30
by @mmnashfaq
59/60
***
Yana futa gidan su Ammar a bokin sa yaje duk da halin su baizo d'aya ba amma basu da abokan daya wuce su biyun nan a duniya, shak'uwa ce mai karfi a tsakanin su tun suna yara har suka girma, saidai Ammar kwata kwata baya son halin bunsuranci da Saifuddeen yakeyi hakan yasa kullun suka zauna sai sunyi fad'a, amma fad'an baya zuwa ko ina dan basu juran fushi da juna, yana zuwa gidan yayi horn mai gadi yazo ya lek'a ta b'ulin k'ofan ganin motan Saifuddeen ne yasa ya bud'e k'ofan da saurin gudun kar yayi laifi danko y'an gidan baya tsoro kaman yadda yake tsoron fad'an Saifuddeen, shigo da motan yayi maigadi yana gaishe shi amma bai samu azzikin amsawa ba ko kallan inda yake baiyi ba ya futo yayi shigewan sa ciko, tab'e baki maigadi yayi yace "mutum fari amma zuciyar sa bak'i, koda yake hanun sa da aljihun sa fari ne tunda kullun yazo koya zageni saiya mun kyauta mai tsoka, shidai baya son kula mutane ne kawai matsalan sa"
D'akin Ammar ya shige dan yasan mutan gidan basu tashi ba tukunna, yana shiga ya samu Ammar yana bacci, zama yayi kusa dashi ya janye fulon daya d'aura kansa kai, Ammar yanajin anja fulo da k'arfi ya tashi yana zare ido danya zaci b'arayi ne suka kawo masa hari, suna had'a Ido da Saifuddeen ya sake ware Ido yace "Saifu lafiya ka futo da sassafen nan?
Yatsina fuska Saifuddeen yayi yace "Ina ko lafiya ai tunda ka ganni da asuban nan kasan ba k'aramun abu bane ya futo dani"
Matsowa kusa dashi Ammar yayi yace "baka da lafiya ne inane yake maka ciwo naji idan fanni nane na duba ka idan kuma bai shafe niba muje asibiti"
Tsaki Saifu yayi yace "ce maka nayi ba lafiya ba bawai bani da lafiya ba"
Ammar yasan ba abun kunya bane yanzu su raba hali, saiya kwantar da kansa yace "kayi hak'uri aboki na kasan dole na shiga damuwa saboda ganin ka a lokacin da nasan baka futowa, nasan duk inda kake ko a Spain ne baka futa aiki sai 10, kuma 9 kake tashi a bacci, ka duba lokaci fa yanzu 5:54 ne ko 6 baiyi ba, ba dole na tambaye ka, amma ina jinka maiya faru?
Nunfashi yaja ya dafe kansa yace "Ammar yarinya nane tace bazata bini Spain ba ni kuma bazan iya rabuwa da ita ba, shine nakeso ka sama Mata gurbin karatu a ATBU duk da result d'inta bai futo ba amma inaso ta fara karatu wannan shekaran, sannan inaso kasawa rayuwar ta Ido karka bari wani ya kalleta, Ammar banaso asamu matsala aduk abunda na indaya maka idan aka samu matsala kasan halina zamu samu mummunan matsala dakai"
Tsaki Ammar yayi "yace niba d'an iska bane irin ka dazan ajiye mace a waje na, kaida kaga hakan ya dace da rayuwar ka, kaje kayi tayi amma kaji na rantse maka bazan ajiye kowa ba a wajena"
Kallon sa Saifuddeen yayi yace "wannan ba irin Matan da kake tunani bane Ammar, wannan ta babban ta da sauran, dan tana da girma da kima a wajena, kuma ba ita kad'e bane ita da k'anin tane, kayi hak'uri ka daure kamun wannan alfarman"
Ammar yace "bazanyi ba Saifu kaje ka nema Mata gidan karuwai ta zauna amma nikam bazan iya irin wannan ba, zaka iya tafiya tunda ka gama fad'an abunda ya kawo ka"
Saifu had'a hanun sa yayi waje d'aya yace "Ammar ka dubi girman Allah kamun wannan alfarman, sanin kanka ban tab'a ganin mace naji na taimake ta ba amma wannan ta tsaya mun arai bazan iya barin ta ta tafi ba, ni zan biya Mata kud'in makaranta abincin da zasu ciki gidan da zasu zauna da kud'in kashewa duk ni zan d'auki nauyin su, admission kawai da gidan da zata zauna nakeso ka nema mun sai kuma sa Ido a duk wani motsin ta, dan bana so kowa ya rab'e ta ballan tana yace yana sonta, ka taimake ni kamun wannan daga shi bazan sake neman komai a wajen kaba"
Tsaki Ammar yayi yace "bansan maiyasa wani lokacin baka da fahinta ba kwata kwata Saifu, nace bazanyi ba tunda itama karuwa ce irin ka ka barta taje ta nemi wajen da zata zauna da kanta, kuma ai tasan hanyan da akebi a samu admission taje tayi komai da kanta, waima da kake cewa na kula maka da ita, meye had'in ka da ita da bazaka barta ta koma gaban iyayen taba, kafi kowa sanin ba wanda na tsana a rayuwa ta kaman macen da bata da kamun kai, dan haka ka fuce mun a d'aki bana son irin wannan banzan maganan"
Saifu zuwa yanzu hak'urin sa da nutsuwar sa sun sub'uce masa ji yake kaman zuciyar sa zata fashe tsaban bak'in cikin abunda abokin sa yake fad'a masa cikin k'unan rai yace "nina kawo kaina wajen ka, dole ka fad'a mun duk abunda kaga dama, ka rubuta ka ajiye daga yau ni Saifuddeen na rabu dakai rabuwa nahar abada, wallahi Ammar kokai ka aifeni ba halak'an da zata sake shiga tsakani na dakai" key motan sa ya d'auka ya futa ransa a mungun b'ace tada motan yayi ya danna horn d'in da saida ya tashi duka mutanen gidan, maigadi jiki na b'ari yaje ya bud'e masa get, a 360 ya futa a layin, bai tab'a takaicin rashin kula abokai ba sai yau, ada baya ya d'auka Ammar zai maye masa gurbin duk wani aboki a rayuwar sa amma yanzu ya tabbatar wa kansa ba haka bane, Ammar ba kowa bane a garesa kuma sun rabu kenan rabuwa na har abada, gidan da Amna take ya nufa yana zuwa ya futa ya bud'e get d'in ya shiga, a takure waje d'aya ya samesu, sai suka bashi tausayi ya zauna yana huci kaman wani kumurci, Amna da Abbas yanayin sa ba k'aramun tsoro ya basu ba, sunaso su tambaye sa abunda ya faru amma tsoro ya hanasu, Amna ce tayi k'arfin halin tasowa tazo ta tsuguna a gaban sa cikin sanyin muryan ta tace "Yaya Saifuddeen kaman ba haka ka futa a gidan nan ba, halamu ya nuna wani ya b'ata maka rai a waje" ta k'arasa maganan kaman zatayi kuka, ji yayi kaman ya rungume ta ko zaiji sassauci abunda yakeji a zuciyar sa, sai kuma ya fasa ya zuba Mata Ido, ganin yadda idonsa yayi ja kuma yana kallon ta cikin b'acin rai yasa tayi saurin tashi ta koma inda take, suka sake takurewa waje d'aya, kallon su ya cigaba dayi kafin ya tashi ya futa batare dayace musu komai ba yaje ya tada motan sa yabar gidan.
Ammar yana ganin yadda Saifu ya futa sai yaji kwata kwata bai kyauta masa ba kuma tunda suke haka bai tab'a faruwa a tsakanin su ba, Saifu bai tab'a bud'e baki yace zai rabu dashi ba sai yau, yana cikin tunanin yaji an dafasa ta baya ya juyo da saurin Daddy sa ya gani yana kallon sa kafin ya koma ciki shima bin bayan sa yayi yana shiga yaga mutanen gidan su a falon kowa yanaso yaji maiya faru, Daddy yace "waye ya futa da irin wannan gudun?
Kanshi ya sunkuyar yace "Saifuddeen ne Daddy" suka had'a baki wajen cewa Saifuddeen kuma maiya faru? Yace "yazo neman alfarman da bazan iya masa bane shine yayi fushi ya futa yace har abada bazai sake zuwa inda nake ba, kuma ya rabu dani har k'arshen rayuwar sa"
Umma tace "wani irin abu ya nema? Kanshi a sunkuye yace "Umma wai so yake na nemawa budurwan sa admission sannan ina kula da ita har saiya dawo, ni kuma bazan iya kula da wata mace ba, tunda tana da iyaye taje iyayen ta su kula da ita su Mata duk abunda ya dac...bai k'arasa ba yaji sauk'an mari a fuskan sa Daddy ya nunasa da yatsa yace ban tab'a tunanin baka da halacci ba sai yau, nayi tunanin ko a gidan nan Saifu yace zai ajiye budurwan sa tayi karatu zaka bata d'akin ka ta zauna, amma ko kunya babu kake maimaita mana abunda ka fad'a masa, koda yake rayuwar kane kayi duk yadda kakeso ni zan mishi duk abunda yakeso" yana gama maganan ya haura sama a hankali kowa ya watse ya barshi, dan ba wanda ya goyi bayan abunda yama aminin sa, tashi yayi jiki a sanyaye ya koma d'akin sa wayan sa ya d'auka ya kira layin Saifu amma yak'i d'agawa ya kira yakai sau talatin amma ba'a d'aga ba daga k'arshe yaji wayen a kashe, tashi yayi ko kayan jikin sa bai canja ba ya d'auki key motan sa ya futa yana shiga gidan su Saifu ya wuce Mom ba tare daya gaishe taba, d'akin Saifu ya shiga bakin sa d'auke da sallamah yaje ya tsuguna a gaban sa yace "natuba aboki na kayi hak'uri na gane kuskure na yanzu muje zan maka duk abunda kakeso" ko kallon inda yake Saifu baiyi ba, saida yaga Ammar yana bashi hak'uri yana kuka kafin yace "karka damu Ammar na hak'ura amma zan Mata komai da kaina, da d'in ma nazaci damuwa ta damuwan kane shiyasa naje da k'ok'on barana, amma yanzu komai ya wuce zan d'aga tafiya ta sai na gama komai"
Kallon sa Ammar yayi yace "Saifu karka bari mace tayi nasaran raba amintan da muka ginasa tun muna yara, idan har ka hak'ura yanzu tashi muje ka kaini wajen ta"
Saifu yace "ban shirya kaika wajen ta ba yanzu ka bari idan na siya Mata nikaf sai muje dan ko kai ban yarda ka kalle taba, kuma duk ranan daka sake kukayi magana ko ka kalli fuskan ta Allah ya isa"
Shidai Ammar da to yayi ta binshi duk yadda yaso Saifu ya sake suyi hira yadda suka saba k'i yayi daga k'arshe ya masa sallama ya futa, bayan tafiyan Ammar Saifu ya futa a ranan yayi cuku cukun nema Mata admission, lokacin da aka tambaye sa sunan ta kame kame ya fara, saida ya kirata ta fad'a masa, ya Mata registration kafin ya nemawa Abbas nashi a general Hassan ya nema musu gidan haya mai kyau a kusa da ATBU, daga nan kasuwa ya wuce ya siya Mata waya da Sim, kafin ya sake shiga cikin kasuwan ba k'aramun siyayya ya Mata ba har suturan sawa saida ya siya Mata da yawa, ya ajiye Mata kud'i mai yawa a k'asan katifan daya siya Mata, guess house ya koma yana shiga yace su taso su tafi, a tsorace suka bisa, Yalwa suka koma ya kaita har d'akin su, kafin suka futa ya nunawa Abbas school d'insu, ya musu sallamah ya futa, ba k'aramun murna sukayi ba da sabon rayuwan da zasu fara.
Ammar har dare yana jiran yaga kiran Saifu amma shuru gashi idan ya kira wayan sa sai ace masa tana kashe, dole ya hak'ura akan dasafe zaije ya samesa, k'arfe bakwai ya tafi gidan su Saifu a k'ofan gidan suka had'u lokacin Saifu ya futo da mota zai futa, ganin ko kallon inda yake baiyi ba yasa yabi bayan sa wani d'an matsakaicin gida yaga ya tsaya baifi minti biyu ba suka futo da wata yarinya fuskan ta rufe da nikaf daf zasu shiga mota Ammar yayi saurin futowa ya k'arasa wajen su yace "Saifu horan ya isa haka"
Murmushi Saifu yayi yace "ba horo bane inaso na saba yin komai da kaina ne shiyasa" shuru Ammar yayi kafin yace wa sunan Gimbiyan taka"
Saifu yace "wannan ba hurumin ka bane, mu zamu wuce dan mungama yin komai
Ammar yace..........
***