TIKITIN WUTA

Tikitin Wuta Kashi Na Biyu

by @fatimafantah


Sh 5


Mai da idona nayi kan bulalin, na daɗe da fahimtar karatun wannan Duniyar, wannan bulalin na rakiyata ne. “Muje…” halittar ta faɗa cikin muryar da na kasa tantance daga wane jinsi take, amma nasan tabbas a wannan Duniyar babu babu batun jinsi, balle nace mace ce... "Zabau" Zubar bulalarta bisa sassan jikina ya katse min tunanina, "wayyoooooooo!" Na faɗa cikin sautin da nake tsammanin idan a Duniya ne zai zagaye lardin da muke.

 Tafiya muke tana watsa min bulalar nan, har muka isa cikin wasu kwazazzabai, cike suke da macizai da kunamu.

 Na galabaita ga tsananin yunwa da ƙishirwa, sai dai ganin mun soma yawa a cikin ramin yasa ni rikicewa, bayan wannan wahalar ga duka ga tafiya ga shi ƙafata na zubar da jini, gangar jikina ma ta daɗe da ɗayewa, kamannina sun gama canzawa zuwa wasu kamannin daban.

  Bebi! Wannan suna har na tsane shi, domin duk yayin da naji an anbace shi nasan sabuwar azaba ce.

 A'mali ta bayyana. Ina ma akwai bangon da zan jingina na rage wahala! Kai! Ina kaico, kaicon rayuwar da na aikata lokacin da nake raye.

 "Kalli nan" A'mali ta faɗa tana nuna min wani hoto mai motsi, kamar an ɗauke shi da camera HD tsabar yanda ya fito raɗam. Kai wannan ma fitowwar shi tafi kowace irin camera. Matse ƙwalla nayi, na sani idona tuni ya gama zubar da hawayen ruwa sai dai na jini. "Kin gani?" Na gani A'mali. Na faɗa tamkar in shiga cikin videon in roƙi waɗannan bayi na Allah su yafe mani, domin na gama fahimtar bulalin da na sha, waɗannan bulalin ne da na ke yi wa musu a cikin dalilai marasa tushe da hujja marar makama. Walida da Husna tare da yayansu Imam, sune ƴaƴan da abokiyar zama na ta haifa kafin Allah ya karɓi rayuwarta. Na same su a gidan ubansu sannan na dinga jera musu azaba ɗaya bayan ɗaya, nau'in ta kowwace rana daban, na yi tanadin bulali kala-kala na jibgar su, ashe kaina na tanada mawa, babban tanadi kuwa gashi ina ta girbar abinda ba yi bi-da-bi. 

 Sunkuyar da kaina nayi, ina kallon macizai da kunamu sun kai girman jinjirin ɗan adam, tiƙa-tiƙa suna kai min hari.

 A'mali tace, abinda kika yi ne, "Lah-Shakkah" yayin da videon ya ɗauke gaba ɗaya.

 Haka muka ci gaba da tafiya cikin wannan rami, cikin ramin ma akwai wasu ramukan wani lokaci sai in ji ƙugi cikin su ana kukan neman agaji inda babu mai agazawar kamar dai yanda nake yi.

 Duk inda muka ji irin wannan sai A'mali ta bani labarin irin aikin da suke yi a rayuwarsu ta Duniya. Nace, "wato dai duk mune wanda muka ɗauki son zuciya muka ɗora a matsayin tsanin da zamu hau mu gina rayuwarmu, gashi ko muna tafiya cikin ginin da-na-sani".

 A'mali ta ce, "kowwace mummunar ɗabi'a tana da kwarin sakamakonta, da ace ke ma kina da ɗabi'u irin na ma'abotan wannan ramukan sai kin shiga ta ciki kin fito sannan zaki ci-gaba da tafiyar ki. Wasu sun kasance masu aikata alfasha kuma suka yi jinkirin tuba suka mutu basu nemi gafarar ubagiji ba shiyasa suke karbar nasu sakamakon, wasu kuma basa biyayya ga iyaye, shiyasa kika ga nasu ramin yayi zurfi kamar yanda girman mummunar ɗabi'ar su take"

 Cikin kuka nace, "kenan duk abinda kayi akwai sakamakon aikin ka a nan"? Lah-Shakkah, kar ki manta ubangiji bai bamu ɓoye ba, ya faɗa mana komai game da tsari da hukuncin shi, yayi ma muminai bushara kuma yayi ma wanda suka fanɗare suka zaɓi abinda yayi musu na daga son zuciyarsu bushara".

 "A Duniya kina ga abin kamar zai zama ba mai yiyuwa ba...." Amma a yanzu ina ganin shi a zahiri, ina hangen waccan rayuwar tamkar a mafarki, mafarkin ma a mafi gajartar barci". 

 "Yi min shuru tunda kin gane a lokacin da ganewar bata da amfani" A'mali ta faɗa cikin ƙosawa da jin zantukana. 

 

 "Bebi" aka kira ni cikin wata galabaitacciyar murya wacce ta tabbatar min da wannan muryar bata zamo cikin muryoyin halittun wannan Duniyar ba, masu magana cikin izza da ɗaukaka da tsanani cikin lafuzzan su.

 Cikin muryar da ke kaskantar da ji-ji da kan mu da fandarewar mu ga mahalicci.

 To muryar waye wannan? Kafin na zaluƙo amsa naji ance, "Bebi, kema cikin wannan wahalar kike?" Malam Dogo na fada a mamakance.

 Ganin shi nayi cikin wahalar da tafi tawa, macizai da kunamun da ke cikin ramin sun maƙale shi har bisa kan sa. 

"Ni ne" ya fada a ɗimauce.

Juyawa nayi gefe sai na hangi sauran mutanen da nake kira aminan arziki na, sune abokan mu’malata abokan shawarata, abokan da bana aikata komai sai tare da su a Duniya.

 Shamaki, Nana, Hajiya Ƴar Doss, Khaleey, Beauty, Habashiyya, BB, tare da sauran jama'ar mu. Ashe ba ni kaɗai nake cikin wannan wuyar ba? Na faɗa ina ƙare musu kallo, kowwanen su ɗauke da tikitin su na wuta, sakk kalar nawa.

 Hajiya ƴar doss tace, "Bebi kin ji abinda muka ji?" A koke nace, "naji abinda yafi naku".

 Shamaki yace, "nayi ihun dama na zama turɓaya! Na yi ihu na maimaita, "dama Ubangiji ya mayar da ni Duniya na aikata alkhairi".

  "Ku yi mana shuru!"

Wasu muryoyi suka haɗu suna bamu umarni tamkar saukar aradu.


Taku Mai Ƙaunar Ganin Farin Cikin Ku Fatima Muhammad Sani Ku Kasance Lafiya.


TIKITIN WUTA

By FatimaFantah


Sh 6



 Baki ɗaya muka tsorata har kanunmu na haɗuwa da na juna, cikin kuka na ce wannan shi ne gwarama. Tafiya muka ci-gaba da yi ba mai yi ma wani sannu kowwa ta kanshi yake abinda ake ce ma nafsi-nafsi, har muka isa wani wuri mai matsanancin duhu tamkar garin da hadari yayi wa mamaya. 

 Gefe na juya na kalli Hajiya Ƴar Doss, kallona tayi irin kallon tashin hankali, a wahalce tace Bebi nan zamu shiga? Ri-gi-gi-gim! Wata irin tsawa mai saka tsinkewar numfashi ta kassara ragowwar ƙarfin da ke cikin gangar jikinmu. A fusace aka ce, "nan za ku shiga ya ku waɗannan matayen masu zaluntar mazajen auren su, shin ba kun san abin da kuka aikata a cikin duniya kuna masu alfahari ba…….? Waige-waige muke kowwa na laluben hanyar da zata sada shi da cikin duhun domin ƙauracewa muryar da ke amo mai lalata kowwane irin nutsuwa da kwanciyar hankali, balle kuma mu dama ba mu da shi. 

 A ƙagauce muka tsunduma cikin duhun, mutane ne birjik kowwa na ta lalube, a cikin duhun kowwa da inda ya nufa, wasu a gurgunce wasu a makance wasu kuma a durƙushe wasu kuma da rarrafe suke tasu tafiyar.

Cikin ƙaraji na ce "Ashe dai zaluncin duk da muka yi baƙin duhu ne, ashe azabobi ba sai ranar alƙiyama za su fara ba, daga inda mala'ikan da ke dakon jiran ƙarewar numfashinka ya dira gare ka daga lokacin alƙiyamar ka ta tsaya. Kaico! Haƙiƙa da kowwane ɗan adam ya san daga lokacin da ya mutu alƙiyamar shi ta tsaya da bai aikata wasu abubuwan ba. Kaicon rayuwata, wayyo ni Bebi". 

 Rasa inda zan yi nayi nima na shige mutanen da duk aiki ɗaya antaya mu cikin baƙin duhun da yayi mana ƙawanya.

 Muna tsaka da tafiyar la-ila-ha-ula wata irin ranƙamemiyar kaca ta durfafo cikin filin. Mutane suka ci-gaba da darewa kamar dabbobin da Kura ta kai masu farmaki.

 Duk da gudun da muke bai zama togaciyar da zai hana sarkar zabarar wadansu daga cikin mu ba. Cikin waɗanda ta yi awon gaba da su har da Hajiya Ƴar Doss. Hankalina ya kai ƙoluluwar tashi na ganta sarkar na janta tana dalalo wuta. Ɓatt suka ɓace tare da mutanen da ta kwasa, mu kuma sauran mutanen da ƙafarmu muka cigaba da gwagwiya muna tafiya, domin tuni yatsunmu sun yi kaca-kaca sun kone ƙurmus, sai dai kuma da sun kone sai wasu su fito haka suke konewa wasu na fitowwa bi-da-bi cikin wahala.

  Malam Dogo da ya ɓilla can wani sashi a cikin duhun da na ganshi Duniya guda yana ta tafiya a wahalce, shima wani maƙallami mai kama da maƙallamin lema ya keta bayan shi ya ratsa cikin shi yayi sama da shi ko ina zai yi da shi? Ba ni da amsa kamar yanda nima ban ina nake ba, magana ɗaya na riƙe daga bakin A’mali wani wuri zamu Kwarin Barhoot, kenan duk wanda ke hanyar da nake shima can za shi.

  Mun ƙara nisa cikin duhun azaba mai dawwamar da makanta shima Shamaki wata halitta tayi mashi ɗaukar ƙugiyar zabari  tayi gaba da shi. 

 Tuni waɗannan halittun masu rakiyar mu sun ɓace, sai wasu halittu masu nau’in Kare-Kare, Kura-Kura baƙaƙe wuluk suka cigaba da rakiyar mu, cikin tsananin yunwa da ƙishi na ce, A’mali…… kallona tayi, ta saki dariyarta mai ƙuna zuciya. Ban damu ba na ce, "A'mali na gaji...." Bata ce komai ba, sai dai bayyanar sunduƙina ya wuce da kaso mai tsoka daga hakin da nake ciki. A’mali tace, "wannan wurin shine mafi tsanani a hanyar ku don haka wannan guzirin da kika samo nan zai fi yi maki amfani..." Cikin shessheƙa nace, A'mali ina su Hajiya Ƴar Doss"?

 "Tana can wani inda ya dace da wasu halaye da take aikatawa..." Daga haka bata kuma cewa komai ba.

 Gefe nesa da ni na hangi su Nana, da Khaleey waɗannan halittun suna yagin su suna farka fatar jikinsu, a tsorace na ce A’mali waɗannan halittun kar su far mani nima. A’mali ta ce, ki kwantar da hankalin ki, waɗancen mutanen suna wulakanta Sallah shiyasa waɗannan halittun ke faffarke musu jiki, don haka da kin zama mai wannan ɗabi’ar da tuni kema sun ƙarar da ke kamar yanda zasu ƙarar da waɗancan kuma zasu yi masu jagoranci har zuwa wani wuri da akayi tanadi ma masu wannan ɗabi’ar". 

 Lumshe ido nayi, a Duniya duk mutumin da yake ce maka ka gyara, ko da da kalmar kaji tsoron Allah yayi maka nasiha, to tabbas shine masoyinka. Gashi ina kallo su Hajiya Ƴar Doss da nake ganin na ni da masoya kamar su sun kasance cikin uƙubar da ta fi tawa. Hamza maigidana kodayaushe mai tunatar da ni ne game da Sallah da sauran ibadu, wanda bai zama dole ba sam bana aikata su, amma sallah da yake sa min ido ina aikata ta, ga shi na tsira daga azabar waɗancan dabbobin masu cinye naman jiki kamar Kura ta samu akuya. Kaicona! Dama.ana komawa Duniya na rungumi mijina na ƙaunace shi mu ci-gaba da tafiya bisa tafarkin da yake nuna min wanda yake cike da ni'imomi da jin daɗi da a halin yanzu suka yi mani fauti.

 A'mali tace, "muje". Ba musu na amsa da "to" jikina na karkarwa.

 

 A'mali ta buɗe abinda ke ciki sunduƙina wani abu ne siffar shi tayi kama da ta keken dawaki irin na mu na Duniya, a takaice dai za a kira shi da amalanke. 

 A’mali ta ce, "maza ki hau". Kafin ta ƙarasa har na bayyana kan amalanken, a guje ya tafi da ni ya fice dani daga cikin wannan duhun, su Khaleey, Nana da Beauty nan na bar su waɗannan halittun sun tisa ƙeyarsu zuwa wata hanya da nike jiyo sautittika masu firgita mai saurare.

 Na bar cikin duhun baki ɗaya sai dai duk da haka tafiyar babu dadi, amma da waccen wahalar gara wannan tafi ta sauki, na yi nisa cikin wani irin daji babu komai sai wasu manya-manyan namun dawa. Cikin dana sanina na karo ba iyaka na ce, wannan halittun kuma zasu iya farmani a koda wane lokaci, zuciyata cike fal da karewar guzirina, na soma jin wata girgizar ƙasa tana girgiza ni, kafin ƙwaƙwalwata ta shiga ɗakin nazari tuni amalanke na ya fara wargajewa. Timm na faɗo ƙasa babu shawara, miƙewa nayi a hanzarce ganin waɗannan manya-manyan namun dawan, zakoki da damisoshi tare da wasu irin murɗa-murɗan macizai wanda kallo daya zaka yi musu ka tabbatar zasu iya yi ma Ɗan Adam haɗiyar magani a kowane lokaci. A guje na dinga tsere da su, na galabaita ƙwarai da gaske, hakan ya tilasta mani faɗuwa ƙasa wan-war, na sani da ace ƙasusuwa da tsokar jikina irinta Duniya ce da tuni ko labarin buzuna babu, balle ni da nake cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi a daidai wannan lokaci.

 Na yi nisa na lula Duniyar ba mutu-kwana, naji A’mali na feso wata irin dariya, ita kanta yanayinta sauyawa yake yi, wani lokacin tazo da rangwame wani lokaci ta zo da tsanani. "Ki tashi!" ta fada cikin matsanancin ƙaraji. Miƙewa na yi a wahalce su kuma namun dajin nan suka hau ma gangar jikina, sun ƙarar da ni a gare su na zama nama na faɗi ƙasa tare da bajewa.

 Buɗe idonuwana nayi na ganni a cikin wani ɗaki, wata halitta mai matsakaicin kyawu tace da ni sannu. "Yawwa na fada", ina miƙewa cikin tsamin jiki kadaran-kadahan. Shin wannan rayuwar mai birkita ƙwaƙwalwa ina ta kawo ni kuma? Kafin na nemo amsa halittar tace, shin zaki iya tunawa da azumin da kika zaɓi wata rana ta alhamis kika aikata shi? A hanzarce nace tabbas. Tace wannan wata hasna ce ta azuminki, zaki zauna nan cikin nutsuwa iya sa’o’in da kika ɗauka na wannan azumi.

 Kasake nayi, wai kenan muminai masu aikata alkairi suna ibadoji da nake jin ba zan iya yanke jin daɗina na aikata su ba, su ne cikin jin daɗi marar iyaka a wannan rayuwar da take fassara aikin ka Duniya a lokacin da kake raye? Idan ko haka ne ashe ni da ire-irena mu ne muka yi asara, muka biyewa ɗan guntun jin daɗin da bai fi a ɗora ƙwayar sikari a bisa harshe ba, ba zaka tantance zaƙin shi ba, baka san ina yayi ba, sai ka rantse ma ba'a ɗora ma baka ji ɗan-ɗanon sa ba. To kamar haka jin daɗin da muka yi shekara da shekaru muna yi a Duniya ya kasance a gare ni.

 Nisawa nayi tare da sakin wata sassanyar ajiyar zuciya, ba zan manta ranar da nayi wannan azumi ba, shine ƙwallin ƙwal da nayi a tsayin wannan shekarar bayan ƙauracewar watan Ramadana. Yanzu da a ce na lazimci azumin Alhamis da Litinin da kodayaushe zan ta zama cikin irin wannan dadɗan ɗaki mai sanyi da ni’ima da ƙamshi mai sanya nishaɗi, ga wasu halittu masu yi mani hidima. 

 Haka na wuni cikin jin daɗi, lokacin da ya zamto lokacin ƙarewar sa’ar da nayi bakina a kulle, lokacin ya zamto sabon shafin tafiyata ni da A’mali.

 Haka muka cigaba da tafiyar mu, maganar jin daɗi nayi bankwana da shi tun a ɗakin azumina na litinin. 

 Wani wurin mu haɗe da su Hajiya Ƴar Doss wani wurin in ga anyi sama da su an jefa su cikin wani kogin azabar, su Shamaki ko tunda suka bace ma ganina ban kuma yin tozali da su ba. Wasu abokan tafiyar tawa kuma sai muna cikin tafiya, sai kawai in ga an ɗauke su, idan na tambayi A'mali sai tace mutanen da suka baro a Duniya ne suke masu addu'ah, ni ko dama wa zai min addu'a wanda kowwa murna yayi da mutuwata? Ƴaƴana kuma ban tarbiyyance su da suyi min addu'ah ba balle ta zo min, mijina da ƴanuwana na mutu da addu'ar su mummuna a kaina. To kau wa zai tuna da ni? Wata zuciyar tace, ai kinga zahiri tunda kin ga ba wani abu da yazo gare ki ya rage maki wahala da azaba. A'mali ta juyo ta ce, "kuma ke kika yi wa kan ki". Ban ce komai ba, domin na fi kowwa sanin hakan.

 Mun yi nisa can na hango wata ni’ima irin wacce ido ke muradin gani kodawane lokaci, zuciya ke kissimawa, sai dai hasashen mai hasashe da hangen mai hange bai taɓa hasaso ta ba. 

 Sai dai nisanta da ni ta gefe ya tabbatar min da ba zan taɓa isa inda take ba.

 A’mali tace, ya kike ji da ganin waccan daular? Cikin narkewar nadama na ce, "ji nake da ma na kasance a wancan wurin". Dariya ta fashe da ita, "aiko ba zaki taɓa kasancewa a can ba, domin kuwa nisan da ke tsakanin ki da ita yafi nisan da ke tsakanin sama da ƙasa. Wancan wajen shi ake kira *GIDAN AMINCI* Farin ciki da jin daɗi, annushuwa da nishaɗi, nutsuwa da kwanciyar hankali, suna a wancan wuri, duk wata ni’ima da kika sani akwai ta a can, irin wacce hasashen mai hasashe bai taba hasaso ta ba, tsammanin mai tsammani bai taba tsammaninta ba, a can ne muminai suke dakon jiran kiran mai kira su tashi a gaban Ubangiji suna masu farinciki, su kasance a cikin jin daɗi madawwami". "Ashe wawa ne wanda ya rusa wannan goben dawwamammiya da ƴar guntuwar yau ɗin sa mai gushewa, kai tirr ina baƙin ciki dan nadamar kasancewata a cikin waɗannan asararru, kai wayyo kaico!" Na ƙare maganar tamkar ana tsawa.

 Sam A'mali bata damu ba, cikin ƙasaita ta ci-gaba da maganarta. "Yanzu ke ma kin iso a wannan kwarin da na baki labarin sa, wato Kwarin Barhoot, kwarin da bayin Allah kafirai da mushrikai da mujrimai da sauran bayi wanda suka fanɗarewa Allah suka bijire zasu kasance a ciki har zuwa ranar da mai kira zai yi kira".

 A firgice nace, wayyo Allah na! Kina nufin duk wannan tafiyar ta shekaru aru-aru a nan za na kasance har zuwa ranar tashin alƙiyama?! Wayyo Allah na, ashe duk wancan wasa farin girki ne yanzu za'a fara wasan.

 Dariya ta sheƙe da ita, "Lah-Shakka" ta ba ni amsa.



Taku Mai Ƙaunar Ganin Farin Cikin Ku Fatima Muhammad Sani Ku Kasance Cikin Ƙoshin Lafiya


TIKITIN WUTA

By Fatima Fantah


Sh 7

Cikin tsananin kaɗuwa da razana na yi tsaye tamkar an dasa bishiya, kallon wata irin Duniya nake mai cike da tarin azabobi da nau'i-nau'in azabobi.

 Dukkan abinda ya faru da ni kankanin lamari ne akan abinda ke gudana a halin yanzu gaban idanuna, wanda baki baya iya faɗar sa, hasashe da hangen mai hange baya hangosa. 

"Bebi" Amali ta kira sunana. Azabar da nake shaidawa ta sa na mance sunana, dukkan wani abu da yayi saura a cikin abinda na sani lokacin da nake raye ya ɓace ɓat a cikin Duniyar ƙwalƙwalwata. Wannan shi ne haƙiƙanin tashin hankali, wannan shi ne haƙiƙanin wahala, wannan shi ne gaskiyar azaba.

 Amali ta ce, "ita ma wannan akwai ta gabanta, akan waccen wannan za ki iya kiranta somin tabi, akan wacce zaki tarar bayan an yi sakamako, an yi ma kowwa signing zuwa gidansa madawwami.

 Wannan Kalmar abar tsoro ce, kuma a bar dubawa ce ga bawan da Allah yayi ma dokoki, “Khalidina Fee'ha” a cikin kowwane sakamako ita ce abar dubawa".

 Sam bana jin ma me A'mali take faɗa, firgicin da nake ciki ya kaye ji da ganina da motsi na ya katse duk wata na’urar sadarwa ta ƙwaƙwalwata.

 Muna tsaye mutane maza da mata marasa adadi suka ƙaraso wajen kowwane ya yi tsaye cikin nadama da tsoron wanann wuri.

 Wasu manya-manyan halittu suka ƙaraso in da muke, halittun sun linka mu girma ga su da manya-manyan fika-fikai, ko ba’a faɗa ba waɗannan su ne mala’ikun da ake faɗa mana a rayuwarmu ta Duniya sune suke bin umarnin Ubangiji Allah ba da saɓani ba. Summun, Bukmun, Umyun basu sauraren kowwa, ba su jin kowwa, ba su ganin kowwa balle su ji roƙon mai roƙo, ko su tausaya ma wahalar wanda ake wahalarwa, aikin su kawai suke na cika umarnin Allah, iya su kaɗai sun zamanto a bun tsoro kafin a isa ga Duniyar azaba mai suna Kwarin Barhoot.

 Fuskarsu turɓune ga dukkan alamu basu san da al’amarin sauki ba, haka Allah ya halicce su domin bayinsa kangararru irin mu.

 Cikin fuskarsu mai ban tsoro suka yo kan mu, baki ɗaya mutane suka dare suna neman matsera, sai dai babu ƙafar gudu babu wurin da za’a je a tsira. Su ko cikin cikita aikin su suka shiga finciko mutane suna watsa su cikin Kwarin Barhoot, baki ɗaya basa gajiya da aikin watsa mu ciki har aka zo kanmu.

 Mun yi tsaye a wani wuri mai kama da gidan kurkuku aka fidda mu da ni da wasu mutane.

 Ɗaya bayan ɗaya aka fara yi mana abinda na kira da hukunci, wani faffaɗan rami aka tafi da mu. Hankalina da ya daɗe da yin tashin gwaron zabi tamkar na siƙe saboda tsananin tashin hankalin da ke walagigi da ni.

 Wasu abubuwa ne suka soma yo sama daga cikin wani irin rami, wanda yafi ƙarfin a kira shi da rijiya gaba dubu, rami ne iya ganin mai gani, cikin shi wasu irin halittu na kai kawo, wuta ja-jawur tana ci daga ƙasan shi, harshen ta yana yo sama yana laso abin da ke tasowwa kamar wani faranti ko kaskon suya. Abin na tasowwa a hankali sai kuma wani irin ihu da ƙara mai firgitarwa suka riƙa fitowwa tare da ɗagowwar abin.

  Na jiƙe na yi sharkaf da kitsen naman jikina da ke narkewa yana yankowwa kamar an kanga kwanon kitse a jikin garwashi. Bakina ya bushe, kalamaina sun ƙare babu abinda ke fita daga maƙoshina sai wani sauti da nake yi kamar an shaƙare bajimin Sa.

 Abubuwan suka ida fitowwa tarwai muna kallon su. "Tandar Kwarin Barhoot" shine aka faɗa da wani kalar sauti da ban san kwatan-kwacin sa ba a rayuwar Duniya.

 Tabbas abin yayi zubi da tanda, mai ɗauke da manya-manyan gidaje, kowwane gida akwai mata a ciki suna wani irin kukan azaba, ina tsaka da ƙarasa ɗimaucewa na hangi Haiya Ƴar Doss, Malam Dogo da Shamaki.... Kafin na yi wani dogon tunani naji jigib an jeho wasu mata kusa da ni, juyawar da zanyi na yi ido huɗu da Khaleey, Beauty da Nana. Ƙafafuwansu ɗaure da wasu irin sarƙoƙi, an yi hanging ɗin su da wasu irin ƙarafa.

 Kafin na rufe ido, wata irin majaujawa tayi ƙasa da su cikin ramin da tandar nan ta fito.

  Ɗaya daga cikin sojojin da ke kai kawo a wannan wurin ya daka mana tsawa, jikina na karkarwa yana ƙwambarewa saboda razana.

 Wasu mutane ya ɗeba ya jefa kan tandar, take jikinsu ya ɓalle gunduwa-gunduwa, ya nemi gidan da yayi mashi a cikin gidajen tandar wanda ruwan narkakkar darma ta zama man suyar jikun nan da ke ciki.

 Mutanen da suke ciki suna magowwa da neman ɗauki, sannan ɓallewar kowwace gaɓa bai hana ƴaruwarta ɗanɗanar azabar da take ciki ba. 

 Na shiga uku na furta cikin yaren da ni kaina ban san me nake faɗa ba.

 "Bebi" A'mali ta kira sunana. A firgice na juya, "Bebi wannan shine aikin ki na ƙarshe yayin da kika taka matakin ƙarshe na barin Duniya, wannan sakamako ne na mutanen da suka hana "AURE" Ubangiji Allah bai yi rangwame ga wanda yayi wannan aikin ba ba tare da wani dalili ba... Dukkan wanda kika gani a bisa wannan tandar ya aikata kwatankwacin wannan laifin ne... Kema kin aikata hakan ga mijinki Hamza, wannan shine sakamakon abinda zaki girba, kuma zaki kasance a nan har zuwa ranar da mai kira zai yi kira, ku tashi a lokacin da kuka manta sunan kawukan ku, gangar jikinku ta rududduge, gashin jikinku ya zama fari, kuka kasance a ƙarƙashin ikon Allah maɗaukakin sarki, bako da sulɗani akan dukkan gaɓɓanku....... A nan za'ayi hukunci a fitar da sakamako, mai haƙƙi zai nemi haƙƙin sa, babu abinda zai kasance gare ku sai abinda kuka aikata. Lah-Shakkah! Maza ki je ki amsa kiranki......"

 Durƙushewa nayi kan gwiwoyina ina dukan kaina, kaicona dama na zama turɓaya. Kafin na kai ƙarshe wata majaujawa tayi ƙoli-ƙoli da ni ta zabari ƙafafuwana ta haɗa da hannuwana tayi cikin wannan ramin da ni.

 "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Nake ta maimaitawa a haukace, ɗaki-ɗaki da wuraren azaba na soma karo da su kala-kala.

 Na zagwanye na ƙare, sannan majaujawar ta yo ƙoli da ni ta jefa bisa tandar. Kamar yanda na yi tozali tana faruwa da waɗanda na gani sun karɓi hukunci kalar nawa, haka ta kasance da ni.

 Yatsun ƙafata suka soma guntilewa, sai ƙafar da hannayena, babu inda bai rabe ba da jikina kowwane sashe yana cikin raminsa a cikin tandar har zuwa kaina. Kowwace gaɓa tana amsa raɗaɗin da ke cikin tandar azabar. Ihu nake ina maimaitawa, "yalaitani kuntu turaba dama ban aikata sharri ba, dama ban bi son zuciyata ba, dama na zamo turɓaya......"


 Wayyoooooo Allahhhhhh! Firgigigit na farka daga mummunan mafarkin da nake yi, wanda na gaza tantancewa a raye nake ko a mace. Wayyo Allah! Wayyo Allah!! Wayyo Allah na!!! Na ke maimaitawa ina ƙanƙame jikina wuri ɗaya.....



Ta ku mai ƙaunar ganin farin cikin ku, Fatima Muhammad Sani Fantah Ku Kasance cikin ƙoshin lafiya.


TIKITIN WUTA

By Fatima Fanta

Ina ƴammata ina samari💃🏽


Daga jin kiran kun san na musamman ne.

 Junior AR Photography masu hoton Ƴan Gayu, masu hoton Big Girls da samari masu ji da gayu. 

 Kai har ma su Mummys da Aunties ba a ce banda su ba, su ne jagayyar masu fiddo Hajiya Naira. 

 To sun kira ni da babbar murya, sun ce a faɗa muku suna yin hotuna tsala-tsala masu kyau a ɗauke ka ka ganka kamar a ƙasar turai Junior AR kenan.


Suna hoton Bukukuwa

Suna hoton Birthday

Suna hoton Suna 


Sannan sun yi kyakkyawan tanadi da rangwame ga masu buƙatar hotunan sallah.


 Na san yanzu kun fara tambayar kan ku a ina ne zaku same su? 

 

 To ba wani abu ne mai wahala ba. Junior AR suna nan a unguwar yari da ke birnin Katsina.

 Ko ku tuntuɓe su ta wannan numbern, ***. Ko ziyarce su a shafukan sadarwa @t Junior AR Photography.




Sh 8


Sake curewa nayi wuri ɗaya ina ambaton sunayen Allah tare da faɗin "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un!" Nafi tsayin mintuna goma jikina na karkwarwa tamkar an jona min wayar lantarki. Hotuna da bidiyoyin abin da ya faru da ni a mafarki ke yawo cikin kwakwalwar kaina tamkar yanzu yake faruwa, wayyo Allah! Wayyo Allah Na!! Na faɗa hannuwana dafe da hargitsattsen gashin kaina.

 Mikewa nayi da ƙyar ƙafafuwana sun sandare tamkar na kwana na wuni cikin ƙanƙara hakan ya sa na faɗi ƙasa timm. A wahalce na rarrafa na isa jikin bango na dafe bangon na miƙar da hannuna na kunna hasken ɗakin. Da kyar na kalli agogo, karfe biyar saura gugguɓin asuba ya soma kawo jiki. Dafe ƙirjina nayi na kasa motsin kirki, sai kuka nake da ihu cikin firgicin komawa halin da na baro a kowwane lokaci nayi wa agogon ƙuri. 

 Ƙwan-ƙwan-ƙwan bugawar ƙofar Hamza ta sa ni sakin fitsari a tsaye. "Bebi, ki tashi…." Kafin ya ƙarasa na buɗe ƙofar a haukace ina ƙan-ƙame shi. Sam bakina ya kasa furta komai, "ka yafe min! Hamza ka yafe min.... Hamzaaaa....... Na shiga maimaitawa ba miƙdari.

 Shi ko Hamza tamkar gunki yayi mutuwar tsaye, yana ambaton sunana, "Bebi Bebi" cikin zaton ko na yi gamo. Kaɗa kai nake ina kallon shi, tun bakina na furta maganar har muryar ta soma dashewa. Idanuwana na zubar da hawaye kamar an buɗe famfo ina kallon shi ina ƙara riƙe rigar shi ya fara karanto ayoyin Alƙur'ani mai girma da tsammanin gamo na yi da sheɗanun aljannu cikin bacci. 

 Tabbas babu abinda ya kai zancen ubangiji saka nutsuwa da yaye duk wata masifa da ke tare da Ɗan-adam. Shuru nayi na nutsu amma idanuwana sun kasa daina zubar da hawaye, na ƙan-ƙame Hamza gam, na yi mishi riƙo tamkar ɗa yana son komawa cikin mahaifiyarsa, numfashi nake maidawa ina cigaba da ambaton sunayen Allah.

 Hamza ya ɗago ni daga jikinshi yana ƙare ma fuskata kallo, nayi firi-firi kamar daga lahirar na dawo. A hankali ya ce Bebi, wata irin matsananciyar ajiyar zuciya na saki, Hamza don Allah ka kira ni da sunana Zainabu ba Bebi ba, bana son wannan sunan..... 

 Kallon mamaki yake yi min, anya ko wannan Bebi ce, ko dai wata aljana ce ta fito daga dakin tayi suffar Bebi ta iso gare shi.

 Ɗago ni yayi daga jikin shi cikin muryar lallami ya ce, "sallah zan je in yi lokaci na wucewa". A kidime na ce, "zan bika masallacin, don Allah kar ka tafi ka barni Hamza"... Sororo yayi yana kallona, sai kuma ya saki fuska, haba Bebi… ina kika taba ganin mace taje masallaci a haka, ki koma ɗaki kema sai ki yi sallar taki ko?...….. Kaɗa kai nayi don girman Allah Hamza kar ka tafi ka barni, ba zan iya zama ba zan bika wallahi…..zan bika......"

 Gyaran murya yayi ya ci-gaba da karanto ayatul kursiyyu, domin tabbas a yanzu ya tabbatar da gamo nayi.

 Hannuna ya kama ya kai ni kan kujerar da ke cikin bedroom, yana juyawa na bi bayan shi. Tsaye yayi, ya kasa gane me ya faru da ni? Ga alamu ba abinda yake tsammani ba ne. 

 Na riƙe hannun shi gamm, na yi mashi ƙuri tamkar ya faɗo daga wata sabuwar Duniya.

 

 Ganin abin nawa na yi ne yasa ya riƙo hannuna ya shigar da ni toilet. Baya zai rufe ƙofar nayi yuf na riƙo hannun shi. Ya gane abinda nake nufi sarai, hakan yasa ya toge bakin ƙofa. Da ƙyar na yi wanka ina waige-waige.

 Cikin hanzari na kama alwala, ina alwala ina kuka ina jera istigfari. Hamza ya fito ganin lema bakin ƙofa ya kalle ni da alamar tambaya. Cikin shessheƙar kuka nace, "ka canza rigarka, ba zata yi sallah ba" kallona kawai yake, shi kan shi ya faɗa cikin dogon tunani.

 Okay kawai ya faɗa, bara naje na canza rigar nayi sallah kin ga gari ya soma yin haske. Jinjina kai nayi. "Zaki iya zama ko?" Ɗaga kai nayi alamun eh. Ficewa yayi da sassarfa ya nufi ɗakin shi.

  Haka na lallaɓa nayi sallah na ci-gaba da istigfari har Hamza ya dawo. Tsugunnawa yayi yace, “Bebi ya jikin” Zainab sunana Abban Waleeda. Fuskar shi cike da alamar tambaya ya kalle ni, sai dai yayi shuru ba tare da iya furta min kowwace irin kalma ba.

 Ɗan sake fuska yayi, Zainab, ki bar kuka hakanan, na lura kin yi mummunan mafarki ne ko, dama wani lokacin sheɗanu na zuwa cikin mafarki su rikita ƙwaƙwalwar ɗan adam, don haka ki yi ta ambaton sunayen Allah komai zai gushe kin ji ko? Ɗaga kai nayi "to Abban Ameera".

 Ganin na ɗan samu nutsuwa ya koma ɗakin shi.

 Ni ko nayi zaune kan sallaya kaina bisa sit ɗin kujera, nayi lagadam tamkar an jefa tsumma a ruwa. Kuka nake marar sauti, har kaina ya soma wani mummunan ciwo wanda ke nuna tabbas kwakwalwata ta fara gajiya da tunanin da take ciki. 

 Wayata ta soma burarin neman dauki, ban iya motsawa ba balle na dubi inda take, har ta tsinke ban iya kai mata ɗauki ba. Wani kiran ya sake shigowwa. Zira'in hannuna nasa na jawo wayar da nufin kasheta gaba ɗaya “Hajiya Yar Doss” na gani ɓaro-ɓaro kan screen ɗin wayar.

 Gabana ya faɗi yayan cikina suka hargitse, take suka hautsine wanda suka haddasa min kiran gaggawa da hanzari na nufi toilet.

 

 Da ƙyar na fito ƙafafuna sun soma yin nauyi. Idanuwana da ke yi tamkar zasu faɗo ƙasa na dubi agogo da ƙyar. Karfe takwas saura, idan ban mance ba karfe tara ne zamu je wajen Malam Dogo akan maganar auren da Hamza zai yi.

 Cikin shaƙaƙƙiyar murya na ce, "ko Mata ɗari zaka aura kaje ka aure su Hamza, babu ruwana cikin abinda Allah ya halasta. Tabbas nayi kuskure, son zuciyata ya kai ni yana niyyar ya baro ni, amma nagode ma Allah da ya taɓo ni bisa darjajjiyar lakar da ta kwashe ni..”

 Rufe ido nayi a hankali, rayuwata ta baya ta shiga dawo min cikin ƙwaƙwalwata. Sunana Zainab, inkiya Bebi… suna mafi muni a gare ni a halin yanzu.


Ta ku mai ƙaunar ganin farin cikin ku, Fatima Muhammad Sani Fantah Ku Kasance cikin ƙoshin lafiya.


TIKITIN WUTA

By Fatima Fantah✍🏻



 Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un.😭😭😭


Yayin da al'amari ya girmama ya wuce zato da tsammanin ƙwaƙwalwa sai ta aika da saƙon gaggawa ga zuciya domin bagautar samun mafita. Ita ma ya wuce da saninta tayi ragwancin ɗaukar shi domin ya yi mata nauyi, sai ta aika da saƙon ambato ga masarrafin sauti domin fitar da zance don samun sauƙin raɗaɗi, sai dai shima masarrafin sautin ya gagara aiwatarwa a gare shi.*

 Sai dai ido kaɗai ne yake isar da saƙon da harshe ya kasa furtawa, ya yi ma zuciya nauyi ya wuce da tsammanin ƙwaƙwalwa. 😭😭😭


May your gentle soul rest in Jannatul Firdaus. Allahumma Ameen🤲🏻 Maryam Siyuɗi Ibraheem we will never forget you.😭




Sh 9

 


 Sunana Zainab inkiya Bebi sunan da ambatonsa ke firgita ni ya ke jefa ni cikin kogin razani a halin yanzu.

  An haife ni a jahar masu kara, kunya da kawaici, sai dai almakashin mutuwa yayi min girtsinmin raba ni da mahaifiyata, ba a jima ba kuma shima mahaifina ya bar wannan filin daga ya koma ga mahaliccinsa a gidansa na gaskiya. 

 Dalilin hakan yasa nayi bankwana da gidan mahaifata na koma jahar kwankwasiyya da zama a wajen ƙanin mahaifina Malam Isma'il. Ban samu matsala da matar shi ba sun riƙe ni cikin aminci da kulawa har zuwa lokacin da halayena suka soma gundirar su da saka ma zukatan su ƙunci da fargabar me gobe na zata zama.

  

 A wani dare ya kirawo ni ran shi a matuƙar ɓace bai zafafa muryar shi ba ya kira ni a tausashe ya ce, “Bebi, miyasa kike nuna ɗabi’a da halayyar da ni baki ganni da ita ba sannan ba ki ga wani a cikin zuri'armu da ita ba? Bebi wannan ɗabi’ar da kika laƙabawa kan ki mummunar ɗabi’a ce da ba zata kai ki a tudun na tsira ba sai dai ta jefa ki a cikin tafkin da na sani.”

 Sunƙui na yi da kai ina sauraren nasihar da yake yi min wacce wannan ita ce karo na ba iyaka. Amma kullum ta bayan kunnena take wucewa ba na sa ran ta taɓa shiga cikin kunnena. 

 “Bebi” ya sake ambaton sunana. Da ƙyar na ɗaga kai na kalle shi cikin ladabin kura na ce “Na’am Baba" 

Gyaran murya yayi ya kalleni irin kallon da uba yake yi wa ɗansa. "Bebi ki cire wannan ɗabi’ar son abin Duniyar daga tsarin rayuwarki, ki daina koyi da rayuwar wasu ki rungumi rayuwar da Allah ya ƙadddare ki da ita, da haka ne kaɗai zaki samu ƙana'ar zuciya. Idan kika yi haka Ubangiji mai rahama ne watarana sai ki ga ya yalwata arzikinki ko na mijin da kika aura ke ma kin zo kina rayuwa fiye da wacce kike mafarki kuma kika ɗora kan ki a kai." Numfasawa nayi tamkar na karbi nasihar Baba na ce "to baba Insha Allahu zan yi kokari in gyara".

 Alhamdulillah ya faɗa. Ya maganar exam ɗin ku? "Mun kusa kammalawa" na ba Baba amsa.

 "Yawwah to Alhamdulillahi. Tunda kun kusa kammalawa ina so a cikin samarin nan da kike tarawa ina so ki faɗa min wane ne yafi kwanta miki a rai?" Da sauri na ɗago na kalle shi, domin a cikin tsarin rayuwata sam ban kawo aure a yanzu ba, to aure a shekara sha bakwai zuwa sha takwas ay an yi min yankan ƙauna. Na fi gane ma abinda ƙawata Halimatus Sa’adiyyah Saleh wacce muke kira da Khaleey ta faɗa min, cewa a wajen samarin da muke tarawa zamu samu kuɗi da abubuwan more rayuwa, aure gintsirmi kawai zai yi mana don haka sam babu tsarin aure cikin zuciyarmu wata faffaɗar daula muke tsarawa zamu samu a tattare da samarin da suka ƙaunace mu.

 "Bebi!" Kiran da Baba yayi min katse min tunanina. Nisawa nayi na ce na'am Baba, cikin in-i-ina na ce "Baba a cikin su babu wanda na tsayar….. saboda wallahi......." dakatar da ni yayi, "Bebi kar ki faɗa min haka don kin ga bana zama. To hatta mutanen unguwar nan suna faɗa min cewa kina da manema da yawa, Mamanku ma haka ta faɗa mun kina da manema masu zuwa wajenki da gaske amma sai ki ce baki tsayar da kowwa ba, ba zai yiyu ba". Baba ya ƙare maganar shu a zafafe.

  Jimm nayi domin ban san amsar da zan bawa Baba ba, ashe duk abinda nake karr suke kallona. Numfasawa nayi, wata zuciyar mai nema ta mayar da ni tafarkin ƴan Duniya tayi gaggawar bani shawara. Da sauri na ce. "Baba wallahi duk yawancin su da maganar da ba ita ba ce suke zuwa shiyasa ma bana kula su……." Zainabu… Baba ya kira ni da babbar murya.

 Yanda ya kira ni da ƙarfi yasa ƴaƴan cikina juyawa. "Duk abin da kike na sani Bebi, na biyo maki ta lalama ne domin baki cikakken ƴanci saboda bana son tilastawa ƴaƴana akan komai da ya shafi rayuwarsu, na fi so na basu cikakken ƴancin su. Amma na lura sam ba ki san da hakan ba. To tun da cikin masu son ki babu wani sahihi babu wani na azo a gani cikin su to bari ki ji, akwai Alhaji Hamza dan gidan Malam Ladan wanda matarsa ta rasu shekarar nan da ta gabata, ya zo har nan ya nemi iso a wajen mu, don haka zai zo wajen ki shi da gaske yake idan ya zo sai ku daidaita nan da dan lokaci a yi auren ku.

 Gaba na ya faɗi dammm tamkar an sako min aradu daga saman bakwai, na ɗago da ƙyar na kalli Baba. Wani irin jinjina kalmar nake "aure… aure ni za a yiwa aure"? Tamkar idanuwana su zubar da kwalla nace Baba aure?  

 Wani irin kallo ya watsa min. "Aure kuwa Zainabu, aure zan yi maki ita ce maslaha da sahihiyar amanar da zan riƙewa Yayana, ba zan zuba ido ina kallo ki ci gaba da tafiya akan wannan hanyar da ba zata haifa miki ƴa mai ido ba. 

 A yanzu kin ga na tabbatar da abinda ake faɗa ɗin, fuskar ki da yanayin ki sun tabbatar min da komai.

 Shi yasa nayi maki hikimar da ni zan tabbatar din. Wani murmushin kasaita yayi mai tattare da manyance, ya ce sai ki shirya zai zo gobe idan Allah ya kai rayuwarmu, maza tashi ki ɓace min da gani.

 Miƙewa nayi da ƙyar, sam a bakina babu haruffan da zasu wakilci ƙuncin da nake ciki, ashe Baba kallon mai saman ruwa yake yi min. 

 Shikenan kuma irin rayuwar da Khaleey ke faɗa min ta zama wasiƙar jaki kenan?

 Kafa na ja na isa cikin ɗakin mu ni da Safna. Ban iya furta mata komai ba na haye kan gado na kwanta.

 Kallona ta yi, a hankali ta ce Bebi me ya faru ne? Babu komai na faɗa. Nisawa nayi Safna yaushe ma muke da exam? Sai ranan Laraba ta bani amsa a taƙaice. Wani irin dogon tsaki na ja. Domin kenan ina da kwanaki hudu kafin zuwan laraba ranan da zan haɗe da ƙawata Khaleey mu tattauna wata sabuwar matsala da ta kunno kai cikin rayuwata.

 Sake jan tsaki na yi na kara lafewa kan gado. Safna ta sake cewa, Bebi wai lafiya kike ta tsaki me Baba ya fada miki ne? Miƙewa nayi a fusace, kin dame ni da me Baba ya faɗa min, me Baba ya faɗa min. To munafunci da gulmar da kuke kai masa a kaina ya juye min. Sai me kuma? Kada kai Safna tayi ta ce Bebi koyaushe baki gane abinda na ke nusar da ke, ki sani ni masoyiyar ki ce tunda har jinina ya gauraya da naki haka naki ya gauraya da nawa…… Dakatar da ita nayi ta hanyar ɗaga mata hannu, cikin wata irin tsawa na ce dakata Safna! Ki min shuru kawai tunda ba zaki taɓa ganewa ba. Miƙewa tayi tana murmushin da ita kaɗai ta san ma’anar shi. Ki sani hanyar dai da kuke bi ke da Khaleey ba mai bullewa ba ce. Da ke wata ce mai tunani da ba za ki taɓa biyewa Khaleey ba, a matsayin ki na ƴar mutunci yar gidan masu mutunci amma kin biye mata….. wani wawan yunkuri nayi domin fizgota sai dai ban yi nasarar kamota ɗin ba.


 Komawa nayi ina huci ina bude hanci, babu wanda ya isa ya raba ni da Khaleey kuma ita ce kawata ta har abada……

Wani irin matsanancin kuka na fashe da shi, “babu ni babu ke Khaleey, a yau maraba nake nema tsakanina da ke Khaleey.” Dafe kai nayi, sauran abubuwan da suka zamto min tamkar hakar mai ginin rijiya a wajena suna ci gaba da bijiro min daki-daki.

 A ranar Laraba na zabga sammako domin zuwa makaranta, na ji ance idan kaji wani zai yi sammako kai ka bi dare domin tsintar abinda shi ba zai samu ba...


Ku kasance lafiya, taku mai ƙaunar ganin farin cikin ku Fatima Muhammad Sani AKA Fantah.


  

JUNIOR AR PHOTOGRAPHY

 Ina ƴammata ina samari💃🏽


Daga jin kiran kun san na musamman ne.

 Junior AR Photography masu hoton Ƴan Gayu, masu hoton Big Girls da samari masu ji da gayu.

Kai har ma su Mummys da Aunties ba a ce banda su ba, su ne jagayyar masu fiddo Hajiya Naira.

To sun kira ni da babbar murya, sun ce a faɗa muku suna yin hotuna tsala-tsala masu kyau a ɗauke ka ka ganka kamar a ƙasar turai Junior AR kenan.


Suna hoton Bukukuwa

Suna hoton Birthday

Suna hoton Bikin Suna


Sannan sun yi kyakkyawan tanadi da rangwame ga masu buƙatar hotunan sallah.


 Na san yanzu kun fara tambayar kan ku a ina ne zaku same su?

 

 To ba wani abu ne mai wahala ba. Junior AR suna nan a unguwar yari da ke birnin Katsina.

 Ko ku tuntuɓe su ta wannan numbern, ***. Ko ziyarce su a shafukan sadarwa @t Junior AR Photography.


Sai kun zo

TIKITIN WUTA

By Fatima Fantah


Sh 10



A ranar Laraba na zabga sammako domin zuwa makaranta na ji ance idan ka ji wani zai yi sammako kai ka bi dare domin tsintar abinda shi ba zai samu ba.

 Hakan kuwa na yi, lokacin da ƙarfe bakwai tayi ina cikin harabar makarantarmu na yi zaune gefe kan wani dakali da aka zagaye itatuwan da suka ƙawata filin makaranta. Zuciyata cike da tunani ina yi ina duba agogon hannuna, har ƙarfe takwas ta kawo jiki.

 Hango ƙawata Khaleey yasa wani sassanyar farin ciki ya dirar min cikin zuciyata. Daga nesa ta washe min fararen haƙoranta, sai dai bata samu martani daga gare ni ba domin takaicin hukuncin da Baba ya yanke min.


  A hanzarce ta karaso wajena, "Bebi, My Bebi wa ya taɓa min ke a wannan sanyin safiyar?" Ta ƙare maganar tana ɗora hannuwanta akan gwiwowin ƙafata. Murmushin takaici na yi na ɗan girgiza kaina. "Khaleey" na kira sunanta a sanyaye. "Mine ne Bebi" ta faɗa cikin tsan-tsar kulawa.

  "Matsala tayo saukar ungulu a cikin rayuwata, ta danno ga-ga-ri-galle a cikin rayuwata tamkar tifa marar birki, ina hangen babu abinda zai iya tare ta Khaleey".

  Kallon up and down ta yi min. "Matsala, kamar saukar ungulu, ga-ga-ri-galle tamkar tifa marar birki, wannan wace irin matsalace haka Bebi? Kamar yaya? Ki faɗa min Bebi". Ta ƙare maganar tare da dan ɗaga sauti. 

 Dogon numfashi na ja tare da buɗa hanci. Wannan wata dabi’a ce da na koya a wajen Khaleey. 

 "Khaleey, matsala ko ga-ga-ri-galle kamar yanda na faɗa miki, ta danno kamar tifa marar birki, domin daga Baba ta danno kai. Ga-ga-ri-galle ce domin matsalace da take nema ta mayar da mafarkina wasikar jaki, matsala ce da take nema ta guntile duk wani jin dadi da shagalin da na tanadarwa rayuwata."

 Dogon tsaki Khaleey ta ja. Bebi, kin san bana son ayi ta jan abu, ki faɗa min wai mene ne? Ni ki faɗa min don Allah ba bayanin matsalar na ce ki min ba.

 Sake numfasawa na yi, Khaleey, wai Baba aure zai yi min…. 

 What!? Ta faɗa a matukar razane. Aure Bebi? Da gaske abinda kunnena ya jiye min kenan, aure". 

 Sake numfasawa na yi aure wai Khaleey na faɗa a daƙile.

 Wani irin murmushi ta saki wanda ban san ma'anar shi ba. To wa za ki aura? Kin san dai waɗannan samarin mu kan mu bamu tara su ba domin mu aure su, mun tara su domin bayani na samun Hajiya naira, naira maganin mutanen zamani.

 A cikin su wa ki ke ga zai aure ki? Tsuru na yi ina kallonta tamkar na samu T.V Khaleey a cikin su babu wanda na taɓa jin ɗigon son shi a cikin raina, domin na riƙe shawarar ki da kyau, soyayyah zata iya ruguza mani komai.

 Bugu da ƙari kuma basu ma yi min kalar mazajen aure ba. Wani murmushin ta saki. "Wanda kike so ai wannan sam ba matsala bace, kuma na tabbata suma ba zasu aure ki ba."


 Don haka wannan boss ɗin matacce ne, Uhmmm! Na saki murmushin takaici. Khaleey, wannan boss ɗin a raye yake, domin Baba shi da kan shi ya zaɓo min mijin da zan aura, domin duk abinda nake ba wai ƴan gidanmu kaɗai ba, a’a har mutanen unguwa sun sa ido a kaina kamar sune suka haifeni.

 Share zancen mutanen unguwa, ni ba abin da ya dame ni da su. Yanzu Baba ya zaɓo miki mijin aure? "Ehh" na bata amsa. 

 Shuru tayi irin na mai nazari. To yaya mijin yake? Kin san shi? Yaushe zai zo?

 Sake gyara zamana nayi bisa dakalin.

 "Uhmm, wanda aka kira da mijin har ya zo ma."

 "Ya zo?"

 Ta fada tana zaro ido. 

"Ya zo kuwa, tun ranan litinin. Dan gidan makwabcinmu ne sunan shi Alhaji Hamza, matar shi ta rasu shekara ɗaya da ta wuce, yana da yara uku."

Taɓe baki tayi tare da faɗin, "na ji kince Alhaji; Alhaji ne mai naira ko-ko Alhajijiya ne, an biya mana ne a jike ake?"

 Kaɗa kai nayi, "a'ah, wannan Alhajin Naira ne Khaleey".

 "Ban san shi ba amma ina jin labarin shi a wajen mutanen gidanmu da mutanen unguwa. Nan gidan Malam Ladan yake, ya fara business Allah ya ɗaukaka shi, yanzu haka yana da manyan filazoji da manyan shaguna na kayan blouse da cosmetics, idan dai maganar Hajiya Naira kike to gaskiya ya aje ta kam."

 Wata irin dariya ta saki har ta razana nutsuwata. Sai da tayi mai isarta har na soma tsoron ko matsalar kwakwalwa ta diro mata a nan take? Dafa kafaduna tayi, tare da sakar min wani irin kallo.

 "Ana maganar Hajiya Naira ta ya zaki ce mafarkin ki zai zama wasiƙar jaki? Ay ita Hajiyar da ake magana akanta, ita ce ke mayar da mafarkin ya zama gaskiya kowwane iri, ni na tabbatar da hakan Bebi." 

 "Bari kiji, Ummanmu da aurenta. Da aurenta? Kenan Babanku na da rai? Na jefa mata tambaya, cikin tsintsar mamaki. Da aurenta kuwa, haka ma Anty Luba da Anty Na'ima.

 Numfasawa nayi, maganarta tafi ƙarfin na bi ta da zance, wannan wani shafin tambaya ne da ya buɗe cikin ƙwaƙwalwa ta mai zaman kansa". Numfasawa nayi, Khaleey me kike nufi da hakan? Ta yaya zan tara irin kuɗin da muke mafarkin samu? Ina aure? Dariya ta sake fashewa da ita. Za ki samu ko har nima na samu".  

 Wannan ba aikina bane, aikin Mama ne, domin ba zaki iya fahimtar karatun daga baki na ba.

 Kawai daga nan makaranta zamu waske muje gida ki ganta tayi miki cikakken karatu akan matsalar da kike ta kambamawa.

 Murmushi ta saki, "Bebi dama na daɗe ina bata labarinki, amma wannan Father ɗin naki ya hana ki je ko da sau ɗaya ki gaisheta duk irin amincin da ke tsakaninmu.

 But tunda wannan kyakkyawan al’amari ya kunno kai kawai sai mu waske daga nan mu je".

 Amma kin san Safna za ta fadi naje wani wuri daga school ko? Wata dariyar ta sake shekawa.

 Wannan ki barta, yau ba kunnen uwar shegu kika yi da maganar Baba ta sai kun rika tafiya tare ba? To haka ma zaki yi gobe, sai ki yi fatali da ɗumumuwan su ki sako ƙafa ki zo muje gun Ummanmu, ita zata warware maki komai, ta ƙare maganar tana sakin wani shu’umin murmushi.

 Numfasawa nayi, baki ɗaya maganganun Khaleey sun rikirkitani, motsinta ya jefa ni cikin rudani. Wata maganar Safna ta fado min, 

"Bebi da ke wata mai tunani ce da baki biyewa Khaleey ba a matsayinki na mai mutunci yar gidan mutunci……."


 Wasu zafafan hawaye suka kwararomin kan fuskata.

 Cikin gunjin kuka na ce, "rijiyar hawayena shin ba zaki kafe ba?"

 Shafa kumatuna na yi domin tabbatar ko akwai ruwan hawayen ko sun sauya launi zuwa hawayen jini. Domin a halin yanzu wutar da-na-sani ke ci a cikin ƙwaƙwalwata.

 Hawaye ne na fada ina kallon hawayen da na shafo kan fuskata.

  Maganar Safna tana yawo a cikin kwanyata tamkar yanzu ne ta fada min ita. "Me ya sa ma tun farko ban fahimci wannan zancen ba ni Bebi?"

 Safna… na ƙare maganar ina haɗa kaina da gwiwa takuna a cikin dirzajjiyar lakar nan na ci-gaba da dawo min cikin kwanyata.

  

 A safiyar Laraba na yi fatali da faɗan da Baba yayi min a jiya, ba tare da wani tunani ba na saka ƙafata na fice har da kyakkyawan tukuicin jan tsaki.

 Kai tsaye gidansu Khaleey na nufa, duk da buɗaɗɗen kwatancen da tayi min, amma da tambaya na gane gidan. “Gidan Hajiya Lawwa, wacce tayi ƙaurin suna da Ummanmu. Uhmm, sunanta ba ƙauri ya yi ba, a badinin rayuwa ruɓewa ya yi yana wari, gidan Ummanmu... Gidan da na karbo TIKITIN WUTA..."


Ta ku mai ƙaunar ganin farin cikin ku, Fatima Muhammad Sani Fantah Ku Kasance cikin ƙoshin lafiya.