38
by @mmnashfaq
75/76
***
Saboda ji da yayi zuciyar ta baya bugawa ko kad'an, duk wani halamu da zai nuna maka mutum yana da rai babu a tare da ita, kifa kansa yayi a jikin gadon yana furta Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un, Zainab maiyasa kika bari namiji yayi nasaran rabaki da duniya, baki birgeni ba Zainab naso ace kin rayu kiga lokacin da mijin ki zai dawo gare ki, maiyasa Mata suka d'auki kishi mai tsanani sukasa wa zuciyar su yanzu? Share hawayen sa yayi ya juya ya futa zuwa wajen Inna Turai, Inna Turai tana tsaye a k'ofan d'akin zuciyar ta na dokawa da k'arfi domin ta k'agu taga futowan sa dan ta futar daran Zainab tana raye, saidai kuma bata son ta mutu ba tare data nemi gafaran ta ba, yana futowa tace likita ya jikin tan dai?
Ya girgiza kansa yace "Inna Turai saidai muyi hak'uri domin Zainab ta rigamu zuwa gidan gaskiya, kuka Inna ta saka mai k'arfi tare da durk'ushewa a wajen tana cewa mutuwa baka mun adalci ba maiyasa ka d'auke ta batare dana sanar da ita zalincin dana Mata ba, maiyasa ta mutu ba tare dana nemi gafaran taba, ta d'ago kanta ta kallesa tace "likita dan Allah ka kaini wajen ta na nemi gafaran ta tunda ance gawa yana jin duk abunda ake fad'a saidai bayi da ikon mayarwa ne kawai"
Tausayi ta bashi ganin yadda take kuka, shima wani kukan ne yazo masa amma saiya daure gudun karya dad'a d'aga Mata hankali, dan mutuwan Zainab ba k'aramun shigan sa yayi ba yace "zan kaiki ki ganta saidai idan kinmun alk'awarin bazaki Mata kuka ba, dan a halin da take ciki yanzu addu'an mu tafi buk'ata ba kuka ba" kai ta shiga gyad'a masa kaman jinjirin k'adangaren, gaba yayi ta bisa a baya, ganin Zainab a kwance bata nunfashi yasa ta kasa rik'e kukan ta cikin kuka tace "na zalince rayuwar ki Zainab na kai mijin ki wajen....ganin idon Zainab na motsi yasa ta kasa k'arasa maganan ta tace "likita duba ka gani kodai ido nane yake mun gizo?
Kallan ta yayi da jajayen idon sa yace "mai kika gani?
Tace "idon Zainab ne naga kaman yana motsi yanzu kuma duba bakin ta kaman mai shirin cewa wani abu" da sauri ya juya ya kalleta ganin ba gizo idon sa yake masa ba yasa yace "Alhamdulillah bani waje na sake dubata yanzu nan, oxygen ya jawo ya saka Mata tare da bata taimakon gaggawa, ganin nunfashin ta ya fara harbawa duk da da k'arfi yake futa amma yaji dad'in ganin ta dawo bata mutu ba, ranan a wajen ta ya kwana dan ya kasa tafiya ya barta burin sa ta farfad'o yaji abunda ya tada Mata ciwon, wasa wasa saida tayi sati biyu kafin nunfashin ta ya dawo daidai, ya cire Mata oxygen, tana bud'e Idonta ta fara kallon d'akin da take kafin ta sauk'e Idon ta akan doctor Mansur da Inna Turai da take gefan sa, murmushi suka sakar Mata dukan su a tare kafin suka fara jero Mata sannu, kulawa na musamman suke bata har jikin ta ya farayin sauk'i, yau ganin ta cikin walwala kuma da halamu ta samu sauk'in jikin ta sosai ya jawo kujera ya zauna kusa da ita ya zauna yace "ranki shi dad'e tunda kin samu sauk'i ya kamata ki koma d'akin mijin ki"
Murmushi kawai ta masa dan zuwa yanzu taji damuwan ya ragu sosai a zuciyar ta kuma bata jin son Umar ko kad'an a rayuwar ta saidai salwantar da rayuwar ya'yan ta da tayi shikam yak'i gogewa a zuciyar ta sai kuma maganan Umar na cewa bata da ma'aifa shima yana Mata zafi a zuciya, tasan tabbas Umar ya cika butulu azzalumi maha'inci, amma ba komai akwai Allah, doctor Mansur buga gefen gadon yayi yace "kina tare dani kuwa?
Sunkuyar da kanta tayi hawaye ya fara kwaranya a idonta, yace subbahanallahi maiye haka Zainab? Mun samu mun shawo kan wannan matsalan amma kinaso ki dawo mana dashi baya"
Had'a hanun ta tayi tace "tuba nake likita amma bazan koma gidan Umar ba domin ya sake ni, damuwa ta yanzu bansan inda zan dosa ba, na guji kowa nawa akan sa ciki kuwa harda iyaye na, gashi daga k'arshe irin sakayyan da yamun kenan"
Kafin yayi magana Inna Turai ta shigo ta zauna a gefen ta tace "Hajiyah kiyi hak'uri da abunda zan fad'a miki, nasan duk abunda ya faru nice sila, domin ni na jawo Alhaji yake miki duk wulak'anci da yake miki a yanzu, Hajiyah shekara ishirin da biyu da suka wuce..... Zainab saurin d'aga Mata hanu tayi tace "bana son jin labarin wannan shekarun dan nasan idan kina fad'an abunda ya faru ba iya sauraran ki zanyi ba hankalina zai tafi kan abunda na aikata a lokacin, yanzu kuma mungun abunda mukayi yake ta cutar da rayuwa ta, ki rik'e labarin kawai na yafe miki nima ki tayani rok'on Allah ya yafe mun nawa kura kuran"
Inna Turai idon ta yana zubar da hawaye tace "nagode Hajiyah amma nasan idan ban sanar dake laifina ba, zuciya ta bazata tab'a samun nutsuwa ba, fatana Allah ya baki lafiya kodan kiga sakayyan da zai miki.
Doctor Mansur yace "yanzu ki tashi muje mu d'auko motan ki da kayan ki da duk wani abunda kike buk'ata, sai na kaiku gidan mu kafin komai ya dawo daidai"
Murmushi ta sakeyi tace "daidai da kayan jiki na dazan samu wanda zan saka dana cire sa na k'ona dan nasan idan yana jiki na Allah bazai tab'a karb'an tuba na ba"
Doctor Mansur yace "Zainab kar zafin sakin da aka miki ya sakaki yin sab'o, ki zamo d'aya daga cikin mutane masu yadda da kaddaran su, nasan duk abunda ya faru dake jarabawa ne idan kikayi Imani dashi kuma sai kiga Allah ya miki canji mafi alkhairi a rayuwar ki, dan haka ki tashi muje ki iba suturan ki da duk wani abunda ya kasance naki kuma wanda zai miki amfani a gidan, saina kaiku sabon gidan dana gina dan nasan idan na kaiki gidan mu, bazasu barki ciwon ki ya lafa ba sunyi ta miki nasiha kenan akan ki koma gidan ki, ni kuma bazan barki ki koma yanzu ba harsai naga kin samu lafiyan da zaki iya jure k'ananun bak'in ciki tukunna"
Jinjina kai tayi hawaye na sauk'a a fuskan ta tace "banyi niyan cewa komai ba, amma ya zamo dole na fad'a maka kad'an daga ciki kodan ka yarda bank'i karb'an jarabawa naba, duk abunda kukaga Umar yana dashi ba ta hanyan da Allah yace mu nema ba ya nemesu, ta haramtaccen hanya ya tarasu, Umar rik'ekken dan mafiya ne, dan haka yasa nace bazan d'auki komai nasaba, amma idan ka dage zanje na ibo kaya na nayi amfani dasu"
Inna Turai a razane ta tashi tace "Hajiyah kina nufin Alhaji dan k'ungiyan asiri ne?
Zainab tace ba nufi nakeyi ba tun ina da cikin fari ya fara wannan mummunan hark'an"
Doctor Mansur yace "karki damu zan siya miki wani, abunda nake buk'ata a wajen ki yanzu ki kwantar da hankalin ki, idan kika samu lafiya sai muje mu nemi gafaran iyayen ki" godiya suka masa kafin ya ibesu ya kaisu gidan sa, gida ne d'an madaidaici mai mungun kyau, tun lokacin ya cigaba da kula da duk wani abunda zasu buk'ata da lafiyan ta Inna Turai tana taya sa domin tace bazata koma gidan Umar ba kuma bazata koma k'auyen su ba harsai ta fad'a wa Zainab mungun tuggun da aka had'a baki da ita aka Mata"
Umar yana rungume da Hanifa dan tun bayan futan Zainab a d'akin take ta masa borin sai yaje ya kirata ta sake Mata kuruwan y'a, k'ok'arin had'e bakin su waje d'aya yakeyi yaga jini ya d'igo a hanun sa yayi saurin sake ta yana cewa "ki jirani yanzu zan dawo" bai tsaya jin abunda zatace ba ya futa da sauri d'akin sirrin sa ya shiga ya saka kayan zuwa meeting kafin ya murza jan kyallen daya d'aura a hanun sa, yana zuwa wajen meeting d'in yaga kowa fuska a murtuk'e yaje zai zauna kaman yadda ya gansu a zauna, tun kafin yakai k'asa yaji an daka Masa wata gigitacce tsawa kafin aka fara magana cikin b'acin rai da bada umurni, Shugaban sune yace.......
***
Mmn Ashfaq