Tikitin Wuta Kashi Na Huɗu
TIKITIN WUTA
By Fatima Fantah
Sh 15
My lovely na ga fuskarki ba yanda na barki ba, fada min da me da me ya faru da bana nan? Murmushin ciki nayi muna ci-gaba da taku zuwa sashen da dakinsa yake. Kasa furta komai na yi shi ko yana kara damke tafin hannuna cikin salo da nuna da gaske a koyaushe cikin shauƙin so da ƙaunata yake.
Sake murza tafin hannuna yayi tare da sake faɗin, Sugar mie baki ce komai ba… Da ƙyar na furta "ba komai Honey, kawai kewarka ce take damuna gashi kuma Allah ya dawo min da kai lafiya."
Bayyanannen murmushi yayi tare da sakalo hannun shi bayan wuyana. Karɓar jakar hannuna yayi tare da yi min wani ƙayataccen kallo, “Na yi kewarki fiye da yanda kika yi tawa, tunda na tafi kewarki nake da har takai ina ji kamar na baro dukkan aikin da ya taru a office dina na zo nayi tozali da wannan kyakkyawar fuskar nan taki” Ya kare maganar yana sumbatar goshina.
Murmushi nayi kawai ina kallon kyakkyawar fuskar shi. Taimaka mashi nayi ya yi wanka ya canza kaya masu saukin nauyi.
Ina zaune ina ta jujjuya kalaman Khaleey sam nutsuwata ta gagara samun wurin zama a cikin jikina, sai yaƙe nake ina yayo mayafin farin ciki ina lulluɓe zantukan Khaleey da shi. Sai da ya gama wasu abubuwan da ban san me yake ba a laptop sannan ya ce "Bebi dauko min jakata."
"Toh" na faɗa sannan na mike cikin sanyin jiki da ya rikide ya zama tamkar ina yanga na dauko jakar.
"Ga ta" na faɗa tare da komawa gun zamana.
Runtse idonki ya fada, ban musa ba na runtse idanuwana ina sauraren shi.
"Yawwah bude" ya fada bayan ya dora min wani abu a hannuna wanda yafi kama da kwali.
Ware ido nayi ina kallon wani hadadden kwalin wayar salula a tafin hannuna. Numfashin farin ciki na saki domin wayar ta yi gaba da mafarkina, waya ce kirar kamfanin apple wacce na gani ba jimawa a hannun Khaleey ko ba a fada min ba na san ita ce gama hawa a wayoyin zamaninmu, domin na san komai na Khaleey daban ne.
Kasa magana nayi, shi ko ya zura min ido yana bin kowwane motsina da kallo. Da kyar numfashina ya bani zarafin amaye abinda ke bakina. Wannan tawa ce Honey? Sunan da ya lakabi min a bakina yace na rinka kiran sa da shi.
Jinjina kai yayi "taki ce halak malak My Baby, ke na siyawa kuma kin ma fi da haka a wajena, ke ma kin sani. Duk abinda zan yi maki bai kai tukwicin sona a gare ki ba…" Wasu hawayen da na kasa tantance ko na menene suka ziraro min? Da sauri na rungume shi I Love you Honey. I love you too ya fada yana shafa bayana.
Sosai nake jin farin cikin samun wayar nan, duk da tarin tunanina akan abinda Khaleey ta fada min bai hana ni watayawa ba a duniyar farin ciki na.
Sallolin magrib da isha muka yi tare gefe tunanin yanda zan yi amfani da maganin da Khaleey ta kawo min nake, Hamza ya siya min wannan tsadaddar waya ina ga in na mallake shi ni ɗaya kamar yanda Khaleey ta faɗa min? Tabbas Khaleey ta zo min da magana mai kyau. Amma a yanda Hamza yake maƙale da ni ko yaushe ya zan iya amfani da maganin nan?
Numfashi na maida ina ci gaba da jan cazbi ba tare da sanin me nake faɗa ba. Baki ɗaya na lula duniyar tunanin maganina.
Wani sashin zuciyata ya kawo min shawarar da nayi na'am da ita har da sakin ajiyar zuciya. "Ka baccin karya duk tadin da Hamza zai maki ki ƙi tashi har sai ya tafi masallaci tunda baya bari jam’in Asuba ya wuce shi." Shine abinda zuciyata ke ƙara jaddada min.
Murmushin samun mafita nayi, cikin kwarin gwiwa na na mike, yaye abayata nayi. Honey bara naje na kawo mana Dinner ko. Jinjina kai yayi ya ce a aje min da lipton. Okay Honey na fada ina murmushi.
Abinci na jejjera a dining sannan na dauko flask na na zuba tafasasshen ruwan da ke ciki na jefa lipton da wani garin haɗin lipton da Hamza ke amfani da shi.
Ganin bai fito ba har na kammala yasa na koma ɗakin na kira shi. Koyaushe yafi son na kasance tare da shi, haka muka jero har zuwa dining muka zauna.
A shiririce muka ci abincin domin Hamza sam baya bari na huta wajen tsokanata, kamar yarinya ƙarama yake cewa sai ya bani abinci a baki. Haka muka gama cikin farin ciki da nutsuwa. Daga wajen cin abinci na wuce ɗakina na sake wanka na saka kayan barci masu kyau da birgewa, sannan fesa turarika da humra wanda nake ta kaya da su na amarci.
Kai tsaye ɗakinsa na nufa, ina shiga dakin ya mike ya rungume ni, cikin sassanyar murya ya ce, "you look like a glowin flower bebina." Hannuwana na sa na mayar da martanin rungumar da yayi min.
Kalallame ni yayi da kalaman soyayya masu tsayawa a rai da narkar da zuciya, jin tsayuwa na neman gagarar mu baki daya yasa muka zube kan gadon gaba daya.
Duniyar masoya muka lula har zuwa wani lokaci mai tsayi, sai da muka samu nutsuwa sannan muka tsaftace jikinmu muka koma wani irin nutsattsen barci.
Cikin bacci na rika jiyo sautin Hamza yana kiran sunana, bulum nayi na ki amsawa, domin na tabbata asuba ce tayi.
Duban agogon da ke maƙale jikin bango yayi “kai lokaci ya kusa kurewa” ya fada a kagauce. "Bara na dawo sai na tashe ki Bebi yau kin yi nauyin barci sosai" ya fada yana ficewa a gurguje.
Yana fita na mike na fice daga dakin, cikin sauri na ruga dakina na dauko maganin da nake ta boyonsa a tsakanin sakon kujeruna. Kicin na ruga na dauko cup, na kasa nutsuwa gani nake duk inda na tsaya kamar Hamza zai shigo ya ganni ina shan maganin.
Da sauri na shige toilet zuciyata na bugawa fat-fat tamkar zata tsinke.
Wani sashi mai cike da son cika muradaina na son abin Duniya na aikata maganin kaman yanda Khaleey ta yi min bayani.
Ina gamawa na wanke kofin na mayar da shi mazaunin shi a kichin sannan na koma toilet na yi wanka tare da alwala.
Sam raina babu dadi, amma son tara abin duniya da neman mallakar abin da ba nawa ba saboda rashin godiyar ubangiji yasa na yi wancakali da duk wani tsoro da fargabar da ke cikin raina.
Ina cikin sallah Hamza ya dawo, ko da ya leko yaga ina sallah yace yawwa, na kasa zama can nayi azkar saboda bana son hasken rana ya sauka a duniya kina ta barci.
Juyawa yayi ya koma dakin shi. A dan zaman da muka yi na kwanaki kadan na fahimci shi din mutum ne mai ibada da kula da addini.
______
Bayan kwana uku amfani da maganin na fara ganin canji, a ranar da su Waleeda da Yasir suka dawo, ranar sati biyu cif-cif da bikinmu. Kwanakin na fara canzawa fatar jikina tayi kyau har wata kiba nayi irin wacce mutane ke kira da cikar daki.
Ina zaune muna taɓa hira da su Waleeda Hamza ya shigi niƙi-niƙi da kaya, wata irin siyayya ce marar misali yayo min.
Kafin ka ce meye kuma ya sauya kayan dakina gaba ɗaya. Sannan ya bani kyautar miliyan daya tare da makullin mota. Abin ya kusa rikita kwakwalwata. Da kyar na iya kame hankalina, jikina na rawa na shige daki. Tamkar na shiga jerin masu rangwamen hankali na fara rawa da tsallen murna idan na tilla makullin motata na cabe sai na sumbaci kudin da hamza ya bani naira miliyan ɗaya kash.
Sai da nayi murna mai isa ta sannan na tsaya ina tuna Khaleey da Ummanmu ashe dai Khaleey alkhairi ce a rayuwata kai duba min wannan al’amari?
Cikin sati biyu abin kamar zubin hauka, ni kaima na soma ganin abin yayi yawa.
Sai dai wani sashin zuciyata na faɗin, "ay duniya gidan kashe ahu ne in ji Ummanmu, kuma iya kudinka iya shagalinka" da ire-iren waɗannan zantukan nayi watsi da abin da ya ɗarsu a raina.
A hankali nace ko dai zan nemi gidansu Khaleey ne, duk tsayin lokacin nan bata leƙo. Zaune na tashi daga kwancen da nake. Zuciyata ta karfafa min gwiwar na aikata hakan. Ban bata lokaci ba na mike na tsala wanka na fesa turare na dauki jakata na fice zuwa gidansu Khaleey.
Bakina dauke da sallama na sa kai cikin falon gidan, ba kowwa sai Babansu yana shan garin kwaki da sugar. Ban yi mamaki ba saboda a zuwa daya tak da na yi a gidan, na fahimci yanda Ummanmu take tafiyar da Baba Saleh. Babu mutunci babu kimantawa babu daraja balle kulawa. Haka yake a gidan kawai cikon benci.
"Sannu da zuwa Hajiya" kalaman Baba ya katse min tunanina.
"Yawwa" na faɗa a yamutse.
"Wajen Hajiya aka zo ko? Tana ciki bacci take, shiga ciki, shiga kiyi sallama". Bin shi kawai nake da kallo zuciyata cike da tambaya "shin wai dama haka yake ko yaushe tamkar zararre? Ko ko dai ya akayi?"
"Oyoyo!" Ihun Khaleey ya maida ni cikin hayyacina" bakina har kunne na karasa gare ta.
"Sannu da zuwa ƙawata, dama na san zaki zo. Ba ma yau ba, tun shekaranjiya muke duban hanyar ki ni da Ummanmu..." Murumushi nayi, nima zuwan yana raina sai yau na samu damar hakan.
"Muje ciki" ta faɗa tana jan hannuna.
Ɗakin Ummanmu ta kaini, galala na bi ɗakin da kallo. A cikin ma falo ne mai rai da lafiya, yasha kaya ƙirar Dubai. Ita ko Ummanmu ta hakimce tamkar wata sarauniya.
Fuskarta cike da fara'a tace, "sannu Bebi dama nasan zaki zo, gashi kuwa, amma kin yi late na ɗauka yanzu kin daɗe da zuwa." Murmushi kawai nayi, nace 'Ummanmu ina wuni. "Lafiya lau" ta faɗa tana kallona.
"Yaya al'amurra suka kasance?" Wannan shine abinda nake ta son in ji. Shuru nayi, can nace, magani yayi sosai, kuma Hamza ya siya komai wanda nake so har ma da wanda ba na ra'ayi. Gaskiya naji daɗi sosai Ummanmu, domin wannan dama shine mafarkina koyaushe inga na tara abin duniya".
Murmushin ƙasaita Ummanmu tayi, ai na sani dama wannan shi ne mafarkinki shiyasa na dage don taimaka miki ki cika burin ki".
Abu na gaba da za a yi shine, kema zaki kawo abinda za a share maki hanya ta gaba. Kina kankanuwarki zaki shiga jerin manyan mata.
Cikin zakuwa nace ti Ummanmu. Nawa zan kawo? Dubu ɗari biyu da hamsin kawai zaki kawo, kar ki wuce gobe baki kawo ba, daga zaran kin zo zan kai ki wajen Malam Dogo, dama shine nake sakawa a gaban dukkan al'amurra na kema a yanzu zaki bi sahu. Ki shiga layi a gidanki sai yanda kika yi."
Nisawa nayi nace to Ummanmu. Goben zan dawo. "Khaleey ta murmusa tace, ƙawata kin ga abinda nake faɗa maki ko, Malam Dogo shine maganin kukanmu shi yake shige mana gaba a cikin duk abinda zamu yi. Shine sirrinmu.
Kuma mata da yawa sun je, mata da yawa suna zuwa muna mu shige musu gaba.
Ajiyar zuciya na saki. Nace zan zo Khaleey, ay biyan buƙata yafi dogon buri.
Agogon hannuna na duba, bari na tashi na koma. Kar Hamza ya dawo yaga ba na nan.
"Uhmm, nan gaba duk zaki daina wannan tsoron." Ummanmu ya faɗa tana miƙewa tsaye.
Tare muka fito har falonsu, Baba yana nan zaune. Sai faman Allah ya kiyaye yake. Babu wanda ya kula shi muka fice waje.
Sai kin zo suke ta faɗa. Ni kuma na ja ƴan ƙafafuna na fice.
Ta ku mai ƙaunar ganin farin cikin ku, Fatima Muhammad Sani Fantah Ku Kasance cikin ƙoshin lafiya.
TIKITIN WUTA
By Fatima Fantah
Sh 16
A hankali na ci gaba da tafiya tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki, sosai tunanin al’amarin nake. Tabbas na san tun da na fara sanin kaina nake son kayan kawa, nake kaunar alatu da more rayuwa, kullum a cikin tunanin irin wannan rayuwar nake har zuwa lokacin da na hadu da Khaleey rayuwarta ta ɗauki hankalina yanda take facaka tana kashe kudade abinta. Ganin hakan yasa na manne mata tare da nuna mata kwadayina ga son irin rayuwarta, bata jim nusasshe ni hanyar da take bi tana samu. Na bi hanyar amma ni ta zame min ba mai bullewa ba sai ma rikito min kaddarar aure baki daya. Ta yiyu na samu abinda nake so sai dai zuciyata mai cike da muradi da son mallakar abinda ya fi haka yasa na kasa bijirewa Khaleey akan abinda ta zo min da shi har ta kai ni ga abinda suka zo min da shi yau.
Sosai zuciyata ke bugawa, wani sashe na son bijirewa amma wani sashe na cikinta na min karfa-karfa wanda nake jin sa kaman wani tilasci.
Ajiyar zuciya na sauke na tsayar da mai napep na kama na sanar da shi muhallin da zai kai ni. Bai bata lokaci ba ya kaini har bagiren da gidana yake, na fito a sanyaye na fiddo dari biyar guda biyu na bashi na shige gida.
Na tarar Suwaiba ta gama komai na girki ta gyare ko’ina hakan ya bani damar shigewa muhallina na tsala wanka na canza kaya na cigaba da dakon zaman jiran hamza.
Na dade zaune ban ji shigowwar shi ba, ina zaune ina ta faman tufka da warwara na ji parkin motarsa a harabar gidan. A guje su Waleeda suka shigo falon suka nufi ƙofar fita wajen Abban nasu.
Tare suka shigo yana suna ta zuba surutu, kai tsaye wurina ya karaso, fuskar shi dauke da murmushi ya ce, "Gimbiyata sannu da gida". Yawwa na faɗa sannan na mike cikin yanga na karbi jakar hannun shi.
Kwalin chocolate din Metro ya mikawa su Waleeda gashi tsarabar da nayo muku. Bakin su har kunne suka karba a guje suka yi dakinsu.
Hannunshi ya sa ya damƙo hannuna, cikin lallausar murya yace, "My Luv kina lafiya dai ko" jinjina kai nayi domin tabbatarwa.
Yawwa, muje My heart. A nutse muka taka muka zuwa sashen shi.
Muna shiga ko kayan jikin shi bai rage ba jikin shi har zanzana yake yace, "Bebi kin ga abinda na siyo miki?" Ya fada yana zazzago wasu zubabbun sarka da yan kunne duk da ban waye da sanin gold ba zuciyata ta soma hakaito min wannan sarƙar gold ce. Idona tamkar ya zubar da kwalla na ce, Hamza wannan zinari ne ko? "Jinjina kai yayi zinari ne Bebi, gani nayi har yanzu baki mallaki gold ba kina matata ya kamata a ce kema kina da gold dinnan."
Farin ciki nake ji, amma tunanin duk siyayyar nan ba ta Allah da Annabi bace yasa nayi sakwat tamkar kwalin da babu kaya.
Anya babu kuskure a cikin wannan sabgar? Shedaniyar zuciyar da ke min jagorancin hawa keken bera tace, "ba wannan ne mafarkin ki ba Bebi? A halin yanzu kin soma taka matakin da kike mafarkin takawa, don haka sam kar ki damu."
“Bebi ko batai maki kyau ba…” zancen Hamza ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na fada.
Murmushin dole na kakaro, "tayi kyau sosai Hamza, nagode Allah ya kara girma." Ameen ya fada tare da rungume ni, hannu nasa nima na rungume shi zuciyata cike da tunani kala-kala.
Cikin salo da dubara na taimaka mashi yayi wanka tare da sauya kayan jikinsa.
Kashe gari wajen karfe tara Khaleey ta doko min kira, hakan ya tunatar da ni ajandar mu ta jiya. Tamkar dole na mike na shiga Bedroom dina. Can cikin lokar ma’ajiyar sirrina tare da dukiyata na bude na fiddo kudi naira dubu dari biyu da hamsin, ba tare da wani dogon tunani ba na saka su jaka na saka Hijabi na tafi gidan su Khaleey. A shirye tsaf na tarar da su cikin wani salo Ummanmu ta rungume ni "sannu da zuwa diyata, na so a ce asubanci kika yi amma ko da yake kina jiran umarnin mijinki ne ko?"
Daga kai nayi lokacin da nake barin jikinta. Murmushi kawai tayi tace muje ko…? To Ummanmu na fada.
Gaba daya motar Ummanmu muka shiga. Babansu Khaleey ya karaso kamar ko yaushe cikin shigar shi tamkar za shi bara ya ce "Ummanmu sai kin dawo Allah ya kiyaye."
Kamar ko yaushe yau ma bai samu darajar da za a amsa mishi ba. Shin wai Baban su Khaleey ba shi da zuciya tsakiyar kirjin shi ne kamar sauran mutane? Na tambayi kaina. Kafin na lalubo amsa kunnuwa suka tsinkayi muryar shi yana kiran Ummanmu ban karya ba, a taimaka min da abin kari… Bata amsa mashi ba ta fiddo naira dubu daya ta cilla mashi ta figi mota muka fice daga gidan.
Mun yi tafiya mai tsayi sosai har muka bar kwaryar birnin kwankwasiyya a zatona wani wuri ne kusa zamu tafi amma sai naga tafiyar ta shalle da hasashen da nayi.
Mun yi tafiya mai tsayi sosai sannan muka ratse muka bi wata hanyar biri, tun muna wuce kwarorin mutane har muka afka cikin lafiyayyen kungurmin daji. Ni kam yawun bakina ya soma kafewa, duk da su Ummanmu sun zama tamkar wata tsoka a jikina bai hana jikina sanyi da inda muke bi ba, wannan hanya ta ihunka banza kururuwarka wofi kenan.
Khaleey ta kalle ni fuskarta fall cike da murmushi tace, "yawwa kawata mun karaso fa." Kallo mai cike da alamar tambaya nayi mata, ganin Ummanmu na kokarin fakin wajen wani dankareren iccen kuka yasa na tabbatar da mun iso din. To ina ne nan muka zo? Yawwa ku fita muje, kun san idan sha biyu tayi Ba a samun Malam Dogo.
Wani irin tashin hankali ya rikito min wanda ya haddasa min gurbacewar ciki da karuwar gudun bugawar zuciya. Bala’e! Na fada a zahirance yayin da nake kokarin ficewa don neman wajen da zan juye lalurar da bagiren da muka zo ya haddasa min.
Gudawa nake ji Khaleey, na fada lokacin da nayi nisa cikin duhuwar shukoki. Khaleey ta kwashe da dariya, gaskiya Bebi ban taba ganin matsoraci kamar ki ba, haba don Allah ta fada tana miko min goran ruwan roba.
Tsarakake jikina na yi na tashi. Ummanmu na fada ina karasawa inda suke tsaye. Yawwa muje tace ba tare da ta tsaya jin bahasin lalurata ba.
Wani wawakeken kogon kuka muka kutsa kai a ciki. Tamkar wani birnin shaidanu haka aka kawata shi da wasu irin kananun kwarangal iri-iri wasu sun yi kama da na mutane wasu ko sai dai a saka su cikin rukunin wasu tsuntsaye ko kananun dabbabi. Babu kowwa a wajen sai tarkacen da na kira su kayan tsafi.
Zuciyata na ta faman bugawa fat-fat tamkar zata tsinke, sai rarraba idanu nake tamkar an kai akuya mahauta. Wurin zama muka nemarwa kanmu. Na yi tsumi su ko su Ummanmu ko a jikinsu.
Dariyar da ta cika kunnena ita ta saka ni suman zaune, cikin karaji naji an ce barkan ku da zuwa wajen Malam Dogo… Da sauri na dago kaina ina karewa kazamin mutumin kallo wanda nisa da Allah da munin aiki ya canza kamannin shi ya koma tamkar wata dabba, amma ya kira kan shi da Malam Dogo.
Za a iya kiran shi ƙazami da duk ma'anar ƙazanta kayan jikin shi da gani sun ɗauki lokaci mai tsayi ba wanki, haƙoran shi sun yi jajir tamkar danyen gauta, tsami da warin jikin shi duk ya gauraye wurin.
Barka da zuwa ya sake fada cikin muryar shi mai kama da kukan gardamammen injin markade.
Ummanmu ta gyara zama har da wani gyaran murya, "Malam Dogo barka da wannan lokaci"
"Yawwa barkanmu kadai"
"Ya kuke ya al'amurran ke tafiya?"
"Lafiya ƙalau Malam Dogo, babu wata matsala".
"Yawwa d kyau, komai daidai"
Ummanmu ta sake tankwashe kafa, "Malam Dogo kamar yanda muka saba wannan diyata ce Bebi na kawo maka, ita din sabon aure ce bi ma'ana dai ita din amaryace, na kawo ta domin ka kafata kamar kaffafiyar kusa a cikin danyen katako ka kafata ta zauna daran-dam a gidanta, sannan da baƙar mallaka irin wacce ka saba kayi mata ta koma sai ita, ita daya, ina nufin ita daya a gidanta Malam Dogo kamar dai yanda ka saba…"
"Yi shuru ba sai kin ida bayani ba, na ji komai na gane komai na fahimci komai."
"Bebi kin mallaki Hamza, Hamza ya zama naki sai yanda kika yi da shi, ko uwa ko ubansa ba zasu shiga gabanki a gare shi ba Bebi…"
Jinjina kai nayi, to to to Malam Dogo godiya nake, Allah ya bada…
"Ameen ya faɗa cikin mummunar muryar shi."
Huru hanci yayi kamar na bajimin sa ya ce, "Da kyau Bebi."
Wani kullin maganin da ban san daga ina yake ba ya fado bisa jikina. Zabura nayi tare da neman hanyar guduwa, Ummanmu ta dankwafar da ni, tare da fadin Bebi me yasa kike haka kamar wata karamar yarinya.
Numfashi na sauke tabbas a ranar naga abinda ko a mafarki ban taba hasaso shi ba.
Kasake nayi ina sauraren bayanin da ya dauko yi min. “Wannan maganin ki samo ƙarangiyar kusa, da tsamiyar ƙasa sai ki hade da maganin wuri ɗaya, sai ki datsi gashin da ke saman mararki, da kuma gashin da ke saman goshin ki wato gashin ki na ƙarshe ki hade su ki kone kurmus, idan kin kone su ki hade da maganin ki dake su lukwi sai ki zuba a cikin abin shan sa, idan yasha tabbas kin mallake shi fiye da yanda kike so."
Wani abun da ban san ko meye ba ya miko ma Ummanmu "gashi a binne shi cikin kasa tabbas Hamza ba zai sake yin komai ba sai da izinin Bebi, ki je ki shimfida kujerar mulkinki zaki samu dukkan abinda kike so Bebi.”
"Godiya muke Malam Dogo" Ummanmu ta fada.
Khaleey ya faɗa yana maida dubansa kan Khaleey. Wata tsokar nama kwaya daya tal ya tillo gashi. Ki saka ta a cikin gabanki, ta gauraya da jinin al’adarki ki saka ta karfe sha biyun dare ki kwanta barci idan uku na dare yayi ki cire ki hada da sauran naman kasuwa ki yi ma Jibrilu farfesu tabbassss…. Jibrilu ko iyayensa ba zai sake tunawa da su ba zaki aure shi har ki mallake dukiyarsa gaba daya babu wanda ya isa ya daga maki yatsa."
Godiya muke Malam Dogo…
Ku tashi ku tafi. Ummanmu tayi saurin surar jakata ta aje kudin da na saka a jakata baki daya.
A hanzarce muka bar cikin kogon, ina ta juye juye ina kallon wani katangalallen gidan kasa haɗe da kara inda nake tsammanin nan ne gidan Malam Dogo.
Mota muka shiga muka kama hanyar gida. Tamkar zan fasa kuka nace wannan wane irin abu ne Ummanmu? Dafa ni tayi, ki kwantar da hankalinki Bebi, kina tunanin cewa dukkan mutanen da kike gani sun taka wasu matsayai da mukamai a banza suke samun su? Kina tunanin matayen da suke fada aji a gidajen su daga ruwa sai kuka suke yi? To ki bar wannan zancen ki aje wannan tunanin ke karamar yarinya ce shiyasa baki san haka ba, amma kina da burin mallakar abin duniya har ki zama wani abu nasan ba ki san ya ake ba shiyasa na share maki hanya kamar yanda na fada maki zan yi maki tun ranar da kika fara ziyartar gidana. Kin ga wadannan su ne madogarata, sune tubalin biyan bukatata ba wani jinkiri.
Numfashi na furzar amma Ummanmu kazantar da ke jikina zan saka mashi a ruwan sha yasha? Uhmm. Baki ji abinda aka fadawa kawarki Khaleey bane? To bari ki ji wannan ba komai bane, abinda yasa aka ce kiyi haka… ita mace sirri ne da ita, duk aikin da aka yi aka hada da wani abu na jikinta... Uhmmmm, gama hawa ne ba lallai nan kusa ya kare ba, yana daukar lokaci mai tsayi. Don haka ko iyayen Hamza sun farga sun yi kokarin karyawa to fa ba zai karyu ba, don an hada da wani abu na jikinki sirrin kenan. Kin ganni nan da zan bude miki jikina zaki ga yanka iri-iri wanda nake adana sirrikana da duk irin mallakar da nake so, tun ina kankanuwata har ta kai ni a matakin da nake kai a yanzu.
Yanzu Hamza naki ne sai dai ki je ke daya ki sha sharafinki ki kafa kujerar mulkinki ki kawata fadar ki, nan da dan lokaci kin koma a top class kar ki sha mamakin sunan kamfanin Hamza ya tashi daga El-Ladan ya koma Bebi Enterprices.
Kar ki wasa da maganin nan, ki aikata shi yanda Malam Dogo ya faɗa maki.
Jinjina kai nayi ina ta sauraren ta.
Har muka isa tana ƙara kora min bayani, ban tsaya gidan ko kaɗan ba na nufi gidana kimanin ƙarfe biyu na azahar.
Ta ku mai ƙaunar ganin farin cikin ku, Fatima Muhammad Sani AKA Fantah Ku Kasance cikin ƙoshin lafiya.
TIKITIN WUTA
By Fatima Fantah
Sh 17
Ban tsaya gidansu Khaleey ko kadan ba na nufi gidana a lokacin kimanin karfe biyu na azahar. A wannan karon ma ban samu Hamza ya dawo ba duk da ba al'adar shi ba ce dawowa a irin lokacin amma idan na fita ba da izinin shi ba ji nake kamar da na sa kai falona zan gan shi cikin gidan.
Ganin ba kowwa yasa kai tsaye nayi falona ina kara gyara rikon jikkar hannuna.
Mai da ƙofar dakin nayi na rufe na koma kan kujera na zauna daɓas jikina cikin kasala kamar na nome gandun sarki.
Wata irin ajiyar zuciya na sauke tare da saurin dafe sashen zuciyata , na yi shuru sai faman raba ido nake kamar wacce ta saci zoben matar sarki. Ko da yake watakila ma wacce ta saci zoben matar sarki sata ta fi ni nutsuwa.
Ajiyar zuciya na sake saukewa na sauke hannuna da ƙyar na buɗe jakata na fiddo maganin da Malam Dogo ya bani. Mene ne ƙarangiyar kusa? Na tambayi kaina. Kafin na nemo amsa wayar Ummanmu ta diro cikin tarho ɗi na.
Tamkar kar in ɗaga amma ba ni da yanda zan yi tamkar dole na daga kiran na kanga a kunne “Bebi gobe Khaleey za ta kawo maki karangiyar kusar nan ki maida hankali ki yi amfani da maganin nan kin ji?” Daga kai nayi kamar tana kallona. "Hello kina ji na ko Bebi" Murya a dusashe na ce "to Ummanmu."
"Yawwa ɗiyata" ta faɗa tare da tsinke wayar.
Zuru nayi ina kallon wayar. Cikin rashin sanin takamaiman mafita ta na fiddo maganin na saka shi a sakon kujera.
A sanyaye na mike na shige bedroom na yi wanka na shirya. Sam na kasa samun nutsuwar da zan fita wajen su Waleeda balle har na taba hira da su. Hakan yasa na yi ta zama cikin falo zuciyata na ta faman tufka da warwara.
Har hamza ya dawo na gaza sakewa, shi ko ganina a wani yanayi yasa sai kokarin faranta mani rai yake yi.
Kashe gari Hamza bai jima da fita ba Khaleey ta kawo min karangiyar kusa kamar yanda Ummanmu tayi min alƙawari. Khaleey ta saka ni a gaba ta datsi gashin gaban kaina cikin rakadi da kara min kaimi ta saka ni na shiga toilet na datso gashin da ke saman marata.
Muna gamawa muka koma bayan gidan muka kona maganin kamar yanda Malam Dogo ya fada.
Khaleey tayi farr da idanu sannan ta fashe da dariya ta ce "mun gama Bebi yanzu muje na taya ki mu yi haɗaɗɗen girki sannan ayi sobo a cikinsa za a zuba mashi maganin kamar yanda Malam ya fada.
Doguwar ajiyar zuciya na sauke na ce to Khaleey. Yawwa kawata naga duk kina ta wani sanyi-sanyi mun yi mun gama fa. Abin dadin ma fa yau tun da asuba Ummanmu ta je ta rufe abin nan da Malam Dogo ya bada don haka saura kiris ki gangare tudun nasarar nan, ki kafa daularki ƙawata Bebi.
Jinjina kai nayi "hakane Khaleey ay ni da Ummanmu sai godiya." Na faɗa wani abu danƙare ƙarkashin zuciyata.
Tare da ita muka yi girki na musamman bayan mun gama na zuba maganin a cikin soɓon. Hannu ta miƙo muka tafa, "Bebi well done" ta fada tana wani irin murmushi.
"Nima kin gani jira nake kawai period dina ya zo, da zaran ya zo zan aikata nawa aikin kin ga shikenan kawata sai dai mu tsikari duniyar mu da bakin allura."
Zaro ido na dan yi "Kai! ai ke na ki lamarin ya grime ma tunanina wallahi. Don ni bama zan iya ba wannan ma kawai ke dai ayi shuru."
Dafa kafadata tayi "Uhmm, Bebi ki bar wannan maganar, yanda Ummanmu ta fada maki mata sirrine damu wallahi duk abinda aka hada shi da jikinmu to an yi an gama ina fada maki tamkar yankan wuƙa, amma dai zaki sha mamaki ay."
"Tooh, Shikenan." Na fada a sanyaye.
Yawwa ni yanzu tafiya zan yi Bebi ni ban zo da niyyar zama ba, amma da naga kina sanyi-sanyi ne kina so ki yi wasa da damar ki shiyasa na tsaya na taimaka miki komai ya tafi daidai, yanzu kuma komai ya zama a kammale don haka kawai zan wuce."
Cikin mamaki nace, "Haba Khaleey ko abincin da muka girka ba zaki ci ba? Mu yi komai tare kuma ki ce zaki tafi, haba don Allah ki ma bar wannan zancen."
"Bebi ba zaki gane ba ne nima akwai abinda nake so na yi a gidan lokaci ya kusa kurewa kuma." Ta faɗa a ƙagauce.
"Shikenan to, nasan hidimomin ki manya ne, gwara ki tafi kar na watsa miki lamarin."
"Yawwa ko ke fa kawata" tana fadar haka muka fice daga kicin din muka nufi falo. Bata tsaya komai ba ta suri Jakarta ta tafi.
_______________________
Bayan na gama shiryawa tsaf Hamza ya dawo kamar ko yaushe cikin nishadi da nuna soyayyar shi gare ni ya shigo sannan da tsabar tarkacen abubuwa wanda yanzu har sun gundire ni.
Yana gama wanka na kawo mishi abincin da muka shirya, cikin jin dadi ya ci abincin shi bai jinkirta ba ya hada da sobon ya sha. Kallona yayi cike da so da kauna yace, "Bebi soɓon nan yayi daɗi sosai sai na bada tukwici."
Murmushin yake nayi domin kuwa tunda na shiga sabgar su Ummanmu na rasa cikakken farin cikin zuci komai jin sa nake bai kai ba a raina.
Cijewa nayi nace "Nagode Honey."
Tun da Hamza ya sha sobon nan abubuwa suka fara canzawa daga fari zuwa baki, Hamza ya zama tamkar wani sokon yaro, ya zama macen na koma namijin, komai na yi shine daidai. Haka nake fita bana ko tambaya tun ina shayin ya dawo ya tarar bana nan har na zama ƴar gari. Na koma naje inda nake so a lokacin da na so, ba tambaya bare neman izini.
A hankali Ummanmu ta bude min hanyoyin zubar da rashin mutunci kala-kala, ta koyar da ni wulaƙanta mijina samfur-samfur. Kamar yanda Ummanmu ta mayar da maza akwatin ɗibar kudi a mallakesu a shaƙi kudinsu, shi kuma auren ba shi da ƙima ko kaɗan balle a darajta shi kawai wani makangi ne da yake mata kariya akan wasu munanan abubuwan da take yi.
Nima a bisa hanyar ta ɗora ni, duk da raunin da na samu na kasa yin koyi da ita ɗari bisa ɗari. Ta gefen Khaleey ko ita ma a lokacin ta yi nasarar auren Jibril baki daya ya baro garin haihuwarsa ya tare birnin kwankwasiyya a wajen Khaleey. Idonsa a rufe ita kaɗai yake gani duk da abin da nake aikatawa na kan ga nawa a ajin koyo na ɗaya na Khaleey ko ya taka matsayin aji na goma.
Iyayen Jibril sun yi har sun gaji, a cewar Khaleey Jibril ya riga ya mallaku sai dai a lahira ya tashi a matsayin dan su amma nan duniya na ta ne ita kaɗai.
Baki ɗaya rayuwarmu muke bisa raɗin kanmu, mun mance da duk wata ƙalallahu ko ƙala rasulu duniya muke bi ita muke so, duk da ni nawa lamarin ya kan samu tasgaro saboda Hamza yana da kula da addini sannan uwa uba mutum ne mai ibada hakan yasa abubuwan surkullen namu basu kama shi yanda ake so.
Muna cikin haka na haifi yarinyata ta farko Ameera, lokacin su Safna da sauran "yanuwa da dangi da suka zo barka da taron suna suka ga irin lalatar da na ke tafkawa, wacce suke ji a waje a wai, amma a wannan taron sunan sun ga tabbas.
Hamza ya zama bawa a wajena ni kuma na kafa kujerar mulki yaransa su Waleeda na tsoro na kamar rai da ajali saboda aƙubar da na ke ɗan-ɗana musu a wasu lokutan.
Safna ta yi min fada hade da nasiha sai dai ni ko kadan ban ma fahimtar ta domin na yi nisan da ba na jin kira.
Basu yi kasa a gwiwa ba suka sanar da Iyayenmu. Baba ya kira ni yayi min faɗa yayi min nasiha da fadar irin halakar da nake ciki, amma sam zuciyata ta kekashe duk wani wa'azi a nan naji shi a nan nake barin shi ko bana ɗaukar ko kalma ɗaya balle nayi amfani da ita.
Hakan ya tilasta ma su Baba da Malam Ladan yin rokon Allah domin ko gidansu sai na ba shi izini yake zuwa, babban abin takaicin gani ƙaramar yarinya wacce shekarunta kadan suka gota ma ishirin kamar yanda Baba yace.
Basu yi sanya ba suka dage da rokon Allah a hankali na fara lura abubuwana sun fara sanyi hakan yasa muka sake yin wani mummunan aikin wanda a lokacin muka kira da babban aiki.
A haka dai hankalin Hamza bai gushe ba kamar lokacin baya, sam abun bai kama shi ba yanda ake so.
Haka muka yi ta gungurawa a cikin sakanni, suka rikide suka zama daƙiƙu, suma suka rikide suka zama sa'o'i, suka juya suka zama kwanaki suka zama makonni har suka zama watanni suka rikide suka zama shekaru.
A cikin shekarun abubuwa da yawa sun faru, ciki har da haihuwar ƴata Hidaya, a haihuwar Hidaya a cikin familyna babu wanda ya zo. Suma family Hamza ganin takaici ya hana su zuwa, domin har yanzu ina murza kambuna kullum bama gajiya da bin Malamai wanda ya dace a jefa su layin bokaye domin basu da banbanci.
Wata rana ina zaune Safna tayi sallama, na yi mamakin ganinta gidana kwarai da gaske, amma sai na share mamaki na na mike tsaye ina kallonta.
"Cikin Gadara na ce Safna me ya kawo ki gidana? Ke da kika ce ba ki sake zuwa inda nake."
Murmushi tayi ta nemi wuri ta zauna. Cikin lumana ta ce “Bebi ina mamakin yanda kika koma, kuma kullum cikin mamaki nake mai tattare da ƙunci da takaici. Ɗabi’a daya tak ta kwadayi ta ja maki shiga cikin wata mummunar rayuwa. Bebi kina tunanin abinda kike wai bazai biki ba…..”
Kafin ta kai karshe na dakatar da ita a hasale.
"Dama a duk lokacin da kika zo gidana nasan wa’azi ya kawo ki, shin ban fada maki ki daina zuwa yi min wani wa’azin ki can ba?"
Murmushin takaici tayi, Bebi duk da nasan cewa ko lahira ba zaki tuhume ni da ban taba tunatar da ke akan hanyar da kika hau ba ta da kyau ba domin tun kafin mu kawo warhaka nake tunatar da ke.
Amma ke "yaruwata ce ina takaicin ganin ki cikin wannan halin na bata da tabewa, shiyasa ko na yi fushi na nesance ki sai wata zuciyar ta saka ni na dawo gare ki, domin nice dolen ki. Kuma zan bi duk wata hanya da ta dace domin mai do ki bisa hanya madaidaiciya, wannan alwashi ne na ɗauka.
Sannan na sani Hamza baya iya rabuwa da ke baya iya sakin ki duk da irin cin kashin da kike mashi, nasan da hakan amma bari kiji abinda baki sani ba Hamza aure zaya yi, kamar yanda kike fada kin riga kin kafa daula to wata itama za ta shi go cikin fadar ki akan idon ki zata kafa daular ta. Ke kuma lokacin taki daular zata ɓare ki koma ƙasa cikin ƙasƙanci.
Kin san wani abu, ba kowwa ba ce face Aminatun gidan Malam Namadi yarinya ce mai ambaton Allah mai zikirori da karatun Alkur'ani mai girma, ina mai tabbatar maki duk wani tsafe-tsafen ku da tsubbace-tsubbacen ku ba zai hana ayi auren nan ba da izinin Allah.
Tunda ta sako zancen aure na yi suman tsaye.
Aure… Hamza zai yi aure ta ya Hamza zai yi aure alhali Shamaki ya tabbatar min da Hamza ba zai taba ko da taga yin aure balle har ya nemi auren?
Kallon Safna nayi a harzuƙe nace, "karya ne Safna ba zai taba yiyuwa ba."
Murmushi tayi "Bebi kenan za ki sha mamaki zaki kwan-kwaɗi ruwan mamaki ƙwarai da gaske kuma nan ba jimawa zaki neme ni, ina mai tabbatar maki zaki zo ki neme ni Bebi."
Tana faɗar haka ta juya ta bar ni tsaye sororo tamkar an dasa ita ce.
Ta ku mai ƙaunar ganin farin cikin ku, Fatima Muhammad Sani Fantah Ku Kasance cikin ƙoshin lafiya.
[7/21, 9:19 PM] The Elequent Writer: *TIKITIN WUTA*
*_By Fatima Fantah_*
***
*_Sh 18_*
Tana gama faɗar haka ta bar ni tsaye a wurin tamkar an dasa icce. Kan kujera na faɗa sharaf, da sauri numfashina ke tafiya tamkar wacce tayi gudun ceton rai. Dole na ziyarci gidan Ummanmu yanzu ba sai an jima ba. Na faɗa da ƙarfi ina ɗora hannuna kan ƙirjina.
Miƙewa nayi da sauri na shige bedroom na saka Hijabi na dauki makullin motata na fice a gidan.
Ban samu Ummanmu ba sai dai Hajiya Ƴar Doss da Nana.
"Nana ina Ummanmu?" Na tambaye ta ina neman wurin zama. "Bata nan ta fada tana kallona, ya dai lafiya na ganki a hargitse."
"Nana ina cikin tashin hankali domin kuwa Hamza aure zai yi."
"Aure?" Ta fada tana tashi daga kwancen da take. "Aure Nana."
Na bata amsa a taƙaice.
"Nana anya aikin Shamaki yana ci kuwa? Aikin banza aikin wofi kawai yake yi, domin kuwa baki daya al’amurrana sai cakudewa suke". Dafe kaina nayi "ina cikin tashin hankali Nana." Na ƙare maganar wasu hawayen tashin hankali na gangarowwa daga kwarmin idona.
Hajiya Ƴar Doss ta dafa ni, Haba Bebi, ki kwantar da hankalinki mana, mijinkin ne karfin jinine da shi duk abinda ake yi kina gani baya kama shi yanda ake so sai dai rabi da rabi. Ki duba ki ga mijin Nana, har mage da wuri take fa kuma ya sani amma tak baya iya furtawa, ga Khaleey can har yau Jibril ya kasa magana akan duk dukiyar da take wawura a wajen shi. Ga beauty nan itama abinta zan-zan amma ke naki mijin sai dai abin ya dan kama shi kadan shima sai an yi aiki na tsiya. Don haka kada ki zargi Shamaki domin tunda aka binne maganar auren baban Mama da wacce zai aura wallahi har yau ko zancen bai tada ba, a karshe ma kayan auren da ya kai da suka matsa mishi sai yaje cewa yayi ya bar musu kyauta."
Don haka ki kwanrtar da hankalinki ki tashi muje wajen Malam Dogo idan na Shamaki bai karbu ba ai kin san na Malam Dogo iyaka ne.
Jinjina kai nayi to mu je yanzu motana akwai mai a ciki kawai mu tafi yanzu. Nana da ke kwance tace, muje don Allah ku sauke ni bakin ni’ima Zubair na can na ce da ya zo ya dauke ni amma yanzu kawai ku aje ni da ku bar ni nan ni daya.
Murmushi na kalato nace kai Nana wallahi ke guba ce da aurenki kina bin wasu mazan, mage da wuri wallahi bana iyawa.
Tabe baki tayi, ke ni raba ni da wancen shashashan tun da naga mun cinye kudin shi na ji ban iyawa don haka shi ne na koma mage da wurin don ni nayi imani da kudi bana iya rayuwa da su kalilan. Don haka muje ki aje ni can.
Yawwa Hajiyar Doss, ki ce ma Malam Dogo ya maganar BB mun zaku fa Salisu ya sawwake mata naji aikin shuru, ko da yake ba ma sai an fada mashi ba gobe zamu zo.
To yayi Hajiya yar Doss ta fada tana shiga motata.
Ba mu jima ba muka isa wajen Malam Dogo kamar ko yaushe yayi mana alkawarin Hamza ba zai yi auren nan ba kai kace shi din shi ke sawa shi ke hanawa.
Raina fess muka dawo cikin Kano, na sauke Hajiya Yar Doss a gidanta na nufi hanyar gidana.
Har na kusa isa nayi kwana zuwa gidan Safna. Fakin nayi na fita cikin isa da ƙasaita. Ina isa tsakiyar falon ta na tarar da yaranta Nasir da Habib. Ganina yasa suka ruga suna kiranta, Ammi ga Anty Bebi.
Bin su nayi da harara na carke ina jiran Safna. Fuskarta dauke da fara’a ta shigo ku je daki ta faɗa tana tura yaran can cikin gidan.
Kallona tayi tana ƙara faɗaɗa fuskarta da murmushi. "Bebi har kin zo dama na fada maki za ki neme ni."
Wata irin tsawa na daka mata. "Dallah Malama yi min shuru, wai da kike cewa zan zo gidanki zan neme ki na zo na yi me to? Har akwai abinda zan zo na yi a wajen ki? Ke kan ki kin san ko can baya bama jituwa balle yanzu...
Dago idonta tayi da ya cika da kwalla, wani murmushi tayi ta ce, "da kika sauya ba… Da kika sauya Bebi ki ka shigo da halayen da bamu san ki da su ba mun kasa jituwa saboda halayen mu basu yi daidai ba. Ke daya jal kin baude kin kangare kin like ma mutanen da kacokam ma ba masoyanki bane. Ke Safna! Yanda na fadi ke din da karfi hakan ta mayar min da martini. Na fada din ba masoyan ki bane makiyanki ne Bebi, domin kuwa duk wanda ya nesanta ka da Allah to ba masoyinka ba ne babban maƙiyinka ne.
Ba zan manta ba, tun lokacin da kika ɓullo da sabbin halaye a cikin rayuwarki, Baba ya ce "yana tsoron halayen da kika shigo da su, wanda be san me zasu haifarwa goben ki ba, gashi ko goben kin tayi muni tayi wari sai doyi take yi amma kin kasa ganewa… balle ki dawo hayyacinki ki ƙamsasar da ita Bebi.
Safna! Na faɗa tamkar na haɗiye ta.
Bebi! Ta faɗa tana kallona ido cikin ido
Wani irin wawan tsaki na ja a hasale nace, "na ji Safna, amma zan fada maki ne ba Hafixa ba ko wacece Hamza zai auro na fi karfinta wallahi, dama na zo ne kawai don in isar maki da wannan sakon."
Uhmmm! Bebi in kaya ne ke ka kai su. Ta fada tana min wani kallon da ya ƙarasa harzuƙa ni.
Tasowa nayi tamkar na kai mata duka, wallahi na faɗa maki na fi karfin su ke ma je ki sanar da su, ni ɗaya ce matar Hamza har duniyar nan ta naɗe Safna!"
Murmushin takaici tayi cikin salon rainin wayo, ta ce "na ji don Allah ki tafi bana son hankalin yarana ya dawo kanki don bana son su ji irin wadannan kazaman kalaman naki ya gurbata masu kwakwalwa."
"Iyyeh, da kyau Safna don na zo gidanki kike da ikon fada min haka, to bari kiji na fi karfin wulakanci a wanann kurkukun gidan naki."
"Naji ki je don Allah, ay na ce ki tafi ko, ti ki je Allah ya raka taki gona."
Ficewa na yi fuuuu, rashin mayar da martani maganganun Safna na kona min rai.
Cikin takaici da tunanin wane irin kallo ma take min na isa gida.
Ina shiga na tarar su Waleeda da Yasir suna sallah su ko Ameera da Hidaya sun yi zaune suna ta kallon TV, sun saba kamar yanda nake sarauniya a gidan to babu wanda ya isa ya sa su ko ya hana su a cikin gidan. Ko Hamza mahaifin su ba sa shakka balle yayunsu su Waleeda.
Wuce su nayi kawai na shige bedroom.
Sam na kasa fahimtar ma me nake ji a kaina har wucewar la'asar na gaza fitowwa, sai wajen Magrib na fito na hada sallolin Magrib da isha din domin ibada wuya take min sosan gaske tun da na dulmiya a cikin rayuwar da naga halakarta a zahiri cikin barcina.
Hamza ya shigo bayan sallar magriba ya wuce dakinshi. Ina gama abinda na ke na wuce dakin shi kamar yanda na saba, ba arziki domin ban ruhu da rigar mutunci ba. Na ce "Hamza wai da gaske aure za ka yi.?
Juyowa yayi ya kalle ni sama da ƙasa, wani lokaci in abin ya sake shi sai yayi ta mamakin halayen Bebi. Amma yana sonta bai taɓa gazawa a yin addu'ar Allah ya shirye ta ba.
Nisawa yayi yace, "Bebi kenan aure zan yi."
Uhmm. Dama na san su Alhaji Sule sai sun hure maka kunne ka yi auren nan, ai dama sun tsane ni.
To bari kaji Hamza, "ka sani babu wata macen da zaka kawo gidannan babu wata macen da wata mace irina ta haifa da zan zauna da ita ka ji na gaya maka."
Ina fadar haka na juya na fice daga ɗakin. Kaɗa kai yayi zuciyar shi cike da mamakin Bebi.
Komawa nayi dakina na kwanta, kaina yana ta sarawa, kwanciya nayi kan gado na kwanta ina ta faman tunani a haka bacci yayi awon gaba da ni.
Tun da safe wayar Ummanmu ta shigo wayata, cikin son jin me ya faru na sake zayyana mata batun auren Hamza. Fada ta shiga yi tare da jaddada mani babu wata macen da Hamza zaya aura domin mu bamu zama da kishiya. Naji dadi a raina duk da a kasan raina na kasa samun nutsuwa.
Muna gama wayar na shirya na tafi gidan Ummanmu a can na samu Khaleey sannan muka wuce wajen Shamaki.
Bata rai na yi da jin bukatun da ya bijiro min da su wanda idan na cika su tabbas Hamza ba zai taba aure ba.
A hankali na ce "Shamaki gaskiya ba zan iya aikata abinda ka fada min ba, tun ina kankanuwa ta ban taba aikata zina ba yanzu kuma ba zan fara ba.
Ummanmu ta nisa ta ce. "Bebi yanzu kin ga aikin ki zai iya baci kin san dai yanda abin nan yake." Kada kai nayi "kawai bara na koma wajen Malam Dogo Ummanmu hakan zai fi min."
A bayyane Ummanmu ta nuna min bacin ranta, ban damu ba na tashi nayi tafiyata. Gidan Hajiya Ƴar Doss na tafi.
Cikin salo tace Bebi, kin san ni Baban Mama be san ina wannan sabgar ba kuma ba na so ya sani. Abinda za a yi ki bari gobe da karfe tara sai mu koma wajen Malam Dogo ya bamu abinda yace din. Ina mai tabbatar maki an gama wani batun auren Hamza.
Nisawa nayi nace to. Allah ya kaimu lafiya. Ameen ta fada.
Bara na koma gida saboda kaina ciwo yake Hajiya tun jiya.
Allah ya sauke Bebi. Sai goben mun yi waya.
Gida na koma haka nan na wuni sam raina babu dadi. Zuciyata ta cika da takaici da bakin ciki wanda na rasa ma ainufin ko na mene ne.
Ina zaune bayan sallar isha Hamza ya kira wayata. Ban amsa ba bayan na mila na sha iska na tafi dakin shi.
Ban iya yin sallama ba na sa kai cikin bedroom din shi.
Tsaye nayi ƙerere, Hamza na ga kiranka, na san da dalili shiyasa na zo.
Kallona yayi, to ki zauna mana ko daga tsaye zamu yi maganar. Ban musa ba na zauna gefen gado.
Wani murmushi yayi, a hankali cikin tattausar muryar shi yace, "Bebi waya fada maki maganar zan yi aure.?"
"Wacce ka aiko ta fada min." Na bashi amsa cikin gadara.
"Uhmm Bebi kenan. Idan ma nayi aure ai kece kika zama silar da zan yi aure, saboda kin sani ke kanki Bebi rabon ki da zuwa inda nake kin manta balle ayi batun sauke hakkina da ya rayata a wuyanki. Bebi duk abinda kike ina sane da shi duk abinda kike aikatawa ina sane da shi..."
Wani irin tsoki na ja na mike dama iya kiran da kake min kenan? To ka je kayi ta sani din in ka sani sai me? Sai aka yi me? Wani tsakin na sake yi na fice na tafi dakina.
Wanka na sake ina ta faman tunane-tunane bayan na gama na saka kayan bacci na fita na leka dakin su Waleeda. Ameera da Hidaya suke da gado kamar yanda na tsara Walida da Yasir da Kubra suna kwanciya kasa kan katifa.
Watsa musu harara nayi nace me ya hana har yanzu ba ku yi bacci ba? Hidaya ta shagwabe tace Mommy kallo muke yi.
Okay to a yi bacci hakanan saboda makaranta. Juyawa nayi wajen Waleeda "ke fa kin min zuru da idonki kaman na mujiya." Cikin rawar jiki tayi saurin rufe fuskarta da blanket.
Kashe hasken dakin nayi na rufe kofar na koma dakina.
Kan gadona na kwanta tare da duba sahar wats app na dan tattauna a group din mu na Kasaitattun Mata, group dinmu ne wanda Ummanmu ta bude shi kuma take jagorantar shi.
A takaice kai tsaye a cikinmu jama'ar Ummanmu babu wata macen kwarai a cikinmu. Bayan mun kara tattaunawa naja blanket na fara sheka barci ba tare da biya ko basmala ba domin rokon kariyar Allah a baccin da ba ni da tabbacin tashi ko kuma na tafi kenan.
Wani irin kuka na fashe da shi na duba agogo har karfe goma na safe ta kawo jiki. Dafe kaina nayi da ke azababben ciwo tare da sakin wata irin ajiyar zuciya.
Bazan taba mantawa da wannan mafarki ba, mafarkin da ya nuna min makomata, kamar yanda Safna take yawan fada min ina cikin halaka ashe babu musu a zancenta ina cikin halaka bayyananniya da ni da mutanen da na saka abin koyi a rayuwata.
Wayata ta sake daukar kukan neman agaji a wannan karon ma ban dubeta ba domin nasan zancen, Hajiya Yar Doss ce.
Na yi shuru na dafe kaina, to yanzu ina ma zan je? Ko na tafi wajen Baba? Ko wajen Safna za ni? Wa zan nema ne? Ko yaya wasu kalmomin da zasu rage min fargabar da nake ciki nake nema. Ya nuna min yanda zan yi ko na samu na aikata wani kyakkyawan aikin alkhairin.
Mikewa na yi tamkar iska zata kwashe ni na nufi dakin Hamza. Shirye yake tsaff cikin shirinshi na tafiya kasuwa.
Wani irin kallo yayi min mai cike da alamar tambaya. Nima tsuru nayi ina kallon kyakkyawar fuskar shi. Sannu ya ce, yanzun nan nake cewa zan leƙa na ga ya jikin naki? Kin ji sauƙi ko?
Wani irin kuka ya kwace min da sauri na durkusa kan gwiwowina “Hamza don Allah, don girman Muhammadu Manzon Allah ka yafe mani… Ka yafe mani Hamza…”
Ta ku mai ƙaunar ganin farin cikin ku, Fatima Muhammad Sani Fantah Ku Kasance cikin ƙoshin lafiya.
TIKITIN WUTA
By Fatima Fantah ✍️
Sh 19
Hannuwansa yasa ya ɗago ni daga durƙushen da nake. Kallo na yake irin kallon da na kasa fassarawa, kasa nayi da idanuwana domin a halin yanzu Hamza wani irin kwarjini yake yi min. A hankali cikin dusasshiyar muryata da tuni kuka ya dakushe na maimaita “ka yafe min Hamza ka yafe min duk abinda na yi maka don Allah...”
Kallona yake kaman sabuwar halitta a hankali ya ce "Bebi duk abinda kika aikata a gare ni ina jin shi a matsayin kaddarata, a rubuce yake hakan zai same ni, kuma sai ya faru da ni walau ki zama sanadi ko kuma wani can daban ya zama sabab din. Don haka ko sau ɗaya ban riƙe ki a raina ba, na yafe maki duniya da lahira Allah ya yafe mana baki ɗaya. Ya ƙare maganar cikin wani sauti mai sanyi.
Tamkar an feso min ruwan kankara kalaman shi suka dira cikin kunnuwana wani sabon kuka na fashe da shi.
"Nagode Hamza, nagode Hamza Allah ya saka maka da alkairi.” Hannuwansa biyu yasa ya rungumeni jikinsa. Tun bayan farkawata zuciyata ba ta daina matsananciyar bugawa ba tamkar ana buga ganga kasancewata jikin Hamza yasa na soma jin wata nutsuwa na dirar mani. A hankali na ci gaba da sauke ajiyar zuciya wata na bin wata.
Sai da ya tabbatar bugun zuciyata ya daidaita ya dago ni daga jikinsa. Sam na kasa hada ido da shi sai ajiyar zuciya da nake saukewa a hankali. Ɗago fuskata yayi "Bebi." Ya kira sunana.
"Don Allah ka rika kirana Zainab bana son sunan Bebi..."
"Shikenan Zainab."
"Ina so zan bika ka aje ni gidan Safna don Allah." Na kare maganar ina sharce hawayen da suke ta faman sintiri kan fuskata.
"Hakan zai sama maki nutsuwa?" Jinjina kai na yi alamun eh.
Ƙuri yayi yana kallona, ko dai na zauna a gidan? Ya sake tambayata.
"A’a ina so naje gidanta…"
"Shikenan. Muje to."
Tare muka fita yana gaba ina biye har muka isa jikin motarsa. Shiga yayi ya bude min kofar gaba na shiga. Zama na yi tare da buga uban tagumi. Sedai ya juyo ya kalle ni sai kuma ya mayar da hankalinsa kan tuƙin da yake.
Tunani yake, Allah shi ya barwa kan shi sanin me ya faru da Bebi wanda baya ko shakka ko mene ne ya same ta ne a cikin barci.
"Mun iso" na ji ya fada. Firgigi nayi bakina na rawa nace "to, toh, na kare maganar a firgice." Budewa nayi na tafi, har na yi takun da zai kai biyar na juyo. "Allah ya kiyaye Allah ya tsare Abban Ameera."
Ameen ya fada yana ta ci gaba da kallona.
Ya daɗe bai tafi ba, tamkar ya jawo hannunta ta fada masa ai nufin halin da take ciki, amma tunda Safna ta bukata watakil ganinta ne zai saka ta nutsuwa.
Tayar da motar yayi ya tafi zuciyarsa cike da tunani da tambayoyi kala-kala.
A hankali nake tafiya cikin duniyar da na yi bankwana da ita. Ashe ina da rabon dawowa na aikata alkhairin da na ke ta roko a cikin mafarki a dawo da ni in aikata.
Sallama na yi cikin falon Safna. Tana zaune gaban TV kira’ar karatun Ahmad Suleiman na fitowwa daga masarrafin sautin TV din, muryoyin su sun hadu biyu suna rera karatun a tare.
Da sauri ta mike jikinta na rawa ta karaso inda nake, Bebi lafiya? Hamza sakin ki yayi ne? Ko dukanki yayi? Kada kai nake ina kara kuka da zubar da hawaye. Bebi to me ya faru?
Wata irin shesshekar kuka taci karfina na fada jikinta a sanyaye.
Shuru tayi tana sauraren kukana. A hankali take ta bani hakuri tare da kalaman da suke sanyayar da zuciya. Cikin kukan na ce "Safna ki yafe min ki yafe min don Allah."
Kada kai tayi Bebi ni ban taba rike ki da komai ba a raina daidai da rana daya ban rike ki ba, hasali ma kullum shiriya nake roka maki a wurin Allah. Don Allah ki nutsu ki faɗa min me ya faru.
Nagode Safna Allah ya saka maki da alkhairi.
Nisawa tayi tace ki daina kukan haka ki fada min me ya faru.
A hankali nace "ba komai kuma ba abinda Hamza yayi min, kawai wani mummunan mafarki nayi Safna, wani irin mafarki ne nayi Safna….. Kuka yaci karfina na kasa ƙarasa maganar. Kaɗa kai tayi, "Bebi ki daina kuka haka, shi mafarki ba gaskiya bane wanin shi ishara ne wani ko shirme ne wani kuma ma sheɗanun aljanu ne ke birkita ma mutum ƙwaƙwalwa."
Nisawa nayi "nawa duk ya wuce wannan lissafin Safna, sam ba shirme bane ba kuma shaiɗanun aljanu ba ne."
"Ikon Allah ta faɗa a dame. Abinda za a yi ki tashi muje gun Malamin Islamiyyar mu yasan fassarar mafarki sosai zai fassara maki mafarkin ki. Nasan Insha Allahu za ki samu nutsuwa."
"Kada kai nayi, bana bukatar fassara Safna. A’ah Bebi kar ki gardama, ki tashi muje."
Waya ta dauko ta kira Kabeer mijinta ta nemi izinin fita, nima murya shake nace kira Hamza ki fada mashi zamu je. Kallona tayi irin kallon mamaki ban damu ba ta kira shi din, ki gaya mashi nace. Fada mashi tayi yace ba komai sai mun dawo.
Wanke fuskata na ƙara yi muka fita ba nisa daga gidanta zuwa Islamiyyar, mun ci sa'a malamin yana Islamiyyar bai kai ga tafiya ba. Safna ta gaishe shi tare da yi mashi bayanin abinda ya kawo mu a takaice.
Ganin halin da nake ciki ya sa ya bude dan ofis din shi muka zauna.
Kallona ya yi, "baiwar Allah wane irin mafarki ne kika yi haka?"
Sauke ajiyar zuciya nayi, murya shake nace. "Malam daga kwanciya barci na farka na ganni a cikin kabarina… Babu wani alamu da ke nuna ba a mace nake ba… Abinda nake iya fada a mafarki na zayyana mashi cikin kukan da na kasa dakatarwa.
"Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Ya fada yana jinjina lamarin. Ikon Allah wannan mafarki naki aya ce a gare ki da sauran ma dukkan wanda yaji labarinsa.
Amma Malama Bebi ki godewa Allah, wanda yake shiryar da wanda ya so, ya halakar da wanda ya so. Ki gode masa da ya tabo ki daga hanyar da kika fada ta halaka. Da kin mutu a haka, ko a cikin mafarkinki an nuna maki ba mai taimakonki ko da da addu'a ne, an nuna maki iyayenki na fushi da ke, an nuna maki tarbiyyar yayanki ba a daidai take ba, an nuna maki duk abinda kike ba a kan daidai kike ba.
Amma ki godewa Allah, Allah ne ya taimake ki domin kuwa da kin bar duniya kina aikata wannan halayen da dabi’un naki da kin fada a cikin wannan makomar da Allah ya nuna maki a cikin mafarki.
Kuma tabbas akwai rayuwa bayan mutuwa, wacce bawa zai yi kafin ranar tashin alƙiyama, wannan itace rayuwar barzahu kuma bawa zai fuskanceta da fassara aikin da ya aikata kamar fassarar kalmomin turanci wato fassarar kalma da kalma. Wannan rayuwa Allah ya boyeta sai wasu bayi masu imani Allah ya kimsa ma saninta daidaiku a cikin bayinsa yardaddu. Don haka ki godewa rabbil alameen domin yana son ki da rahama, gashi a yanzu kin dawo bisa turba ta gaskiya.
Yawan kukana ya ƙaru cikin matsananciyar nadama nake wacce bata misaltuwa.
Malama Bebi, ki daina kuka kin ji. Allah mai karbar tubar bawansa ne, ki yi tuba irin tuban wanda ba zai sake komawa ga aikata wannan zunubin da yake aikatawa ba . Ki je kiyi biyayya ga mijinki domin shi miji ba abin rainawa ba ne ba abin wulaƙantawa ko cin mutunci ba ne. Mijin abun mutuntuwa da darajtawa ne, kuma umarni ne na Allah ba son ran wani ba ne. Wata rana an tambayi Manzon Allah S. Wa yafi haƙƙi akan mace. Sai yace mijinta. Sai aka ce wa yafi haƙƙi akan namiji? Sai yace mahaifiyarsa. Shi namiji kin ga mahaifiyarsa ita tafi haƙƙi a kan sa. Amma ita mace, mijinta shine yafi haƙƙi a kanta fiye da ma iyayenta. A wani wuri kuma Manzon Allah S. Yace, da za ayi umarni ayi ma wani sujuda bayan Allah S.W.T da an bawa mace umarni tayi wa mijinta sujada. Kin ga kenan shi miji haƙƙinsa ba ƙarami bane kan matarsa, musamman wanda ya tsare maki naki haƙƙoƙin. Don haka ki je ki gyara tsakanin ki da shi, ki gyara duk wata ɓarnar da kika aikata a gare shi. Gyara tsakanin ki da shi gyara tsakanin ki da ubangijinki ne. Domin da gaske ne aljannar ki na ƙarƙashin ƙafarsa.
Su kuma wadannan mutanen ki rabu da su baki daya, domin halakakku ne ɓatattu, domin duk wanda ya yarda da aikin bokaye ko mutanen da suka rigar malanta suna bokanci wallahi yayi shirka, domin babu mai sa wa ko hanawa sai Allah.
Ki duba lamarin fa, ita wannan matar da kika fada itace ta saka ki a cikin wannan ɓatar baki ganta a mafarkinki ba, shin me wannan ke nufi? Amsar ita ce ta fada cikin bayin da Allah yayi ma sakin talala a wannan duniyar, bayinsa wanda ya kyale su su sha sharafinsu a duniyar nan wacce bata kai darajar fiffiken sauro a wajen shi ba, amma a lahira kuma yayi musu tanadi na azaba irin wanda wani a cikin bayin sa bai taɓa hasasowwa ba kamar yanda ya faɗa a cikin al'ƙur'ani mai girma.
Don haka idan kina ganin zasu karɓi wa'azi ki musu nasiha sai ki yi musu, amma ko sun karɓi nasihar tasu ki rabu da su. Sannan ki daina kukan nan ki shagala wajen bautar ubangiji da gyara abinda kika ɓata, ki yawaita karatun Ƙur'ani da sauraren wa'azin Malamai, domin tunatarwa tana amfanar mumini. Kin ji ko.
Jinjina kai nayi, nagode Malam na faɗa.
Yawwa zaku iya tafiya Safna. Ita ma Safna kuka take domin sauraren labarin mafarkina ya rikita ta. Ba komai ya faɗa.
Miƙewa muka yi a sanyaye domin jin labarin mafarkina ya saka musu wani tsoron Allah.
Har muka isa gida ba wanda yayi magana kowa da abinda yake tunani.
Safna ta zaunar da ni kan kujera ta ɗauko min ruwa masu sanyi. Kada kai nayi domin sam bana buƙatar komai.
Aje ruwan tayi ta fuskance ni, "Bebi ki daina kuka haka, Alhmdlillah kin ga Allah ya kawo maki shiriya."
"Bebi kullum addu'a nake Allah ya shiryar da ke, domin ke ƴaruwata ce jinina yana yawo a jininki haka jininki yana yawo a jinina. Ko yaushe addu'ata Allah ya shirye ki ya nuna maki gaskiya, da ni da su Baba wannan shine fatanmu."
"Gashi Allah ya karɓa mana adu'armu. Yanzu ki godewa Allah ki je ki ɗabbaka abinda Malam ya faɗa maki, wannan kyakkyawar dama ce da Allah ya baki, ni kaina wannan mafarkin naki ya ƙara farkar da ni daga wasu abubuwan da na shagala da su. Don haka ki daina kuka, kin ji ko?"
Jinjina kai nayi. Na share hawayena.
"Yawwah ko ke fa, bara na dafa maki lipton ki sha sai ki ci abinci. Ki ta faɗar Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un."
Nisawa nayi tare da faɗin nagode.
Haka na wuni a gidan Safna, duk yanda na yi ƙoƙarin dakatar da hawayena, da zaran na tuna wani abun sai kukan ya dawo.
Da ban haƙuri da ban baki tare da ƙarin nasiharta gare ni ya tausar min da zuciyata.
Sai yamma liss Hamza ya dauke ni muka koma gida.
Ta ku mai ƙaunar ganin farin cikin ku, Fatima Muhammad Sani Fantah Ku Kasance cikin ƙoshin lafiya.