FreeArewaPen original
Mr and Mrs MAIDOKI
- 1views
- 45chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Youtube: Marubuciya Azizat Hamza ***: Azizat_Hamza Tiktok: Marubuciya Azizat Instagram: Marubuciya Azizat ***: ***
Sample · Page 01
*MR & MRS MAIDOKI* ©AzizatHamza2023 01 ****Date 03-03-2018*Mr & Mrs MAIDOKI ne rubuce ɓaro-ɓaro a bangon ƙaton hall da ke cikin shararren hotel ɗin nan na Transcorp Hilton da ke Abuja, sannan HAPPY 10yrs ANNIVERSARY ya biyo a ƙasan sunan. A gefen rubutun kuma ƙaton hoton mata da miji ne cikin shiga na alfarma. Namijin dogo ne, baƙi mai haske, yana sanye da babban riga na shadda fara da ta sha aikin hannu da zare mai kalar ruwan gwal. Sai kuma ita macen, fara ce, tana sanye da farin designer wedding gown haɗe da farin turban da ya matching gown ɗinta. Daga hoton za ka gane cewa su ɗin 'ya'yan masu ƙumbar susa ne. Ah! To! Wa zai kama katafaren hall ya kira mutane don kawai a taya shi murnar cika shekaru goma da aure a 2018 idan ba ma su naira ba.Hayaniyar mutane ya cika ko ina domin mutane sun fara hallara dan gudanar da wannan bikin ANNIVERSARY. A can wani ɗaki kuma duk dai a nan hotel ɗin wata mace ce zaune kan gado wata make up artist na tsantsara mata kwalliya. A wannan hotel aka yi dinner aurensu shekaru goma da suka wuce, shi ya sa suka zaɓi yin bikin Anniversary a hotel ɗin saboda ya tuna musu cewa a nan ne mafarin komai. Duk da dai a masallaci aka ɗaura auren bana tunanin sun yi tunanin komawa masallacin da aka ɗaura auren dan su ba da abin sadaka bisa tunawa da cewa a fa nan aka shafa musu Fatiha. Amma dai kowa da irin tunaninsa. Wasu mabiya addinin kirista su kan yi bikin vow renewal, wato bikin sake maimaita alƙawurran da suka ɗauka yayin ɗaurin aurensu a coci. Za a sake ɗaukan alƙawarrin together forever, till death do us part. Duk da dai babu irin wannan al'adar a musulunci kaman dai Mr and Mrs Maidoki suna ƙoƙarin koyi ne da al'adar vow renewal.Shi bikin Anniversary kaman bikin Birthday ya ke. Al'ada ce da ta samo asali daga turawa. Amma kasancewar boko ya ratsa ko'ina a duniya musamman ƙasashen Africa, da bikin Birthday dana Anniversary duka 'yan Africa suma sun ara suna yi. A Nigeria dai bikin Birthday ya zama ruwan dare a cikin mutane amma kuma bikin Anniversary sai 'ya'yan wane da wane da kuma gogaggun wayayyu ke girmama bikin.Mr and Mrs Maidoki gogaggun 'yan boko ne sannan 'ya'yan masu faɗa a ji ne a ƙasar dan haka babu wanda zai ɗaga murya na cewa me yasa za suyi bikin anniversa...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.