TSANANI

24

by @mmnashfaq

47/48




***




Yace "Amna idan baki manta ba kafin ku fara jarabawa nace miki akwai wani magana mai muhinmanci da nakeso muyi dake, shine naga ya dace ace yau nasanar dake halin da zuciya ta take ciki akanki, Amna ba wani magana bane face na sheda miki tun lokacin dana d'aura idona akan ki Allah ya jarabe ni da sonki had'i da sha'awan kasancewa dake, dan haka ina mik'o k'ok'on bara na ki taimake ni ki amince na aure ki, ni kuma na miki alk'awarin baki gatan da baki tab'a samu ba a rayuwar ki na duniya baki d'aya"


Amna jin abun takeyi kaman a mafarki wai yau itace mijin Malama Aisha yake cewa ta aure sa wannan wani irin rayuwa ne, maiyasa wasu basu d'auki cin amana a matsayin komai ba, d'ago Idon ta da yayi jajazur tayi ta zuba mishi na y'an wasu sekonni, dakyar ta iya bud'e bakin ta tace "Baba kasan abunda kake fad'a mun kuwa? Kasan matsayin Malama Aisha a wajena kuwa? Ta jero masa tambayan idonta yana zubar da hawaye.


Sake matsowa yayi kuwa da ita har k'afan su yana gogan na juna yace "Amna da kinsan yadda nake sonki nasan da bakiyi mun irin wannan tambayan ba, Amna ina sonki fiye da rayuwa ta dan Allah ki amince da aure na, idan baki son zama gida d'aya ne da Aisha zan gina miki naki gidan daban, idan kuma Aishan ne bakiso gaba d'aya na miki alk'awarin yanzun nan basai anjima ba zan saketa, ta tafi gidan su, sai muyi rayuwar mu mukad'e, nifa idan zaki yarda ki aure ni komi kusanci na da mutum kikace na rabu dashi wallahi na rante miki zan rabu dashi a take, ki taimaki rayuwa ta ki aure ni Amna, idan kika k'i amincewa da aure na nasan rayuwa ta tana cikin hatsari"


Shuru tayi tana kallon sa kaman baza tayi magana ba ta daure tace "inaso ka bani lokacin domin nayi tunanin kasancewar hakan"


Ya rik'e hanun ta yana murzawa a hankali, kafin yace "kince mun duk hukuncin da muka yanke akanki daidai ne meyasa zakice mun yanzu sai kinyi tunani?


Tace "ban zaci abunda kake nufi ba kenan, shiyasa na baka wannan girman, dan a lokacin kallon uban daya aifeni nake maka ba wanda zaizo neman aure na ba, kuma kasan ba abunda baya son dogon nazari da neman shawara akai, kasan ina da k'ani bani iyayin komai ba tare da shawaran sa ba"


Ya sake hanun ta yace "hakan yana da kyau nasan Abbas idan yaji maganan auran mu zaiyi farin ciki" yasa hanu a aljihu ya ciro kud'i ya k'irga dubu hamsin yace "ga wannan ki tashi kuje kasuwa yanzu ki siyo muku kayan sawa dana kwalliya"


Karb'a tayi kafin ta masa godiya ta tashi tashiga cikin d'akin Malama Aisha wajen da ta b'oye kud'in ta da rawanin Baffa taje ta d'auko ta d'auki k'aton hijabin Malama Aisha ta saka, harta futo yana zaune a inda ta barsa, ya kalleta fuskan sa d'auke da murmushi yace "harkin shirya?


Kai kawai ta d'aga masa ba tare data ce komai ba ta futo tsakar gida, Abbas ta gani yana aiki ta tsaya tana jiran ya gama.


Abbas ya gama wanke wanke yana share wajen yaji muryan ta tana cewa zoka rakani kasuwa" ya juyo ya kalle ta yace "kasuwa kuma Adda Amna? Kafin ta bashi amsa Baba ya futo yace "eh kasuwa zakuje Abbas nina aiketa" kallon ta Abbas yayi yaga kwata kwata ba walwala a tare da ita ya d'auriye hanun sa suka futa, tafiya sukeyi har suka wuce kasuwan baiga ta tsaya ba, ya rik'e hanun ta yace "mai yake damun kine Adda Amna naga kaman baki cikin nutsuwar ki?


Kaman mai jiran yayi maganan ta saka masa kuka, cikin kuka ta bashi labarin yadda sukayi da Baba, shuru Abbas yayi yana nazarin maganan ta, duk da shi yaro ne amma Allah ya bashi kaifin tunani da hangen nesa, gani tayi ya tari mota batare daya ce Mata komai ba, motan na tsayawa yaje yace Malam a ina zaka tsaya, driver yace mishi bauchi, hanun ta ya kamo kawai suka shiga motan, suna fara tafiya ta kallesa tace "ina zamuje Abbas?


Kai tsaye yace Mata bauchi" zare ido tayi tace wa muka sani a garin da zamuje? Yace "Allah" daga nan ba wanda ya sake magana a cikin su har suka isa bauchi, driver ya tsaya a inda suke parking yace kowa ya futo, suna futowa sukaji wata Mata ta tare napep tana cewa bayan airport, suna jin haka suma suka shiga sukace akaisu nan, bayan an sauk'e Matan mai napep yayi ta zagawa dasu ya juyo ya kallesu yace "har yanzu bamu iso inda zaku sauk'a bane?


Abbas yace ka sauk'e mu anan mun iso, futowa sukayi suna kallon filin wajen da aka sauk'e su, wajen ba k'aramun kyau ya musu ba dan ya k'awatu da kwalta, kafin suka biya mai napep d'in kud'in sa, tsakiyan titi sukaje suka zauna kowa da tunanin da yakeyi a zuciyar sa, ta kalli Abbas tace "Abbas yanzu kasa munzo garin da ba wanda muka sani a ina zamuna kwana? Me zamuna ci? Wani irin rayuwa zamu gudanar anan? Ta jero masa tambayoyin tana tsaresa da Ido.


Ya kalleta yace "Adda Amna inaso a kullun kina tunawa duk inda muke akwai Allah kuma shi kad'e zai taimake mu ba mutum ba, nagaji da rayuwa a Tilde, kowa idan yayi yunk'urin taimakon mu sai kaji da wani abu a ransa, yanzu ba mai taimako dan Allah, tunda kina da kud'i a hanun ki mu shiga cikin gari mufara neman haya, har Allah yasa mu samu, daga nan kuma saimu fara tunanin kalan sana'an da zamu farayi"


Tace "to Allah yasa mun shigo garin nan a sa'a, ta ina zamu nufa yanzu?


Yace "mubi duk inda mukaga mutane suna bi, idan mukaje waje mai cinko son Jama'a saimu tambaye su gidan haya, amma kafin mu shiga gari mu nemi waje mu huta, dan ji nake kaman zanyi amae"


Amna tayi murmushi tace "gwanda kai amae kaji nifa tunda na shiga motan nan komai ya kunce mun badda salatin Annabi ba abunda nakeyi, dama haka akeji idan an shiga mota?


Yace "ta ina zan sani Adda Amna, dukan mu yau muka fara shiga fa, nifa har keke napep d'in yafi mun dad'i fiye da mota, shifa mota hanjin cikin mutum yake girgiza, Allah yasa bai tsinka mana hanjin ciki ba dai, kwanciya sukayi a wajen da suke suna hutawa kafin zuwa anjima su shiga gari.



Larai tunda ta tashi yau bata da walwala daurewan da takeyi ma ta kasa, haka kawai taji hankalin ta ya mungun tashi, ba wanda takeso ta gani kaman Amna, dan sai yanzu take dana sanin futa a gidan, dan tasan ba mai ceton Amna a gidan idan ba ita ba, abincin karyawa ne a gaban ta amma ta kasa ci, burin ta Baffan ta ya futo ta mishi sallama taje taga halin da Amna take ciki, tayi nisa a tunani batasan lokacin da Baffa Sule yazo kanta ba, sai ji tayi ya buga k'afan ta a hankali, tayi firgit ta dawo daga tunanin Amna data tafi, kallon ta yayi yana karantan yanayin ta kafin yace "Larai tun jiya na fuskanci akwai abunda yake damun ki, kuma kin kasa fad'a mun, idan kin d'auke ni uba a gare ki, ki fad'a mun abunda yake damun ki yanzu?


Sunkuyar da kanta tayi hawaye na zuba a idon ta tace "Baffa kayi hak'uri nagaji da kawo k'aran Goggo akan Amna ne, labarin yadda komai ya faru a gidan rasuwa ta bashi, kafin ta d'aura da cewa "ni yanzu tsoro na d'aya karta fad'a wa Amna ba ita ta aifeta ba ta jefa rayuwar ta a garari, duk cikin ya'yan Goggo bamai Mata biyayya da Amna take Mata, amma narasa me yarinyan nan ta tsarewa Goggo a rayuwa ta tsane ta haka, dan Allah Baffa Sule ka taimaki rayuwar Amna ka dawo da ita gidan ka, tun kafin bak'in cikin Goggo ya harba Mata ciwon zuciya ta mutu"


Shuru Baffa Sule yayi yana nazarin maganan ta kafin yace "nima na jima ina wannan tunanin a zuciya ta, mai d'aki nama tace na d'auko Amna zata rik'e ta tsakani da Allah, amma saboda gudun masifan Goggo yasa na hak'ura na barta, saidai yanzu kam duk abunda zai faru saidai ya faru dan nayiwa kaina alk'awarin inganta rayuwar yarinyan nan har Allah ya kawo Mata mijin aure na aurar da ita kowa ya huta, yanzu tashi muje gidan muga a wani hali take yanzun" tashi tayi suka futa tare suna tafiya suna tattaunawa akan maganan.


Goggo basu suka farka ba sai k'arfe takwas d'in safiya tana bud'e Ido ta duba wajen da Amna take ajiye musu kunu da d'umaman tuwo, taga wayam ba komai tace "mai zan gani kadde yarinyan nan bata gama mana abun karyawa ba? Tashi tayi ta futo taga murhun ba'a hura wuta ba, a zuciye ta kwalawa Amna kira yakai sau goma amma bataji an amsa ba, ji tayi ranta ya mungun b'aci, taje d'aki tana duba karan da zata daki Amna da Abbas dashi, d'anyan kara ta samu ta nufi d'akin Lantana ta rufa Mata baya, suna shiga sukaga ba kowa a d'akin da mamaki Goggo take kallon d'akin, Lantana tace ina sukaje?


Goggo ta furzar da iska mai zafi daga bakin ta tace "lallai sai na raba raini da yarinyan nan, dan yanzu naga raini ya fara shiga tsakanin mu, muje Lantana ki hura wuta ki d'aura mana abun karyawa kafin ta dawo ki huta gajiyan ki a kanta, dan kinsan D'ahare suna futowa sukaga ba abun karyawa zasuyi ta mita"


Lantana tace "waye zai d'aura muku abun karyawa? Kema Goggo da gangan kika fad'a abunda bazai tab'a yiyuwa ba, kije ki d'aura da kanki ko kuma kisa su D'ahare su d'aura miki, ta bud'e baki zata bata amsa kenan sukaji sallaman Baffa Sule da Larai, futa sukayi Lantana ta sunkuya har k'asa ta gaishe shi, ya kalli Goggo da taketa cika tana batsewa yace "ina Amna?


Tsaki Goggo tayi tace "ai kabani ajiyan ta dole ka tambaye ni ita, nasan Larai ta fad'a maka duk abunda muke shirin aikatawa akan Amna, kuma aikin gama ya gama tunda na fad'a Mata komai dangane da rayuwar ta yanzu haka ma na koreta tabar mun gida na, nace taje can ta cigaba da karuwanci kaman yadda uwarta tayi ta aifeta"


Baffa Sule dafa kansa yayi yana furta Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un, ya maimaita soba adadi kafin ya shiga d'akin Baffa da ya dawo nasu Amna tunda ya rasu, ganin d'akin a yaye ba rufi, ga kasan ba fulo duk ruwa ya cakub'a shi, ya damk'e idon sa yana kiran sunan Allah, tare da cewa Salihu ka yafe mun ban rik'e bayan ka kaman yadda na maka alk'awari ba, amma yanzu nayi alk'awarin kula da rayuwar su har abada, tunawa da Goggo tace ta koresu yasa ya tashi da sauri ya futa, d'akin Goggo ya shiga yace "Ki duba girman Allah ki fad'a mun inda yarinyan nan taje?


Tab'e baki tayi tace "anya Baffa Sule ba danne yarinyan nan kakeyi ba, naga duk kabi ka damu daga cewa na koreta, toka kwantar da hankalin ka nasan zata dawo ku cigaba da abunda kuka saba, nima nan yanzu jiranta nakeyi ta dawo daga karuwancin data tafi tazo ta mana abun karyawa domin duk gidan nan ba d'an shege ko d'an goyo da zata futa ba tare data gama mana abun karin kumallo ba"


Sai yanzu Baffa Sule yaji hankalin sa ya kwanta saboda jin tace bata koreta ba, futa yayi yaje ya zauna a k'ark'ashin bishiya yana jiran dawowan ta ba tare daya sakece Mata komai ba, shidai burin sa Amna ta dawo ya d'auke su sukoma gidan sa da zama, Larai ji tayi itama baza ta iya zaman gidan ba taje ta had'a kayan ta tabar garin ba tare data ma Goggo sallama ba.



Tafiya yakeyi yana gudu ya sake wak'a a motar yana bi yana rawa, kwata kwata baya lura da hanyan da yakebi domin yasan hanyan ba'a cika binsa ba saboda yayi bayan gari, yawanci masu koyan mota ne kawai sukebi ta wajen sai d'ed'ekun mutane, bai ankara ba yaga wata yarinya ta taso, bisa ga alamu ganin gudun da yakeyi ne ya firgita ta tarasa inda zata nufa k'ok'arin taka birki ya farayi.


Amna da suke kwance a gefen titi jin k'aran mota yana zuwa ta inda suke, a razane suka tashi, ganin irin gudun da motan yakeyi ba k'aramun tsorata ta yayi ba ta rasa ina zata nufa, Abbas yana ta kwala Mata kira danshi ya samu ya tsallaka titin ya koma can gefe, ganin irin birkice wan da tayi gashi mai motan gudun sa yakeyi kaman baisan da mutum a wajen ba yasa ya dawo da gudu dan yaja hanun ta, amma ina kafin ya k'araso yaga motan ya..........







***






Mmn Ashfaq