7
by @nanadiso10
7
LATYFAH IMAM
Nana diso
WANNAN SHAFIN NAƘINE HAJJ HAUWA🥰
Tsoro, firgici, kaɗuwa yanayi, suman hucen gadi shine halin da latyfah imam tashiga, atake idanuwanta suƙa kaɗa cike da ruwan kwallah mai nuni da hawayen da yaciƙa yafara bin kwancinta, gaba dayaa duniyar tata taji ta ɗauke mata wani ƙalar dumm kunnanta yayi yadda ƴar sandar maccen ta dagowata daga zaunen datake yasa tafara dawowa cikin hankalinta, tarasa me zatayi addu'a ko kukan kokuma ihu. Sautin kukan nawal da kururuwar da ammy takeyi yasata kara zubawa gawar Abdul idanuwa, atake tafirgita tare da gigicewa tana kallon ammy dake kokarin kwaɗa mata ƙarfe ana riketa " Kutafi da'ita ku kasheta kokuma kubarni nakasheta nazhiga uku tsinanniyar yarinya ta kashemin ɗa, daman kin auresa dan ki kashe shi?." Duk irin yadda aliyu da ammy ke zaginta bata dago ba sai idonta da yasauka akan taƙardar da tasakata ƙara fashewa da kuka, sosai ta wara idonta tashiga karantawa _NI ABDULKARIM MAI LEMA 'NASAKE KI LATYFAH IMAM BABUNI BABU KE'_ wani sabon hawayene yafara zubar mata zuciyarta kamar zata fashe saboda zafi, daya daga ciƙin ƴan sandan ne ya hanƙaɗata itakuma dayar tashiga tura ta tana kokarin saka mata ankwa. Alokacin ne takara shiga ɗimuwa rikici da gigita, " Ban kashe shi ba banice nayi kisan ba wallahi ban kashe shi ba." " Idan baku fita da'ita ba wallahi sai na kasheta ni cewar ammy tana jijjiga abdul da akashiga yimasa gwaje gwaje. Tare da jami'an tsaro da ammy da mumy harda aliyu fa umar aka tafi asubuti inda ammy tabada damar amakata a kotu. Mumyce tace " dadai kinbari angama bincike." Tana kuka kamar ranta zai fita tashiga faɗin" Haba mumy wanne kotu kina ganin tayi kisa nasan ta kashemin abdul ta kashemin ɗana tashiga faɗa tana mai rusa kuka." Aliyu ma da idonsa gaba daya yayi jajir saboda tashin hankali sai kiran wayar dady yake amma taki shiga haka ta yaya hamid shima taƙi babban yaron dady da aka tafi dashi shikuma tana shiga amma kuma ba'a dagawa. " I can't find them amiey akashe latyfah akasheta inbahaka ba ni zan kasheta yafaɗa kuka yana ƙufce mata.
Karfin arzuki da rashin gata ba karya baniba ko ba'ayi maka bayani ba zaka tabbatar da mai kudi asaman talaka yake batare da anhuce da'ita police station ba akayi babbar kotu da'ita wanda tuni manyan ƴan sanda sun haɗa rahotunta na statement, bata gani bataji bata sauraro tadawo mahaukaci babu abunda kunnenta ke jiye mata saka da ta kasheshi? Haka tata kaddarar tazo wannan shine tukuicin alkhairi wannan shine sakamakonta, sauƙar babban kulki dataji akanta yasa hawayenta kara tsiyaya, ko da suka isa kotun akwai case na mutune sosai, amiey da mumy da duk wasu ƴan uwa da yaran mumy kowanne ya isa kotun domin na buƙatarsu nawal ma da mai gadi sun isa kotun, mubugun zuciyarta bazai iya bayanuwa ba radadin da zuciyarta take mata bazai iya lissafuwa ba, tashin hankalin da take ciki ƙanta yakasa dauka, acikin duniyarta ta haukaci ta makance takuma kuramce!
Ya mai girma mai sharia ayau 12 ga watan April munsamu case din matar da takashe mijinta ta hanyar caccaka masa kwalba akansa saboda zaiyi mata kishiya.
Sai alok'acin ta dago ƙanta ta kalli alkalin tana kara rushewa da wani sabon kukan, iyami datashiga cikin ihu da kururuea tashiga faɗin wallahi bata kasheshi ba sharri za'ayi mata wallahi bata kashe shi ba karya sukeyi azzalumai, umarni aka bayar da fita da iyami dake tsinewa ahalin mai lema. Sosai ta runtse idonta zafin zuciyarta yana kara tsananta haɗe da zafin da kanta keyi.
"Nine Barrister Suleiman nine lauyan masu ƙara."
" ko zamu iya ganin lauyan wacce ake ƙara?"
Ya mai girma mai shariah batada lauya.
Tunda Barrister Suleiman yafara magana batace masa ƙanzil ba har yagama sai kuka datakeyi hakan yabawa kotu daga shariah zuwa nan da watanni biyu karshen watan. " Dan haka kotu ta aika wacce ake tuhuma da laifin kissan mijin zuwa gidan yari. A hankali ta ambaci innalilahi wainna illahirrajiun tare dakara rushewa da kuka! Atake aloƙacin ƴan sanda suka shigo suka tafe da'ita amiey nata tsine mata albarka.takalmin da su laila suka shiga wurga mata yasa ƴan sanda tsawatar musu. Ko da aka fito iyami tana tsaye an rirriketa kallon iyami tayi tace " iyami an aikata ba banyi ba bansan tayaya hakan yafaru ba iyami anzalunceni." " nasani latyfah imam bazaki taba aikata ba bazaki taba ba Allah yatsinewa zuri'ar mai lema Allah yasakawa talaka abisa zaluncin da wasu masu kudin suke musu hajiya fatima Allah ya wulakanta ahalinki kamar yadda kika wulakanta ahalina inshaa Allahu zuri'arki sai sun wulaƙanta, daya daga cikin ƴan sandan ne ya kifawa iyami marin da sai data tsugunna saboda masifar zafi da radaɗi. Kukan latyfah imam ne yayi karfi ganin yadda suka zage suna duƙan iyami, duk yadda sukaso iyami tayi shiru batayi ba, ganin yadda suke duƙanta yayi yawa yasaka dpo din tsayar dasu.
Amiey dake faman kuka mai ƙarfi ganin kuma ankasa samun su dady har yanzu yasaka cikin wani babban tashin hankali, aliyu ne yashigo ciƙin gidan hankalinsa atashe hakan yasa sauran ƴan uwan nasa suma ƙara tayar da hankalinsu, mumy da itama al'amarin yagigita ganin yadda likitocin sukace ai babu alamun rai atattare dashi yasata firgicewa da shiga dimuwa dan ita bata tunanin latyfah imam zata iya wannan aika aika amma ganin yadda taƙi magana a kotu yasata yarda da tabbas ta aikata ɗin. Aliyu kuwa zaman dirshan yayi akasa hankalinsa yana ƙara tashi kuka yakeyi mai cin rai hakan yasa sauran ƴan uwan nasu kara ƙarfin kukansu kenan abdul yarasu? " ya mutu ko Ali? Ya mutu? Ta kashemin shi? Shikenan ta kashemin shi." Kallon mahaifiyar tasu yayi cike da tausayinta dan duk cikinsu tafison abdul duk da rashin jinsa daman hausawa nafaɗin fitinan nan ɗa akwai shiga rai." amiey Anrasa gawar tasa likitoci sunyi duban duniya ba'agansa ba." Banganeba hajiya tafada? . Ansace gawar yafada yana kuka. Suman mahaifiyar tasu ne yasasu kara sakin wani sabon ihun, laila nakiran ƴansandan suna kara gayamusu. Cikin awanni 24 anrasa inda gawar takasance duk yadda akasaka mataƙan tsaro da daƙatar da asubutin da akayi da kuma bincikar ma'aikatan da ake kanyi da duba cctv camera dasuka shigayi ba'a ga fitarsa ko motsinsa ba. Wata dattijuwa ce ma yanzu dake zaune tun wayewar garin safiya agurin ta ƙalli dan sandan tace " officer wakuke nema ne haka? Tunjiya naga asubutin cike da mutane gashi dukanku da bakaken kaya." " Wallahi babaah wani yarone yabata ɗan gidan alhaji mai lema jiya muka kawoshi asubutin amma an nemesa an rasa duban duniya ba'agansa ba." " ikon Allah naga wata mata tazo nan amma babar macece datazo sai naga tabi tacan bayan asubutin amma gaskiya banga wanene suka rike ba amma tabbas naga jini yana dan diga aƙan yaron to sai nayi tunanin ko sallamarsu akayi ne." Afurgice dan sandan yajiyo yana kallonta tayi masa bayani dallah dallah amma duk mutanen gurin sai suka nuna ai basu masan hakan tanan yanakara tabbatar wa akawai sarqaqqiya a wannan abun.
Nawal ce tsaye gaban Adam tana zuba masa idanuwanta da suka kaɗa sukayi jajir. " ina tsoro Adam ina tsoro sosai kada akamani ni bakowa bace ba kaga masu kudin nan zasu iya komai domin yaransu kai kaga matakan tsoron dake garin nan?." Murmushi yayi kamin ya ajiye maga cheque na 10m sannan da mukullin gida da mota. Zaro idanuwa tayi tana daukar takardar " Are you serious Adam? DanAllah da gaske ta fada tana fashewa da kuka. " Bana alkawari in ƙi ciƙawa yarage naki idan kika faɗa ko kikayi subutar baƙi yarage naki dan banida hannu aciƙin komai yafaɗa yana nuna mata video din sanda ta zuba masa kwayoyin kodin da koƙen da sanda ta fasa ƙansa da kwalba da sanda ta caka masa." Bakaramin tashin hankali tashiga ba amma ganin wannan uban ƙudin yahanata damuwa sosai " Har abada babu mai jin haka tafada tana zuba cheque da muƙullan jaka." " wannan kuma yarage naki." " amma kanada labarin anrasashi aciƙin asubutin da aka kaishi?." Da dan mamaki yaƙalleta kamin kuma yace " Koda saceshi sukayi bazai rayuwa ba kwayoyin da muka zuba masa bazasu taɓa barin kwakwalwarsa tayi aiki ba." Taƙe taji gabanta kuma yawadi wannan wani ƙalar rashin imani ne? Last maganarsa ce tashiga yawo aƙanta " Nawal kije kiyi aure nima am married yanzu and nayiwa ƙaina alkawari I will be a better person saboda dadyna, bayan ta buga masa kwalba kuma yace " Latyfah I want you I have feeling for you." Irin yadda yadinga maganganu akan matar tasa yashiga yawo akanta. " zaki iya fita no more harkallah tsakanin mu." " thank you tasaka kai tafita.
Amiey don't kill yourself ammy addu'a zakiyi masa danAllah laila tafada tana kuka. " I want to kill latyfah imam da hannuna inaso kuje ku kwace gidan mahaifinku yau ɗinnan duk wani tallafi da ake basu ajanye. " amiey angama inji lailah tagayawa aliyu a waya yace ta tsaya zaije a dakko aboƙanansa ƴan iska.
****
Yanzu da kadakko wanga yaro ka ajiyeshi anan me zamuyi masa kada fa ɗan mutane ya mutu kajawowa ƙanka wata masifa. Banza yayiwa kakar tasa yana cigaba da ƙinkin ƙan nasa wayarsa ce tayi ringing " abuja yafaɗa cikin sanyin murya irin tasa yana mai kashe wayar ya ajiye gefe, yanzu ba magana nake maka ba farhan? Da ƙanka sai kace kwallon mangwaro zuba mata idanunsa yayi da yasata kara wuƙi wuƙi da idanunta tana faɗin shegen ido kamar na mujiya ko katashi kakai report kokuma nakira mahaifinka. Ganin tafara dakko wayarta yasashi faɗin " Ki kirasa zance kekika aikata". Kujimin jairin ɗa to yana ma numfashi ta liƙa tare da kallon sa, " subhnlhi wanda yayi wanga aiki yacika azzalumi kaji dazun nan aka bada sanarwa dan gidan alhaji lema da yarasu an sace gawar, da mamaki yajiyo yace " ina kikaji?" A'ina zanji kuwa? Bayan radio." Okay kawai yace " yana kara kiran driver dinsa sannan yaƙira mom dinsa yasanar mata komai kuma gashinan zai tawo a mota. " Farhan kada kayi wasa da rayuwarka danAllah." " mom kiyi supporting dina kada kiyimun baki." Babanka yasani ta jiwo masa tambayar? " yes Mom danAllah kizaka ready nasan zaki iya daƙin da ake ajiye minister nakeso asakashi yadda zai samu tsaro. " " Duk wannan bakada damuwa cewar mom tana katse wayar.
<
Karatun qur'ani ne ke tashi aciƙin makiken daƙin da yakasance mamallakin mutum daya kasancewarsa mai tsananin addini yasaka duk sanda zai kwanta sai yakunna suratul baƙara bama yanzu da mutuwar take zame masa sabuwa duba da sabawa dayayi da rayuwa da matarsa, tsananin sha'awar dake damunsa acikin satiƙan nan tunda suka dawo kasar nan yasanya shi fara tunanin maganar ummynsa nayin aure, duk yadda yaƙai da matsantawa ƙansa gurin sallah da karatun alkur'ani da azumi amma sha'awar tasa bata gushewa wannan ke ƙara tabbatar masa da bakarmin gata abiy yayi masa ba domin aurar dashi da wuri, shekararsa kusan 12 tare da amina rashin haihuwar da suka fuskanta afarko ne amma akallah da yanzu yanada budurwar ƴa mai shekara goma 11 a duniya ko ɗa. Yanada shekara 28 mahaifinsa yayi masa aure wanda a lissafinsa yanzu shekararsa 40 daidai, karar sautin wayarsa dake vibration yasashi zura hannu ya dauka tare da karawa akunnensa. " Abni baku fita aikin ba?" " Ya ummy barka da safiya yajiƙinki?" " Am okay yanzu ina aikin danAllah karka bawa mahaifinka kunya danAllah kaga ƙarfinsa yaja yanzu yana buƙatar taimakonka." " Toh ummy bari nashirya yafaɗa yana katse wayar." Sai da yayi addu'ar tashi daga bacci kamin yayi addu'ar shiga bandaƙi yatura kofar, a gaggauce yayi wanka sannan yafito wayarsa dake ƙara yasashi sakawa akunnensa " Yayanmu good morning." " Morning." " Dafatan kana lpya? Ya karin hakurin mu?" A takaici yace " Alhamdulilahi wake magana?. "Yayanmu yanzu bakada numbata tafaɗa da alamar shagwaba! Katse wayar yayi dan bayason damu ko batafada ba yasan kursum ce kanwar amina duk da uba daya suke ba uwa daya ba. Ko dayagama shiryawa yafita dady ne kaɗai a palon ga abincin da aka cika a dinning shifa har tsoron kudin abiy yakeyi wani zubin idan yana rayuwa da kudinsa kamar su ƙare idan kuma ya rike hannu inba yaransa ba ko ummy bata isa karbar komai ba ballantana hajja rigima. " Afwan abiy bacci ne yakwasheni jiya bansamu na kwanta da wuri ba." " Kanada sanin ba bacci na kawoka kayi ba? Ko ? Kasuwancina zaka taimaka min, banhanaka cigaba da naka ba amma wannan aikin nawa dole ka taimaka min dan haka banson kara ganin fuskarka karfe 8 agidannan? Idan bamu jajirceba ban tunanin zamu cimma abunda yakawo mu, ashekarun baya na kauda kaina na barka ka gina ƙanka amma yanzu kuma dole kasamun hannu." " Kayi hakuri abiy inshaa Allahu zan maida hankali." Nana ce tafito daga daƙi sanye da wani t-shirt iya gwewa sai wando fari sai tayi rolling hannunta dauke da jaka da mukullin mota, abiyna good morning yayanmu good morning." " Nana abiey yafada ransa abace?" Naam abiey tafada tana zaunawa." Ba zancen kawa nakawoki yi anan ba karatu nakeso kiyi sannan ki taimakamin ta fannin kasuwanci na ko da wasa kar nakara jin wata magana ta kawa ko aboki.anan sannan bakida right na driving motocin da kika gani nawa ne nikadai zan iya driving sai yayinki duk inda zakije shi zai kaiki koni, ma'amalar banza da maza ko biyewa kawaye zai iya jawomiki fushina ba dan ƙarmi ba." Mamakine sosai ya cika Yayansu dan haka yajiyo ya dan saci ƙallon mahaifin nasu dan abune sabo agurinsa jin abiey yana faɗa. " ki kama kanki da mutunci kanki mazan waje ba muharramanki baniba." " abiey inshaa Allahu zan kula tafada batare da nuna damuwarta akan fuskarta ba ko ba'a fada mata ba tasan anty ce tagayamasa wata maganar.
PRISON...
WACCE RAYUWA KUKENAN LATYFAH IMAM ZATA KASANCE ACIKI??
ABDUL YA MUTU?
WANENE YASACE ABDUL?
INA JIRAN COMMENT DINKU.
******
*GIRMAMA MIJI DOLE NE
KUSANI WULAKANTA MIJI KO TOZARTASHI ZAI IYA ƘAI MACCE GA MUMMUNAN RAYUWA.*
*DUKKAN WANI TSANANI YANA TARE DA SAUKI BABU ABUNDA YAFI ƘARFIN ALLAH DUKKAN WANI HALI KIKE CIKI ARAYUWARKI TA GIDAN AURE KISANI SANARWA UBANGIJINKI SHINE ƘADAI MAFITA BA ZUWA KINA GAYAWA MUTANEN DA ZASU ƳADAKI BA.*
*SAMUN SAƁANI DOLE NE KO DA WAKIKE ZAUNE AMMA KAU DA KAI DA HAKURI DA FUSKANTAR JUNA SHIKE SAKAWA ACI RIBAR ZAMA.*
*MIJIN KAWARKI BA MIJINKI BA KO CIKI DAYA SUKA FITO KOWANNE DA RA'AYINSA DA KUMA DABI'ARSA*
*WANI NAMIJIN MAI KYAUTA NE,WANI NAMIJIN KUMA BASHIDA KYAUTA KWATAKWATA, WANI NAMIJIN MAI HAKURI NE,WANI NAMIJIN KUMA BASHIDA HAKURI, WANI NAMIJIN MAFAƊACINE WANI KUMA BA MAFADACI BANI.*