TSANANI

23

by @mmnashfaq

45/46




***




Suna Ido biyu da wanda ya dafata ta tashi a razane tace "Malam lafiya wani abu kake nema anan?


Yace "lafiyan kenan, tabbas ni kuwa nake neman abu, dan tun iso wanku nake wajen nan, kuma naga kaya yamun badda ke gaki babban yarinya amma ki tsaya kina harka da k'aramu yaro, ba girman ki bane hakan, shiyasa nace bazanzo tunda ya tafi masallaci ni na biya miki buk'atan dashi bazai iya biya miki ba, yanzu ki tashi mu tafi d'aki na tun kafin ya dawo danke kalan kayan mune"


Amna ta kalle sa sai taga a bige yake hanu tasa a cikin rawanin Baffa ta zaro wuk'a, a hankali ta rik'e ta bayan hanun ta tace ka rufawa kanka asiri kayi gaba inba haka ba zan maka illa yanzun nan"


Hanunta ya kalla sai yaga wuk'a ta ciro ya shak'e mata wuya suka fara dambe danso yake ya karb'a wuk'an ya Mata bille dashi a fuskan ta kafin ya tafi da ita d'akin su.


Abbas har yayi alola zai shiga masallaci yaji gaban sa ya fad'i, ya fasa shigan ya taho gun Amna da gudu ganin ya hango wani k'aton mutum suna dambe da ita.


Yana zuwa ya d'auki dutse ya kwad'a masa akai a take jini ya fara zuba akansa, Amna tace mun shiga uku Abbas jini yanata zuba a kansa baya nunfashi idan ya mutu ya zamuyi?


Yace "karki damu da wannan shiya kawo kansa bamu muka kirasa ba, ya dudduba wajen yaga ba wanda ya gansu yace yanzu tashi mu tafi gidan Malama Aisha kawai sai muyi sallan acan"


Tashi tayi ta bisa suna tafiya tana waiwayan mutumin, a bud'e suka samu k'ofan ta suka shiga, Amna tana ta sallama taji shuru"


Abbas yace "ki shiga ciki ki duba ta ni kuma zanyi sallah anan na kwanta" tace mishi to kafin ta shige cikin d'akin a kan gado ta sameta tana bacci, toilet ta shiga tayi alola tazo ta tada sallah kafin tahau gadon itama ta kwanta a gefen ta a take bacci mai nauyi ya d'auke ta, Malama bata farka ba sai k'arfe takwas d'in safiya nan ma Baba ne ya shigo ya samesu suna bacci da mamaki yaketa kallon Amna gefen Malama Aisha tana bacci, wani farin ciki yaji a ransa ganin Malama Aisha tana motsi yasa ya fara dukan ta a k'asa a hankali yana kiran sunan ta, tana bud'e Ido ta sauk'e su akan Amna da taketa baccin ta, tashin ta tayi tace "Amna yaushe kikazo?


Amna tace "da asuba" tana fad'an haka ta juya ta kwanta ta cigaba da baccin ta, zata sake magana Baba yace ki barta tayi baccin ta dan naga Abbas ma yanata baccin a falo"


Futowa tayi ta ganshi yana baccin sa, dawowa tayi tana ta sak'e sak'e a zuciyar ta, kafin ta shiga toilet ta wanke jikin ta kasancewan bata sallah shiyasa bata tashi da asuba ba, tana zuwa kitchen taga Baba ya zage sai abun karyawa yake had'a musu.


Tace "ina kwana Baba! Ka kawo aikin na k'arasa"


Ya amsa mata gaisuwan fuskan sa a sake kafin yace "yau na hutar dake kije ki kwanta ki huta kawai abunki yanzu zan gama aikin komai"


Da mamaki take kallon sa mutumin da yake fushi da ita akan tabar su Amna sun tafi, sai gashi yanzu kuma ya sake fuska yanata wani irin abu, kodai yaji kunyan abunda ya munne jiya oho, abun ba k'aramun mamaki ya bata ba saidai bata kawo komai a ranta ba tajuya ta futa ta koma d'aki kusa da Amna taje ta zauna tana kallon ta da tausayawa dan tunda take bata tab'a gamuwa da yaron da tun yana k'arami yake cikin jarabawan rayuwa ba sai Amna, har Baba ya kammala aikin abun karyawa Amna basu tashi ba, ganin har goma ya wuce suna bacci gashi yunwa yakeji kuma bayaso suci abincin ba tare dasu ba yace taje ta tashi Amna shi kuma zai tashi Abbas, dakyar suka iya tashi sukaje suka wanke baki, Baba ya zubawa kowa abinci da kansa, bayan sun gama Abbas ya tattara wajen Baba ya kalli Amna yace "maiya sake futo daku da daddare wannan karan?


Sunkuyar da kanta tayi dan bata son abunda zai na had'asu da Baba, cikin nutsuwa da sanyin murya ta basu labarin duk abunda ya faru" 


Malama Aisha tace "innalillahi wa'inna ilaihin raju'un, dama na zargi hakan tuntuni, dan najima inaji a jikina Goggo ba ita ta aife kuba, ta taso ta rungume Amna tace kiyi hak'uri Amna insha Allahu watarana sai sun zauna a inuwan ku" sai kuma ta saka kuka.


Tsaki Baba yayi yace "Aisha wannan wani irin shashancin banza ne? Keda zaki kwantar wa yarinya da hankali sai kuma kiyi k'ok'arin tayar Mata, idan bazaki iya lallab'a taba, zan d'auke ta na kaisu gidan Yayana su zauna, domin naga halamun bakisan yadda ake lallab'a yara ba"


Daga Amna har Malama Aisha sake baki sukayi suna kallon sa da mamakin jin abunda yake fad'a, Malama Aisha tace "duk da ban tab'a aihuwa ba ni mace ne, kuma ciwon y'a mace na y'a mace ne, duk wanda yaji labarin Amna indai yana da imani dole ya tausaya Mata, kuma aihuwa ai na Allah ne shi yake bawa duk wanda yaso a lokacin daya so, banga laifin da nayi ba da zaka mun gorin aihuwa anan, ko tausayin Amna danaji shine yaja kamun gorin aihuwa?


Tsaki yayi yace karki gaya mun maganan banza, ke ba hali kiyi laifi a miki fad'a saikiyi ta k'ok'arin fad'awa mutum maganan da ranki yakeso" shuru sukayi suka barshi yana ta fad'an sa, daya gaji dan kansa ya tashi ya futa a gidan"


Amna tace "Malama meya b'ata wa Baba rai yau naga yanata fad'a kuma hakan ba halin sa bane, ko baya son zaman mu a gidan ne?


Murmushi Malama Aisha tayi tace "tin jiya daya dawo baku nan yaketa fad'a a gidan, kuma da kansa ya sauko d'azu daya ganku, amma hakan ba komai bane a halin maza, karkisa wani abu a ranki Baba yana son zaman ku a gidan nan, dan yana muku kallon ya'yan daya aifa a ciki sa ne shiyasa baya son ku tafi ku barsa"


Abbas yace "idan yace zai cigaba da miki fad'a akan mu zamu tafi, tunda ke muka sani ba shiba, ta sanadiyar ki mukazo gidan bata sanadiyar shi ba" Malama Aisha tace duk ba za'ayi haka ba, kuyi hak'uri muzauna domin kuna d'auke mun kewa sosai" hira suka tab'a akan rayuwar su kad'an kafin suka tashi suka Mata gyaran gida, Baba bai dawo ba sai dare, ya shigo da manyan leda a hanun sa Abbas yana ganin sa ya tashi ya karb'a, d'akin Malama Aisha suka shiga da kayan Malama Aisha da Amna suka mishi sannu da zuwa.


Ledan kayan ya bud'e ya ciro kankana lemo ayaba da k'atan d'aurin nama ya mik'awa Amna, kafin yaba Abbas nashi, ya tashi ya futa ko kallon inda Malama Aisha take baiyi ba, Amna tana ganin futan sa tace "mai hakan yake nufi banga ya baki naki ba?


Malama Aisha tace "karki damu yana fushi dani ne, zanje na bashi hak'uri anjima ko gobe da safe"


Ajiye abunda ya bata Amna tayi tace "bana buk'atan su indai zaina fushi dake akan abunda ba laifin ki bane"


Yana lab'e yana jin duk abunda suke fad'a, jin Amna tace bazata ciba yasa ya dawo d'akin fuskan sa a sake yace "Aisha naki yana d'aki na tashi muje kici"


Tashi tayi ta bisa suna futa Amna ta kalli Abbas tace "anya zaman mu a gidan nan zai yiyu?


Abbas yace "nima abunda nake tunani kenan amma mu dad'a hak'uri zuwa gaba kad'an"


Washe gari da safe Malama Aisha ta shirya ra tafi makaranta tabar su Amna a gida akan idan sun gama aikin zasu biyota, tana futa Baba ya shigo d'akin yace Amna tabar abunda takeyi yana son magana da ita"


Gaban tane ya fad'i tazo ta zauna nesa da k'afan sa, matsowa yayi kusa da ita ya zauna shima a k'asa yana kallon ta fuskan sa d'auke da murmushi yace...............






***





Mmn Ashfaq