FreeArewaPen original
SHU'UMAR MASARAUTA 1
- 1views
- 50chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Page 1
*SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba. SHAFI NA ƊAYAMasarautar Zazzau (1953) Wani irin zafi take ji yana ratsa ta tun daga tafin ƙafarta har zuwa tsakiyar kwanyarta, dalilin haka ya sabbaba mata karkarwar jiki tamkar wacce ta ji kiɗan gangi. Wanda hakan ne ya haifar mata gumin da ke tsatssafowa daga kowacce kafar da ke cikin ilahirin jikinta. Ba yau ne karo na farko da haka ya taɓa faruwa da ita ba, sai dai a wannan ranar ji take tamkar an saka ta a tukunya ana dafa naman jikinta da ruwan zafi. A hankali ta cije baki tana yarfe hannu haɗe da lumshe idanu. Baiwa Maimuna da ke bayanta tana mata fifita cikin ƙwarewa a makirci ta fakaice ta, ta yanki ƙasan jelar gashin kanta ɗan ƙanƙani ta yadda ba za ta fahimci ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.