02
by @azizat
*MR & MRS MAIDOKI*
©AzizatHamza2023
02
***
*Date 05-03-2018*
BIE na kwance kan makeken gadonta ta zurawa ceiling ido. Abubuwane da dama ke wanzuwa a ranta. Kwana biyu kenan da failed Anniversary dinner ɗinsu.
Ba haka ta so anniversary ɗinsu ya kasance ba. Amma kuma ba za ta iya haƙuri akan ganin Labiba a wajen hidimarta ba.
Irin comments da ta yi ta gani a social media da yadda aka twisting labarin gaba ɗaya sai hankalinta ya ƙara tashi. Kwana biyun nan ko barci bata iya yi.
Wani comment da ta gani ana yabon Labiba Sada da cewa sharri aka mata ya sa ta yi wurgi da wayan ya fasa mirror ɗin ɗakin. Bata sake bin ta wayar bama har yanzu. Maid ɗinsu ta shigo ta gyara wajen da glass ya fashe ta ajiye mata wayar a saman bedside wardrobe.
Ta ya ma za a ce wai sharri ta yiwa Labiba. Ko dan bata watsa abin da ta gani a social media ba a lokacin. Laifinta ne ai, da bata rufa musu asiri ba tun lokacin da yanzu babu wanda zai zo yana maganar wai sharri ta yiwa Labiba.
Daɗin abin ma ta gama zama da Adam, ta gama auren, su je su yi tsiyarsu. Za ta karɓi 'ya'yanta, sannan kamfanin AdBie nata ne dan haka dole Adam ya siyar da shares ɗinsa. Kai ƙarshe ma canjawa kamfanin suna za ta yi. Ba za ta juri ganin Ad dake jikin AdBie ba. Lokacin da suka shirya buɗe kamfanin sun yi tunanin saka wa kamfanin suna kala-kala daga ƙarshe watarana suna zaune suna yin breakfast ta cewa Adam ta samu perfect suna.
Da ƙyallin farin ciki a idanunta tace masa "Sweetness sunan kamfaninmu AdBie. Adam and Bie, AdBie"
Shikenan kuwa clothing brand ɗinsu ya koma AdBie.
Shekaru biyun farko da buɗe kamfanin sun yi fama da matsaloli amma daga baya suka positioning kansu a matsayin number one top couples clothing brand a Nigeria.
Bie tana son fashion shi yasa ta karanta fashion and design a makaranta.
A yanzu ba kaya kaɗai suke yi ba AdBie na yin jaka da purse na mata sai kuma wallet da sling bag na maza.
Shekarar data gabata suka buɗe AdBie skincare products, kayan kwalliya da shafe-shafe.
A lokacin ne kuma abubuwa suka fara zama ba dai dai ba.
Lokacin da suka lauching products ɗin Bie ta shooting talla inda aka nunata ta fito daga wanka sanye da bathrobe tana shafa products ɗinsu da ta gama ta saka wani red gown mai kyau ta baza gashinta baƙi mai sheƙi.
Kafin a sake tallen Adam ya kalli videon tallen ya fara faɗa yana faɗin bai yarda a sake videon ba saboda rigar da ta saka ana ganin cleavage na boobs ɗin Bie dan saman rigan da net aka rufe.
Sun fi minti talatin suna masifa da junansu har Bie ta kira shi ɗan ƙauye.
Adam kuwa ya dage akan in dai aka sake videon nan to ba zai yafe mata ba. Wasa wasa maganar video sai ga shi sai da aka zauna da Abbie wanda ya goyi bayan Adam. Dole dai sai wata model ɗin daban aka ɗauka ta yi musu tallen mayukansu.
Bata san ya aka yi ba sai ga videon sun hau social media. Ta rantse masa ba ita bace ta ɗaura videos ɗin nan amma bai yarda ba. Ƙila videographer da ya mata videon ne ya ɗaura bata sani ba, amma dai wannan na ɗaya daga cikin dalilan da ya sa lamarin aurensu ya taɓarɓare.
Tun daga lokacin suka ja baya da junansu.
Abubuwa sun yi ta faruwa bayan nan amma dukka basu kai cin amanar da ta gani a wayar Adam ba. Adam da best friend ɗinta Labiba. Ba za ta taɓa yafewa ba.
"Anty Bie, Alhaji na kiran ki" Maid ɗin gidansu dake sanye da uniform riga da wando kalar ruwan toka ta faɗa tana risinawa
Sai a lokacin Bie ta sauke rinannun idanunta daga kallon ceiling ta kalli maid ɗin ta mata nuni da hannu akan ta tafi.
Kusan 20 mins da zuwa kiranta tukunna ta sauko ƙasa bayan ta yi wanka ta ziro Abayar da ta gani a kusa.
Tana tafiya cikinta yana wani ƙugin yunwa. Ita ba Azumi ba amma rabonta da abinci tun safiyar ranan dinner.
Bata yi mamakin ganin duka 'yan gidan a falon ba.
Ta samu kujera kusa da Nadeem ta zauna tana faɗin "Good morning, Abbie"
"Good morning, Bilkisu" yadda Abbie ya kirata da ainihin sunanta ta san magana ce za a yi mai mahimmanci.
Baby ake kiranta a gida dan ita ɗin mai sunan mahaifiyar Abbie ce, kuma ita ce autan gidan, sannan a yanzu ita kaɗaice mace dan Anty Zahira ta jima da rasuwa, tun kafin aurenta da Adam.
Daga baya da sunan Bie ya kama bakin mutane sai ya zamana har a gida an fi kiranta da Bie akan Baby.
Ta kalli Ammie wacce ta ɗauke ido daga kanta tana duban wayar hannunta. Ta haɗiye gaisuwar da ta ke son yi dan ba alamar akwai amfanin gaisuwar a yanzu.
"Mun yi magana da Babangida jiya" Abbie ya fara magana
"Ina so na ji abin da ya haɗa ku daga bakin ki"
"Abbie bana gaya maka yana neman ƙawata ba" ta faɗa cike da haushi har yanzu tana jin ɗacin abin a ranta.
"Bana son rashin hankali Bilkisu, bayani za ki min"
To ta ina za ta fara bayani?.
Ta bayanin ita da Adam basa haɗa gado kusan shekara ɗaya wanda hakan ya kawo musu matsaloli ko kuma ta lokacin da ta fara zargin Adam yana neman mata, ko kuma a lokacin da ta ga chats da kuma hotunan tsiraicin da Labiba ta tura wayar Adam tana faɗin. Ta shirya tarbansa yau.
"Ke nake jira" Abbie ya katse mata tunani
"Erm Abbie, Adam da Labiba sun ci amanata"
"Ban gane ba?"
Bie tace "Abbie, i swear to God Adam is sleeping with Labiba"
"Kin san zargin da kike yiwa mijinki kuwa?, kin san girman zargin da kike masa?"
"Abbie ba zan masa ƙarya ba, na kalli chats ɗinsu, and Adam bai ƙaryata haka ba"
"Babangida ya faɗa min komai, me yasa ba zaki yarda da mijinki ba"
"Abbie he's lying to you, ƙarya yake maka. Ba zan iya zama da maƙaryaci mai cin amana ba, ka gaya masa ya sake ni kawai"
"Bilkisu!"
Ta yi shiru hawaye na taruwa a idanunta.
"Ni da Alhaji Salihu mun yi magana, gobe za mu yi zama da ku"
Ta miƙe tun ma kafin a ce ta tashi. Ba wani zaman da za ta yi da Adam, ta sani ba zai wuce maganar ta yi haƙuri saboda 'ya'yan dake tsakaninsu bane. Ba zata yarda ba, za ta riƙe 'ya'yanta kar ma a gurɓata musu tarbiyya da irin tarbiyyansu gidan Adam.
Ta shiga ɗaki ta ɗauki wayarta iphone X da ke kan gado ta kunnata, har screen ɗin ya ɗan tsage saboda bugun da ta sha jiya.
Tana kunna wayar kaman jira ake sai ga text ɗin Adam ya shigo.
KI ZO GIDA, WE NEED TO TALK
Ta ja ƙatuwar tsaki ita da gidansa sai dai kwashe kaya, amma ba za ta koma ba.
Tana ƙoƙarin danna masa kira sai ga kiran Yaya Jamal ya shigo wayarta
"Ya Jamal" ta kira tareda fashewa da kuka.
"Bilkisu me ya faru?"
"Ka tayani faɗawa Abbie cewa na gama auren Adam"
"Calm down, ina zuwa gidan yanzu"
Ta kashe wayar tana goge hawaye. Babu mai bin bayanta akan wannan maganar sai Ya Jamal.
Ta shanye kukanta ta dannawa Adam kira. Ringing biyu sai gashi an ɗauka.
"Hello" ta faɗa da muryar da ke nuna tana ƙiris da zazzaga masa masifa
"Happi... Kin tashi lafiya" ya kasa ƙarisa kiran sunan
"Adam ba hira yasa na kira ba. Abbie ya ce za a yi zama da mu, please Adam na roƙeka ka rubuta min saki kafin ayi zaman nan"
"Ka sake ni kawai kowa ya huta. All i care shine ka rabani da aurenka ka je ka auri karuwarka"
Kashe wayar yayi. Bie ta ja tsaki tana faɗin ai dama bai damu da ni ba
Minti goma sha biyar sai ga kiran Ya Jamal ya ce mata ya iso yana falo.
Ta fito da sauri dan ta san Ya Jamal ne kaɗai zai saurareta.
Ko gaisawa basu yi ba ta tsaya yi masa bayanin abin da ya faru da dalilin da ya sa ta attacking Labiba a wajen dinner
"Amma ba kya ganin divorce ba shine best option ba, think about Adnan da Anwar"
"Ya Jamal na gama auren Adam" ta katse shi. " ba abin da zai sa na sake zama da munafuki mai cin amana, zan riƙe Anwar da Adnan a wajena ba abin da zai same su" sunan 'ya'yanta da ta kira ya tuno mata fa kwana biyu kenan ba ta saka su a ido ba, bata ma san ina suke ba, suna wajen Adam ne ko suna Maidoki Family House.
Ta yi ajiyar numfashi, idan ta koma ɗaki za ta kira Nanny Asabe ta ji ina yaranta suke.
"Bilkisu" Ya Jamal ya kirata a hankali ganin ta dulmiya wata duniyar
"Yeah" ta faɗa hankalinta na kan yaranta
"Please ki daure ki cire zancen saki a ranki, ki bari su Abbie su yi zama a duba yiyuwar kawo masalaha, rabuwar aure ba wasa bane, akwai consequences dayawa. Balle ke da Adam kun gina abubuwa dayawa tare, ga kuma arzikin 'ya'ya biyu"
"Na ɗauka za ka goya min baya ne" ta miƙe tsaye
"Please ki zauna" Ya Jamal ya faɗa yana nuna mata kujera
Tana mugun ganin girman Ya Jamal. Tun kafin ta yi aure take girmama shi fiye ma da yayunta Nadeem da Qaseem.
Jamal cousin ɗinta ne wanda ya ke ɗan ƙanwar Abbie, a gidansu ya taso. Ammie ta ce lokacin da aka haifeta aka kawo shi gidan saboda rasuwar mahaifiyarsa. Ya girmi yayunta duka dan kuwa ya bawa babban yayanta Qaseem kusan shekara biyu.
Tun Bilkisu na ƙarama yake sonta, a gaban idonsa ta gama ƙuruciyarta har ta zama budurwa. Bai san ya aka yi ya fi shaƙuwa da Bilkisu akan yayarta Zahira ba. A hankali wannan shaƙuwa ta rikiɗa ta koma soyayya. Sai dai bai iya bayyana wannan soyayya ba har Abbie ya masa tayin Zahira yayinda itama Zahira ta riga ta fito da cewa shi take so
Bayan rasuwan Zahira Nenne wato kakarsu ta yi maganar Jamal ya auri Bilkisu amma hakan bai yiwu ba dan Bilkisu ta riga ta shata layi akan ba zata taɓa yin auren haɗin gida ba. Dake akwai maganar Adam Maidoki a ƙasa sai maganar ta mutu a haka.
"Bilkisu" ya kirata da murya mai rauni. Har yanzu yana son Bilkisu, igiyar aure dake kanta shi ya sa ya tattara soyayyar ya bisine a can wani keɓanceccen waje dake zuciyarsa
"Dan Allah ki bi umurninsu Abbie"
"But Ya Jamal, this is not fair" Bie ta faɗa kamar za ta yi kuka
"Na sani. Ki yi haƙuri"
"Ya Jamal" ta kira shi sounding serious
Bai amsa mata ba ya bita da kallo yana tattare nitsuwarsa ga sauraren abinda za ta faɗa
"Aurena da Adam Maidoki ya ƙare"
Yai shiru wani abu na ƙyastuwa a ransa.
Ya san Bilkisu da kafiya da rikici. Idan ta ce bata yin abu to ko sama da ƙasa za su haɗu ba za ta yi ba. Kafin aurenta tana rayuwa ne according to her rules.
Shi yasa soyayyarta da Adam ya zo mi shi a bazata, saboda Bilkisun da ya sani ba zata taɓa yarda ta yi soyayya da mutum kamar Adam Maidoki ba.
Lokacin da Abbie ya yi masa maganar haɗa Bilkisu da Adam har ƙorafin baki ya yi akan ba lallai Bilkisu ta yarda ba.
Amma sai gashi daga tafiyarsa course na wata shida sai dawowa ya yi ya samu Bilkisu ta yi nisa a soyayyar Adam Maidoki.
***
"Babangida" Alhajinsu ya kira shi da irin kiran da Uba ke wa ɗansa idan zai masa magana mai mahimmanci
"Na'am, Baba"
"Ni da Alhaji Imran mun yi magana, kuma mun tsaida shawara guda. Ka je ka samu iyalinka ka bata haƙuri ka dawo da ita gida"
Adam ya zaro ido waje. Anya akwai yiwuwar sulhu? Maganarsa ta ƙarshe da Bilkisu bai masa daɗi ba. Yadda ta yi ta zaginsa tana aibanta gidansu, da kuma zagin mahaifinsa shi yasa shi faɗin zai mata abinda take so ɗin.
A duniya duk abinda zaka masa kada ka taɓa darajar iyayensa. Mahaifiyarsa ta rasu tun yana shekara uku shiyasa shaƙuwarsa da Alhaji ta fi ta duk sauran 'yan'uwansa. Alhaji baya wasa da lamarinsa. Tun suna yara da ya dawo zai ce a kira masa Babangida. Bayan rasuwar mahaifiyarsa bai yarda ko ɗaya daga cikin matansa sun tsangwame shi ba. A Uwargidansa ya damƙawa renon Adam dan ita ce suke zaman lafiya da marigayiya.
Adam na girma soyayyarsa na ƙara girma a zuciyarsa saboda yadda Adam ɗin ya taso da biyayya da girmama manya.
Alhaji Salihu Maidoki yana da 'ya'ya goma shauku amma Adam da suke kira Babangida saboda sunan Baban Alhajin da ya ci shine mafi soyuwa a gurinsa, sai dai yana ƙoƙarin ɓoye hakan a mafiya lokuta, duk da haka kusan katafaren 'yan gidan sun san Adam Babangida shine favourite son.
"Baba, a ganina gara na bawa Bilkisu lokaci ta yi tunani, ko jiya ta rantse min ba za ta koma gidana ba, tace idan ban saketa ba zata kai ƙarana kotu"
"Haka tace?" Alhaji ya faɗa cikin takaicin matar ɗan nasa
Zaman da aka ce za su yi da iyayensu bai yiwu ba saboda a ranan da za a yi zaman wata ƙanwar Alhaji ta rasu a can Zaria shi ne suka wuce can duka har da Adam ɗin. Ba su dawo ba sai da aka yi sadakan uku aka ƙara kwana huɗu akai saboda rikicin gado da ya riƙe su.
Alhaji bai ce komai ba ya ɗauki wayarsa ya kira numbar Bilkisu. Daga yadda ta ɗau kiran amma ta yi shiru ba ta yi magana ba ya nuna da gasken dai rashin kunyar yaran zamani za ta masa. Da muryar da take nuna umurni na wanda ya isa ya bada umurnin ya ce "Bilkisu ina jiranki a gida yanzun nan"
Bai jira amsar da za ta bashi ba dan baya buƙatar hakan. Ubanta ma bai isa ya take umurninsa ba balle ita.
Yana kashe wayar ya kira numbar Abbin Bilkisu.
Cikin raha suka gaisa. Tafiyarsu bata yau bace, tafiyarsu ta faro ne tun lokacin Imran El-Sayed yana jami'ar Oxford suka haɗu ranan graduation ɗin first degree ɗinsa. Marigayi Nasir El-Sayed yayan Abbie shi ne abokin Alhaji Salihu Maidoki na ƙut da ƙut.
Duk da alaƙar kasuwanci da kuma haɗin 'ya'yansu aure da suka yi har yau Abbie a matsayin yayansa ya ɗauki Alhaji Salihu.
Ko a yanzun ma da Alhaji ya kira shi ya ke masa maganar ya zo a yi zaman yaransu cike da girmamawa ya amsa masa.
Kuka ne kawai Bilkisu ba ta yi ba lokacin da Abbie ya kirata ya ce ta shirya su wuce gidansu Adam. Ita fa duk da Alhaji ya kira ya ce ta je ta yi shirin watsi da maganarsa ne. Ganinsa ta ke a mai babban laifi saboda duk abinda Adam ya yi a wajensa ya koya, shi yasa tun farko ta ji tsoron shiga gidan da suka yarda da polygamy. Matan Alhaji Salihu Maidoki uku ne, idan ka haɗa da wacce ya saka da kuma wacce ta rasu, mata biyar ya aura kenan.
Adam baya cikin irin mazan da ta ke son aure. Bai ticking ko ɗaya cikin list ɗinta ba, but love happens.
Lokacin da Abbie da Bilkisu suka iso sai Alhaji ya ce Adam ya buɗe taro da addu'a. Bie sai hararansa take tana kiransa munafuki a cikin ranta.
Matashiya Alhaji ya fara bayarwa na yadda aka riga aka zama ɗaya, domin Imran El-Sayed ƙanine a wajensa. Ya cigaba da bayani har ya taho kan batun abinda ya sake ɗinke zumuncin wato auren Adam da Bie da kuma 'ya'ya biyu da suka haifa.
Bie ji take ɓaɓatunsa kawai yake. Dama Alhaji akwai son girma da wani izza na bogi, ta juya ido tana jan tsaki a cikin ranta.
Ita aka bawa damar ta yi magana. Jikinta har ɓari yake wajen kawo bayananta tana harhaɗa bayananta Turanci, Hausa dama larabcin da bai zauna a bakinta ba.
Maimakon ta faɗi damuwarta da matsalolinta sai ta buge da zagin Adam tana kiransa da maciyin amana.
Abbie ne ya daka mata tsawa. Ta ƙare maganarta da cewa "Abbie na gama auren Adam, it's over"
Alhaji Salihu ya kalli Adam ya ce "Babangida me ya haɗa ka da matarka"
Adam ya ɗan kalli gefen Bie kafin ya fara bayani
"Baba, tun lokacin da muka samu wata matsala last year Bilkisu ta dena bawa aurenta mahimanci..."
Bie ta katse shi "Munafuki, so now, sharri zaka ɗaura min kenan. Kana son rufe maganar cin amanata da kayi da ƙawata"
Adam ya cigaba "Har ta kai mun kusan shekara bamu yi mu'amalar aure ba. 9 months to be precise" Adam ya ƙarisa bayaninsa saboda in dai za a yi zaman sulhu dole ne a fara daga inda matsala ta faro.
"He's lying. Koma mene ne that's not enough reason for cheating Mr Adam Maidoki, sai dai idan abin a jini yake"
"Bilkisu!" Abbie ya daka mata tsawa
Zai ƙara magana Alhaji ya ɗaga masa hannu.
Maganar yaran bai kai a fara tada jijiyar wuya ba. Basu lokaci za a yi su je su warware matsalarsu da kansu.
"Babangida"
"Na'am"
"Ina baka umurni ka ɗauki matarka ku je gida. Ka je ka lallaɓeta ku sasanta kanku"
"Never" Bie ta faɗa da ƙarfi
Alhaji ya kalli Abbie yace " ko akwai wata magana da zaka ƙara akai?"
Abbie ya ɗan tanƙwara kansa dan ya nuna biyayyarsa ga Alhajin ya ce "Alhaji abin da ka faɗa ya yi daidai, idan akwai ƙari bai wuci maganar da muka yi da iyalina ba akan ya kamata dukkansu biyu su je su ga marriage counselor"
"Marriage counselor?"
Abbie ya gyaɗa kai yace "suna taimakawa wajen gyara aure sosai"
"Ah! Tunda dama rayuwar tasu ta 'yan boko ne ai sai su je kawai su gyara tsakaninsu a can"
Abbie ya yi dariya
"Ku tashi ku tafi, za mu kiraku" Alhaji ya faɗa yana kallonsu