1
by @nanadiso10
1
LATYFAH IMAM
NA NANA DISO
WANNAN LABARIN YAFARU AGASKE MUN CANZA WASU ABUBUWA NE TARE DA KARA WASU, HAKKIN MALLAKATA NE BANYARDA WATA KO WANI YA SANYAMIN ACIKIN YOUTUBE CHANNEL DINSA BA.
KUYI FOLLOWING DINA A AREWABOOK @ https://arewabooks.com/u/nanadiso10
__________
Dariyar dake tashi ababban palour din zai tabbatar maka da hira ce irin ta ƴan uwa, tunda abdul yashigo babu wanda yaƙula sai ammi itama sama sama yagaisa da'ita, kallonsa ƙawai takeyi dan ita tafi kowa baƙin ciki da wannan auren, kowa yasanta asalin fulany ce kyakyawar gaske dan duk ƴayanta babu wanda bazaka zata shuwa Arab baniba saboda kyau, amma arasa wulakancin da za'ayi ɗan nata nafari sai adakko wata kabila can abasa kuma yarinyar ko masu aikin gidan Alhaji me lema sunfita kyan gani itafa baƙin yarinyar ma tsoro yake bata, Amma dan nata ya haɗa har ita yana fushi tsaki taja tana sauraron karamin dan nata mai suna Ali yace " ai matar brother sai ta goyamu duƙanmu." Dariya gabadaya aka kuma sawa laila ce tace " hmmm wai danAllah daman akwai masu irin hancin nan ? Hancinta fa ƙamar an diga mata." Sosai mutan palourn suka kara kwashewa da dariya ammi ta kallesu tace " wai duk bayanin nan da kukeyi ina kukaganta ne?. Ali ne yadago yace " Ammi ai hoton da nuna miki a cikin kamfanin dady na dakko miki ai can take aiki Ingayamiki, ai wallahi bro daga ranar da mutane suka gane wannan guzumar matarka ce shikenan class dinka ya sauka." Hamid ne ya tashi tsaye yana jan tsaki yace wallahi kuji tsoron Allah billahillazi ba ku kukayi ƙanku ba Allah ne ya halicce mu duƙan mu, ba finta kukayi ba farin da kyan menene amfaninsu babu kyan hali , harara aka shiga zabga masa daga uwar har ƴayan Sautin dariyar su ne yasakashi mikewa tsaye baice musu uffan ba yafita zuciyarsa kamar ta fito, yama zama abun dariya kenan? Tabbas dady yagama hukuntashi dan auren wannan katuwar yarinyar baka babban hukunci yayi masa, kiran wayarsa ne ya katse masa tunanin da yakeyi, dagowa yayi ya zuba manyan idonsa akan screen din wayar, Anas shine abunda yagani a rubuce. Dauka yayi yana amsawa kasa kasa. " Okay naji zamuzo but sai gobe sannan ya katse wayar zuciyarsa na wani ƙalar bugawa saboda baƙin ciki.
Ko da yaƙarasa gida ya taddata palour, dagowa tayi ta ƙallesa duk da baiyi sallama ba amma kuma bai hanata faɗin sannu da zuwa ba.
Tun daga sama har ƙasa yaƙe kallonta wani ƙalar abuni ya tsaya a tsakiyar zuciyarsa, tsaki yaƙaraja na babu adadi, Takaici da baƙin cikin duk yadda yakeda dukiya da daukaka irin ta ahalinsa mahaifinsa yarasa wacece zai zabo masa sai wannan mummunan yarinyar, yayi karatu aturai yayi aiki ga kyau da Allah yabasa acan ma mata har rububinsa sukeyi baisan adadin ƴan matan da yayi ba saboda kyansa acan, kwatsam andawo dashi dan kawai a aura masa wata macen da ko akan katifarsa bai iya ganinta batare da yayi amai ba, duk ƴammatan sa amma dady yakafa ya tsaya akan bakar yarinyar nan zai aura, lukutar macce maccen ma baƙa katuwa mai tumbi? Mara gashi? Mara hanci ga babban lebe? Kuma bama pink ba? Ga kuraje fuskarta bak'inta har wani oily yakeyi, innalilahi yafada sanda yatuna aboƙanan sa ya zasuji babban yaro irinsa hadadden saurayi mai kudi kuma fari dashi tas? Kara kallonta yayi yana tofar da yawo, tare da buga ƙafarsa yana faɗin dady bakayi ba. duk tana ƙallon abunda yaƙe mata batace komai ba sai ƙara mai da hanƙalinta datayi ga aikin dake gabanta dan bakaramin mai da hankali takeyi ba yanzu saboda babu abunda yake ɗauke mata kewa sama da aikin nata, dan baƙin cikin datake ƙunsa zai iya sawa zuciyarta ta buga takasa sabawa da ƙalmomin mutane akanta mamakin mutane yana yawan kamata, uhmm tace tana ƙara gyara zamanta. Tsaki yakaraja yana ƙara tofar da yawu tare da faɗin fat ugly kawai ancuceni wallhi ya haye benen yana mai shigewa daƙinsa ya banko ƙofar.
Wasu zafaffun hawaye ne sukafara wanke fuskarta wannan wani irin aure ne? Kokuma maganganun da iyami tafada gaskiya ne innalilahi wainna illahirrajiun nashiga uku tashiga kuka cikin siririyar muryarta, sosai take kukan da duk mai tausayi zai iya tayata, shafa hancinta tayi tana mai kara fashewa da kuka, tumbin dake jikin t-shirt dinta takallah tana mai kara sautin kukan nata, karar wayarta dataji yasata dawowa daga tunani ta tsayar da kukanta tana mai saita muryarta saboda ƙada mai kiran yagane, ta dauki kusan saƙanni sannan ta dauki wayar wacce ke gab da tsinkewa sunan Nana datagani yasata saƙin numfashi tana mai sallama tare da ƙarawa a kunnenta." Sis ko kina kusa damijinki ne? Naga kira na biyu bakiyi picking ba? Shirun da yabiyo bayane yasaka Nana kara maimaitawa amma batayi magana ba sai kuma sautin kukan da tafaraji. " Ke bakya gajiya da kukane LATYFAH IMAM?." " Kema fa making fun of me kikeyi haba nana inada kyan da namiji zai making love danine?." Dariya nana tayi sosai saboda abunda LATYFAH IMAM tace " kinaso kicemin abdul bai taba tabaki ba? Are you for real." Kukan ta takarawa sauti tace tayaya zai taba giwa tifa katuwa mai tumbi? Mummuna." " subhnlhi haba latyfah why are like this? Wannan wacce ƙalar magana kikeyi? Babu kyau fa bari Kiji in gayamiki wallahi shape dinki babu namijin da zai ƙallah ya ƙauda kai kibarki mai kyauce baƙinki mai kyau ne and you're so beautiful ki yarda da maganata ƙinsan dai ƙinfini kyau." Dogon tsaki latyfah taja tana goge hawayen dake zuba a fuskarta wannan shine ƙaro na babu adadi da nana ke gayamata haka but tayaya zata yarda bayan tasan su nana shuwa Arab ne kawai dai nana siririya ce amma idan ka kalli ƴan gidansu sai ka kara kallo saboda kyau duk da kyansu nana na yawan gayamata baban yaya yafi kowa kyau agidan amma saboda bata taba ganinsa ba sai tace ina ai babu wanda yakai mom dinsu kyau,to idan bama rigaima da yaɓa magana irin ta nana ba tayaya zata dinga hadata da ƙanta bayan kowa gudunta yakeyi hatta da yayanta sunsha gayamata ita dai da baba mai kudine sai ya haɗa da muƙullin gida da mota kamin ta auru saboda muni. Muryar Nana ta dawo da'ita daga tunanin datakeyi tace " kitashi kije ki faranta ran mijinki Latyfah karki manta yanada hakki akanki kamar yadda iyami kullum take gayamiki kicigaba da hakuri da abdul kinga yanayin tarbiyarsa bata nan bace ba duba da mahaifiyarsa yadda ta batashi ." Murmushi tayi tanajin ƙaunar kawar tata har ciƙin ranta duk da kyanta da kudinsu bata taba kyamatarta tazamar mata yaya ƙanwa, cikin sanyin murya tayi mata godiya tare da ƙashe wayar , murmushi tayi tana gano yadda zatayi making love yau tare da Abdul yes itama tagaji tana buƙatar soyayyar mijinta, mikewa tayi tashiga bangarenta duba da ita daƙinta yana a ƙasa yake kau da komai tayi gefe jiƙinta har tsuma yakeyi yau kusan 6month da aure but babu abunda take ƙunsa sama da baƙin ciki, ko data gama wanka wani short wando tasaka da half vest ita ƙanta tasan tayi kyau sosai, turaruka ta zuba jiƙinta tana ƙara kallon yadda halittar jiƙinta ta bayyana suka cicciko murmushi tayi tafita daga daƙin ta hau saman benen tanajin tsoro har cikin ranta ko data isa jiƙin kofar ta dauki loƙaci mai tsawo kamin ta bude kofar wacce tayi sa'a a buɗe take. Sallama tayi gabanta yana bugawa sosai, ko karasowa batayi ba ya daga ƙai ya ƙalleta take yaji tsigar jiƙinsa ta mike amma ganin fuskarta yasashi jan tsaki sannan yace " ke lafiya?." " Banda hakkin shigowa daƙin mijina ne? Tafada cikin zaƙin muryar da sai da ya ajiye kofin hannunsa sannan yasaki wani fitananne murmushi ya ƙalleta yace " Ni Abdul mai lema nene zan kwanta dake? Are you mad? You're ugly? You're black? Abeg fitarmin daga daƙi malama banason ganinki wallahi babu abunda zakiyi da zakisa hanƙalina ya tashi ko nayi sha'awaeki i want beautiful white classy lady mai kyau mai aji fara mai hanci mai gashi mai ido sannan wayayyiya, amma kefa? Ƴan aikin gidan mu dake kauye sunfiki ƙyan gani look at me danAllah ni type dinki ne? Na dace da ugly girl irinki, abeg out yadaka mata tsawar da sai datayi saurin fita tana kuka." A hankali yashiga sauke ajiyar zuciya akai kai yes tanada komai da yake bukata ajikin macce but tayaya shi abdul mai lema zai kwanta da bakar mummunar maccen nan? No no no yafada yana mikewa tare da sakawa kofarsa key.
Ko da safe da suka tashi saurin shiryawa tayi, idanunta sun ƙumbura saboda kwana tayi tana kuka tana gayawa Allah , tabbas didi tafaɗa gashi maganganunta su ke tabbata, dan ko da wasa yace babu ita babu yimasa girki dan wallahi bazai iyaci ba dan baya tunanin zata iya girkin ma hakan yasa bata bata lokaci gurin girki, yau black abaya tasaka tayi kyau itama yau ta tabbatar da she's beautiful but amma ita daya ke gani sai didi da nana why sauran mutanen basagani? Tana tsaye a kofa taji yace ke fatty. Juyowa tayi tace ina kwana, ko kallonta baiyiba yace " yau zanfara shiga offices babuke babu nuna kinsanni wallahi ko da wasa kika nuna ni mijinki ne sai na wulakantaki, akwai babies dina da abokaina akamfanin kada ki sake ki nuna kinsanni nagayamiki bazaki zubarmin da mutunci ba kamarni abdul mai lema aganni da wannan sukutar yarinyar." " okay tace tana goge hawayenta sannan tafita tayi hanyar titi tana ganinsa har ya huce bai ko tsya ya ƙalleta ba, tana tsaye taji horn tana juyawa taga nana ce dan haka babu bata lokaci ta shiga suka wuce ma'aikatar tasu. " hy sisi good morning, why abdul baya tafiya dake?." " Saboda bancika maccen gaban mota ba, saboda ni mummuna ce tafada tana fashewa da kuka...
MUJE ZUWA?
KOWANNEN MU MAI KYAU NE BABU MUMMUNA A DUNIYA.