SHU'UMAR MASARAUTA 1

Page 9

by @ameeraadam60

*SHU'UMAR MASARAUTA*



    ©AMEERA ADAM


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*


Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.


*Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400*


 SHAFI NA TARA


  Ayarin dakarun masarautar da ke tafe da su Baffajo tafe suke cikin gajiya sakamakon doguwar tafiyar da suka yi, a farfajiyar wata bishiya suka yada zango suna hutawa sai bayan sun huta sannan suka ci gaba da tafiya, cikin zuciyarsu kowa da abin da yake ayyanawa. Ganin magriba ta fara dosowa ya sa suka yanke shawarar kwana a cikin dajin washegari da asuba sai su ɗora daga inda suke tsaya.


Ƙauyen Gangare


 Ganin yanayin da Umaru ya koma gida da shi ya sa Mai gado shan jinin jikinta. 


"Mai gida ya kuka yi da Mai gari na ganka duk a sanyaye." Ƙasa ya yi da murya ya furta. "Ina yarinyar nan take? Zan kai ta gidan Mai gari" Kallon rashin yarda ta bi shi da shi ta sake gyara goyon Jawahir da ke bayanta. "Me za ta yi a gidan." 


Kamar zai yi kuka Umaru ya ce, "Malam Malmo Mai gado ban san ya za mu yi ba, sun buƙaci na mallaka wa Mai gari ita." Rass! Ta ji gabanta ya faɗi, sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi ƙasa da murya. "Ba zan iya rabuwa da Jawahir ba Mai gida, na san Malam Malmo sarai ba zai wuce tsubace-tsubbace zai yi da ita ba." Umaru ya waiga kamar wanda ake kallo duk a tsorace ya ce. "Ya zamu yi yanzu? Mene ne mafita?" 


Masarautar Huddam


  Wuni guda haka Fulani Umaima ta yi shi cikin rashin ƙwarin jiki, ba ta san dalili ba amma haka kawai za ta ji gabanta na faɗuwa. Har ta so dannewa ta ji zuciyarta na azalzala ba za ta iya jure rashin zuwa wurin Bamaguje ba.


  Tsufansa ya sake fitowa sosai don jiki da hannuwansa har karkarwa suke yi. 


"Ta zo duniya da ƙarfin iko, shi kuma yana gab da dawowa gidansu na gado."


 Bamaguje ya furta bayan ya gama sauraron ƙorafin Fulani Umaima. Ta ɗago a hargitse bakinta na rawa, ƙirjinta na dakan lugude. "Su waye? Kuma daga ina suke." 

 

"Garaje ga dami, daɗina da ke gaggawa Umaima. Na ɗauka za ki tambayi alaƙar shi da masarauta da ita kanta yarinyar." Ajiyar zuciya ta sauke. "Tamkar tagwaye haka suka kasance tsakaninta da Hidaya, sai dai waccan ruwan sanyi ce salam a kan wannan. Ban san a wanne muhalli zan tirke ta ba, abu ɗaya na sani ita ta kasance daga cikin wata irin zuri'a masu matuƙar hatsarin gaske. Na ga takobi a cikin jininta sannan wuta na gewaye sashenta, takaicina ɗaya Mahaifiyarta ta riga da ta binne duk wani al'amari da sirrin da ke ƙunshe a cikin rayuwarta. Daga ni har sauran matsafan duniya duk wani bincike da za mu yi ba za mu tantance takamaiman ainihin tushenta ba. Sai dai kuskure guda mahaifiyarta ta tafka wanda da shi kaɗai za mu iya cin galaba a kan wannan yarinyar."


 Cike da zumuɗi Fulani Umaima ta furta. "Mene ne shi? Duk wuya duk tsaninsa zan nemo shi..."


"Bincike ya bayyana mini tana da matuƙar tasiri a rayuwarsa. Ina nufin jaririn da kika sa Maimuna ta fitar da shi shekara goma sha ɗaya baya, shi yake gab da shigowa gidan sarautarku. Sai dai kuma ita da shi za su kasance tamkar wuta da ruwa a fannin gaba, kowannensu ba zai ƙaunaci ɗan'uwansa ba. Shigarsa tamkar dasa nakiyar da ke tashin zamani da alƙaryarki ne, ba tun yau ba; na gaya miki shi ba kamar ɗan uwansa ba ne. Ruhinsa ɗauke yake da zaratan dakarun da ke sarrafa zuciya da tunaninsa, tun ranar haihuwarsa na fahimci zanen ƙaddararsa ya wanzu dalilin da ya sa na baki shawarar matse kunamar nan a cikin bakinsa, ashe tagwaye ne halwar tsafina ya gagara nuna mini. Tun yana jariri ya sauka a fadar Sarkin fararen aljanun doron ƙasa, da ke tsakiyar dajin Wuruju a daidai wurin da Baiwa Maimuna ta dire shi. Sun naɗa masa kambun da babu mai iya sauke shi sai mutum ɗaya wato wannan yarinyar." Bamaguje ya ƙarasa maganar yana haska wa Fulani Umaima inuwar wata yarinyar. Ta tsinci muryarsa ya ci gaba da faɗin.


"Mu koma maganarmu ta baya na kuskuren da mahaifiyar Fargi ta tafka. Ta bar tauraron 'yarta a sake wanda duk wani matsafi kallo ɗaya ko bincike ɗaya idan ya yi a kanta zai fahimci muhimmancinta gare sa. Duk wanda ya mallaki ruhinta shi zai kasance mafi shahara a faɗin yankin nan a ɓangaren gawurtar tsafi da sihiri, runduna ce guda a tare da ita domin mahaifiyarta kafin ta mutu ta riga da ta juye mata nata jinin a jikinta."

 

"Mene ne mafita, don ta ni gabaɗaya a mutu har liman a rasa mai jan sallah." Cewar Fulani Umaima da zuciyarta ta gama ƙeƙashewa. 


"A baya na fid da rai da samun wannan ɗaukakar, amma idan kin yadda me zai hana mu jefi tsuntau biyu da dutse ɗaya?"


Mai Gado


"Guduwa ita ce mafita, sai dai mu bar garin nan amma ka san muddin muna cikin ƙauyen nan Malmo ba zai bar mu da sauran numfashi ba." Shiru ya yi yana tunanin shawarar da ta kawo, ganin ya tsaya yana nazari ya sa Mai gado ta faɗa ɗaki ta ɗaura kayansu a cikin ɗankwali ta fito.


 "Allah ya sani na ɗauki aniyar kula da yarinyar nan, Malmo azzalumin mutum ne, na san halinsa sarai tun da ya ƙallafa rai a kan yarinyar nan ko mun damƙa musu ita sai sun hallaka mu don gudun tonuwar asirinsu." Mai gado ta faɗa tana miƙa wa Umaru ƙullin kayansu, sai da ya karɓa sannan ya furta. "Na gode wa Allah ya sa kika fahimtar da ni da tuni na sa mun yi tsalle mun afka cikin rijiya gaba dubu. Yanzu dai babu sauran lokaci mu bi ta ƙofar baya." Cikin sauri Mai gado da Umaru suka hankaɗe katangar karan da ke gewaye da gidan, kamar masu shirin tashi sama haka suka dinga sauri suna kutsawa ta ciki bishiyu duk da a lokacin magriba ta kawo kai. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka ƙarasa wani ƙaramin gari a lokacin dare ya tsala sosai babu haske sai na farin wata, a gajiye suka zube a gefen ganuwar garin suna sauke ajiyar zuciya. Cike da galabaita Jawahir ta fara mutsu-mutsu sai a lokacin suka shiga damuwar abin da za su sama mata ta sha. Gorar ruwa Mai gado ta kunto ta ba ta sannan suka yi jigum-jigum, har sun zauna da sunan hutawa Umaru ya furta.


 "Mai gado an ya wurin nan yana da kyau kuwa? Me zai hana mu ƙarasa cikin garin nan mu nemi alfarma?" 


Mai gado ta yi murmushin takaici, "Duk in da za mu je matuƙar za su fahimci ba na shayar da yarinyar nan dole za su harbo jirginmu, kuma su ɗora mana zargi da tambayoyi a kanmu. Abin da muke gudu kuma ya faru ka ga an ƙi cin biri an ci dila." Umaru ya yi jum sannan ya furta. "Ina ganin mu ƙarasa bakin kasuwa mu kwana asubar fari sai mu bar garin, mu ɗora daga inda muka tsaya." Ta gamsu da shawararsa don haka suka yi gaba suna tambayar kasuwar garin har Allah ya datar da su, suna gab da shiga kasuwa suka ga wata mai fura da nono suka siya nono sannan suka ƙarasa. A bayan rumfunan kasuwar suka yada zango bayan sun take wa Jawahir cikinta da nono, babu jimawa baccin gajiya mai nauyi ya yi awon gaba da su. 


Sanyin asuba ne ya bige su suka farka don haka kamar marasa gaskiya suka sake nufar doguwar hanyar suka ci gaba da tafiya. Ba su yi tafiya mai nisa ba suka tsaya suka gabatar da sallah sannan suka ɗora daga inda suka tsaya. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka tarad da wani ayarin mutane, yara, manya, maza da mata. Sai kuma Dogarawan da ke kai kawo a kansu, kallo ɗaya Umaru ya yi musu ya fahimci bayi ne aka kama. Da yake suna ɗan nesa da su da sauri Umaru ya ja hannun Mai gado ya furta, "Maza zo mu gudu idan Dogaran nan suka gan mu na tabbata kashinmu ya bushe don mun zama Bayi na har abada." Yana rufe baki suka juya da sauri. Cak! Suka tsaya cikin faɗuwar gaba, Mai gado ta riƙo hannun Umaru jiki na karkarwa.


 "Gidan uban wa za ku gudu?" Kalaman Sojan masarautar mai ƙirar samudawa ya ratsa su, gabaɗayansu aka rasa mai bakin magana. Ganin haka ya sa Dogarin tsula wa Umaru bulala a baya, cikin azaba ya hau susar baya yana faɗin. "Tuba nake ranka shi daɗe ba guduwa za mu yi don Allah ku yi mana rai." Da hannu Dogarin ya nuna musu hanyar da sauran mutanen da ke zaune a ƙasa suke, babu musu Mai gado da Umaru suka bi hanyar ba tare da sun furta komai ba. Tun da suka tunkari wurin mutanen wurin suka zuba musu na mujiya suna kallonsu. 


 Bai san dalili ba haka kawai yake jin ƙirjinsa na bugawa, zuciyarsa kamar za ta yi tsalle ta hudo ƙirjinsa. Duk taku ɗaya da Mai gado take yi tana kusanto shi ji yake kamar ana ɗana wa zuciyarsa ruwan dalma, da wata irin ƙuda da wani surutai da ya gagare tantance harafi ɗaya ballantana ya yi wa kalaman nasu hisabi. Da yake hannunwansa biyu a ɗaure suke a jikin itace, kansa ya tura cikin ƙafafuwansa yana runtse ido. Bai yi aune ba ya fara jin sautin kukanta a tsakar kansa, yana yunƙurin buɗe idonsa kamar a mafarki ya ji an furta. "Ita daban ce don haka ta fito daga cikin wani irin ahali, tarayyarku alheri ce mai samar da taimakon juna a koyaushe. Sai dai zuciyoyinku za su gagara ba ku haɗin kan da za ku cimma manufarku ta alheri. " Firgigit ya ɗago kansa cikin mamaki, ba yau ce rana ta farko da ya fara jin waɗansu irin surutai a kansa ba. Amma na yau sun matuƙar dagula lissafinsa. "Wace ce ita?" Ya furta a fili. A daidai lokacin aka kama Umaru aka ɗaure ita kuma Mai gado aka kama ƙafarta ɗaya aka ɗaure, ta ci albarkacin jaririyar da ke bayanta. 


"Idan muka kama hanya a yanzu babu wani sauran hutu da za mu ƙara yi a hanya, domin mun kusa shiga cikin ƙasar Zazzau." Wani turɓunannan mutum ya furta fuskarsa a murtuke babu fara'a. A galabaice cikin yunwa, ƙishirwa da wahalar tafiya suka ɗauki hanyar da za ta sada su da ƙasar Huddam. Sai da suka yi tafiya ta kusan sa'o'i shida sannan suka ƙarasa cikin masarautar ta Huddam.


 A lokacin da suka je daidai ƙofar shiga Jawahir da ke a bayan Mai gado ta fara wata irin jijjiga idanuwanta suka fara yunƙurin kakkafewa, cike da tashin hankali Mai gado ta sauko ta, ganin halin da take ciki ya sa ta ƙwallah kururuwa cikin neman agaji. Da sauri Dogaran da ke wurin suka buga mata tsawa. "Hattara dai muna gab da shiga masarauta..." Ganin Jawahir na ci gaba da shiɗewa ga wani irin jini da ke tsiyaya daga hanci da kunnenta ya sa Mai gado ta furta.


 "Ku taimaka mini ɗiyata za ta mutu." A fusace wani Dogari ya ƙarasa da niyyar zubga mata bulalar da ke hannunsa, gannin halin da Jawahir ke ciki ya sanyaya jikinsa, yana shirin yayyafa mata ruwa suka ji gijif alamun faɗuwar abu. Suna waigawa suka hangi Kamalu ya faɗi ƙafarsa ɗaya na jijjiga, daga ƙugunsa zuwa tafin ƙafarsa take ya sauya launi zuwa jawur, jini ya fara zuba daga cikin kunnuwansa. Ganin haka ya sa Dogarawan suka sa aka ɗauke shi aka shiga da shi ciki, jiki a sanyaye Mai gado ta rufa musu baya hannunta rungume da Jawahir da har lokacin ba ta daina kakkafewa ba.


Fulani Umaima


 Da yanayin damuwa ta dube shi, "Ban fahimci kalamanka ba Bamaguje." Bamaguje ya tattara nutsuwarsa wuri ɗaya ya furta. "A lokacin da nake ƙarami burin mahaifina kenan ya mallaki ruhin wannan yarinyar, sai dai kash binciken farko da ya yi ya bayyana masa lokacin da yarinyar za ta zo duniya ba ya raye. Ni kaina na yi tsammanin a farkon rayuwata za ta wanzu, amma sai ga shi sai da tsufa ya make gangar jikina. Ina son ko ba yanzu ba idan kun haɗu da yarinyar nan ki ribace ta har zuwa wannan tsibirin nawa. Domin ba za mu iya kamata da alƙaluman tsafi da sihiri ba, idan kika yi haka tamkar kin kawo ƙarshen rayuwar yaron da kika sa aka fitar da shi daga cikin masarautar ne. Wannan kaɗai za ki aiwatar mini sauran bayanan zan yi miki su daga baya." Fuska ɗauke da damuwa ta furta. "Ban santa ba ban taɓa ganinta ba ta yaya kake tunanin zan gane ta har na ribace ta na kawo maka ita?" Murmushi Bamaguje ya yi ya furta. "Daga shi har ita ba su kasance kamar kowa ba, kuma shigarsu cikin masarautarku zai ƙara tayar da rikitattun al'amuran da ke cikinta. Masarautarku shu'umar masarauta ce da ke raye a ƙarƙashin ikon waɗansu ɓoyayyun hallitu. Ko ban faɗa miki ba shurin da ke cikin turakar Takawa akwai dalilin wanzuwarsa, tun da kin san banza ba ta kai zomo kasuwa. Zan sake bincike game da wasu al'amuran ko za mu da ce a wannan karon." Bamaguje yana rufe baki ya watsa wani baƙin jini a cikin wata tukunyar ƙasa take wuta ta fara ci gangan-ganga, shiru ya yi yana nazartar abin da yake faruwa zuwa can ya saki wata irin dariya. Shiru Fulani Umaima ta yi tana kallonsa cike da ƙosawa. "Wani abin farinciki da ban za ta ba, kusan gabaɗayansu ruhinsu na da kusanci da juna..." Kalamasa suka katse sakamakon ganin wutar gabansa ta ɗauke yo kansa kamar za ta ƙone shi sai kuna ta ɗauke ɗif, bai so haka ba amma ko babu komai ya tsinci waɗansu abubuwa da za su ba shi narasa a game da yarinyar. 


"Ki sa ido sosai a wurin da kika binne jariran da kika taɓa binnewa a bayan ɗakin Sarki Abdul'aziz. Matuƙar kika ga an tone ta ba kowa ba ne face jininsa, ina nufin jininsa da kika fitar da shi. Idan har kika ga kan tinkiyar da kika rataye a ɗakinki wanda a kullin jini yake ɗiga a kan zanin kishiyarki ya fara tsutsa ta tabbata gabaɗaya su biyun suna da kusanci da ke, wato suna rayuwa a cikin masarutarku. Idan ba ki manta binciken da na yi miki a baya na gaya miki akwai wanzuwar rayuwar waɗansu ruhi masu ɗauke da rikitattun al'amura a cikin masarautarku waɗanda suke yunƙurin shiga al'amuran masarautarku. Lokacin ganawata da sarkin baƙaƙen aljanin ƙarƙashin ƙasa ya yi, zan ba shi aikin matar wani attajiri akan kishiyarta, ki ba ni wuri sai wani lokacin idan kin sake dawowa." Fulani Umaima guntun tsaki ta saki cike da takaici, ta yi masa bankwana ta koma ɗakinta. 


 Lokacin da aka shigar da su Baffajo sashen Bayi aka wuce da su, kusan gabaɗaya jikinsu a sanyaye yake sakamakon ganin halin da Kamalu da Jawahir suke ciki don a tsammanin mutane da yawa mutuwa za su yi. A hankali Kamalu ya fara buɗe idanuwansa yana ganin mutane dishi-dishi, ajiyar zuciya ya sauke ya yunƙura da ƙyar; da sauri Baffajo ya ɗago shi yana zubda ƙwallah. Mutanen da ke wurin suke bi su da kallo cike da mamaki, Inna wuro ta share ƙwallah tana faɗin, "Na faɗa maka Kamalu ba zai mutu ba." Baffajo ya jinjina kai yana tallafo haɓarsa, "Amma har yanzu jikina yana ba ni za su iya halaka mini shi, wataƙila ba za su bar mana shi ba." Kamalu da ke zaune bai tanka musu komai ba sakamakon wata irin juwa da ke ɗibansa, waani dattijo tsoho ya gani a gabansa ya sakar masa murmushi tare da faɗin. "Muna ta ya ka murnar dawowa cikin ahalinka, ka tashi ka ƙarasa bakin rafin can ka ɗebi ruwan cikinsa ka ɗura a kunnenka, ka damƙi ƙasar cikinsa za mu yi maka iso har bayan turakar Mai martaba yanzu, aikin da za ka zartar sai kai domin abin salsala yake bi." Kamar wanda aka ƙara wa ƙarfi haka Kamalu ya miƙe daƙau, Dattijon ya kama hannunsa ya fara tafiya Baffajo da Inna wuro suna ƙwala masa kira, ko waiwayensu bai yi ballantana su saka ran zai tanka musu.



*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar ***.*