6
by @nanadiso10
6
LATYFAH IMAM
Nana Diso
KUYI FOLLOWING DINA A AREWABOOK https://arewabooks.com/u/nanadiso10
Naje gida? Tafaɗa cike da shock me kenan ya saƙeni? Tasaka kuka tana mai barin shashin nasa, yau dai tashiga uku dan tasan mijin nata ba'irin mazan nan ne zaka juyasu anyhow ba, tabbas sai tabar gidan nan ko da na kwana daya ne, sashinta ta shiga tana ƙara rushewa da kuka mai tsanani, sosai hankalin yaran nata yatashi suka rikota suna zaunar da mahaifiyar tasu Ali ne yashiga tashin hankali dan zatace duk yaranta irin yarannan ne masu masifar son uwa, " ammiey menene yafaɗa idonsa yana ciccikowa da ƙuka. Yadda ammy ke shasheƙar hawaye zai tabbatar maka da tana ciƙin tashin hankali " Wai dadynku ne yace natafi gida, daga Nacewa ugly girl dinnan monkey harda marina." Laila ce tace " Tabbijan akan waccan jaƙar yarinyar mai ƙama da buhu? Shine za'a wulaknta mana ammy?." Aliyu ne yashiga ajiyar zuciya yanajin wani zafi ciƙin ransa saboda abunda mahaifin nasu yayiwa uwarsu miƙewa yayi zai fita ammy ta ƙamo hannunsa tana faɗin " No Ali karkaje zai iya tsinemaka kaga jiyama sai da yayimun magana akanka kubarni na zauna lafiya dashi kuna ganin sauran ƴan uwan naku lafiya lafiya dasu." " Haba ammy marinki yayi fa! Har ma yace kije gida akan monkey girl dinnan haba ammy wulakantacciyar yarinyar nan itace za'a haɗa dake to kitafi ina? Kauyen zaki koma cikin gidan kasa? Haba ammy." Babban yayan nasu hamid yanajin komai dama dashi bayashiga shirgin sabgar su dago ƙansa yayi yace " ammiey kiji tsoron Allah kisani wannan yarinyar da kuke wulakantawa Allah ne ya halicceta ba ita tayi ƙanta ba mutum kamar dan adam ace kuna haɗashi da dabba? Shifa dan adam mai daraja ne? Hasken fatanku ko duhun fata nazai ƙaremu da komai ba sai tsoron Allahn mu, wallahi daƙinsan latyfah imam da cigaban da taƙawo arayuwar dady da bakiyimata wannan muguwar tsanar ba, ke kuma laila wallahi kiji tsoron Allah ina gayamiki bakisan gidan wa zakije ba zakiyi aure kuma zaki haihu daga ke har Ali wallahi dukanku zaku haihu kuma duk abunda kukayi sai anyi muku." Ammy ce ta rufeshi da faɗa sosai tana fada masa daman bayasonta ai ita tanama tantama ko ita tahaifeshi anya badan kishiya baniba." Allah yabaki hakuri ammy gaskiya ce sai nafada muku sannan shi Abdul din dakikeyi danshi sanin darajarki yayi yanzu kwana nawa rabonsa dayazo yaganki? Babu abunda yasa agaba sai shaye shaye da bin mata saboda tsabagen iskanci har offices lalata yakeyi da mata sannan kina zagin matar dake hakurin zama dashi." Sai da gabanta yafaɗi najin maganar hamid din dan tasan shi baya karya no matter what gaskiyar nan sai yafaɗeta kuma sai ya tabbatar da'ita kamin yayi maganar. " Ni yau zamu tafi da dady sai Allah yakara sadamu da alkhairi yafaɗa yana ficewa daga daƙin." Aliyu ne yace " kinji sharrin dayakeyiwa Abdul ko? Wallahi karya yakeyi shi wayasan menene yakeyi aboye. Duk banza tayi musu tatashi tashiga ciƙin daƙinta tana kuka dan tabbas aliyu gaskiya yafada bazai taba yiwa Abdul karya ba.
Haba dadyn umar kayi hakuri mana maganar tatafi gidama adaina zancen nan dajin kakeso taje? " Mumyn umar abun yana damuna akan dabi'unta da'ita da yaranta hameed ne kadai ya bambanta wallahi sai ace ke kika haifesa duk yarana ina kokari akansu kuma Allah yataimaka min akan tarbiyarsu shi da yatashi naga take takensa bagashi nayi masa aure ba yazauna da matarma ya gagara daga tozarci sai wulakanci kwanaki ancemin gaban ƴan aiki ya mare yana zaginta. Mumy ce tace " Ni wallahi yarinyar ma nakeji baiwar Allah rannan gabana ammy kece mata monkey saboda Allah fa! Amma kayi haƙuri dadyn umar inshaa Allahu zasu gyara su yaran harda yarinta shima Abdul harda yarinta." " uhmm ga katina nan dayan zai kibawa ammy yanzu jirginmu zai daga zan haɗu da sauran abokaina acan tafiya ce da zata daukarmin lokaci sosai dan zanyi kusan shekara nida hamid. " Batare da nuna damuwa ba tace ubangiji Allah yakaiku lpya yatsareku yabada sa'ar abunda akaje nema to amma umar fa tafaɗa badan nuna damuwar jin haushinta ba sai dan ganin matsyar da mahaifin nasa yasakashi tunda shi kadai ne danta namiji sai mata da duk suna gidan aurensu." " Bazai taba yihuwa intafi da su biyu ba duk masu hankali nabar Ali akan dukiyata wannan kuskurene shine zai kula da komai nawa na nan." " To badamuwa dady Allah yashiryamana su yayi musu albarka tafaɗa dattijuwar." " Ameen kema Allah yayimiki albarka.
LATYFAH bata kirani ba ummy har yanzu fa? " Ko bataga kiran naki ba? " " Eh to ina zargin haka Amma bari najira anjima gobe zamu koma ko ummy?." Banida tabbaci nana naji mahaifin naku yana faɗin ko mu zauna anan. Zaro ido tayi tana faɗin aikinafa ummy. " ai tare zaku tabi zakije kiyi course acan inaji har PhD ma." Wani kalar tsalle tayi cike da murnar da bata iya rikewa ba sai fita tayi da gudu ta'isa palon baban nata tana zuwa ta fada jiƙinsa anty nata dallah mata harara " ke wai Nana bazaki girma baniba? Ko maryam datake ƙanwarki bata abunda kikeyi haba." " ke kyalemun yarinyata banason taƙura ke ta rungume Nana menene? " " Abiey ina sonka abiyna ina sonka dayawa dayawa ." " Nima inasonki dayawa dayawa kije ki haɗa kayanki na nan idan da abunda kike bukata acan gida sai kiyi magana sa turomiki dashi munada 1 hours kawai, bari zanga ummy yafaɗa yana barin part din. Wani malolon baƙin cikine yacikawa anty wuya kenan da Nana zasuyi tafiyar nan tabbijan tafaɗa tana nufan sashinta maryam tasamu ciƙin daƙin nata tana aiki a system. " ake kina zaune ana can ahaɗa munafurci agidan nan." " haba anty me isa kikeyin haka? Yanzu idan abiey yatafi da nana ai karatunta yakaita idan da karatuna yakai kinsan dani zai tafi, abiey yagayamin tuntuni yakuma min alkawarin nima us din zanje masters da PhD kidaina sakawa kanki damuwa mahaifimun na mana adalci daidai gwargwado banason kisamin wani abu acikin raina game da ƴan uwana danAllah, kina gani ummynsu ba haka take ba ko kaya tayiwa nana sai tayimun tunda kinga mahaifinta mai kudin gaske ne kuma yayanta yanzu shine babban mai kudi a riyadh kina dai gani ansiyawa nana waya irinta sak yayan nata yabani da kaya hakan bazaisa ki ajiye kishi ba Anty mu zauna lpya dasu da zuciya daya, yadda yaya zai kira waya haka kema zai kiraki nima haka ai abiey bai bata gidansa ba kowa yana bashi hakkinsa sai kuskuren da baza'a rasa ba wannan kuma ajizanci ne irin na dan adam, tafaɗa tana barin gurin." Murmushi tayi da samun ɗiya kamar maryam dan da tanabiye yayarta da tabbas takashewa ƙanta aure tuntuni, komai ta kawo sai ƴarta ta tinasar da'ita akan badaidai baniba.
Ko sanda Abiey ya isa daƙin ummy tana kwance tasan zatayi kewar mijin nata da siyasarsa da kasuwancinsa bai taba sawa ya rasa basu lokaci ba, yana kokari sosai gurin kasancewa tare dasu, saukar baƙinsa dataji nr yasata murmushi tana faɗin har ka shirya? " Nasan zaki samu sosai da rashina gashi tafiyar tamu har yaranki biyu zan dauka, kiyi mana addu'a da fatan alkhairi ya ummy yafada yana jan hancinta." Rungumeshi tayi tana faɗin Alkhairin Allah da tsarensa yatabbata agareka da yaranmu dama duk wasu matafiya Allah yabaku sa'a yasa muku albarka, " Ameen yaa Allah yace yana sunbatarta na kusan mintuna sannan ya saƙeta. " Zuwa wani watan zaku fara zuwa idan kikazo kikayi 1month itama anty sai tazo tayi ko? ". Duk yadda ka tsara hakan yayi.
A gaggauce yayi wanka yana fitowa yayi sallar walha, duba da karfe 12 jirgin nasu zai tashi gashi kusan 11 yanzu, kayansa yasa wani yaronsa ya debo masa agidansa na can yana fitowa palour yaga ma har ankawo komai dan haka ya hada akwatuna guda biyu da duk abubuwan buƙatarsa ,sannan yasak wani yard mai kauri sosai kalar ruwan kasa, bakaramin kyau yayi ba, ko da yasakko kowanne yafito anata bankawana a tsaitsaye ya gaisa da hajj da anty sai maryama da yarungume yana faɗa mata lallai lallai ta tsaya tayi karatu yadda yakamata, inshaa Allahu yayan mu zanyi. Yna barin gurin daƙin ummy yashiga tana tsaye hannunta rike da karamar jaka ashe Dambu ne tayi masa sai kilishi datasa aka ƙarbo musu. Ya ummy barka da safiya ƙinga na makara yau baki tashine ba. " Kwnanka nawa baka bacci abni da zan tasheka." " DanAllah ummyna kikula sosai nasan yayarmu zata kula dake banda saka damuwa ummy kinga bakida ishashiyar lpya." " Damuwata daya zan saka ka kulamin da ɗiyata kaga ita macece nasan nana batada rawar kai amma kakula idan da hali idan tatashi school anema mata ko qur'an school tana zuwa, nifa nafison tayi aurenta da wannan karatun da aikin." " murmushi yayi wanda yatabo masa ciwon dake damunsa indai zaiyi tafiya amina tana bashi wata irin kulawa tayita yimasa addu'a yanzu batanan sai dai ummy. " Ba tunani zaka shiga ba Kaji tsoron Allah dangirman Allah ka guji bin mata idan har kasan bazaka iya hakuri ba kayi aurenka kawai amma banason ka lallata rayuwarka, kasani ya Abni Ka aikata abinda za kayi murnar dawowarsa gareka wata rana.Saboda duk abinda muka aikata tabbas zai dawo ko adawo mana da shi gare mu ko akanmu." " ummy Inshaa Allahu zan kula sosai ummyna Nagode zanje gidansu amina daga can zamuyi airport to tace tana hana ƙanta kuka tanufi daƙin su amina maryama ke hada mata kayan suka gama tayi mata faɗa sosai antyma tayimata hajja kuwa da bataso atafi da'ita ba sai tace " asarar kawai kudi zaaje kenan." " Nana tana dariya tace " ko zaki bimu asarar kudin? Haɗo kayanki." Banza tayi musu har sukaa tafi.
LATYFAH IMAM muna sauraronki dangane da cigaban wannan hannuwan jarin me dame zakice akan wannan reshe da kuke aiki dashi? " Barkanmu da wannan lokaci ashekara daya danayi aiki na lura da wannan ƙamfanin namu baya samun cigaba ta bangaren zama nantar da abubuwan da yake siyarwa, yanada kyau su sabunta kwalayanmu da ledarmu sannan mu sabunta sababbin talluna, aharƙar tallah yakamata ace mun samo celebrities sune yakamata ace sunyi mana sannan asamu tashoshi da sukayi fice abasu, tunda kamfani ne mai karfi zaiyi kyau a haɗa da challenge wanda sukayi daidai sai abusu kyauta. Tafin da akasaka yasakata jin murna har ciƙin ranta dan hakan ya nuna aikinta yayi kyau. Bakaramin baƙin ciki abdul yaji ba, yanzu saifa su dauketa mtseew yafada.
Nawal kuwa tunda abdul yabarta a offices dinsa ta zuba masa manyan kwayoyi acikin lemonsa duk yadda taso yayi lalata da'ita amma sai yace mata bayajin dadi bazai iyaba, har mamakin kiss din ma tanayi yana ƙauda kansa? Ko sanda suka dawo lemon yasha sosai ya dauketa sukayi gidansa, dan ya rantse babu inda zai raka su dady airport.
Latyfah kuwa tana fita daga offices gidan su nana taje ko dataje mai gadi yasanar mata ai anyi rasuwa ne suntafi Canada, nan hankalinta yatashi tashiga kiran numbar nanan da sai yanzu taga missed call dinta dayawa amma a kashe, sai data tsaya tayi order na abinci sannan tasaka ƙai zuwa cikin gidan nata, ko datashiga bataga masu gadin ba dan haka directly hanyar palour tayi sallama tayi ta tura inda idonta yasauka akan jini dake kwarara akasa sauƙar da ƙanta da zatayi taga abdul ne gaba daya halittarsa ta canza ƙansa babu abunda yakeyi sai jini, wani ihu tasaka tana saƙin abincin da jaƙarta ta nufesa tana girgizasa haɗe da faɗin maigadi? Mai gadi? Kwalbar da tagani agefen kansa ta saka hannu ta fizge tana kuka sosai amma ina taƙasa sai hannunta daya yanke jini yana zuba, karar motar ƴan sanda datajine yasa hankalinta tashi " Gatanan gatanan ta kasheshi mai gadi da nawal suka shiga faɗa....
LATYFAH IMAM TANA CIKIN WANI HALI WAYOOO ....
________
YAU ZAMUYI TSUMI
-KANINFARI 1TEASPOON
-MINANNAS HALF TEASPN
-MAZARKWAILA KO ZUMA
-CITTA HALFTEASPOON
-DABINO 8PIECES
-SASSAKEN BAURE HALF TEASPOON
-BLACKSEED HALF TEAS
-CINNAMON HALF TEAS
-NA'ANA'A HALF TEASPOON.
KI HADESU KI DAFA KINASHA SAU BIYU ARANA YANA SAUƘAR DA NI'IMA SOSAI.