44
by @mmnashfaq
87/88
***
Daddy yace "Alhamdulillah kaman yau kuka fara exam gashi har kun gama, saidai muyi fatan Allah yasa ku futo da saka mako maikyau, abunda nakeso na fad'a muku shine nagama shirya mana tafiyan mu tas insha Allahu gobe zamuyi asuban cin tafiya Tilde cikin rigan Larro kaman yadda kikace, dan bai kamata muyita rik'e ku batare da iyayen ku sunsan inda kuke ba, magana na gana Amna zuwa yanzu ya kamata ki tsayar da mijin da zaki aura, dan bazamu zuba Ido muna ganin irin wannan abubuwan na faruwa dake ba muyi magana ba, gwanda ama tufkan hanci tunda wuri basai abubuwa sun lalace mana ba, yanzu ke muke sauraro ki fad'a mana wanda kike so, idan kuma Saifu ne fad'uwa yazo daidai da zama sai nama iyayen sa magana a tsayar da rana, kinga saiki hak'ura da karatu ki bishi Spain ya nema miki wani gurbin karatun acan"
Daga Amna har Abbas da Ammar gaban su ba k'aramun mummunan bugawa yayi ba, kowa da irin tunanin da yakeyi a zuciyar sa, Ammar tsoran shi kar tace ta amince da Saifu, dan idan hakan ya faru baisan yadda zaiyi da rayuwar sa ba"
Amna cikin girmamawa da sanin darajan Babba tace "Daddy zanso ku dad'a mun lokaci, dan kwakwalwa ta ta kasa zab'a mun wanda ya dace da rayuwa ta, inaso idan Allah ya kaimu Tilde lafiya zanje gidan Malama Aisha domin bani da uwar data fita a duniyan nan, ita kad'e ne zatafi zab'a mun wanda ya dace da rayuwa ta, dan Allah Daddy kamun wannan alfarman"
Daddy yace "shikenan Allah ya nuna mana goben amma ki sani bayan shi ba wani alfarman da zamu sake miki akan aure" ta d'aga kanta tace na amince Daddy"
Ta sake sunkuyar da kanta tace "Daddy inaso naje gidan dana zauna a Yalwa dan akwai abubuwan da nakeso na ibo acan"
Yace ba komai zaki iya zuwa ya kalli Ammar yace ka kaisu su ibo duk abunda take buk'ata"
Ammar yace "to Daddy" su Aleesa sukace suma zasu bisu, tare suka tafi dukan su, yadda sukabar d'akin haka sukazo suka same sa saidai yayi k'ura halamun ba mutum a ciki suna shiga tayita kallon ko ina na d'akin da kallo duk abubuwan da suka faru suna dawo Mata kwakwalwan ta, jikin a s sab'ule taje ta bud'e dirowa ta d'auko rawanin Baffa da wuk'an sa sai kud'in datazo dashi, d'aga katifan tayi kaman zata iba kud'in da Saifu ya ajiye Mata saita fasa tace "kaima da sannu zaka karb'a naka" dauk'an duk abunda tasan yana da amfani a wajen ta tayi kafin suka rufe k'ofan suka tafi, washe gari k'arfe shidan safiya Mommy Daddy! Ammar! Abbas sai Amna suka d'auki hanyan Tilde k'arfe bakwai daidai suka isa cikin garin Tilde, Abbas yana ta nuna musu hanyan da zasu bi a daidai kan kwanan su tace "Daddy dan Allah ku tsaya anan zanma mai shagon nan magana"
Daddy yace Ammar ya tsaya dan shi yake tuk'a motan futowa tayi ta nufi shagon Sama'ila tana zuwa ta tsaya daga waje tana mishi sallama, tasowa yayi yana cewa sannu da zuwa Hajiyah "mai za'a kawo miki?
Amna tsayawa kallon shagon tayi ganin duk ya k'are daidai da fridge da yake ciki yanzu babu tace "baka gane ni ba ko?
Kura Mata Ido yayi amma ya kasa gane ta yace "aiko mai kama dake ban tab'a gani ba Hajiyah"
Murmushi tayi tasa hanu a jakan ta taciro dubu d'ari biyu cif tace "ga wannan dukiyan kane da kake bani ina k'arama, bansan ko zaka iya tuna wata baffulatana mai suna Amna ba, to nice Amna idan ka tuna wannan kud'in kana bani ne idan kayi amfani da dabaran ka wajen so ka cutar da rayuwa ta sai kuma Allah ya kub'utar dani"
Daskarewa Sama'ila yayi a wajen yana mamakin wai Amna ce a gaban sa yau! Amna ce ta dawo kaman balarabiya! Kafin yayi magana harta ajiye masa kud'in a wajen tayi gaba, maimakon tayi wajen motan saita tsallaka titi ta shiga school din da sauri tana raba ido taga ta inda zataga Malama Aisha, ganin Malamai basuzo duka ba yasa tajuya zata futa taje gidan ta taduba ta, Malama Rukayyah ce ta wuce ba tare data ganeta ba, Amna da sauri tace "ina kwana Malama Rukayyah"
Malama Rukayyah ta juyo fuskan ta dauke da murmushi tace "yawwa sannu y'an Mata saidai ban gane waye ba"
Tace "Amna Salihu ne dama nazo neman Malama Aisha ne sai naga bata zo ba" da sauri ta rungume Amna cikin farin ciki tace "Amna ashe da rabon Aisha zata sake ganin ki a rayuwar ta, tana nan hankalin ta a tashe kullun burin ta yaushe zaki dawo, bazan kirata ma kiji muryan ta" number ta takira saida ya kusan yankewa aka d'auka, jin muryan Umma yasa Malama Rukayyah ta gaisheta kafin tace "Malama Aisha bata kusa ne?
Umma tace "tana kusa muna asibiti ne ana k'ara Mata ruwa" Malama Rukayyah tace "Allah sarki maiya sameta?
Umma tace "Aisha bata jin magana ba wanda bai bata shawara ba akan yaran nan, munce Mata ba yawan kukan ta bane zai dawo Mata dasu addu'a suka fi buk'ata a wajen ta amma tak'i ji, gashi zataje ta kashe kanta a banza"
Kafin Malama Rukayyah tayi magana Amna ta kwace wayan kasancewan tana jin duk abunda suke fad'a muryan ta yana rawa tace "Umma kuna wani asibiti ne? kice mata gamu nan mun dawo gareta bazamu sake zuwa ko ina ba" ta k'arasa maganan cikin kuka, Umma tace "waye ked'in? Tace "Umma nice Amnan da take nema tana ina ne?
Umma tace "Amna badai Amnan da take ciwo akansu ba? Malama Aisha najin Umma ta ambaci sunan Amna ta tashi da sauri tare da karb'an wayan tace "Amna kune? Amna tace eh mune kina ina dan Allah?
Cikin kuka tace "ina garin mu Birnin Kudu Amna, amma dan Allah ki jirani a gidan Malama Rukayyah yanzu zamu taho na tafi dake"
Amna tace "basai kinzo ba ni zanzo har inda kike, yanzu zan karb'a number ki a wajen ta, na kiraki da number na" tana kashewa ta kirata da number ta tace "dan Allah karki taso ki rubuto mun sunan unguwar ku kawai a Birnin Kudu" kashe wayan tayi tama Malama Rukayyah da take ta binta da kallo sallamah kafin ta koma motan Daddy ya kalleta yace "kin jima Amna kuma kin dawo da kuka maiya faru"
Tace "Malama Aisha bata da lafiya yanzu haka tana asibiti a kwance a Birnin Kudu"
Yace "subbahanallahi mai yake damun ta? Tace "Umman ta tace mun wai damuwan rashin mune ya aifar Mata da ciwon" jinjina kai yayi suka cigaba da tafiya ba tare dayace komai ba, mutane ganin mota maikyau yana ta dannawa daji yasa suka futo suna ta kallon su, a gidan Goggo suka tsaya Amna tana futowa ta gangara bakin ruwa wani sabon kuka ne ya zo mata aiko ta sake sa da k'arfi tana durk'ushewa a wajen, Abbas shima zuwa yayi ya rungume ta suna kuka gwanin ban tausayi, Daddy ya matso kusa dasu yace "ko baku son mutanen rigan su ganku ne shiyasa kukazo kuka b'uya anan?
Amna ta girgiza masa kai tace "ba haka bane Daddy ba abunda mukayi wa mutanen rigan nan da zamu b'uya musu, nan wajen da kake gani kullun da hantsi kafin Baffa na ya futa kiwo anan muke zama mu biyu yayita bani bari kala kala, har aka aifa Abbas ya dawo mu ukun mu kullun bamu da wajen zaman daya wuce nan"
Daddy ya shafa kanta yace kiyi hak'uri ba kuka ya makata ki masa ba addu'a yafi buk'ata a gareki ba kuka ba kinji, ya kama hanun su yace muje ku nuna mun gidan ku, gaba Abbas yayi suka bisa a baya suna zuwa gidan yayi sallamah Goggo ta amsa masa, ta d'ago tana kallon su, Amna ganin Mata biyu zaune da tsohon ciki ta k'ura musu Ido a tsorace tace "D'ahare Maree yaushe kukayi aure?
Goggo a zabure ta mik'e tace "badai Amna bane a gabana?
Amna tayi murmushi tace "nice Goggo" ashar Goggo ta watso tace "baki isa ba aradu ai dama tunda muka bud'e Ido mukaga kin gudu a gidan nan nasan akwai abunda kika taka, wato kin kwashe kud'in Bappa kin tafi burni yin karuwanci to Aradu ki bud'e kunnen ki dakyau kiji ni koki bada kud'in da kika sata konayi ta dukan ki har sai kin mu"
Abbas ne yayi dariya yace "Goggo kisan abunda kike fad'a dangane da Adda na dan yanzu ba da bane kuma ni da kike gani hukuma ne a gaban ki kina fad'an abunda bai dace ba zanyi ta dukan ki sannan muje mu d'aure ki a birni muna gana miki azaba"
Ido Goggo ta zaro tace "aradu wasa nake Mata sannun ku da zuwa da fatan mun samaiku lafiya ya gida da iyalan ku"
Daddy yace "mu ya kamata muyi miki wannan gaisuwan bake ya kamata ki mana ba, kece ma'aifiyar Amna?
Dad'a tsurewa Goggo tayi dan a zaton ta laifi Amnan tayi akazo tafiya da ma'aifiyar ta tace "aradu ba nina aife ta ba hasalima bansan uwarta ba, saidai kuje gidan Baffan su Sule nasan shi yasan uwarta dan Baffa Salihu baya iya yin komai ba tare da sanin d'an uwan sa ba"
Jinjina kai yayi ya juyo ya kalli Amna yace "zaki gane gidan"
Tambayan dariya yaso ya bata wai gidan Baffan ta akecewa zata gane tace "nasan gidan ba nisa da nan ma, amma dan Allah kafin muje wajen sa ku barni na tafi wajen Malama Aisha domin na duba lafiyan ta" ta k'arasa maganan cikin kuka, Daddy yace "bazan hanaki zuwa wajen Matan data rik'eki tamkar uwa ba, saidai kibari mu fara zuwa wajen Baffan ki tukunna, sun juya zasu futa kenan sukaji sallaman Baffa Sule yana dariya yace "Allah nagode ma daka nuna mun dawowan y'ata ina raye ban mutu ba, yanzu akaje aka sheda mun dawowan ku, Amna Abbas ashe zaku dawo gare mu?
Amna da Abbas zuwa sukayi suka rungume sa suna murnan ganin sa, Amna tace "Baffa Sule kayi hak'uri ka yafemun nasan mun d'aga maka hankali na rashin sanin inda muke, amma ba yadda zamuyi ne dole yasa muka tafi, amma ka yafe mana dan Allah"
Yace "na yafe muku Amna, kuma naji dad'in ganin ku cikin nutsuwa ba tare da wani abu ya faru daku ba, saidai yanzu bazaki sake tafi ki barni ba, saidai idan kinyi aure ba yadda na iya dole na barki kitafi"
Tace "Baffa Sule banyi aure ba, na isa nayi aure ba tare da sanin iyaye na ba, tunda muka barku muka samu gurbin karatu a birni, nima bazan so na sake barin ku ba dan duk d'an halak baya raina asalin sa, kune tushe na kuna fara bud'e Ido nagani a duniya ta, duk inda na shiga ina zama ne kawai amma bana samun kwanciyan hankali kaman yadda nake samu anan, duk da kulawa da soyayyan da suke nuna mun amma rayuwa cikin ku yafi komai mun dad'i, saidai ina neman alfarma d'aya Baffa Sule"
Yace "ki fad'a koma meye zan miki koda kuwa da duka azziki na zai k'are, idan a kanki ne zan sadaukar saboda nayi farin ciki da ganin ki, halamu ya nuna mun kin cigaba da kamun kai dana sanki dashi, amma duba y'an uwan ki da uwarsu ta nuna sune ya'yan so duba kiga yadda rayuwar su ta kasance yanzu ko wannen su yana da yara uku uku ga cikin na hud'u ba tare da sunyi aure ba, kedai Allah ya miki albarka yasa ki gama da duniya lafiya"
Tace "Amin Baffa na, Baffa Sule dama akwai wata Malama Aisha data sadaukar da rayuwar ta akan mu shine bata da lafiya nakeso muje yanzu mu duba ta nida Abbas" labarin irin taimakon da Malama Aisha ta musu ta bashi da abunda yasa suka gudu a gidan ta"
Baffa Sule yace "ai basai kin nemi alfarma bama, yanzun yanzun nan zamu tafi danko gida bazamu koma ba"
Daddy yayita kallon su cike da sha'awa kafin yace "muma baza'a barmu a baya ba ku shiga mota mu tafi tare, suka shiga mota har zasu tafi Amna ta kalli su D'ahare da tausayawa tace "kunyi asaran rayuwa, yanzu meye riban da kuka samu a bariki? Ku lissafa abunda kukeso idan na dawo zan baku kud'in ku siya" ta shige mota suka d'auki hanyan Birnin Kudu.
Zainab bayan sun karya doctor Mansur yace "ku futo mu d'auki hanya dan bana son tafiyan rana, suka futo suma suka d'auki hanya.............
***
Mmn Ashfaq