28
by @mmnashfaq
55/56
***
Tace "da baka sha wahalan bani number ba domin bani da wayar dazan kira ka"
Zaro Ido yayi waje domin bai yarda da abunda tace ba amma danya k'ureta sai yace "jiya lokacin dana kusan bige ki naga waya a hanun ki"
Murmushi tayi tace "idan ka yarda bani da waya saidai idan baka yarda ba shikenan"
Hanu yasa a aljihu ya ciro d'ayan wayan sa ya mik'a Mata yace ki rik'e wannan kafin na siya miki naki" karb'a tayi ta masa godiya har zai futa ya dawo yace akwai kayan tea a kitchen idan kuna buk'ata, ta d'aga masa kai kawai hamun taji, ya fice yana mamakin kansa na biye Mata da yayi, harya isa gida yanajin wani abu na fusgan sa akanta, tunda yake daga Matan Nigeria harna Spain bai tab'a bin ko d'ayan su ba su suke kawo kansu yayi yadda yaso dasu daga k'arshe ya koresu wasu sabbin suzo, amma wai shine yake bin duk abunda k'araman yarinya ta fad'a kuma tana zana masa ka'idodi yana bi, abun ba k'aramun mamaki ya bashi ba, amma yasan idan sukaje Spain sai yadda yayi da ita, dan bata isa ta gudu masa ba sai yadda yaso zaiyi da ita kuma sai abunda yace zatayi.
Abbas yana ganin futan sa ya kalli Amna cikin sanyin murya da nuna girmamawa yace "Adda Amna kaman abunda kike shirin aikatawa bai dace ba"
Ta kallesa tace "kaman ya bai dace ba?
Yace "kiyi hak'uri da abunda zan fad'a dan bansan ko zai b'ata miki rai ba, Adda Amna ke yace kuma uwa a gareni bai kamata nayi jayayya da hukuncin da kika yanke ba, saidai inaso na miki wani k'aramun tunatarwa, kinyi saurin yarda da mutumin nan kuma har kike ganin zai yarda da ka'idodin da kika shinfud'a masa, na farko mutumin nan yafi mu shekaru waye wa da sanin duniya, shifa a birni aka aifesa yayi rayuwar sa a birni da kasashen turawa, sab'anin mu da aka aife mu a jeje mukayi rayuwar mu a tsakiyan shanu da tumakai taya kike ganin zaki iya masa wayo, anawa shawaran idan ya dawo kice kin fasa bazamu bisa ba, idan yaga zai iya taimakon mu ya taimake mu idan bazai iyaba ya kore mu duniya fad'i ne da ita, idan wani yak'i ka wani kuma lokacin zaiji yana sonka, shiyasa akoda yaushe akeson mutum yabar k'ofar rayuwar sa a bud'e karya damu da wanda zasu futa kuma karya sa rai akan masu shigowa, mu rik'e Allah da addu'a danshi kad'e zai taimake mu a cikin wannnan *TSANANIN* rayuwar da muke ciki, ki yafe mun Adda Amna idan magana na ya b'ata miki rai, ban fad'a dan ban yarda dake bane saidan ganin duk wayon mu y'an birni sunfi mu, musamman shi daya fimu komai a rayuwa"
Murmushi tayi hawaye na zuba a idon ta tace "ina wayon yake Abbas da ina da wayo da abubuwa da dama basu faru dani ba, nagode wa Allah daya bani k'ani mai tunatar dani idan na kusan kauce hanya, Abbas nasan Allah zai cigaba da kareni kaman yadda ya kare rayuwata daga fad'awa halaka tun ina k'arama, kuma nad'au shawaran ka insha Allahu ba inda zamuje ka tashi mu tafi tun kafin ya dawo ya same mu a gidan".
Kai ya girgiza yace ba inda zamuje a daren nan Adda Amna nanfa ba kaman rigan mu bane da zamu futa a duk lokacin da mukaga dama, kiyi hak'uri mubi ta hanyan da mukazo shiya kawo mu kuma shi zai futar damu" suna cikin magana wayan daya bata yayi k'ara ta duba taga ansa my number kasancewar taga yadda Malama Aisha take receiving call idan an kirata yasa wannan ma bai bata wahalan d'auka ba, karawa tayi a kunnen ta bakin ta d'auke da sallamah, saida ya sauk'e ajiyan zuciya kafin ya amsa Mata sallaman ta shuru ne ya biyo baya na wasu mintina shiya fara kore shurun da cewa "baiwar Allah bansan wani irin asiri kika mun ba tunda na ganki na rasa nutsuwa a tare dani duk lokacin dana rufe idona kamannin ki da cikan halittan ki shi yake mun gizo a duk lokacin dana rufe idona, na matsu naga mun bar k'asan nan domin nasamu na kasance dake" ya k'arasa maganan yana sauk'e Mata nunfashi a kunne.
Saida ta tabbatar ya gama maganan sa yayi shuru yana ta aikin sauk'e nunfashi kaman wanda yayi gudu tace "kayi hak'uri bazan iya binka ba na canja shawara" baisan lokacin daya tashi a kwancen da yake ba yace what me kike fad'a? Idan ma wasa kikeyi ki daina domin tunda na taso ba'a tab'a mun alk'awari an kasa cikawa ba, kuma nima ban tab'a cewa zanyi abu na fasa ba, mu daina irin wannan wasan dake"
Tace "ban sanka ba baka sanni ba taya zanyi wasa dakai daga had'uwan mu? Bata jira ya bata amsa ba ta cigaba da cewa wallahi bazan bika ba nafasa, idan kayi niyan nema mana gurbin karatu zaka iya nema mun a k'asa ta basai ka kaini wani jahar ba"
Yace tabbas baki san waye Saifuddeen ba" kitt ya kashe wayan ya zari key motan sa ya futa a falo suka had'u da Mom d'insa ta futo dauk'an abu a falo, kafeshi da Ido tayi tace ina kuma zakaje da tsakiyan daran nan?
Sosa k'eya yayi yace "Mom na kasa bacci ne saboda zafi shine nakeso na futa nasha iska a waje"
A/C d'akin ka ya lalace ne? Dibibicewa yayi ya fara Mata kame kame saboda tambayan yazo mishi a bazata rashin gaskiya ya bayyana a fuskan sa, cikin takaici tace Saifu bazaka daina halinka na bin Mata ba dai, nace ka nutsu ka futo da Matar aure amma kak'i, daga ka lalata y'ar wannan saika lalata k'anwan wancan, kayi hankali da rayuwa Saifu domin ina jiye maka ranan da wannan halin akuyancin naka zai sakaka zubar da hawaye, ina jiye maka ranan da nadama zata riske ka a kurarran lokaci"
Bata rai yayi ya juya yana cewa ba hali mutum yaci lokacin sa sai a saka shi a gaba ana zargin sa ana masa wa'azi, tunda na dawo kin tab'a ganin na kawo miki wata yarinya cikin gidan kine, duk wanda kika ganta ita ta kawo kanta bani na kira ta ba" harya koma d'akin sa bai daina Mata mita ba" zama yayi abakin gado yana takaicin hanasa futa da tayi, dan yaso yaje suyi magana da ita gaba da gaba dan bazai yarda ta mishi kwalele ba, saida ya gama sa ran zaiji dad'i da ita tace ta fasa da k'arfi ya furta kai ina hakan ma bazai tab'a yiyuwa ba"
Mom girgiza kanta tayi kawai ta koma d'akin ta tana takaicin irin tarbiyyan da Abban su Saifu ya bashi, dan ya nuna masa gata fiye da dukkanin ya'yan sa shiyasa yake yin duk abunda yaga dama, saidai tana tausayin ranan da rayuwa zata juya masa tana guje masa ranan dazai ga wanda yakeso halin akuyancin sa yaja a hanasa ita, d'aki ta koma tana addu'an Allah ya shiryar Mata dashi"
Amna ko tunda taji ya kashe wayan gaban ta yake fad'uwa tayi ta maimaita kalman shi na k'arshe da yace bakisan waye Saifuddeen ba, wato sunan shi Saifuddeen kenan, suna mai dad'i ta fad'a a zuciyar ta, tashi tayi taje ta d'auro alola ta fara sallan nafila, bayan ta idar tayi addu'an neman tsari, Malama Aisha ta fad'o Mata arai da irin nasihan da take Mata kullun akan rayuwa, tace Allah ya isa tsaka nina dakai Baba, nasan da baka kawo son zuciya ba da yanzu ina tare da ita, gashi ko number ta bani dashi ballan tana na kirata a waya, dukan su haka suka kwanta ba wanda ya nemi abunda zaisa wa cikin sa
Saifuddeen asuban fari ya bar gidan su yana zuwa ya tadda su Amna suna salla zama yayi yana kad'a k'afa dan jiya dakyar ya samu yayi bacci tsaban k'unan da zuciyar sa yake masa, amma ganin su suna sallah sai abun ya birge shi shima ya tashi ya shiga toilet ya d'auro alola, bedroom ya shiga ya tada sallah, yana idarwa ya dawo falo yaga tana ta addu'o'i bai yanke ta ba saida ta idar ta shafa, juyo tayi ta kallesa gaban ta yana fad'uwa tace "..........
Mmn Ashfaq