ZAZZAFAR KAUNA 181&190
*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
_ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*
*BOOK THREE*
_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_
_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_
_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! ***_
***
*181-190*
Driving yake amman hankalinshi yana wajenta ganin sam bata cikin happy sai yaji shima dai ga shi nan dai,dan a rayuwarshi abunda ya tsana shine yaga Zulaihat cikin damuwa ko kadan ne shima yana kasancewa a cikin damuwar kuwa...kasa shareta yayi har sai da yayi gyaran murya a hankali yace.."what wrong.?" Kamar jira sai ta fara hawaye kamar an kunna famfo,dafa kan shi yayi yana cewa.."Ya Salam." Gangarawa yayi bakin titi yayi parking yana kashe motar ya kamo hannunta yana murzawa a hankali a hankali yana hura mata iska a fuska sun kusa minti goma a haka sanann tayi shuru share mata hawayen yayi yana langwabar da Kai yace.."Tell me maiye damuwarki.?" Murmushi ta sakar mashi tana girgiza mashi Kai tace.."bakomai Kai na ne kawai take ciwo." Take ya k'ara shiga damuwa dan ji yayi da yana da yanda zaiyi da ya maido da ciwon kan a kan shi ya bar mashi matarshi dan bai son yaji ko wani ciwo ya hauta.
Sannu yayi mata a cikin damuwa yana yi ma motar key suka tafi..suna isa gida da kan shi ya zagaya ya bude mata kofa ta fito ya kulle ko laptop din shi bai dauka ba dan a rude yake da ciwon kan da tace mashi tana yi,kama hannunta yayi suka nufi gida suna shiga ya zaunar da ita saman kujara ya cire mata hijab din ta har da dankwalin ma wai suna Kara mata wani ciwon ai...ita dai kallonshi kawai take tana mamaki kamar ba shi ba,wai ita yau Najeeb yake nuna ma kula harda damuwa dan tace mashi kanta yana ciwo just ciwon kai fa tace ba wani ciwon ba na daban Allah kenan.
Bayan ya cire mata ya kwantar da ita saman kujerar tana ra'da mata sorry a hankali ya wuce kitchen custard ya had'a mata wanda yaji madara but bai cika mata sugar ba sosai a cikin bcox shi bai shiri da sugar sam bai ma iya zuba shi ba ko kadan.
Sandwich yayi mata sharp sharp ya fito ya ajiye a gabanta ya koma ya dauko ruwa da lemu ya ajiye ya koma room din shi ya dauki first-aid box ya ajiye sanann ya d'ago ta yana cewa..."Oya tashi ki fara cin abinci sai ki sha magani ko." Shagwabe mashi tayi tana wani k'ara lafewa jikinshi tace.."oooo Huby ni ban son magani fa Allah ko."
Lumshe idonshi yayi yana saukewa a kanta sai kuma Shima ya samu kan shi da yayi mata shagwabar yana cewa.."Ayya!sorry adan kadan zan baki maganin ban son ciwon ya wahalar man da ke that why."
Turo baki tayi tana k'ara kwantawa saman shi tana lumshe idonta, murmushi yayi yana d'ago ta yana cewa.."okay bari na baki da kaina hakan yayi ko.?" Hawaye ta fara yi tana cewa.."ban jin yunwa fa." Zaunar da ita yayi saman cinyarshi yana cewa.."kukanan naki yana wahalar dani sosai,dan Allah ki daina yana ba zuciyata wahala gane wa ne baki yi stop it please."
Share mata hawayen yayi yana b'ata abincin a hankali sai wani shagwabe mashi take tana wani lafe mashi..shi kuwa daurewa kawai yake dan yanda take lefe mashi ba Karamin harzuk'ashi take ba, daurewa kawai yayi yana k'ara control din kan shi.
Bayan ya gama bata abincin sai da sukayi daru sosai sannan ta sha maganin ya taimaka mata ya raka ta har bakin room dinta sai dai bai shiga ba,daga bakin kofa ya tsaya yana jaijada mata akan tayi wanka sai ta kwanta Allah ya k'ara sauki ya juya ya tafiyarshi.
Ba iya nan taso ya tsaya ba taso ya rakota har cikin room din, kuma ya zauna yaita yi mata sannu ya shirya mata da kan shi tun da ai tace mashi bata lafiya..kwanciya tayi tana tunanin hanyar da zata bullo kuma wanda zata k'ara samun kusanci da shi fiye da wannan ma.
Tashi tayi ta shiga wanka bayan ta fito ta saka riga da wando minisiket ta saka,sanann ta kwanta ta shige cikin devut sai bacci yayi awon gaba da ita .
★★
*GUSAU 🥀*
Share hawayenshi yayi yana kallon Baba Bishir,sai kuma yace.."Allah yasa haka yafi alkhari ya basu zaman lafiya Baba yaushe ne bikin Jidda din.?" Tausayin Haidar ya kama Baba Bishir dan dai kawai bai da yanda zai yi da akwai yanda zai yi sai ya aura ma Haidar Jidda duba da irin son da yake ma yarinyar.
Laifine yayi ya aikata kuma yace ya tuba ba sai a yafe mashi ba?amman ace ga na gida sai a ba na dawa,amman shima Abdulkadir din yayi mata hallaci shima mai sonta ne tsakani ga Allah tun da shine sillar barinta bariki ya kuma maido masu ita gida.
Kodan wannan hallacin da yayi masu shima ya cancanci a bashi auren Jidda sannan kuma ba zasuyi mata dole ba wannan a rabuce take ba zasu tab'a yi mata dole ba..gyaran murya yayi yana cewa.."Yi hakuri Haidar haka Allah ya qaddara Kulu ba zata tab'a zama matarka ba,sai kayi addu'ar Allah ya zab'a maka abunda yafi zaman alkhari ba wannan hawayen ba,Kai namiji ne kuma shi namiji ai da dauriya aka san shi Aliyu."
Murmushi kawai Haidar yayi yana k'asa da kan shi,shima Baba Bishir murmushin yayi yana cewa.."sati mai zuwa za'a daura auren in shaa Allah,sai dai ni Haidar Ina da wata shawara mana."
Gyara zaman shi Haidar yayi yana cewa.."Allah ya kaimu to Baba,amman wata shawara ce wannan.?" Dan shuru Baba yayi yana kallon Haidar can ya furzar da iska yana cewa.."Mai zai hana ka nemi auren Saddiqa tun da naga har ta kusa gama karatu saura wata biyu naji Abdullahi yace man ta gama karatunta."
Shuru yayi yana kallon Baba Bishir can yace.."hakane Baba sai dai Ina ganin ko na nemaita ba bani zasuyi ba." "Subuhanllh maiyasa kace haka Haidar.?" Murmushi mai ciwo Haidar yayi yana cewa.."Saboda na lura har yanzun basu huce daga fushinsu ba Baba,bama kamar Muhd da har yanzun yak'i bari mu cigaba da alaqarmu kamar da shine babbar matsalar ma a gani na su sauran basu da matsala."
Girgiza kai Baba Bishir yayi yana cewa.."shi Muhd din.?" D'aga mashi kai kawai Haidar yayi dan yana bukatar Muhd a rayuwarshi yana bashi shawara ta gari duk ya damu da hushin da yake da shi yasan shi mai laifi ne a wajenshi kuma ya tuba ai sai ya yafe mashi ya maida komai ba komai bane,amman kullun cikin bin shi yake yak'i ya kula shi ma sai da aka zauna sanann ya fara ansa gaisuwar shi daga ita kuma bai ce mashi komai shi kuma bai jindadin haka
Murmushin manya Baba Bishir yayi yana cewa.."kana son Saddiqa din ko kuwa?karka ji kunya ta fito ga yaman gaskiyar abunda ke ranka kaji Ali zaki." Kasa yayi da Kai yana murmushi dan ba zai ce A'a ba duk da bai jinta a ran shi amman yasan na gaba zai sota duba da hankalin yarinyar da kuma natsuwarta kamar ta Jidda dan daman tafi kama da Jidda a gidan,ya tabbata idan ya aureta zaiji dadin zama da ita sbd da tarbiyarta za kuma ta ba yaranshi tarbiya iya tarbiya.
Yar dariya Baba Bishir yayi yana ce mashi.."ta ka tafi Allah ya yi maka albarka Haidar." Tashi yayi yana godiya ya tafi,bayan tafiyarshi Baba Bishir ya kira Baba da Yaya Muhd yace komai suke suzo yana nemansu ya kashe wayarshi.
★★
Zaune Jidda take ita da Mama da Saddiqa sai Rukky dan su Nana suna gidan Yaya Bash daman gida uku suke rayuwarsu ba su cika zama gida ba,sai Mama tayi jan ido take samu suke dan watan ni a wajenta..cikin sanyi jiki da tausayi Mama tace.
"Wallahi Jidda sai da aka tsada ranar auren nan naki naji Haidar ya bani tausayi bama kamar Hajia Aisha da ta kirani waya tana yi man murna duk sai naji ba dadi."...furzar da iska Jidda tayi tana cewa.."hakane kam amman sai ayi addu'a Allah yasa haka yafi alkhari Mama,amman ni banji tausayin shi duba da Ina da wanda nike so,ni kuma ba zan iya aurenshi ba dan yanzun wallahi ni ban mashi son aure ni yanzun da AK nike son na rayu har *DA'IMAN ABADAN* "
Murmushi Saddiqa tayi tana cewa."kema ai kina da gaskiya Yaya Kulu sai yayi addu'a Allah ya zab'a mashi abunda yafi alkhari daman ba rabon ya zama mijinki haka qaddararku take idan aka yarda da qaddara sai a zauna lafiya,amman sab'anin haka ai sai rayuka su b'aci a banza bayan komai ya faru daga Allah ne."
"Hakane kam Saddiqa ai Alhmdulh ba wanda ya kawo matsala a wanann sa bikin,dan ko Alhaji Usman ai shi ya anshi sadaki ma gaskiya naji dadi da fahimta ya ta dawo a wannan family amman da duk na dadi Kai ya rabu Allah ya k'ara had'a kawunan ku dai." Cewar Mama da Amin suka ansa su duka sannan suka cigaba da tsara yanda bikin zai kasance.
Suna cikin tsara bikin su Baba suka shigo bayan sun masu sannun da zuwa aka kawo masu ruwan mai dan sanyi suka sha sanann Baba ya fara magana yana cewa.
"Aisha.?"
D'ago kai Mama tayi tana kallonshi tace.
"Na'am Alhaji Allah yasa dai lafiya.?"
Murmushi Baba yayi yana cewa.
"Lafiya lau Alhamdullahi."
Gyara zaman shi Baba yayi yana cewa.."Daman Yaya Bishir ne yazo man da wata magana mai dadin ji da sauraro kuwa." Murmushi Mama tayi dan har hankalinta ya kwanta dan tasa wani abun kuma akayi da ya kira sunanta babu sayawa bayan ba haka suke Kiran sunan juna ba, kallon tayi tana cewa."Alhamdullahi wata magana ce wannan dan naga fuskarku cike da annuri sai kace gonar auduga."
Dariya sukayi su duka suna kallon Baba,nan Baba ya gaya mata ai Baba Bashir ne ya ke nema ma Haidar auren Saddiqa,shi dai har ya bada ma yama ce a daura auren rana d'aya da na Jidda ta tare a gidanta ta karasa karatun,sosai Mama ta nuna amincewarta akan lamarin tasan auren nasu zai k'ara gyara zumincin su da ya kusa garwajewa..ita dai Saddiqa bata ce komai ba sai murmushi kawai da tayi.
Duk da tana da wanda suka fara soyayya da shi a school daman bai turo aka tambayar mashi izini ba,kuma ba zata ki yin biyaiya ga iyayenta ba duba da yanda suke ta farinciki da murna akan lamarin da Baba Bishir ya kawo ..kallonta Yaya Muhd yayi yana cewa.
"Saddiqa."
D'ago kanta tayi tana kallonshi ansawa tayi tana maida kanta k'asa, furzar da iskan bakinshi yayi yana cewa..."inason ki anshi auren Haidar hannu biyu kuma kiyi addu'a Allah yasa shine alkhari a wajenki,nasan Haidar nasan waye Haidar na tabbata zai rike ki amana kuma zai kula dake iyakacin kokarin shi."
Dan shuru yayi yana cigaba da cewa.."Haidar mutune mai tsananin kishi tabbas yana da kishi yana bala'in kishin abunda yake so da kuma kauna,duk wannan abun da ya faru na fasa auren Kulu da yayi kwanankin baya kishin shine ya jawo komai dan nasan waye shi,amman yanzun ya rage kishin nan nashi na hauka,kuma nasan wacece ke ba zaki tab'a yin abunda zai zubda mana da mutunci ba."Cikin sanyin murya Saddiqa tace.."in shaa Allah Yaya ,Allah yasa haka shine alkhari a garemu baki d'aya." Da Amin suka ansa sai jindadi suke dan ba karamin dadi Baba yaji ba wannan auren da Baba Bishir zai had'a ba.
Koda Baba Bishir ya kira Haidar ya sanar mashi da rana d'aya za'a daura aurenshi da su Jidda shi za'a daura mashi auren Saddiqa bai san sanda ya rushe da kukan farinciki ba yana ma Baba Bishir godiya...Dan rasa da bakin da zaiyi ma Yayan Babanshi godiya yayi dan ya gama mashi komai bashi mace mai hankali da hakuri kamar Saddiqa da yayi,Dan ko a mafarkin bai tab'a tunanin hakan zata faru ba.
Dan yasan bai cancanci wannan halincin daga garesu ba duba da irin cin mutuncin da yayi a shekarun baya,bayan ya bar gidan Baba Bishir direct gidan Yaya Muhd ya nufa yana zuwa yayi sa'a dawowar shi kenan gidan yana ba matarshi labarin auren da aka had'a ya kirashi waya.
Izinin shigowa yayi mashi yana shigowa ya fad'a jikin Muhd yana kuka yana mashi godiyar bashi Saddiqa da akayi unexpected dan bai yi tunanin hakan ba duk da sunyi magana da Baba Bishir kuwa.
D'ago da kanshi Yaya Muhd yayi yana share mashi hawayen fuskarshi yace.."Broth." Murza idon shi Haidar yayi dan rabon da Muhd ya kirashi da wannan sunan har ya manta,ya ma mashi maganar balle har ya kira shi da Broth..sake kiranshi Yaya Muhd yayi d'agowa yayi yana cewa.
"Na'am Broth."
Sai kuma suka rungume juna suna dariya sun dad'e suna dariyar sai suka d'ago juna suna kallon juna cikin farinciki Yaya Haidar yace.."Broth har abada ba zan tab'a mantawa da wannan ranar ba, komai yazo man a bazata ga kyautar mata ga kuma dan'uwana rabin jikina ya huce daga fushin shi Kai Alhmdulh Allah na gode maka da ka nuna man wannan ranar."
Zama Yaya Muhd yayi yana cewa.."tuni na yafe maka Broth kasan ba zan dauki lokaci ban yafe maka abunda kayi man ba,sai dai nayi nayi da zuciyata akan ta barni mu cigaba da alaqarmu kamar da sai ta hanani amman kullun cikin yi maka addu'a nike Allah ya rage maka zafin kishin nan naki."
Girgiza kai Haidar yayi yana cewa.."tuni Allah ya raba ni da shi,tabbas kishi halak ne amman ba irin nawa ba,Ina Allah wadarai da kishi na har ban son Ina tuno da baya,inajin ba dadi inajin haushin kaina da kaina inajin Ina ma Ina ma tabbas Ina yi kuskure har gobe ina ma kaina fad'a akan haukan da na aiki,sai dai mai a lokacin idona rufewa yayi zuciyata zafi da rad'adi take man amman haka Allah ya qaddara daman komai ya faru a rubuce yake Allah ya k'ara yafe mana baki d'aya"
Da Amin Yaya Muhd ya ansa suka cigaba da labarinsu dan a gidan Yaya Muhd yaci abincin dare har waya sai da ya kira Saddiqa ya gaya mata zai shigo da safe suyi maganar yanda bikin nasu zai kasance..yaji dadin yanda ta anshe shi ta waya kamar sun saba haka sukayi wayar har bai san sanda yace mata I love you ba, murmushi tayi mashi kawai dan taji dadin kalmar da ya gaya mata.
*WASHE GARI*
Tun da suka tashi yau suka fara shirin gida dan yau daman AK zai zo ga kuma Haidar da yace zai zo shima sosai suka hadu suka gyara gidansu ya gyaru yayi kyau sosai...bayan sun gama gyaran gida suka bulale gidan da kamshi mai dadin shak'a da kuma saka natsuwa,daman already sun girka masu abinci mai dadi da kuma juice da sukayi masu maidadi shima.
Wanka sukayi suka shirya cikin shadda skyblue mai masifar kyau ba karamin kyau shaddar tayi masu ba so Masha Allah,suna cikin shiryawa Haidar yazo har k'asa ya duka ya gaida Mama cike da jin kunyarta ansawa tayi tana tambayar shi ya aiki? murmushi kawai yayi yana cewa Alhamdullahi dan shi rabon da yaje wajen aiki sati biyu kenan tun da yaji labarin za'a kawo kayan Jidda yazo gusau har yau bai koma ba.
Kuma bai jin zai koma har sai an daura mashi aure zai koma da Amaryar shi..bayan sun gama gaisawa da Mama ta koma room din ta bai wani dade da zama ba sosai AK ya shigo shima gaida Mama tayi sannan ya zauna suka fara gaisawa da Haidar..daman shi AK ko can da bai wani rike Haidar ba dan ko zuwa yayi ya taddashi wajen Jidda tana mika mashi hannu su gaisa shine dai yake mashi wani gani gani.
Har mamaki abun ya ba AK ganin yanda yau Haidar ya gaisa da shi har yana mashi murmushi abunda bai tab'a ganin yayi mashi ba,shima Murmushin yayi mashi can dai sai ga shi suna dan tab'a hira kafin Gimbiyoyinsu su karaso.
Bayan sun zo sun gaidasu suka kawo masu abinci basu waje sukayi suka ci suka koshi sannan suka dawo a tare akayi firar nan AK ya gane shima zance yazo wajen Saddiqa yaji dadin haka da yaji rana d'aya ma za'a daura masu aure murna yayi mashi sosai.
Yanda sukayi zancen tare dasu Jidda yayi ma Saddiqa dadi dan daman ita bata son mai zata ce mashi ba idan yazo,ga wata irin kunyarshi da take ji ko Ido bata yarda sun had'a ba tunda tazo duk yanda yaso su had'a idon kuwa bata bata shi damar ba saboda kunya da take ji sai noke fuska take tana sakar mashi murmushi .
Hakan da tayi ba karamin kyau tayi mashi ba da kuma sonta da yaji ya saukar mashi a zuciya ba tare da ya farga da hakan ba,sun dad'e a gidan tare suka tafi har airport Haidar ya sauke AK sanann ya wuce gidansu da yake nan yake sauka idan ya shigo Gusau.
★★
*ABUJA 🥀*
Koda ta tashi daga bacci taji jikinta yayi mata watsai daman ba wani ciwon kan da take pretending ne tayi mashi dan taga zai damu da ciwon nata ko kuwa?kuma taji dadi sosai da ya nuna damuwarshi sosai akan kanta.
Wani wanka ta sake yi tana shiryawa cikin kananun kaya riga da wando ne again minisiket ne dakyal ya kawo cinyarta dan bai da banbanci da pant saboda da karantar shi,feshe jikinta da turaruka tayi tana shafa turaren jiki sannan ta saka hula p-cap ba karamin kyau shigar tayi mata sannan ta fito dan samun abunda zata girka da yake yau friday daman.
Fitowa tayi tana kallon parlon ba laifi amman bai mata yanda take so ba..gyara shi tayi tas ta harda moping sai da tayi sannan ta kunna kayan kamshi tana wucewa kitchen dan tasan tana massalaci saboda yau Juma'a.
Samun kanta tayi da son girka abincin yau harda shi fried rice ta girka masu taji kwai a ciki sai kuma tayi masu salad cream yaji mayonnaise sosai salad din sai da ta saka shi a freeze yayi sanyi sannan ta juye shi a plate tayi raping din shi.
Bayan ta gama tsara dinning din ta koma room dinta tayi alwallah ta kaffabara sallah tayi sallah tana gama wa ta saka wani lace ash color dinkin tea bubu,ba kamaramin kyau kayan sukayi mata ba.
Dan daurin dankwali tayi mai kyau da daukar hankali, k'ara fashe jikinta da turaruka tayi tana daukar wayarta ta fito parlo tana saka ma kunnenta earpies ta fara
sauraron waka.
Zama tayi tana jin wakar tana langwabe Kai sai wani kad'a Kai tayi tana sakin murmushi saboda da dadin da wakar take mata..duk da ba fiye sauraren waka take ba amman yanzun tana sauraren wakokin soyayya dan da kanta take download din su saboda yanzun suna mata dadi sabanin da,da take jin haushin masu sauraron wakokin soyayya.
Tsaye yayi cak yana kallonta yana godema Allah da ya azurtashi da mace har mace kamar Zulaihat komai nata daban yake komai tayi kyau yake mata ,ba karamin kyau tayi mashi ba dan wata natsuwa taji ta saukar mashi da ya shigo ya taddata a cikin wannan
gayun zaune a parlo.
Murmushi yayi yana ida karasowa parlon har gabanta yaje yana tsugunnawa yana kallonta sai murmushi yake bata san da shigowarshi ba balle tsugunuwarshi a gabanta tana can tana jin wakarta ta kuma lumshe Ido tana bin wakar Shamsiya Wanda Momy Gombe ta hau Mai yake *DA ZANCE NA TAHO GA REKA AUTA NA MAZA* bin wakar take tana wani karkarda kai.
_Ka sanya Mani zuciya bugu mai sauri idan har ka kula dole Ina maka kuri,kyakyawa kake gunka naga kyau na hakori sirrin sonka a zuciyata bai da maboyi dare d'aya kauna tazo tayi man dauri Ina son muyi rayuwa ka sani a kan hanya._
Murmushi ya subuce mashi yana sa hannu ya zare earpiece din da ke makale a cikin kunnenta.. firgigi tayi tana mai jan baya tana sakin yar'kara kadan sai kuma ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya ganin shine.
Tashi yayi yana kallonta yace.."Ina kika kai ciwon kan da kike da har kike saka ma kunnenki wanann abun.?"
Turo baki tayi tana cewa.."ai Ina son wakar ne shiyasa fa." Girgiza kai yayi yana cewa.."sai kuma aka ce ki tosa ma kunnen naki wanann kayan karar ko?sai ki cigaba daga yau kiga yanda zanyi dake tun da lafiyarki ba damuwarki bace."
Turo baki kawai ta kama yi tashi yayi nufa hanyar room din shi da kallo yabi dining din da ta jera da wormers masu kyau da daukar hankali...mamaki ya kama shi kodai baki zatayi yau?tambayar da yayi ma kan shi kenan,tabe baki yayi yana shigewarshi room din shi ya rage kayan jikinshi yana fitowa ya nufi kitchen da kallo ta bishi sai kuma ta kalli dinning mai yake nufi da tafiya kitchen?tambayar da tayi ma kanta kenan sai kuma ta tuna maybe abinci zai garki bata san sanda ta nufi kitchen din ba,tana zuwa tayi tsaye bakin kitchen tana kallon iKon Allah...Turo baki tayi tana diredirer kafafu tana turo baki ta shige kitchen din tana zuwa wajen shi tayi..
*Akwai Data available masoya akwai ko wane network kuma cikin rahusa 270 1GB ko wane network,banda 9Mobile shi 300 1GB*
*Zaki biya kudin data idan kina bukata ta wannan account din 8160508316 Jamila Bello Abubakar Opay bank,*** for call or whatsapp*
Share✓