ZULFAH

page 8

by @rabiattu0444

_*🍏ZULFAH🍏*_

         _page 8_


  _@🫰🏻Ummu Maher_

      *{MRS GREEN}*




_*please kuyi following ɗin littafin Zulfah on arewabookstore🫰🏻*_

ZULFAH:: https://arewabooks.com/book?id=64ff0277d73b80a18ea59540

________________________

    *GAWURTATTU 3*



_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!

AMMA ARAB!!!*_


_kai daga jin sunan kasan sunan ya

amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo

muku wani supplement na gyaran jiki

mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB

gidan ƙamshi_


*MUSUK*

*MADARAR TURARE*

*KAJIJI*

*ROT*

*SANDAL*

*HUMFUR*

*SANDAL FLASK*

*SANDAL WUD*

*AALUT*

*GAF-GAF*

*JANNAMI*

*ƘWALAKCA*

*MAHAHABSUFYAN*



*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA

WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA

AYI BABU KE*

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

***

/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S


*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*

Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224


*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*


*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*


*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*


*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*


*MULATO SOAP*

*FACE CREAM*

*FACE SOAP*

*MULATO WHITENING LOTION*

*HAIR GROW OIL*

*HAIR GROW CREAM*

*KAR-KAR OIL*

*MINT LEAVE OIL*

*ANTI PIMPUS SOAP*

*AƘWAI SABULUN NANKARWA*


sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

*ABIN BUKI*

*ABINCIN OFFICE*

*SNACK*


KAMARSU👇🏻👇🏻


*WAINAR MASA*

*SINASIR*

*MEAT PIE*

*CINCIN ƊAN LAUSHI*

*CUP CAKE*


DA DAI SAURANSU.

AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻



_ZULFAH 1_



...........Ji tayi kamar ana kallonta,da sauri ta ɗaga lulu eyes ɗinta tana kallom wanda ke mata wannan kallon tsaf ɗin,don ita arayuwarta ta tsani kallo sosai saboda hakama bata fiya son fita ba saboda kallon da maza ke binta dashi tamkar waɗanda basu taɓa ganin mata ba.

ganin shi take kallo da rinannun idanuwanta yasa yaji wani irin abu ya tsarga masa tun daga kansa har zuwa tafin hannunsa,ya ƙaraso wajenta cike da fara'a ya matso kusa da ita zai zauna.


da sauri na miƙe tsaye ina ƙare masa kallo,kallon tas nake masa ma'ana kallon baka isa ba shima kallon nawa yake,a maimakon ɗazu da annuri yanzu kuwa fuskarsa ta canja alamu sun nuna cewa tabbas yaji haushin abinda nayi masa,kallon kyama nake binsa dashi saboda ni gani nake don yaje ƙasar waje ne zai nunawa mutane ya koyo iskanci ko kuwa me?ahankali na buɗe bakina na fara magana cikin tsiwa.


"look Bilal,ya zaka zo ina cikin shaƙatawa ta ka nemi damar min rayuwa haba wannan wacce irin rayuwace wannan?".kasa magana Bilal yayi ya shafa ƙwantaccen gashinsa wanda ya ƙwanta masa luf,bai ƙara magana ba ya tashi ya fita duk ransa a matuƙar dagule,ko ɓangaren mahaifiyarsa bai shigo ba yazo wajenta amma da abinda zata saka masa kenan?haka ya wuce ɓangaren nasu cikin matsananciyar damuwa.


   ****

"Momi ki duba fa ki gani?ace yaya ya dawo amman ba zai fara zuwa wajenki ba?sai ya fara zuwa wajen wannan mara mutuncin?wacce bata ganin kan kowa da gashi?".

hajiya Maryam ta haɗiye wani irin ƙaton malulun daya tokare mata maƙoshi sannan ta ce"ni wallahi na rasa abinda yarinyar take dashi?da maza suke binta tamkar wata uwarsu?ki duba fa kiga yadda yaron nan mata suke binsa?yana wulaƙantasu amman tun yana can ya dameni da maganar wannan yarinyar,shiyasa yanzu sam bana zuwa sashen waccan fitananniyar tsohuwar,don daga ita har jikarta ba mutuncine ya ishesu................"

tana cikin maganar Bilal ya shigo,ransa duk a matuƙar jagule saboda yadda yaso ya samu Zulfah ba haka yaso ya same taba,tun dama ita Zulfah macece me yiwa maza ƙwarjini ba kowani namiji ne zai kalle ta kallon farko yace yana sonta ba,dole sai yaji ɗar ɗar da kuma haɗi da ɗan tsoronta kafin ya faɗi abinda ke ransa,idanma har kayi dauriyar yin maganar saboda tsare gidanta.


Hajiya Maryam ta ɗan tura bakinta gefe alamar ka ji dashi,wai an saci zanin mahaukaciya duk da tana cikin matsananciyar murnar dawowar tilon ɗanta namiji bai hanata fara faɗa ba tana ce wa.


"to sannu shanyayye! wanda uwar Zulfah ta shanye tun kafin tabar duniya,wallahi tallahi ka bani mamaki Bilal me akayi akayi wata Zulfah,da tun yanzu zaka banbantata dani kaf duniyar nan kana da wanda ya fini ne?da har zaka nuna min Zulfah ta fini?to ka buɗe kunnuwanka ka jini,tun kafin ubanka yaji cewa kana son Zulfah ka cirewa kanka sonta na dole,saboda nasan yana jin komai zaije ya garxaya ya faɗawa waccen fitinanniyar tsohuwar tazo ta fitine mu,don wallahi rufe idona zanyi inci mata mutunci,don idan tana tutiya da ɗanta ni Maryam bata isa tayi min da nawa ba,saboda haka ba gilin gilin ba tayi mai,kuma hawainiyarka ta kiyayi ramata don naga kanka yana rawa sosai sai na ɗoraka bisa hanya".


Nan dai Hajiya Maryam ta shiga faɗawa ɗanta illar auren Zulfah ta ƙara da ce wa"ubanta ma haka yasha wahala da uwarta,ta shanyesa sai abinda tace ya yi shi yake yi kai ko cewa tayi faɗa rijiya ka mutu zai faɗa saboda mugun halinsu a jini yake".shi dai bai iya ce mata komai ba ya tashi ya wuce ɓangarensa,yana jin wani irin mugun son Zulfah na ratsa masa ko ina na jikinsa,son maso wani ƙoshin wahala abinda ya faɗa azuciyarsa kenan,sai kuma wata zuciyar ta sanar dashi fa'idar yin haƙuri,yau da gobe sai Allah a haka yana gwaji Xulfah zata so shi.



yana shiga ɗakinsa,ya yi tsuru yana kallon ɗakin saboda hotunan Zulfah da akabi aka cire masa baki ɗaya,ya cika da mamaki sosai duk da yasan ba kowa ne zaiyi mai hakan ba banda mahaifiyarsa,babu yadda zaiyi da ita duk da yadda zuciyarsa ke yi masa wani irin ƙuna,ya dafa saitin zuciyarsa yana ce wa"ya Allah Ka sanyaya zuciyar mahaifiyata akan farin cikina Zulfah,ya Allah ka bani Zulfah ya Allah ka sanya mata sona ko yaya ne."ya faɗi hakan yana sakarwa kansa shower a banɗaki.



wayarsa ya buɗe tarr hoton Zulfah ya fito akan kyakkyawan screen ɗin wayarsa,tana murmushi tayi kyau sosai dimples ɗinta sun lotsa sosai,ya yi murmushi yana shafa dai dai fuskarta yana ji dama ace yanzu tana ƙwance a ƙirjinsa,ya rintse idonsa yana jin wani irin daɗi yana ratsa sa randa akace gashi ga zulfah sai ya ahayar da ita zumarda bata taɓa ɗanɗana ba saboda yadda yake sonta,da yake jinta ajikinsa ba wai iya son ƴan uwantaka kaɗai ba,a'ah harda wani irin gigitaccen son da bai san yana mata shi ba,tun tana ƙaramarta yake sonta amman bai nuna mata hakan saboda ko kallonta yayi sai yaji gabansa na faɗuwa.ayanzu abu biyu ya rage masa addu'ah sannan ya kama ƙafa da hjy inna saboda yasan yadda take sonshi da ƙaunarsa.yayi wankansa cikin jin daɗi da annushuwa ya fesa ƙwalliyarsa cikin ɗanyar shaddarsa drk blue kasancewarsa fari ba ƙaramin kyau yayi ba yadda kasan wani balarabe ya fito yana angiza wani irin ƙamshi mai sanyaya zuciya ya wuce wajen hajiya Innah.


       ********

Yana fita hjy innah ta shigo,ta kalle ni sosai sannan ta ce"haba haba fisabilillahi Allahu ya Allah,wannan yarinya ko ƴar bani na iya yanzu don Allah Zulfah meye laifin Bilalu?yaro da ɗan jan kunnensa kamar bature,ni sai dana nutsu ma naga duk kamar da ake cewa kunayi cutarsa akeyi,don yafi kyau da komai ke dai wannan cikon da kike yine yake ruɗarsu".ta nuna ƙirjina tana hararata,na gane abinda take nufi saboda haka ban tanka mata ba ban kuma tashi ba,har ta gama rigimarta ta wuce tana bankamin harara tamkar idonta zai faɗo.

tana wuce na ce"jarababbiyar tsohuwa kawai."



     ¢¢¢¢¢¢¢¢¢

*ALIYU*


a hankali yake tafiya yana tuna abubuwa da dama na rayuwa,ayanzu ƙarfin mahaifinsa ya ƙare shi ya kamata ya zama uba awajen ƙannensa,yana son cikawa ƙannensa burinsu na karatu amman ayanzu kaf ƙannensa babu mai zuwa makaranta,wannan abu yana matuƙar ci masa tuwo da ƙwarya,duk sanda zai fita bai wuce ya samo ɗan abinda za'a sanya a baki ba,kullum ƙoƙari yakeyi don yaga kaf ƙannensa basu nemi abu sun rasa ba,amma ya gaza yin hakan saboda halin rayuwa.


wajen wani abokinsa ya wuce a gareji,wanda yake aikin kanikanci yana zuwa ya sameshi yana aikinsa ya buɗe wata hamshaƙiyar mota yana gyarawa,yana hango Aliyu ya saki fara'a don Aliyu mutumin kirkine sosai kuma ya isa akirasada aboki nagari,don duk babunsa bai yarda ya yi roƙo yafi ganewa duk wahalar da zaisha yasha ta shi kaɗai,har ya samu ya kawo gida amman bai yarda da zubar da mutuncin kai ba.


Ahmad ya ce"a'ah yau su gadanga ne awajen namu?sannu da zuwa yau babban baƙo ne yazo min".ya faɗi hakan yana ɗakko masa gujera fara ta roba a cikin rumfa,na zauna ina murmushi na ce"haba Ahmad yanzh nine babban baƙon?".Ahmad ya ɗan murmusa sannan ya ce"haba Aliyu ai kai kullum baƙo kake awajen kowa,saboda kamun kanka da riƙe mutunci,yanzu Aliyu duk wanda ya ganka yasan kana buƙatar taimako musamman yadda kake da ƙannai masu yawa,saboda haka dole a tausaya maka".


na ce"dama Ahmad wata shawara nazo nema awajenka"?.


Ahmad ya ce"ba komai faɗi abinda kake son faɗa,a shirye nake da in baka shawarar da ta dace Aliyu don nima kana bani shawarwari kuma idan nayi amfani dasu sai inga sunyi sun zauna raɗau."dariya nayi sannan na fara faɗa masa abinda ya kawo ni ɗin...


sosai ya girgiza da jin abinda Aliyu ya faɗa masa,da sauri Ahmad ya ce"haba haba Aliyu da hankalinka da komai ka aikata haka?yaushe ka fara rashin tsoron Allah...........✍🏻.




*To kowacce shawara Aliyu yake nema?har Ahmad ya tsorata?sai a feji na gaba zakuji yadda aka haihu a ragaya,acikin wannan littafin na Zulfah*😄yanzu aka fara tafiyar don aƙwai daddaɗar tafiya agaba.🫰🏻🫰🏻🫰🏻🫰🏻.



MRS GREEN CE✍🏻

***