page 5
_*Typing🤳🏼*_
_*🍏....ZULFAH....🍏*_
Na
_*®UMMU MAHER(MRS GREEN)*🍀_
*_TEAM🔥GAWURTATTU 🤟🏻3_*
_*AREWABOOK🤳🏼*_
ZULFAH:: https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540
________________
*_PROMO!PROMO!!PROM!!!_*
_,NI UMMU MAHER ZANYI MAULUD PROMO_
*DAGA YAU ZUWA JIBI INSHA ALLAH,ADUKKANIN LITTATTAFAINA NA RAGE KUƊINSU DAGA 500 ZUWA 300 ONLY😄👏🏻*
zaku iya sharing ɗinsa kowa ya gani ga masu buƙata daga yau 19/9/2023, zuwa 21/9/2023 insha Allah.
*SILAR FYAƊE ₦300*
cmplt doc
*DARASI ₦300*
cmplt doc
*DOCTOR NAWWARA ₦300*
cmplt doc
*ABIN CIKIN ƘWAI ₦300*
cmplt doc
*INDA BA ƘASA ₦300*
cmplt doc
*ƊINYAR MAKAHO ₦300*
cmplt doc
*BASMA ₦300*
cmlpt doc
ina gaida masoyana aduk inda suke.
*mrs green taku ce*😄🍏✍🏻
*masu turowa ta acc*👇🏻👇🏻
RABIATU BASHIR
ZENITH BANK
2212328303
masu magana dani kai tsaye👉🏻👉🏻👉🏻
***
OUM MAHER CE✍🏻
_*Page∆5*_
..........Aliyu ya sunkuyar da kansa ƙasa,ya kasa ko da ɗaga ɗanyatsansa tunani kawai ya ke aransa saboda yarinyar ta bashi mamaki me tsananin gaske,wulaƙanci da tuzarci yau dai tayi masa shi mutum ne me girmama na gaba dashi,sam baya yarda araina sa shima kuma ba shida raini ko kaɗan,duk da yake yana talaka bai taɓa zuwa wajen wani me kuɗi neman wani abuba,abinda ya sani shine kawai aikin kanikancin da yake kullum da safe ya fice sai yamma,shi dai aganinsa ko da me mahaifinsa ya yi mata bai cancanci wannan tozarcin da cin mutuncin ba.
da sauri Zulfah ta miƙe tana yi musu wani irin wulaƙantaccen kallo,yadda kasan idanuwanta zasu fito daman kuma gasu manya,da sauri na sunkuyar da kaina don sam bana son ganin mummunan fuskarta,don duk kyaunta da ake ko ɗawa ni to muninta nake gani,bansan na furta wata kalma ba sai da ta fita,biyo bayan tuno da mahaifina danayi acikin mummunan hali.amman kuma sai dana faɗa na ke dana sanin faɗin hakan.
duk da haka bata tsaya wani abuba ta wuce abinta,tana wani karairaya tamkar zata tsinke,don yadda kasan ƴartsana me remote haka Zulfah take sam ba tada jiki ko kaɗan sai dai tana da sura me kyau da duk wanda ya kalleta da idaniyarsa to sai ta burgesa.
ɗan sandan da mukazo tare ya kalleni da wani irin mugun takaici ya ce"uhm daman ance talaka yafi kowa faɗin rai,duk faɗin ran wannan yarinyar ashe aƙwai wanda ya dame ta?ka dubi halinda mahaifinka yake ciki?na tausaya maka na kawo ka wajenta shine zaka dinga magana a daƙile kana wani ciccinyewa?to wallahi a hakanma Allah yayi maka gyaɗar doguwa da ko wajen nan bazaka bari ba kai ma sai ta sanya an garƙame ka,bakasan ƙarfin ikon wannan yarinyar da faɗa ajinta ba"....tun kafin ya ƙarasa na ce"a'uzu billahi minashshaiɗanir rajim,yanzu har aƙwai me ƙarfin ikon daya wuce ubangiji buwayi gagara misali?to wallahi sajan audu ka tuba tun kafin ka riski hukuncin ubangiji,ai ni aganina babu wanda ya kai Allah ƙarfin iko da kuma izza,saboda komai da mukeyi a duniya yake kuma faruwa to ai da ƙarfin ikonsa ne,numfashinmu,lafiyarmu,tafiyarmu,buƙatar abinci,me kuɗi,talaka,duk Allah ne yayimu kai ɗaya sai dai wanda yafi yi masa ibada."
Sajan ya murmusa ya ce"mlm Ali zan dinga zuwa har gida don ɗaukar karatu saboda ƙwanyarka aƙwaita da ilimi".mukasa dariya muka koma office ɗin tamkar babu abinda ya faru,don daman ni ba mutum ne me ruƙo ba sai ka ƙuntatamin yanzu anjima kuma ka sameni a farinciki,sai kayi tunanin raina maka wayo nake kai na sanya ka a baƙinciki ni kuma akasin haka,to wannan ma baiwa ce daga Allah don duk mutumin da ba shida roƙo azuciyarsa to yayi ta godewa Allah don ya bashi baiwa babba.
abin mamaki tun muna hanya aka saki mahaifina,na rungumesa ina shafa bayansa aduniya ina masifar son mahaifina,duk da wata ƙaddara me girma tayi shawagi acikin rayuwarmu baki ɗaya,amman hakan bai hanani jin tausayinsa ba don ko ma menene tabbas shine ya haifeni.
¢¢¢¢¢¢¢¢
*ZULFAH 2*
duk sanda kuka ji ance zulfah 2 to ƴar mahaukaciya nake nufi don itama sunanta Zulfah don gashin tabon sunanta raɗau a hannunta,don ko da take ƴar mahauciya haka ta taso ta samu kanta mahaifiyarta na hauka amman kuma ga sunanta nan a hannunta.
Cigaban labarin Zulfah 2
tunda wannan mummunar ƙaddara ta samu mahaifiyata sai na shiga taka tsantsan da ita,don duk inda zani da ita nake tafiya ayi ta tsokanarmu da jifanmu akan hanya amman hakan baya damuna,don daman nasaba jin makamanciyar ire iren annan wulaƙancin daga jama'a manya da yara.
rannan muka tashi mahaifiyata ba tada lafiya,abinka da wanda ba shida gata sai naje wani chemist na kusa damu na shiga da sallamata.
sanda na shiga ko kallona baiyi ba,ya cigaba da sallamar mutane masu siyayya amman ni shiru,hakan bai dameni ba baj sanya kuma nayi zuciya na tafi ba,don me nema yana tare da samu saboda haka sai na jingina da ƙofar wajen ina ta kallon silin ɗin chemist ɗin,a zahiri sai ka ɗauka silin ɗin nake irgawa,amman ko kusa ba shi nake irgawa ba tunanin rayuwa kawai nake yadda take gwagwarmaya damu,ko su waye ƴan uwan mahaifina da mahaifiyata oho?.ina cikin tunanin ne naji ya ce"to ƴar mahaukaciya!idan kin gama tunanin kya shigo".
da sauri na bishi cikin shagon,ina buɗe kyawawan haƙora na kallon farko zaka gane ni asalin kyakkyawa ce,ƙazanta da rashin kula sune suka yi wa rayuwata babban giɓi,ba wanka har gwara ma wanki wani lokacin idan nayi wankin mota kan hanya anan nake samo kuɗi,sai inyi wata ɗaya banyi wanka ba har gwara ma mahaifiyata ina yi mata wani lokacin,don a hasashe na adacen baya ita mutunce mai matuƙar tsafta saboda yadda take son taji jikinta da wanka tsaf tsaf,saboda haka nake yawan yi mata wanka duk bayan sati.
Bala me chemist ya tsiramin ido sosai,yana kallon zahirin kyau yarinyar don Allah ya yi halittarsa awajen.ganin irin kallon da yake min na fara kuka wiwi tamkar wacce ya daka.
da sauri ya ce"ke me nayi miki da kike kuka"?.a hankali na ce mishi"babu komai Bala,taimako nake son kayi min don Allah mahaifiyata ce ba tada lafiya tun cikin dare,shine nake so ka rantamin magani anjima idan ta samu barci zan fita aiki sai in kawo maka kuɗin".
na faɗi hakan ina kuka sosai kukan tausayin kaina da mahaifiyata.
Bala ya kalleni sosai sannan ya ce"me yake damunta"?.
da sauri na ce"ciwon kai ne da kuma amai".
tunda na fara maganar ya fara rubutu sannan ya ce"kuɗin maganinki dubu ɗaya da ɗari biyar ne".
da sauri na ce"yanzu Bala a ina kake tunanin zan samo kuɗi har haka?sai inyi ƙwana uku ma fa ban haɗa haka ba,kuma da wannan kuɗin muke cin abinci".yana kallona sosai har na gama baice min komai ba bai kuma katseni ba.
juyawa ya yi a hankali ya fara haɗomin magungunan ya miƙomin,sai murna nake yi don na ɗauka ya barmin maganin ne sai naji yana ce wa"zan baki Zulfah amman kuma zan yafe miki kuɗin maganin ma duka amman da sharaɗi ƙwaya ɗaya idan har kin yarda".
da sauri na ce masa"ko menene zan yi maka Bala indai har zaka barmin kuɗin maganin ni kuwa a shirye nake dana yi maka komai".
da sauri naga yana murmushi tun ma kafin in ƙarasa maganata ya ce"to nagode Zulfah yanzu dai kai mata tasha magungunan sannan ki dawo zuwa anjima idan tayi barcin."da sauri na amsa masa da "na gode".yayi ɗan murmushi sanna na fita ina tafiya ina murna,duk wanda ya sanni yasan ina cikin farin ciki sosai ba kamar ɗazu ba dana zo chemist.
ina kai mata na bata tasha,ina kallonta ta ƙwanta a hankali kan ƴar yamutsatsiyar katifar dana tara kuɗi na sayo mana ita,tuni barci ya ɗauketa har da minshari,na zauna kusa da ita ina cikin matsanancin fasin ciki kana ganin fuskata kasan taf take da tsananin farin cikin samun lafiyarta.
sai dana ga barcin ya ɗauketa sannan na tashi a hankali na ɗan karo mata ƙofar kangon namu sannan na wuce wajen Bala,saboda alƙawarin da nayi masa na komawa bayan tayi barci.
Ina zuwa na sameshi ya fesa uban wanka,cikin wata red ɗin shadda taji aiki sai wangalemin bakinsa yake ya bulbula uban turare ɗan misra,daman kuma gidansa kusa da chemist ɗinne.
ina shiga ya ce"yauwa Xulfah har kin iso"?.na faɗaɗa fara'a ta na ce"eh na iso har tayi barcin ma".ya ce to muje daga ciki sai muyi maganar".da sauri na kallesa don tsaf da wayona kusan shekara 19 ace na nida wayo ai nayi asara,saboda haka na ce"a'a Bala duk maganar da zamuyi muyi ta anan ina ganin hakan zaifi mana baki ɗayanmu".
tuni ya haɗe baƙar fuskarsa baice min komai ba kawai sai naga ya rufe chemist ɗin ni kuma ina ciki,da sauri na fara magana har idanuwa na sunyi jawur na tashin hankali na ce"me kake nufi ne Bala?meye makomar hakan daka aikata"?.
Murmushin mugunta naga ya yi sannan ya tunkaroni ya ce"yau burina na wajen shekara biyar zai cika akanki.........✍🏻
MRS GREEN CE.
domin chart dani kai tsaye ***
*_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 SEPTRMBER._*
_1-ƘWAI A BAKA...!!!🥚_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA...!!!🫗_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
_ZULFAH_🍏
👇🏽
*Ummu maher(mrs green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
***
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
***
Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number.
***
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa*
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
***
***
***
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼