FreeArewaPen original
LATYFAH IMAM
- 1views
- 34chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Writer ce
Sample · 1
1LATYFAH IMAMNA NANA DISOWANNAN LABARIN YAFARU AGASKE MUN CANZA WASU ABUBUWA NE TARE DA KARA WASU, HAKKIN MALLAKATA NE BANYARDA WATA KO WANI YA SANYAMIN ACIKIN YOUTUBE CHANNEL DINSA BA.KUYI FOLLOWING DINA A AREWABOOK @ https://arewabooks.com/u/nanadiso10__________ Dariyar dake tashi ababban palour din zai tabbatar maka da hira ce irin ta ƴan uwa, tunda abdul yashigo babu wanda yaƙula sai ammi itama sama sama yagaisa da'ita, kallonsa ƙawai takeyi dan ita tafi kowa baƙin ciki da wannan auren, kowa yasanta asalin fulany ce kyakyawar gaske dan duk ƴayanta babu wanda bazaka zata shuwa Arab baniba saboda kyau, amma arasa wulakancin da za'ayi ɗan nata nafari sai adakko wata kabila can abasa kuma yarinyar ko masu aikin gidan Alhaji me lema sunfita kyan gani itafa baƙin yarinyar ma tsoro yake bata, Amma dan nata ya haɗa har ita yana fushi tsaki taja tana sauraron karamin dan nata mai suna Ali yace " ai matar brother sai ta goyamu duƙanmu." Dariya gabadaya aka kuma sawa laila ce tace " hmmm wai danAllah daman akwai masu irin hancin nan ? Hancinta fa ƙamar an diga mata." Sosai mutan palourn suka kara kwashewa da dariya ammi ta kallesu tace " wai duk bayanin nan da kukeyi ina kukaganta ne?. Ali ne yadago yace " Ammi ai hoton da nuna miki a cikin kamfanin dady na dakko miki ai can take aiki Ingayamiki, ai wallahi bro daga ranar da mutane suka gane wannan guzumar matarka ce shikenan class dinka ya sauka." Hamid ne ya tashi tsaye yana jan tsaki yace wallahi kuji tsoron Allah billahillazi ba ku kukayi ƙanku ba Allah ne ya halicce mu duƙan mu, ba finta kukayi ba farin da kyan menene amfaninsu babu kyan hali , harara aka shiga zabga masa daga uwar har ƴayan Sautin dariyar su ne yasakashi mikewa tsaye baice musu uffan ba yafita zuciyarsa kamar ta fito, yama zama abun dariya kenan? Tabbas dady yagama hukuntashi dan auren wannan katuwar yarinyar baka babban hukunci yayi masa, kiran wayarsa ne ya katse masa tunanin da yakeyi, dagowa yayi ya zuba manyan idonsa akan screen din wayar, Anas shine abunda yagani a rubuce. Dauka yayi yana amsawa kasa kasa. " Okay naji zamuzo but sai gobe sannan ya katse wayar zuciyarsa na wani ƙalar bugawa saboda baƙin ciki.Ko da yaƙarasa gida ya taddata palour, dagowa tayi ta ƙallesa duk da baiyi sallama ba amma kuma bai hanata faɗin sannu da zuwa ba.Tun daga sama har ƙasa yaƙe kallonta wani ƙalar abuni ya tsaya a tsakiyar zuciyarsa, tsaki yaƙaraja na babu adadi, Takaici da baƙin cikin duk yadda yakeda dukiya da daukaka irin ta ahalinsa mahaifinsa yarasa wacece zai zabo masa sai wannan mummunan yarinyar, yayi karatu aturai yayi aiki ga kyau da Allah yabasa acan ma mata har rububinsa sukeyi baisan adadin ƴan matan da yayi ba saboda kyansa acan, kwatsam andawo dashi dan kawai a aura masa wata macen da ko akan katifarsa bai iya ganinta batar...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.