03
by @azizat
*MR & MRS MAIDOKI*
©AzizatHamza2023
03
***
Kafin su isa gida Bie ta yi tsaki ya fi sau ɗari amma Adam bai kulata ba. Idan har akwai yiwuwar aurensu ya ɗore to dole ne ya nuna mata kuskurenta akan rashin kunyar da ta yiwa Alhaji.
"And where the hell are my kids?" ta faɗa lokacin da ta shigo gidan. Adam na biye da ita saboda so yake su yi magana musamman akan maganar ganin Counselor da aka ce za su yi.
Tun lokacin da taron dinner ya wargaje bata sake saka 'ya'yanta a ido ba. Ranan da ta kira Adam tace ya turo mata yaranta ce mata ya yi wai tareda su ya wuce Zaria. Cike da gadara tace masa ya kawo mata 'ya'yanta dan ba za ta yarda su zauna a toxic environment ba.
Wata mai aiki ce ta fito daga ta ɓangaren kitchen ɗin gidan. Tana sanye da uniform riga da wando kalar navy blue, kwalar rigar kuma fara, sai ɗanƙwali baƙi da ta ɗaura a kanta.
"Nanny Asabe ina yarana?" Yadda take maganar da tsawa kamar Nanny Asaben wata baiwarta ce, kwata-kwata babu alama na girmamawa a muryarta sai tsantsar izza da isa. Kuma ko a ido mai aikin za ta iya bata shekara goma. Tun lokacin da ta haifi autanta Adnan aka kawo mata Asabe, tun daga lokacin suke tare. Asabe ita ce Mai'aikin da ta jima da Bilkisu. Tana da haƙuri iya haƙuri dan kuwa Bilkisu ba ta da tausayin masu aiki kwata-kwata, zaka mata aiki kamar jaki amma kalmar godiya ba zai fito a bakinta ba. Idan kuwa ka yi kuskure kaɗan yanzu zata hau ka da faɗin stupid, ko ta kama zagin zuri'arka da talaucinka.
Daɗin aiki a gidan shine ana biyan albashi mai kyau sannan maigidan wato Adam yana girmama mutane ga kyauta ba kamar matarsa ba.
"Tunda Alhaji ya ɗaukesu ba a dawo da su ba" Nanny Asabe ta amsa a tsanake
Bie ta juya tana kallon Adam wanda yake tsaye bayanta yana danna waya.
"Adam ina yarana?"
"Suna wajen da zasu samu kulawa"
"Family house ɗinku? Kana so ka lalata min tarbiyyan yara ne?"
Ya ɗago ya mata wani kallo.
As if ta damu da yaran, as if tana nitsuwa ta bawa yaran kulawa. Sai yanzu ma abin ke dawo masa. Nanny ke kula da yaransa 24/7. Yanzu da za a tsare Bilkisu ta faɗi halayen kowanne daga cikin 'ya'yansu baya tunanin za ta ci maki 50% cikin 100%.
"Adam ka karɓo min yara na"
Ya buɗe baki zai mata magana sai kuma ya fasa. Idan ya ce wani abu yanzu sai su wuni suna argument akan abu ɗaya. Yana da mahimman abubuwa a gabansa. Clearly yanzu ba lokacin magana bane.
"Adam, Adam Maidoki come back here" Bie ta bi shi da kira ganin zai haura sama.
Binsa ta yi tana masifa tana kiransa munafuki. Kulle ɗakinsa ya yi, ta yi ta buga ƙofar amma bai buɗe ba ƙarshe ta haƙura ta koma nata ɗakin.
Waya ta ɗauka ta kira Abbie tana faɗin Adam ya ƙi gaya mata ina yaranta suke.
"Suna wajen Nadeem" abin da Abbie ya faɗa kenan ya kashe wayar.
Ta hangame baki tana tsinewa yayanta Nadeem da ya ɓoye mata cewa 'ya'yanta na wajensa. Bayan yau ma da ya zo gaishe da Abbie ta haɗu da shi sun yi magana.
Ta danna masa kira tana jin zuciyarta na tafasa. Wato saboda Nadeem best friend ɗin Adam ne shine zai biye masa su cuceta.
Yana ɗaukan wayar kuwa ta fara masifa. Ƙarshe tace ya yi maza ya kawo mata yaranta. Daga background ma tana jin muryan yaran nata na wasa da ɗansa Imran Junior.
"Anwar, Adnan... ka basu wayar" ta faɗa kewar yaranta na shigarta.
Tana ji Nadeem na kiran yaran su zo su yi magana da Mommynsu amma maimakon su bar wasan da suke su zo da gudu sai cewa suka yi we are coming.
"Anwar" ta daka tsawa kamar yaron na gabanta.
"A'a miye wannan, zaki fasa min kunne ne" Nadeem ya cire wayar a kunnensa.
Yaran basu zo ba sai da Nadeem ɗin da kansa ya tashi ya kai musu wayar.
Tambayar yaran na farko shine ina Daddy?. Wato basu ma missing ɗinta ba balle su damu da rashin ganinta na sama da sati guda.
Gaskiya ba za ta yarda ba. Dole yaranta su sota fiye da Adam wannan kaɗai zai sa idan ta rabu da Adam ta iya riƙe yaran a wajenta ba tare da sun yi tunanin Babansu ba.
Bayan sun gama wayar ta shiga tambayar kanta me yasa yaran suka fi shaƙuwa da Adam akanta?
Ta fi maida hankali akan AdBie. Da kuma kasancewarta influencer a instagram. Idan har kaga tana tareda yaran ana wasa da dariya to akwai camera ne da ke ɗaukarsu wanda za a ɗaura a Instagram da hashtag na Happy Family ko kuma My Boys.
Komai zai canja idan ta samu ta rabu da Adam. Za ta ware musu lokaci ta dinga basu kulawa, infact za ta kaisu vacation ne, su ɗan je su huta...
***
A reception suka tsaya dukkansu biyu babu wanda yace da ɗan'uwansa cikanka. Abbie ne ya recommending musu wannan waje.
Kowanne a cikinsu shi ya kawo kansa. Adam ne ya fara zuwa saboda Abbie yace ƙarfe goma na safe aka booking musu session tareda counselor ɗin. Kafin ya fito sai da ya je ɗakin Bie ya tambayeta ko ta shirya tace masa yai tafiyarsa ai ta iya driving.
Sai da ya zo da kusan minti ishirin kafin ta iso.
Kasancewar joint therapy za a yi musu shi yasa likitan na su wanda ya kira kansa da Dr Mansur Lugga ya cewa Adam sai matarsa ta zo za a fara session ɗin.
Minti biyar da zuwan Bie aka ce su shiga ciki.
Adam ya sake miƙawa Dr Mansur hannu suka gaisa duk da kuwa ɗazu sun gaisa a reception.
Bie dai kallon mutumin take tana ayyana cewa tunda therapist ɗinma namiji ne tabbas ba za a mata adalci ba. Gashi mutumin tsoho ne dan zai iya kaiwa 55yrs zuwa 60yrs.
Dr Mansur ya nuna musu inda za su zauna. Couch ɗin mutum biyu ne shiyasa da Bie ta zauna ta takura kanta can gefe saboda kar ma ta mannu da Adam. Dr Mansur duk yana lura da yanayinta.
Bayan sun zauna sai ya fara yi musu bayanin ko shi waye, da kuma qualifications ɗinsa. Asalinsa Clinical psychiatrists ne da ya yi aiki a ƙasar waje. shekaru goma shabiyar da suka wuce da ya dawo Nigeria sai ya fara couples therapy ko marriage counselling. Hakan ya biyo bayan matsalolin da shima ya fuskanta da iyalinsa, wanda sai da suka shekara guda basa tare kuma ba wai rabuwar saki bane. Daga ƙarshe a hankali suka shawo kan matsalarsu suka dawo da soyayyarsu. Wannan dalili yasa ya buɗe marriage counselling centre a nan Abuja. Yanzu shi da matarsa shekarunsu 33 da aure, suna da 'ya'ya huɗu.
Dr Mansur ya fara tambayar Adam akan ya bashi taƙaitaccen bayaninsa.
Adam ya ce " sunana Adam Salihu Maidoki amma ana kirana da Babangida"
Bie ta ja wani tsaki. Ta tuno ƙaryan da ya fara mata kenan farkon haɗuwarsu.
Adam ya kalleta ransa a ɓace. Koba komai wannan mutumin ya kai ya haifeta.
Dr Mansur ya ce " ina jinka Mr Adam" dik da kuwa ya samu duk wani bayanan da ya ke so daga wajen Abbie
"I'm 38yrs. Ina da yara biyu maza, Anwar da Adnan. Na yi degree a fannin Economics, ina da masters biyu ɗaya a Estate Management, ɗaya kuma a Communications. Ni founder ne kuma CEO na Big House residences. Sannan ni co-founder ne na AdBie Couture"
"It was my idea, my business, AdBie nawa ne ni kaɗai " Bie ta katse shi
Dr Mansur ya ɗaga mata hannu yace "Mrs Maidoki ki yi haƙuri ya gama bayaninsa"
"Mrs Maidoki? Oh please!" Ta wani tura baki.
A da tana son a kirata da sunan nan sama da a kirata da komai. Amma yanzu kam ba sunan da ta tsana kamar Mrs Maidoki.
"Dr, henceforth ka kirani da Bilkisu El-Sayed, please"
Dr Mansur yayi murmushi. Ba yau ya fara ganin ma'aurata masu rigima har suke ƙyamar a haɗa sunansu dana junansu ba.
Adam bai sake cewa komai ba. Wannan yasa Dr Mansur ya maida tambayar wajen Bie.
"My name is Bilkisu Imran El-Sayed, amma kowa na kirana da Bie" ta fara bayani bayan ta watsawa Adam harara.
"I'm 32yrs. Na yi double majors a History and Design. Sannan na yi masters a Fashion Design. Ni ce founder kuma CEO na AdBie Couture. My company shi ne first couples wear brand a Nigeria, and we are the best. Clients ɗinmu are all over the world. Lokacin da shugaban ƙasar..."
"And there she goes again, business before family" Adam ya katseta
"Adam kar ka shiga maganata. And choosing business ba laifi bane dan nafi wanda ya zaɓi karuwa akan familyn sa"
"Ya isa" Dr Mansur ya dakatar da su, idan yai shiru abin ba zai ƙare ta daɗi ba. Akwai couples ɗin da a gabansa matar ta mari mijin garin cacar baki. Akwai kuma wanda suka zo last year a gabansa suka kaure da faɗa ƙarshe sai da ya kira Secretary ɗinsa kafin aka iya raba su. Daga ranan kowa yayi hanyarsa basu sake dawowa ba sai kusan wata bakwai, sai ga matar har da ƙaramin ciki da zai iya haura wata huɗu.
Shi yasa duk da jimawarsa akan wannan aikin ya yarda ɗari bisa ɗari da maganar da ake cewa *tsakanin MIJI da MATA sai Allah.*
Akwai ma'auratan da zasu zo idan ya saurari case ɗinsu sai ya ji kamar ba wuya za su dawo dai dai, daga ƙarshe sai su zo su rabu. A mafiya yawa irin waɗanda yake tunanin za a rabu shi ne kuma za ka ga ma'auratan sun gyara tsakaninsu.
Shi yasa ya ke treating clients ɗinsa differently, dan kowanni aure akwai abin da aka gina shi akai, akwai kuma hanyar da aka bi har aka kai ga samun saɓani.
Ya ɗauko takardu guda biyu da biro ya miƙawa kowannensu. Ya ce " tun daga farkon aurenku har zuwa yau ina so ku rubuta abubuwa guda 10 da ba kwaso game da junanku."
Bie ta ja siririn tsaki dan kuwa a tunaninta komai ma na Adam Maidoki bata so. She hates him. She hates everything about him.
Tun kafin Adam ya fara rubutu har ta kai layi biyu tana rubutu tana danna biro kamar za ta yaga takardar.
Bie ce ta fara gama rubutun, ta cewa Dr Mansur ta gama. Shi kuwa ya karɓi takardar a hannunta.
Bayan kamar minti biyar sai Adam ya ce ya gama na shi. Dr ya karɓa ya karanta duka biyu.
Chan ya ɗauko littafinsa yayi wasu rubuce-rubuce. Sai ya ce musu zai basu takarda kowa ya karanta abin da aka rubuta a bayyane.
Ya fara miƙawa Adam takardar da Bie ta rubuta.
Adam ya fara karantawa
1- na tsani Adam saboda maciyin amana ne (TRAITOR, CHEAT, EVIL, SNAKE)
Adam ya kalleta yace " Really?"
"Yes" ta faɗa tana zaro ido
Dr Mansur yace "Mr Maidoki ka cigaba da karantawa"
2- Adam eats a lot (like kaman wanda ya taso a yunwa, ya dinga ci kenan kaman wani Almajiri)
Adam ya yi murmushin gefen baki. Dama tun farkon aurensu take wannan ƙorafin. Tun yana damuwa da hakan har abin ya dena damunsa.
Ya cigaba da karanta takardar
3- Adam baya respecting privacy ɗina
4- Adam snores
5- Adam bai damu dani kamar da ba
6- sometimes yana behaving kamar wani ɗan ƙauye.
7- he's not romantic anymore. Ba abinda yake so sai sex. Ba zamu iya kwana tare mu cuddle ba sai ya ce shi sex. I hate that.
Adam yai shiru wani ɗaci na taruwa masa a maƙoshi. Har Bilkisu za ta tuhumeshi da yawan sex. Ita da ta saka musu sex timetable kuma ya amince da hakan saboda baya son takura mata.
A hakan ranan da timetable ya faɗa za su yi sai ta fara kawo excuses wai ta gaji. Akwai ranan da tace ta gaji yayi ƙoƙarin nuna mata bata isa ba sai ta kama cewa idan ya mata ƙarfi za ta yi ƙaransa for rape. Daga ranan bai kuma nemanta ba for two months ya shareta. A wannan weak moment ɗinne ya biyewa abokinsa Bash ya aikata abinda ya zo ya zame masa jaraba.
Sai bayan wata uku da kanta da ta taso da buƙatarta ta nemeshi. Still bata bashi haƙuri ba. Ya fito daga wanka ta cire towel ɗinsa ta shiga kissing ɗinsa, daga nan kuma suka biyawa junansu buƙata.
Sai bayan kwana biyu Adam ya mata maganar abin da ta faɗa ranan. Sai ta ce masa wai wasa take. Bata nuna abin da ta faɗa is a big deal ba.
Saboda yadda zuciyarsa ya tafasa ko iya ƙarisa karatun bai yi ba ya ajiye takardar yana ƙoƙarin saita nitsuwarsa.
Dr Mansur bai takura shi akan ya ƙarisa karanta sauran biyar ɗinba dan abubuwa guda 13 Bilkisu ta rubuta ba goma ba.
Ya miƙawa Bie takardar Adam yace ta karanta.
Ta karɓa ta fara karantawa
1-Matata ba ta yarda dani ba.
"Ta ya zan yarda da maƙaryaci" ta juya tana masa kallon sama da ƙasa
2- bana jin daɗin yadda ta fi bawa business mahimmanci sama da gidanta. Ina buƙatarta, yaranmu na buƙatarta.
3- bana jin daɗin yadda Bilkisu take ɗaura rayuwarmu a Instagram da Twitter
ta wani gyatsina fuska ta ce "ɗan ƙauye"
4- bana son tsarin timetable da muke da shi na intimacy. 2 days a week akwai cutarwa. And sometimes 2 days a satin ma sai an ƙare da rigima
Wani dariya Bie ta fara. Sai yanzu ma faɗansu na ƙarshe ya dawo mata da ya ce duk abinda ya aikata har da laifinta a ciki.
*"Duk abinda ya faru laifinki ne Bilkisu. We don't have a good sex life. You're my wife, amma kullum sai na roƙe ki. Is that fair?"*
Ta taƙaita dariyar tace " Adam Maidoki, i cursed the day i marry you"
"Mrs Maidoki Dan Allah banda irin wannan maganganu a nan"
"Dr ba dan Anwar da Adnan ba da na jima da kashe wannan baƙin macijin. He has no right to cheat on me. Time table or no time table bai justifying abinda ya mini ba. Zai zo min da sauƙi idan aka ce wata ce daban Adam ya nema, amma cheating on me with my best friend is the highest betrayal da bazan taɓa yafewa ba."
"Dr ka ga rashin trust dana yi magana akai ko. I told her ba abinda ya haɗani da Labiba"
"You're a liar Adam Maidoki" Bie ta daka masa tsawa
"Ki yarda ko kar ki yarda, ni ban kwana da ƙawarki ba"
"Dr ka ji ƙaryar shi ko. He's always denying it. But Allah ya kama shi ina da evidence"
Jakarta ta ɗauka ta fara lalubo wayarta dake ciki. Ranan da Labiba ta turo mata hoton nan bugawa ne kawai zuciyarta bai yi ba. Da Adam na gida ranan da ta turo mata hoton da ba abinda zai hana ta daɓa masa wuƙa. Ko lokacin da ta ga nudes ɗin da Labiba ta tura masa ba ta ji tashin hankali irin na wannan hoton ba. Kwana uku ko bacci bata iya yi ba. Lokacin ne kuma aka fara shirye-shiryen anniversary and Ya Jamal ya bata haƙuri akan ta bari a gama komai cikin kwanciyar hankali.
"Waye a wannan hoton?" Bie ta nuna masa screen ɗin wayarta
Adam ya zaro ido waje bai san da wannan hoton ba. Yaushe haka ta faru?.
"Dr ka tambaya min shi, wannan Adam Maidoki ne ko ba shi ba ne?"
Dr Mansur ya sunkuyar da kansa ya fara rubutu...