page 7
_*Typing🤳🏼*_
_*🍏....ZULFAH....🍏*_
Na
_*®UMMU MAHER(MRS GREEN)*🍀_
*_TEAM🔥GAWURTATTU 🤟🏻3_*
_*AREWABOOK🤳🏼*_
ZULFAH:: https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540
_*Page∆7*_
...........a hankali Bilal ya fara saukowa daga matattakalar benen jirgin,yana farawa da addu'ah da kai ƙarshenta har ya sauko,lallai tsarki ya tabbata ga subhanahu wata'ala ubangijin da yayo mu,domin kuwa Bilal ya haɗa komai na kyau siffar jiki da kuma zati kallon farko zaka hango tsananin kamanin da sukeyi da Zulfah,a kallon farko ma zaka iya cewa yayanta ne wanda suke ciki ɗaya,sai dai kash!ɗan uwanta ne na jini sosai.
kallon familinsa yake yana murmushi mai bayyanar da zallar murna da kuma jin daɗi,murnarsa ke son komawa ciki saboda kuwa sam bai hango mutuniyar tasa ba,wacce yayi dawowar saboda ita don sam bai yarda ya ƙarasa sauran shekara ɗayar da ta rage masa ba acikin jerin gwanon shekara goman da aka ɗibar masa,ya nemi alfarma don a rage masa kuma ya gama course ɗinsa lafiya,sai dai kash!wadda ya dawo saboda ita ɗin da alamu sun nuna bata damu da dawowar tashi ba.
Murashsha ta tsura masa idanuwa sosai,duk motsinsa na kanta ganin ko kallon ƙurar da ta ƙwaso ta baiyi ba, yasa taji wani ƙaton mashi ya daki zuciyarta,da ciwo ace kaso wanda baya sonka son Yaya Bilal ya daɗe yana addabar zuciyarta,duk ɓoyewar da takeyi amman sai da mahaifiyarta ta gano ta,saboda uwa tafi gaban wasa saboda haka yasa mahaifiyarta ƙara tsanar Zulfah,a ganinta saboda Zulfan ne yasa bai son ƴarta don ita ma Murashsha ba baya bace wajen kyau.
tun kafin su gama gaisawa Murashsha ta yi saurin shigewa cikin mota,ta fashe da wani irin wahalallan kuka wanda yasa taji zuciyarta tana mata wani irin zafi,aduk sanda ta tuna irin son da Bilal ya kewa Zulfah sai taji atake ta fara jin haushin Zulfan amman ya zamar mata tilas ta cirewa kanta wannan tunanin,don a gaskiyar magana tana masifar som Zulfah don zata iya cewa tana cikin mutane biyar ɗin farko na rayuwarta,mahaifinta,mahaifiyarta,Innah,Bilal,sai kuma Zulfah.
tana cikin hakanne taji an buɗe motar,da sauri ta goge hawayenta tana murmushi ganin wanda ya shigo ne ya sanya ta ƙara nutsuwa sosai tana jin wani irin mugun farin ciki mai saurin tafiya da mutum,yau itace ga ta ga yayanta Bilal?tabbas yau itace rana ta farko cikin ranakun da ta ajje a ranar tarihi,ƙamshinsa da ƙwarjininsa suka kusa nitsar da ita acikin wannan hali,da sauri ta fara gaishesa cikin nutsatstsiyar muryarta wacce take cike da kamala da kuma raunin,irin raunin ƴa mace wacce ta rasa rabin farin cikin rayuwarta.
cikin nutsuwarsa mai ƙara sanya ta acikin nishaɗi ya ce"lfy ƙlau murai ya kike?"
sunan da yake faɗa mata kenan,alokacin yarintarta wato 'MURAI' ita kuma Zulfah ya ce mata 'MY FAH'.
sosai taji daɗin sunan ta sunkuyar da kanta cikin nutsuwa ta ce"lfy ƙlau Yaya Bilal".
bai ƙara magana ba yayi shiru,daman kuma shi mutunne mara magana sosai magana ɗaya biyu yayi shiru,wannan yana ɗaya daga cikin abinda yasa yake ƙara burgeta saboda tana masifar son namiji me jan ajinsa.
tun daga wannan maganar basu ƙara magana,hjy innah tana shigowa ta ce"a'a ke muraisa dawo gaba malama,zan zauna kusa da mijina uwar iyawa".
da sauri Murashsha ta gimtse fuska kuma taƙi tashi,Bilal ya yi dariya sannan ya ce"no babu komai Murai tashi ki koma gaban,tunda kinga matata uwar gidana ta fiki matsayi".sosai ran Murassha ya ɓaci,ta buɗe bakinta kamar za tayi magana sai kuma ta fasa,sai kuwa Hjy innah ta ce"da kada ki fasa mana zauna uwar ƴan rashin kunya,yo idan bakiyi ba ai sai Allah ya kama ki tunda uwar kima taci ta ƙoshi take ganin mutane da wani irin kallo na ƴan tsibbu".
cikin takaici Murassha ta ce"haba hjy innah ki daina haka fa,ta yaya zaki dinga zagarwa mutum uwa agabansa".banza Innah tayi mata suka cigaba da hirarsu da Bilal,abin kuwa ya ƙonawa murassha rai daman ita Hjy innah haka take,sai ta ƙona maka rai tazo kuma tana hirarta,taso ta barta kusa da yaya Bilal ta shaƙi mayen ƙamshinsa da ta daɗe bata ji ba.amman wannan fitinanniyar tsohuwar ta rabasu,anya ma kuwa wannan tsohuwar za ta bari ayi auren?don itama taga kamar tafi son haɗa Zulfah da Bilal ɗin,in kuwa haka ne aƙwai babbar ƙura don ko wacce irin macece zata iya yaƙi da ita indai kan Bilal ne,don ya zama jini da tsokarta wannan dalilin yasa ko da suka isa gida bata ƙara magana ba ta wuce sashensu cikin baƙin ciki,tana zuwa ɗakinta ta faɗa kan faffaɗan gadonta ta saki wani irin kuka me ciwo da ƙuna.
¢¢¢¢¢¢¢¢¢
*ALIYU*
sosai ransa ya ɓaci da abinda Zulfah tayi mishi,gashi tayi masa asarar ɗan neman kuɗin da yake don su rufawa kansu asiri,shi kaɗai nr namiji agidansu sauran ƴan uwansa duk mata ne,saboda haka ko wani nauyi yanzu yana kansa ƙwanansu biyu yanzu basu ɗora girki ba,kamar kullum yau ma gidan babu abinda aka ɗora,Aliyu ya kallo ƴar ƙaramar ƙanwarsu me shekara biyar hawaye yaji yana son zubo masa da sauri ya share hawayen saboda sam baya son su gane yana cikin wani hali,ya dubi mahaifiyarsa ya ce"Umma kuyi haƙuri da jarabtar da ta samemu in sha Allah komai zaizo da sauƙi,kuma duk me haƙuri yana tare da riba yanzu zan fita in ɗanyi buga buga in samo mana ɗan abin kaiwa baki."
Umma ta ce"to Aliyu Allah yayi maka albarka ya baka abinda ka ke nema duniya da lahira,kuma insha Allah nan gaba komai zai zama labari don ni dai ina ji ajikina wataran zaka zama wani a wannan duniyar tamu".ɗan murmushi ya yi sannan ya ce"amin Ummana".ya shafa kan ƙaramar ƙanwarsa ya riƙo hannunta suka fita sai tsalle take don yanzu tasan za ta samu abinda zata sanya acikinta,yaro kenan yasan me basa shiyasa akeson mu zama masu son yaranmu da ƙaunarsu,ammanfa kada ka bari sansu ya rufe maka idanu ka lalata abinka da kanka.suna fita ya duba aljihunsa naira hamsince dashi, saboda haka ya wuce da ita wajen me ƙosai ya siya mata na hamsin ɗin sai tsalle take tana murna,shima kallon yarinyar yake tausayinta fal ransa ya saka azuciyarsa kuwa duk halin da zai shiga arayuwarsa ba zai taɓa bari suyi ta zama da yunwa ba,ya saki wani irin tsaki a fili yana jin wata iriyar muguwar tsanar Zulfah duk itace ta sanya su acikin wannan halin,kusan ƙwana biyar bai fita aiki ba sai ya ƙara jin tsanarta ta ƙara cika maaa zuciya,sannan ya ƙara ɗaukar aniyar rama duk abinda tayi masa cikin ruwan sanyi da kuma salo.
¢¢¢¢¢¢¢
*ZULFAH 2*
da daddare har mun fara barci ni da mahaifiyata kawai sai naji jiniya,ma'ana motar ƴan sanda kuma bata tsaya a ko'ina ba sai a ƙofar kangon gidanmu daga nj har mahaifiyata muka tsorata,duk da ita ba gane komai take ba amman na lura ba wai haukacewar duka tayi ba,aƙwai sauran wasu sauran ƙwalitis ajikinta.
kai tsaye macen ƴar sanda ta shigo mana tana zare ido ta ce"ke ce Zulfah"?.
da sauri na ɗaga kai na alamar eh'sai kuwa ta ce"ok you are under arest".
ban samu damat ce wa komai ba ta sanya min amƙwa,idanuwa suka kawo ruwa ina ce wa"don Allah ki faɗamin laifin dana yi muku"?.bata ce min komai ba ta tisa ƙeya ta gaba muka tafi,zuciyata cike da baƙin ciki dama ana haka kawai kana zaman zamanka ƴan sanda suzo su kama ka?ba tare da an tabbatar da laifinka ba?lallai kuwa aƙwaj matsala babba a ƙasarnan wato indai kai ba kada ga ta sai ayi ta juyi da kai?tamkar wainar masa?".
ina hango mahaifiyata ta biyosu tana nuna ni tana kuka tana rirriƙeni,amman ko ajikinsu suka hamɓareta suka wuce dani duk da daddare ne bai hanani gane Bala ba,wanda yake cikin motar ƴan sandan goshinsa duk bandeji gashi goshin ya ƙato rum dashi,ga idonsa na dama a tashe sai bankamin harara yake yana wani irin abun yana nutse damtsan hannunsa tamkar zai dake ni,sai alokacin hankalina ya ƙara tashi wato dai Bala abinda zaiyi min kenan?ya so yimin fyaɗe don na ƙwaci kaina kuma yazo ya kaini ƙara?to me hakan yake nufi?.
Tun daga yarintata har zuwa wannan lokacin ban taɓa riskar kaina a matsanancin baƙin ciki ba irin na yau,tabbas Bala ya kai maras mutunci ni da ya kamata in kaishi ƙara saboda lalatamin rayuwa daya so ya yi,shi kuma ashe har ƙara ya kaini don ya cimin mutunci saboda yaga ba nida wani gata?to ni na yarda da Allah kuma shine zaiyi min maganin komai.
muna zuwa aka ɗanyi rubuce rubuce sannan aka sanya a bayan kanta idanuwana sai wani zafi suke min,cike da barci da kuma takaici ƴan sandan wajen sai kallona suke kallo irin na ƙurulli,don ko samun damar ɗauko ɗanƙwalina banyi ba,gashina ya bazo ta ko'ina yadda kasan aljana duk da bana samun damar gyara jikina saboda rashin gata amman hakan bai sa na disashe ba,don da ina samun damar gyara da ba ƙaramar fara bace ni saboda yadda siffata da kuma halittata take,komai nawa abin burgewa ne duk da ayanzu ina da shekara ashirin,kuma na gama cika budurwa komai nawa cike yake ɓam,sai dai rama da ƙashin wuya shima duk na rashin gata ne.
Ina da matsakaicin tsayi,ni ba doguwa ba ni ba gajera ba sannan fara ce ni sosai,rawn face ne dani ba doguwad fuska ba,wacce aka ƙawatata da siririn hanci da ɗan ƙaramin bakina,idanuwa manya ne sosai waɗanda aka ƙawata su da zara zaran gashin ido,idona yafi kala dana turawa don ƙwayar idona ba baƙa bace brown kala ce,ga gashin gaban goshina ya ƙwanta luf luf,tunda na taso ake kawowa rayuwata hari amman Allah bai taɓa bawa wani sa'ar lalatamin rayuwa ba,saboda na dogara da Allah shine me kariya aduk inda kake.
ƴan sandan suka yimin tambayoyi na amsa musu duk abinda ya faru,sukayi ƴan rubuce rubuce sannan sukace mu jirayi zuwan oga saboda case ɗin babba ne,don case ɗin fyaɗe ba ƙaramin babba bane shi kuwa Bala tuni idonsa ya raina fata don yaji ance sai oga yazo,gashi yaji labarinsa ba shida mutunci ko kaɗan ko gidanku ɗaya dashi idan kayi laifi sai an yanke maka hukuncin daya da ce,tuni cikinsa ya ɗuri ruwa ya fara ƙulli ji kake ƙuuuuuuuuu alamar zawayi.......✍🏻😄
*MRS GREEN CE*
domin chart dani kai tsaye ***
*_GAWURTATTUN UKU🔥🔥🔥2023 SEPTRMBER._*
_1-ƘWAI A BAKA...!!!🥚_
👇🏽
*(Ummu Affan)*
_2-NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA...!!!🫗_
👇🏽
*Badi'at Mrs bukhari*
_ZULFAH_🍏
👇🏽
*Ummu maher(mrs green)*
_Littafi ɗaya;400_
_Littafi biyu;800_
_Littafi uku;1000_
Ga masu son tura kuɗinsu ta acc sai su tura a wannan acc ɗin👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ka tura da shaidar biyanka ta wannan no ɗin👇🏽👇🏽👇🏽
***
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan no ɗin👇🏽
***
Ƴan Niger zasu turo katin Moov ko Airtel ta wannan number.
***
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANIN SHAFINMU na facebook,whattpad,telegram,youtube,group da status,zamu tallata muku ne akan farashi me rahusa*
10K ne kacal.
Sai ku tuntuɓe a numbobinmu kamar haka👇🏽👇🏽👇🏽
***
***
***
Domin tallata muku hajojinku a cikin littafinmu na sati ɗaya ya kama👇🏽👇🏽👇🏽
2K
sati biyu
3k
idan kuma kanason har mu gama book muna ɗora maka ya kama
10k kacal.
*Mun gode da zaɓar gawurtattu uku ako da yaushe.🙏🏼*