page 6
_*Typing🤳🏼*_
_*🍏....ZULFAH....🍏*_
Na
_*®UMMU MAHER(MRS GREEN)*🍀_
*_TEAM🔥GAWURTATTU 🤟🏻3_*
_*AREWABOOK🤳🏼*_
ZULFAH:: https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540
*Tallah✍🏻✍🏻✍🏻*
GRP ƊINMU NA
*MU GYARA MATA*
***
com/FZOmqzBp6w5IRfgnxJAt3y
Wannan GRP din mun bud'eshi ne don mufarka mata.
Gyara shine mace💋
Gyara shine ginshik'in mace💃🏼💃🏼💃🏼
*Zamu fara siyar da magunguna ingantattu kuma,Wanda zai dawo miki da martabarki ta y'a mace*
*ina mata masu fama da ciwon sanyi????*
*ina mata masu fama da bushewar gaba????*
*ina mata masu fama da zubewar nono???***
To ga dama ta samu,don kuwa munzo muku da magunguna na kwarai ingantattu,y'an gaske saboda haka yi maza ki antayo kada a barki a baya🖕🏻🖕🏻🖕🏻🖕🏻🖕🏻.
Sai an gwada a Kansan na kwarai........✍🏻
*_Page∆6_*
*ZULFAH 2*
.........da sauri na fara kallonsa kallo kuwa na nuna tsantsar mamakin abinda yake faɗa,mamaki da ruɗun abinda Bala ke faɗamin ya kusa zautar dani na sanya wani irin ihu,saboda kaina ƙiris yake jira ya rabe gida biyu tsabar tashin hankali.
ganin inason tona masa asiri yayi kukan kura ya cafkoni sosai,har muna jin numfashin junanmu ya wankamin marin da sai da yasa naga waɗansu taurari waɗanda sukayi min kama da wuta,sannan ya ciremin yalolon hijabina wanda dashi da babu duk ɗaya ne,saboda tsabar ƙoɗewar da ya yi har kana hango jikina,na sanya haƙorana duka biyu na gantsara masa uban cizo,yaji zafi sosai har yana yarfar da hannu da sauri na wuce don buɗe shagon,sai kawai naji ya janyomin gashina wanda ya sauka har gadon bayana,me shegen tsayi da kuma laushi don ma babu gyara.
ihu nake ina ta neman ɗauki,da alama babu wanda yake jina shi kuwa Allah Allah yake ya samu ya kai inda yake son kaiwar don cikar muradinsa,ni kuwa na sanya hannuwa na rufe jikina,ban tabbatar ina da ƙarfi ba sai dana ga irin artabun da muke sha ni da Bala.
Allah ya taimakeni na hango wani ƙaton ƙarfe me shegen tsayi,ai kuwa banyi wata wata ba na kafta masa akansa,nan da nan wajen ya fara ambaliyar jinj tamkar an buɗe famfo,ni kuwa tsoro da firgici yasa na hango wata ƙofa ta cikin shagon na buɗe da sauri na fito.
da sauri naja baya don ganin wacce take wajen,matar Bala ce da yaranta biyu sai kuka suke daga ita har yaranta,ashe dai shagon nasa ajikin gidansa yake don daman tun ba yau ba nasan matar Bala me suna Hafsat.
da sauri nayi gefe,kunya da kuma nadama suka ziyarce ni alokaci ɗaya tuni na sanya wani irin kuka na durƙushe awajen,kuka nake sosai kuma bani da niyyar dainawa, Hafsat ta sanya hannunta ta ɗagani a hankali sannan ta ce"kiyi haƙuri ki wuce wajen mahaifiyarki duk abinda ya faru a kunnena yake,sannan kuma don Allah ki rufa mana asiri kada ki faɗawa kowa,kuma ina fatan baiyi miki komai ba ko"?.
maganganunta suna isowa kunnawa ba tare dana shirya jin hakan ba na ce"babu abinda ya yimin".ban ƙara ce mata komai ba na wuce zuciyata tamkar zata fito waje,wai me yasa mutane da dama suka ɗauki ɗan adam ba abakin komai ba?kamar yadda Bala ya ɗauki rayuwa da zafi har yana son lalata mata ƴar rayuwarta,rayuwarda babu galihu acikinta?me yasa mutane da dama suke zuwar mata da ire iren waɗannan mugayen halayen na su?ko don sun ganta ba tada galihu ne?abin bai tsaya kanta bama har ya iso kan mahaifiyarta?duk da ba zuwa islamiyya take ba,amman tasha laɓewa ta saurari karatu da wa'azozi kala kala,amman bata taɓa riskar inda akace wannan mummunar ɗabi'ar ta cigaba da yaɗuwa ba.
a haka na ƙarasa wajen mahaifiyata,ina zuwa na same ta a zaune tana ganina tayi saurin tashi da sauri tana kallona sosai,aduk sanda taga na yi dare awaje sai naga damuwa ƙarara acikin ƙwayar idonta,amman bazata iya magana ba sai dai tayi shiru tana kallona cikin tsagwaron damuwa,wato mahaukaci ma yasan ɗansa kenan?.
a hankali na zauna na ƙwanta akan cinyarta,sai kallona take amman babu bakin magana,wannan rashin magana na mahaifiyata ba ƙaramin ɗaga min hankali yake ba,har gani nake ko dai daman can kurma ce?abin yana damuna amman babu wanda zan faɗawa,don babu wanda ya janyoni ajiki balle ma har in faɗa masa.
*BALA*
da sauri ya tashi biyo bayan ruwan da matarsa ta zuba masa,ya ajiye wata irin atishawa tamkar wanda aljanu suka shiga,ya kalli Hafsat wacce haryanzu kuka take,ƴaƴanta ma sai kukan suke daga bisani ya sunkuyar da kansa hannunsa na kansa yana tariyo abubuwanda suka faru.
wani irin mugun ɓacin rai ya ziyarce shi,dayaji bandeji ajikinsa shi dai yake sanyawa mutane bandeji ajikinsu idan sukaji ciwo,ammanfa shi sam baya son yaji shi an sanyq masa ajikinsa,don tun yana yaro ya tsani yaji bandeji ajikinsa rabonda ma yaji ciwon da za a sanya masa bandeji har ya manta.
Hafsat ta fara magana tana kuka sosai.
"wallahi Bala kayi asarae rayuwarka,kuma Allah ba zai taɓa barinka da wannan zaluncin da kaso ka yiwa ƴar mutane ba,azzalumi macuci wanda baisan mutuncin kansa bama ballantana yasan na wasu......"
da sauri ya shaƙo ta ya kawowa bakinta mari sai yaji an riƙo hannunsa,abin mamaki ɗanta ya gani me shekara goma kacal aduniya yana kallonsa yana kuka ya ce"Abba idan ka daki Ummanmu sai na rama mata."bai sake cewa komai ba yaja hannun mahaifiyarsa sukayi ɗaki.suka bar Bala yana kallonsu tamkar zaiyi kuka,ga baƙin cikin abinda Zulfah tayi masa ga baƙin cikin abinda ɗansa ya yi masa.
_*ZULFAH 1*_
Hajiya Innah ta ce"yauwa Zulfah kinga ashe ma yau Bilal zai dawo,to shine Babanki yace muje mu tarosa".bance mata ƙala ba na cigaba da danna wayata don sam bana son ina uzuri ayimin magana musamman ma na waya.ganin bance mata komai ba sai kuwa ta ce"Murash_sha ɗan bani wayarki in nuna mata hoton Bilalu wataƙil ta manta dashi ne".
Ina bidiyo call da wata friend ɗina kawai sai naga hannun Hjy Innah kan wayata wai don inga hoto.
da sauri na cire hannunta kan wayata na cigaba da dannawa,Hjy Innah ta kai maƙura ta ƙwace wayar daga hannuna sannan ta ce"ke wai wacce irin yarinya ce?ba'a isa ayi miki magana ba?".ina kallonta raina yana ƙara ɓaci na buɗe kyawawan laɓɓaina cikin shagwaɓa na ce"to grany me kike son na ce miki?ko dad ɗina da yake da babban matsayi bana zuwa taro sa balle wani Bilal?saboda haka a barni mana,kuje ku kawai ai ina ganin yafi ko"?.
ina faɗar hakan na wuce na karɓe wayata hannun Murash-sha na galla mata wata uwar harara,tayi gefe da sauri tana ce wa"bari in matsa nani na kar zomon ba,nima rataya aka bani".
tuni Hjy Innah ta hau fushi,murashsha kuwa ta dinga ƙel ƙela dariyarta,don tana masifar son ganin faɗan hjy innah da jikarta Zulfah.
Hjy Innah ta ce"oh ni na haifi jika,yarinyar nan gaba dukana zata koma yi maƙiya suyi murna,irin uwarki Murashsha don daman ba sanmu ake ba".
Murashsha tayi mata gwalo ta fice fit.
sosai Murassha ta tsantsara ƙwalliya,don murnar dawowar masoyinta abin sonta dom aduniya tana masifar son Yaya Bilal,sai dai duk kulawar da take bashi shi ko ajikinsa don ba ta ita yake ba,tunowa da hakan da tayi yasa taji tamkar ma kada ta fita don tarosa ɗin,amman tana cikin yin wannan shawarar mahaifiyarta ta shigo,da sauri ta ɓoye damuwarta zata fito sai kuwa ta ce"yauwa ba naga kina wani rawar ƙafa ba,ba gilin gilin ba dai tayi mai saura ki bari a tafi da waccen munafukar,kinga daga nan ke kin zama ƴar kallo sha sha wacce batasan inda ke mata ciwo ba".tana faɗar hakan ta fice,tabi mahaifiyarta da kallo kawai don arayuwarta ta tsani taji wani ya zagi Zulfah abin yana mata ciwo sosai,ta fice don taro masoyinta Bilal ......✍🏻✍🏻
MRS GREEN CE
domin chart dani kai tsaye ***
*_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 SEPTRMBER._*
_1-ƘWAI A BAKA...!!!🥚_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA...!!!🫗_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
_ZULFAH_🍏
👇🏽
*Ummu maher(mrs green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
***
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
***
Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number.
***
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa*
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
***
***
***
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼