya ba ta ƙaunar zaman wurin mahaifiyarta, wannan fa ba shi ne karo na farko na ji labarin wancen shagirigirbau ɗin ya maƙure ta yana yi mata ƙamshin mutuwa ba. Amma an yi ta yanke ta gille, wannan shi ne karo na farko kuma na ƙarshe da zai sake taɓa kowanne bil'adama a sashenki." Fulani Umaima ta ƙarasa maganar tana kai kallonta wurin bayin da ke riƙe da Ruƙƙaya. "A samu Jakadiya ta gaggauta sanar da Mai martaba ina buƙatar ƙwararrun masu magani, don ban san dafin da haƙoransa suke ɗauke da shi ba." Da sauri suka shimfiɗar da ita suka fice, Fulani Babba ta ƙarasa gabanta ido cike da ƙwalla ta furta. "Wallahi ko a mafarki ban taɓa jin Ruƙayya ba 'yata ba ce, tamkar yadda na ɗauki su Khadija haka nake jin ta, ta ya ina sane zan bari Abubakar ya illatata." Sai da Fulani Umaima ta saki murmushin takaici ta furta, "Me ya sa bai kama Khadija ko Sakina ya illata ba, saboda kina baƙincikin kin haifi sauna, wawa, shashasha shi ne ni ma kike burin ƙarfi da yaji na rasa waɗannan biyun da Allah ya ba ni." Tsoron hukuncin da Fulani Umaima za ta yanke ya sake mamaye Fulani babba, ta tsugunna bisa gwiwoyinta don ta san kome Fulani ta gaya wa Takawa hawa yake ya zauna ɗaram. Ba tun yanzu ba ta jima da dawowa daga rakiyarta, don ta lura sai abin da Fulani Umaima take so Takawa yake zartarwa.


 "Tabbas Abubakar bai kyauta ba amma ki dubi girman Allah ki yi haƙuri..." 

"Idan ba ki yi gaggawar fita daga sashena ba wallahi sai na shayar da ke ruwan mamaki." Fulani Umaima na gama magana ta yi ciki cike da zafin rai. Fulani babba ta sunkuyar da kanta ƙasa tana zubar da ƙwalla, dama ya ya lafiyar kura ballantana ta yi zawo. Gari banza ma Takawa ba ƙaunar Abubakar yake ba ina ga an ce ya taɓa 'ya'yan gaban goshi. Cike da zullimi ta fara yunƙurin tashi, daga bayanta ta hangi Muhsin na zaune yana aika mata da saƙon harara cikin kallon tsana. A haka ta ƙarasa sashenta gwiwoyinta a sanyaye, ta windo ta leƙa Abubukar da ke zaune yawu na dalala. Sai a lokacin ta samu damar fashe wa da matsanancin kuka duk da tana da tabbacin bayin da ke zagaye da ita suna sauraronta.


 "Ya Allah ba don ba ka so ko ƙaunata ka jarabce ni da wannan bawa Naka ba, Ya Ubangiji ina godiya bisa baiwa da wannan ni'imar da ka yi mini domin dubbunaina na buƙatar ko da makamancinsa ne. Ya Allah idan rayuwar wannan bawa naka mai tsayi ce Ubangiji ka yalwace shi da lafiyar ya zama kamar kowa, saɓanin halin da yake ciki. Idan kuma mai gajeren kwana ne Ubangiji ka gaggauta ɗaukar kwanakinsa ko na samu salama a rayuwata..." Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya datse ragowar kalamanta.


"Allah ya sanyaya zuciyar uwar ɗakina Ubangiji ya ƙara wa Yarima lafiya." Baiwa Zainaba ta furta jiki a sanyaye kamar kazar da tono wuƙa.


 "Zainaba na ɗauka ko kowa zai furta son ransa ke mai faɗa mini gaskiyar abin da ke cikin zuciyarki ne? A haka kike kiran Abubakar da Yarima kina ga ko a mafarki za a damƙa wa Abubakar karagar mulki ne." Tabbas kalaman Fulani Babba a turba suke domin kowa ya san halin da Abubakar yake ciki kuma ko a garin gaɓa-gaɓa babu wanda zai damƙa masa kujerar sarauta, ina ya san kansa ma balle ya san matsalolin talakawa? Sai da ta ƙara rissinawa ta furta. "Tuba nake ranki shi daɗe, In shaa Allahu Allah zai ba shi lafiya." Fulani babba ta amsa mata sannan ta wuce cikin sashenta. 


 Ganin har zuwa dare babu wani saƙo ya sa Fulani babba ta ɗan fara sakin zuciyarta, har ta zauna su Khadija na soko mata hira wani ta amsa musu wani kuma ta yi musu shiru. Suna cikin wannan yanayin Jakadiya ta iso da kiran da Maimartaba yake yi mata. Take ƙirjinta ya buga dum! Zuciyarta kamar za ta yi tsalle ta fito daga ƙirjinta, da ƙyar ta tattaro jarumtar haɗa kalmomin da ta iya furta wa Jakadiya. A gurguje ta watsa ruwa ta ɗan gyara jikinta, don saboda yadda lalurar fitsarin da yi mata kamun kazar kuku har ji take haka kawai kamar zarni na tashi a jikinta. Da kwalliyarta fes ta ƙarasa turakar Mai martaba ƙamshi na tashi, haka kawai wani lokacin yake jin kamar yana tauye haƙƙinta ko yana yi mata ba daidai ba, musamman yadda ya ga ta fige ta lalace kamar ba ita ba.


 "Barka da hutawa Sarkina." Kalamanta ya ji na sauka a kunnuwansa, wani ɗaci ya ziyarci zuciyarsa kamar wanda ya haɗiyi maɗaci. "Barka!" Daga haka shiru ya biyo baya, ganin yanayin tarbar da Mai martaba ya yi mata ya sa jikinta ya yi sanyi. Cikin sanyin murya ta furta. "Allah ya taimake ka na ji saƙon kana son ganina."


"Wani hukunci muka yanke da muke ganin shi ne mafi alfanu babu cuta babu cutarwa." Mai martaba ya faɗa fuska a haɗe kamar dafaffan kwanannan kunun tsamiya. Ƙirjinta ya hau dakan lugude, gumi ya fara keto mata ta ko ina.


 "Don haka ba ma buƙatar jayayya. Abubakar Sadiq zai koma ɗaya daga cikin ɗakunan gidan ajiya da gyaran hali, na sa a ware masa ɗaki guda wanda zai zauna a ciki, idan ya so duk wani abu da yake buƙata a aiwatar masa a can. Mun yanke wannan hukuncin ne domin sama wa lafiyayyun gidan nan mafita, idan yau ya nemi nasaka wannan jibi wancan watarana ina tunanin kaina zai dawo." Kafin dirar kalaman Takawa tuni hawaye ya gama wanke fuskarta. Cikin kuka ta zube a ƙasa hannuwanta biyu a saman cinyarsa ta furta. "Don Allah kada ka yi mini haka ranka shi daɗe, Allah ya sani Abubakar ba shi kaɗai na haifa ba akwai yayyansa Khadija da Zainab amma wallahi babu wanda na ke jin ƙaunarsa har a cikin jinina kamarsa. Wannan ƙasƙanci ne a ce jininka zai ƙare rayuwa a gidan ajiya da gyaran hali saboda ya kasance mai nakasa, in dai a kan Ruƙayya ne na yi maka alƙawari ko inuwarsa ba za ta ƙara gani ba ballanta shi. Don Allah ka..."


 Cikin tsawa ya katse ta. "Ba mu san lokacin da raini ya gifta a tsakaninmu ba Fulani, da har ake neman yin jayayya da mu. Mu ba ƙananan mutane ba ne sanin kanki ne ba tun yau ba; ba ma taɓa magana biyu. Tashi ki ba mu wuri, wannan hukuncin ba zai tɓa canzawa ba." Fulani babba duk yadda ta so dakatar da hawayenta abin ya gagara, don haka ta fice daga turakar zuciyarta na tuƙuƙin ɓacin rai. Tana shiga ɗaki ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ganin kukan na ta ba na ƙare ba ne ya sa su Khadija rungume ta suka fashe da matsanancin kuka! Yau ita ce rana ta farko da ta ji zama a cikin gidan ya gama fita daga ranta, ta kuma ji wani abu ya tokare mata maƙoshi game da Fulani Umaima sai dai kuma a ɓangare ɗaya shakka da tsoronta ya hana zuciyarta sanar da ita gaskiyar abin da ke ranta. Sun jima ita da yaran a haka sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Abubakar, ta same shi a kwance kamar yadda ta barci. Sai da ta share ƙwallah sannan fito daga ɗakin.


 Washegari tun safe Dogarawa suka cika umarnin Mai martaba, tun lokacin da aka fara jidar kayan Abubakar Fulani Babba take share hawaye don dai ba ta da yadda za ta yi.


"Idan kika matsa mana da magana wallahi ranki zai yi mummunan ɓacin da ba ki taɓa gani ba Fatima." A razane ta dubi Mai martaba, yanayinsa kaɗai ya tabbatar mata babu alamar wasa a tattare da shi. Dole ƙanwar na ƙi ta zubar da makamanta, ta rungumi ƙaddarar da ta afka musu babu sallama.


 Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta tuna yadda suka kwashe da Takawa, a daren ranar da ta sake zuwa sashensa tana yi masa magiya a kan ya bar Abubakar ya ci gaba da zama a sashenta. Hawaye ya gangaro mata sakamakon ganin wata irin birgima da Abubakar ya fara yi a cikin jar ƙasar da ke ɗakin saboda ɗakunan kowannensu babu daɓe a ciki. Wata ƙasar ya ci wata kuma ya burtune jikinsa da ita, tana ji tana gani bayan ta gama kallonsa ta fice daga ɗakin. Abin ka da gidan masarauta take labarin kai Abubakar gidan yari ya gama zagaye gidan kowa da abin da yake tofawa, sai dai mafi yawa daga cikin shakkun Fulani Umaima ya hana su faɗar gaskiyar abin da yake cikin zuciyoyinsu.


"Allah ya taimake ki ni fa don kada a ce na saki linzamin harshena amma Allah ya sani na fara ɗora zargi a kan Fulani Umaima. Lamarin zamantakewar da ke tsakaninki da Takawa akwai fa ayar tambaya." Jakadiya ta yi wa Fulani babba maganar tana yin ƙasa da murya. "Jakadiya tafi kanki tsaye ba mu fahimce ki ba." Jakadiya ta sake yin ƙasa da murya. 


"Bari na fito miki a mutum Fulani, an ya kuwa Fulani Umaima ba ta bi ta ƙarƙashin ƙasa a kan Takawa ba, duba da yadda take cin karen ta babu babbaka a gidan nan kamar wacce ta wanke masa hannu aka. Yanzu musakin yaron nan Bukari me ya yi da zai fuskanci zama a sashen gidan ajiya da gyaran hali." Jin haka ya sa hawaye ya zubo wa Fulani Babba. A fakaice Jakadiya ta saki murmushin cin nasara, don babban burinta ita ma bai wuce ta samu sanadin dandalar arziƙin da su Fulani suke ci ba a matsayinsu na matan Sarki. "Jakadiya al'amurana a yanzu haka na miƙa su a wurin Ubangiji, duk ma wanda ya nemi ya ƙuntata wa rayuwata Allah ba ya bacci yana sane da abin da yake faruwa." Jakadiya ta taɓe baki a fakaice.


"Amma ya kamata ke ma ki tashi tsaye domin kin san da sanyin safiya ake kama fara." Fulani babba ta ɗan sauya fuska don haka kawai ta ji ba ta aminta da waɗannan shawarwarin na Jakadiya ba.


"Ni fa hatta ciwon yaron nan wallahi na jima da ɗora zargina a kan Umaima, saboda Allah yaro shi ba aljanu ba amma an mayar da shi wani iri. Kwanaki fa har barbaɗe na ga tana yi a turakar Mai martaba wai don ya daina jin ɗanɗanonki." A ɗan razane Fulani babba ta dubi Jakadiya sai kuma ta haɗe fuska. "Jakadiya muna buƙatar hutawa a ba mu wuri." Ganin babu fuska ya sa Jakadiya ta fice tana wurgawa Fulani babba mugun kallo.


 "Sakarai da ba ta gaji arziƙi ba kya ƙare a wahale cikin warin jiki da fitsari." Jadiya ta faɗa cikin jin haushin rashin samun nasara a kan Fulani Babba bayan ta fita waje.




Wacce ta shirya biyan kuɗin karatun ci gaban littafin *SHU'UMAR MASARAUTA* Ƙofa buɗe take, za ta iya turowa ta wannan Acc ɗin da ke ƙasa domin free pages na gab da ƙarewa. Waɗanda suka fara biya su min afuwa zuwa lokacin da zan buɗe group bayan na kammala free pages.


*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar ***.*