25
by @mmnashfaq
49/50
***
Motan yayi kanta rufe idonsa yayi ya kurma ihu, itama Amna ganin motan ya nufo kanta zai kad'e ta, ta rufe idonta tana furta Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un, duk jikin ta yana b'ari, dakyar ya iya taka birki ya tsaya futowa yayi ransa a b'ace yazo ya d'auke ta da mari cikin tsawa yace "ke wacce irin mahaukaciya yane da zakizo tsakiyan titi ki zauna, wawiya shashasha kawai, daga gani daga jeji kika futo shiyasa kika tare wa mutane hanya, naso na takaki na kashe banza y'ar iska kawai"
Maganan sa ba k'aramun b'atawa Amna rai yayi ba saidai ba yadda ta iya dole ta bashi hak'uri, ta tsuguna ta saka k'afan ta a k'asa tace "dan Allah kad'o kayi hak'uri wallahi bamu san mota yana wucewa tanan ba, kuma mu bak'i ne a garin yau muka shigo yanzu ma neman gidan haya mukeyi"
Tsaki yayi ya koma mota yana ta zagin ta, Abbas tunda ya rufe idonsa bai bud'e ba saida yaji tashin motan ya bud'e idon sa da sauri ya kalli inda take ganin ta a tsugune kuma bisa ga halamu lafiyan ta qalau ya tashi da gudu yaje ya rungume ta yana kuka yace Adda Amna ba abunda ya sameki? Baiji miki ciwo ba ko?
Ta dad'a rungume sa tace "baimun komai ba Abbas, saidai ya zageni sosai, Abbas y'an birni basu san darajan mutum ba, mu koma rigan mu kawai"
Tasowa yayi ya share Mata hawaye kafin shima ya share nasa yace "Adda Amna kiyi hak'uri da haka zamu saba, kinsan dole mutanen birni bazasu kasance irin mu ba, ki tashi mu shiga cikin gari ko Allah zaisa mu samu gidan hayan"
Tashi tayi ta d'auki rawanin ta suka fara bi ta hanyan da sukaga motan yabi, kutsawa sukeyi duk hanyan da suka gani, har suka futo federal low-cost cin cirindon mutane suka gani, Abbas ya tab'a Amna yace "Adda Amna kaman mai siyar da abinci ne acan?
Wajen daya nuna mata tabi da kallo tace "nima kaman haka na gani muje mu duba, suna zuwa suka ga mai abinci ne mutane sun taru a kanta, d'ari biyar taba Abbas tace yaje ya siya musu abinci, dakyar ya samu ya siya ya kawo musu sukaci, bayan sun gama cin abincin sukaci gaba da zama dan basu san inda zasu nufa ba.
Baba ganin shurun su yayi yawa yasa ya bisu kasuwan ba inda bai duba ba amma basu nan, gida ya koma, dan yasan wajen Malama Aisha sukaje, haka kawai yaji gaban sa yana fad'uwa tunanin sa baisan da wani Ido Malama Aisha idan ta dawo zata kalle saba, yasan Amna ta fad'a Mata duk yadda sukayi, saidai yasan akan Amna ba abunda bazai iya ba, d'akin sa ya koma ya kwanta yana jiran dawowan su, k'arfe d'ayan rana Malama Aisha ta dawo gida, ganin kwanikan wanke wanke a tsakar gida an wanke amma ba'a shiga dasu ba, a zuciyar ta tace "anya yarana lafiyan su qalau kuwa, dan ba halin su bane barin waje ba'a gyare ba, tattara wajen tayi ta share, kafin ta lek'a d'akin tana kwalawa Amna kira, jin muryan ta yasa Baba ya futo yace "har kun dawo?
Tace "eh na dawo ya gida yau baka futa kasuwa bane?
Yace "na futa kaina ne naji yana ciwo shine na dawo"
Tace "subbahanallah Allah ya sauwak'e, bari Abbas ya siyo maka magani kasha saika kwanta, ta kwalawa Abbas kira yakai sau biyar amma bai amsa ba, ta kallesa tace "yau ina su Amna suka shiga ne tunda na shigo nake kwala musu kira ba wanda ya amsa ko sunyi bacci ne? Koda yake nasan idan kana gida Amna bazata tab'a sakewa ba harsai ka futa, inaga taga shigowan kane taje ta kwanta, bazanje na tashe su.
Baba yace "me kike nufi?
Tace "kaman me kenan?
Yace "ya ina tambayan ki kema kina tambaya na, yaran nan tunda na basu kud'i suje kasuwa su siya kayan sawa basu dawo ba, kuma nasan bazasu wuce wajen ki sukaje ba"
Ido Malama Aisha ta zare tana mishi kallon da yasa shi dibibi cewa tace "ka fad'a mun gaskiya Baba, mekama Amna yasa ta gudu?
Kame kame ya farayi ganin bayi da gaskiya kuma zata iya gane sa, kawai saiya hau fad'a yace "nasan dama kin tsani zaman yaran nan a gidan nan, halamu ya nuna mun kin jima kinaso ki koresu, saboda bakisan zafin d'a ba da kinsan zafin aihuwa nasan da hanu bibbiyu zaki karb'e su, yaran nan rayuwar su k'unshe yake da hatsari kala kala, amma tsaban rashin imani da rashin sanin darajan d'a kika rufe idon ki kika koresu, ki bud'e kunnen ki dakyau kijini muddin bakije kin dawo da yaran nan yau ba a bakin auran ki dan bazan iya zama da mace maison kanta irin kiba" yana gama fad'a ya fuce a gidan ranshi a mungun b'ace, dan bai yarda ba ita ta koresu ba.
Malama Aisha jiki a sanyaye ta shiga d'akin ta tana tunanin abunda Baba ya fad'a tace "ya zamo dole naje na nemoku Amna ko dan kaina badan Baba ba, bazan sake sakakin barin rayuwar ku ya wulak'an ta ba koda kuwa zan rasa nawa farin cikin" gorin rashin aihuwa da Baba ya Mata bai dameta ba kaman rashin sanin rigan su Amna, tasan ba inda Amna ta sani daya wuce gidan ta da rigan su, tashi tayi da sauri ta shiga bedroom d'inta domin canja hijabi, tana shiga taga paper da kud'i akansa sa a saman paper an rubata mai sonki har abada Amna, hanun ta har b'ari yakeyi wajen warware takaddan rubutu taga anyi da manyan harufa tafara karantawa kaman haka:-
*Malama Aisha nasan ke uwace a gareni bazaki tab'a jin dad'in rashin mu a gare kiba, kaman yadda muma rashin ki kusa damu tamkar rasa wani jigo na rayuwar mune, dan Allah ki yafemun abunda zan fad'a, Malama bakiyi sa'an miji mai sonki tsakani da Allah ba, Baba ya cika babban mayaudari, ya buk'aci na aure sa ke kuma zai sakeki sai muyi rayuwar mu cikin jin dad'i, ni kuma da Allah ya nuna mun wannan ranan dazan ci amanan wanda ta d'auke ni y'a gwanda ace na mutu nabar duniyan nan, nafara rayuwa mai dad'i dake Baba ya yanke mun jin dad'in rayuwa ta, ya mayar mun da k'unci da bak'in cikin danake tunanin nayi bankwana dashi, ban fad'a miki maganan nan danna rabaki da mijin kiba, saidan kisan dalilin tafiya ta, karki sha wahalan nema na domin bazaki tab'a samu naba, ba rugan mu zan koma ba zanje duk inda Allah ya kaini dani da d'an uwana Abbas, ina sonki Malama so irin na y'a da uwa, zakiga kud'in da Baba ya bani naje na siya kaya dashi, ni kuma bani buk'ata, ko zanyi yawo tsirara bazan tab'a karb'an abunda ya futo daga hanun saba, Allah ya had'a fuskan mu watarana nagode ina sonki*
Kafin ta gama karantawa hawaye ya wanke Mata fuskan ta tas, ta rasa ina zatasa ranta taji dad'i, tayi kuka kaman idonta zai futa kafin ta tashi ta had'a kayan ta a akwati, tana gamawa ta d'auki kud'in da Amna ta bar Mata akan gadon ta futa a gidan, mota ta shiga ya kaita magama, tana sauk'a ta sake shiga motan da zai kaita Birnin Kudu, ba ita ta isa garin ba sai k'arfe taran tare, mashin ta hau ya k'arasa da ita anguwan su, iyayen ta da mamaki suke kallon ta, sukace lafiya Aisha muka ganki da daddaren nan?
Kuka ta saka musu basuyi yunk'urin tambayan ta komai ba, Maman ta taja hanun ta suka shiga d'aki, ruwan wanka tasa aka kai Mata taje tayi wanka, dakyar ta iya cin abinci kafin ta kwanta, ranan ko bacci b'arawo bai iya dauk'an taba, da safe bayan sun karya, iyayen ta suka sakata a gaba suna tambayan ta abunda ya kawota gida, wasik'an da Amna ta bar Mata ta d'auko tace "Abba gashi ka karanta"
Karb'a yayi yana kallon ta dan a tunanin sa takaddan saki ne, da k'arfi ya karanta yadda kowa zai iya ji, bayan ya gama karantawa yace "ki mana k'arin bayani akai domin kin barmu a duhu"
Gyara zama tayi ta basu labarin tun ranan da aka fara kawo Mata Amna ajinta da abubuwan dayayi ta faru da su, har zuwa yau" shuru wajen yayi kowa da abunda yake tunani a zuciyar sa, can Abba ya d'ago ya kalleta yace "ba sakin da mijin ki ya miki bane ya dameni rashin sanin inda yaran suke shine damuwa na, naji tausayin rayuwar yaran nan da kika bamu labari, amma kema kinyi ganganci Aisha taya zaki taho batare da kin nemesu ba?
Ma'aifiyar ta tace "Abban Aisha ai bai sake taba, naji dai duk bayanin da tayi banji ta inda kalman saki ya futo ba"
Kallon ta yayi yace "Hajara nasan ke ba jahila bane, tace mana yace idan bata dawo da yaran ba jiya a bakin auran ta, hakan ba saki bane?
Sunkuyar da kanta tayi tana takaicin dawo Mata da y'a bazaura da Baba yayi tace "hakane Allah ya Mata zab'in alkairi, yanzu a ina zamu samo yaran?
Yayan ta yace "inaga ta nuna mana foton su kawai sai muje mu dubasu a garin ko Allah zaisa mu gansu"
Wayanta ta mik'a musu tace "akwai hotunan ta na ranan da suka gama makaranta a cika, dana Abbas d'in shima, karb'an wayan sukayi suna kallon hotunan Abba k'urawa photon Amna Ido yayi kaman mai karantan wani abu, kawar da tunanin dayazo mishi yayi yace "ina son yaran nan, duk yadda za'ayi ku tabbatar kun nemo munsu, dan haka kawai naji ina buk'atan na taimaki rayuwar su kuma Allah ya jarabeni da sonsu lokaci guda"
Suma hakan ne ya kasance a wajen su, sai yanzu Malama Aisha tayi murmushi ganin duk y'an uwanta sun karb'a su Amna hanu bibbiyu a zuciyar ta sai addu'an Allah ya bayyana su takeyi, shirin tafiya suka farayi a take, Malama Aisha ta rakosu tana musu addu'an Allah yasa su gansu, kafin ta musu kwatancen shagon Sama'ila dan taga Amna tana shiri dashi, hanya suka d'auka kowa burin sa yaga Amna Ido da Ido.
Malama Aisha duk da iyayen ta ba wasu masu hali bane amma suna dana rufin asiri, gasu da had'in kai duk da sun samu baragurbi guda d'aya, wanda batajin maganan kowa a rayuwar ta, duk abunda zuciyar ta ya raya Mata shi takeyi hakan yasa iyayen ta suka futa hark'an ta, yanzu ba maiyi da ita, itama bata neman su domin tace tana da kud'i mutanen duniya ma kawai sun ishe ta dangi basai ta nemo wasu ba.
Yayun Malama Aisha sun isa Tilde lafiya qalau saidai ba irin neman da basuyi wa Amna ba amma ba labarin ta, daga k'arshe wani yace musu yaga lokacin da suka tare mota suka shiga Amna tana ta kuka, saidai baisan inda zasuje ba.
Jiki a sanyaye suka koma da labarin da suka samu a bakin mutane, ranan Malama Aisha tayi kuka kaman ranta zai futa, ba k'aramun tausayi taba mutanen gidan ba, dan sunsan kukan shak'uwa takeyi, suka had'u sukayi ta rarrashin ta sukace zasu had'u dukansu suyita addu'an Allah ya futo dasu aduk inda suke.
B'angaran Baba kuwa tunda ya dawo gidan baiga Malama Aisha ba yayi tunanin ko taje dawo dasu Amna ne, ganin har dare basu dawo ba ranshi ba k'aramun b'aci yayi ba, dan ba rashin dawowan Malama Aisha bane ya damesa rashin dawowan su Amna ne ya d'aga masa hankali gashi baisan inda zaije ya nemo sube, furzar da iska mai zafi yayi yace "ya zama dole na hukunta ki Aisha" da wannan takaicin ya kwana ya tashi basu dawo ba, duk motsi saiya jawa Malama Aisha Allah ya isa.
Tunda ya koma gida yayi wanka ya kwanta yake tunanin yarinyan daya kusan bugewa yau, muryan ta sai kuwa take masa a kunne haka kawai ya rasa nutsuwan sa sai tunanin ta yakeyi tashi yayi ya dafe kansa yace "Saifuddeen ka dawo daidai mana tunanin mai kakeyi haka? Kaida kyawawan Mata suke bibiyan ka mai zakayi da y'ar k'auye" wata zuciyar tace masa ai itama kyakykyawa ce, kwata kwata ya kasa samun nutsuwa a zuciyar sa da jikin sa baki d'aya, tunanin inda ya barta ya damesa, kawar da tunanin yayi ya d'auki kofin coffe yakai bakin sa yana sha amma har yanzu tunanin yarinyan yak'i barin zuciyar sa, tashi yayi ya d'auki key motan sa ya koma wajen da sukayi kusan accident ba inda bai duba ba a wajen amma bai ganta ba, komawa gida yayi yana takaicin rashin ganin ta, ranan haka ya kwana zuciyar sa ba dad'i.
Amna suna zaune sukaga mai siyar da abincin ta gama tana had'a kayan ta tashi sukayi sukaje wajen ta suka gaishe ta tace lafiya wani abu kuke nema?
Amna tace "dama zamu tambaye ki a ina ake samu gidan haya anan?
Kallon su takeyi tun daga k'asa har sama saida ta k'are musu kallon tsaf kafin ta kwashe da dariya tace "badda ku waye zai baku hayan gidan sa, idan ma guduwa kukayi daga gidan iyayen ku kuka futo yawan bariki gwanda ku koma dan ba riban da zaku samu, muma da muke y'an garin watarana sai k'atan banza ya danne mu batare daya bamu ko sisi ba" hak'uri suka fara bata akan ta nuna musu inda zasu samu kawai, ganin sun takura ta da yawa yasa tace subar wajen kota had'asu da hukuma, suna jin haka suka gudu a wajen, hanyan su na d'azu sukayi ta bi har suka koma inda suka futo, mayar da wajen, wajen kwanciyan su sukayi da safe su shiga cikin gari su nemi abunda zasuci da yamma su dawo wajen su kwana.
Saifuddeen duk ya shiga damuwa na rashin ganin yarinyan daya zageta gashi saura kwana biyu yabar k'asan yau da yamma ya futo dan sake duba wajen kozai ganta, wajen da abun ya faru yazo yayi parking kaman a mafarki ya hangosu suna zuwa, futa yayi daga motan yana tafiyan sa na k'ase ta jikin sa yana wani irin k'amshi mai kama zuciya, Amna tunda suka taho sukaga mota a wajen gaban su yake fad'uwa, abunda ya sake basu tsoro ganin mutum mai kama da aljani yana nufosu daurewa kawai sukayi suka taho suna addu'an dayazo bakin su kafin su ankara sukaga...........
***
Mmn Ashfaq