45
by @mmnashfaq
89/90
***
K'arfe goma daidai Zainab suka isa garin su lokacin da suka shiga layin su tsoro ne da fargaba ya d'arsu a zuciyar ta wanda ya aifa Mata sark'ewan nunfashi da kafewan Ido, doctor Mansur juyowa yayi ya kalleta ganin yadda nunfashin ta yake neman d'aukewa yasa yayi parking a daidai wani majalisan dattije, ya futo da gudu ya bud'e k'ofan da take yana cewa "haba Zainab meyasa zaki mana haka, kin mun alk'awarin zaki kwantar da hankalin ki, bazaki bari ciwon ki ya tashi ba amma maiyasa kika kasa cika alk'awari" tsofin da suke wajen da masu wucewa jin abunda yake fad'a kuma cikin tashin hankali yake maganan yasa sukayo kansu suna cewa lafiya bawan Allah"
Doctor Mansur ya d'ago yana goge zufan daya karyo masa yace "wallahi tun daga Abuja na d'auko ta dan na dawo da ita wajen iyayen ta saboda mijin ta yana cutar da ita harya saka Mata ciwon zuciya mai TSANANI, kuma tamun alk'awarin bazata d'aga hankalin taba idan mukazo ita burin ta iyayen ta su yafe Mata, shine fa daga shigowan mu unguwar nan nunfashin ta ya fara d'aukewa, kuma nasan ba komai ya jawo hakan ba sai tsoron had'uwa da iyayen ta data saka a zuciyar ta"
Wani mai suna Mubarak jin abunda yake fad'a yasa ya tura kansa cikin motan Idon sane ya sauk'a akan Zainab da nunfashin ta yake futa kaman tazo gangaran mutuwa, cikin tashin hankali ya futo da kansa yace "Abba Zainab ce fa"
Abbah yace "wata Zainab d'in" bai samu daman bashi amsa ba ya jawo hanun sa suka shiga motan yace "bawan Allah mutafi asibiti karta rasa rayuwar ta dan Allah"
Abunka da uba da y'ar sa, y'ar ma mafi soyuwa a zuciyar ubanta, yana arba da ita a take hankalin yayi mummunan tashi hawaye ya fara zubowa a idon sa yace "d'an nan kayi sauri mu kaita asibiti dan Allah"
Ajiyan zuciya doctor Mansur yayi ganin ciwon ya dawo sanadin da iyayen ta suka karb'e ta ba tare dasun sha wahala ba yace "inane gidan Baba muje na duba ta acan, dan nine likitan ta kuma ina da komai a motan nan" nuna masa saitin inda suke sukayi sukace gidan jikin farin masallacin nan, jan motan yayi ya k'arasa k'ofan gidan, Mubarak ne ya d'auke ta a kafad'a yace su biyosa, akwatin first-aid d'insa ya d'auka yabi bayan su a falon Abba aka kwantar da ita, dan zuwa yanzu bata san inda take ba, kafin wani lokaci Yayun ta maza da k'annan ta Mata da suke gidan auran su duk sun cika a gidan, Umma tana asibiti sukaji labarin Zainab ta dawo ga kuma halin da take ciki suka taho gida, kowa ka gansa hankalin sa a tashe yake, Inna Turai kan komawa gefe tayi tana ta sharb'an kuka dan gani take kaman itace silan komai da yake faruwa da Zainab d'in, doctor Mansur dakyar ya samu nunfashin ta ya dawo daidai ya Mata allurai bacci ya d'auke ta yace a bata waje ta samu ta huta kar hayaniyan mutane yasa ta farka, kowa ya futa amma Malama Aisha ta kasa futa taje ta rungume y'ar uwarta tana kuka dan dama shak'uwa ce mai k'arfi a tsakanin su, amma saida Umar yasan hanyan dayabi ya rabasu, dole yasa suka barta a wajen, Abba yace "ki daina Mata kuka idan kuma kinsan bazaki iya rik'e kukan ki ba kifuta kawai dan kema ba lafiyan bane dake"
Tace "Abbah nayi shuru bazan sake kuka ba dan Allah ku barni na zauna kusa da ita" futa sukayi suka koma falon Umma kowa da abunda yake sak'awa a zuciyar sa Yayan Zainab mai suna Usman ya kasa hak'uri ya dubi doctor Mansur yace "tun yaushe take fama da wannan ciwon?
Doctor Mansur file d'inta ya mik'a musu yace "zata kai shekara uku d'auke da wannan ciwon, dan mijin tane ya fara kawo ta asibitin kafin ya sake ta, ranan daya saketa kuma kulawan ta ya dawo hanuna tare da taimakawan wannan dattijuwan, ya nuna musu Inna Turai, ya cigaba da cewa dan ita take Mata hidiman komai idan bana nan, yanzu watan ta bakwai da rabuwa da mijin ta kuma naga jikin ta Alhamdulillah ta samu sauk'i ba laifi shiyasa na d'auko ta muka taho" labarin komai ya basu tun daga ranan da suka fara zuwa asibitin sa.
Usman yace "gaskiya bamu da bakin da zamu gode maka saidai muce Allah ya biya maka buk'atun ka na alkairi, ita kuma Allah ya bata lafiya, kuma munji dad'in killace ta da kayi harta futa idda ba tare da sun had'u da mijin taba, yanzu saidai mujira farkawan ta idan Allah ya bata lafiya saita fad'a mana abunda ya aifar Mata da ciwon zuciya"
Malama Aisha tana zaune a gaban Zainab ta buga uban tagumi idonta yana zubar da kwalla taji wayan ta ya fara ringing tana dubawa taga sunan my daughter wato Amna kenan, ta d'aga ta kara a kunnen ta, Amna tace gamu a unguwar da kika fad'a mana muna jikin wani farin masallaci"
Malama Aisha tace "ku shigo gidan jikin masallacin nan ne gidan, ta tashi ta futo da gudu ta shiga d'akin Umma tana cewa "Umma bani hijabi na naje na tarb'o y'aya na sun iso"
Umma itama cikin farin ciki tace "masha Allah ga hijabin, ta saka zata futa kenan taji muryan Amna tana sallama, futowa tayi suka rungume juna kafin ta rungume Abbas cikin kuka tace "yarana ashe zan sake ganin ku a rayuwa ta"
Amna yau karo na farko da taji bazata iya kiran ta da Malama Aisha ba tace "Ummi na kiyi hak'uri nasan mun shiga hakkin ki da yawa amma dole ne yasa mukayi hakan" Umma ce ta futo tace "kwadai shigo ayi murnan a d'aki ko?
Murmushi suka Mata kafin Amna tace "bamu kad'e bane da bak'i muke tafe" Kabiru ya futa ya shigo da su falon Umma, nan falon ya sake cika fam dan ma babbane shiyasa ya d'auke su dukan su.
Zainab bud'e idon ta daya Mata nauyi tayi ta ganta a d'akin ma'aifin ta da sauri ta tashi tana bin ko ina da kallo k'irjin ta yana bugawa, tashi tayi ta futo jiri na iban ta, d'akin Umma ta nufa saboda jin muryan mutane a wajen sallama tayi cike da tsoro da fargaban yadda iyayen ta zasu karb'e ta, Malama Aisha ta sake Amna taje ta rungume y'ar uwarta, suka fara murnan had'uwan su kafin suka shigo falon, da fuskan Amna da Abbas ta fara arba gaban tane yayi mummunan bugawa ta kallesu ta kalli Malama Aisha dakyar ta iya cewa suwaye wannan?
Malalam Aisha tayi murmushi tace "ya'ya nane, kema kinji kina sonsu ko? Zainab tace "dole naso duk abunda ya futo daga tsatsan k'anwata mafi soyuwa a gareni"
Amna na ganin su tace "Ummi ku y'an biyu ne dama?
Zainab sake d'ago kai tayi ta kalle Amna da take magana sai kuma idonta ta ya sauk'a akan y'an uwanta da tunda ta shigo bata lura dasu ba, da sauri ta durk'usa a wajen tana cewa dan Allah ku yafemun wallahi bansan ya akayi na butulce muku ba, Umma Abbah dan Allah karku duba d'unbun laifina a gare ku yasa ku kasa yafe mun, ko ku koreni a cikin ku, Allah ko Qur'ani kuka bani zan iya rantsewa akan bansan meya shiga kwakwalwa ta na butulce muku ba"
Doctor Mansur yace "kuyi magana dan Allah inba haka ba ciwon ta zai iya sake tashi domin ciwon ya fara cin zuciyar ta sosai dan Allah kuyi hak'uri ku yafe Mata"
Abbah ya taso ya rungume ta yace "kiyi shuru bana son kukan nan domin kukan shi zaisa nayi fushi dake" saurin goge hawayen ta tayi tace "na daina Abbah bazan sake kukan ba" zuwa yayi ya zaunar da ita kusa da Umma, Malama Aisha taje ta zauna kusa da Amna ta jawota jikin ta tace "nayi kewan ki my daughter"
Zainab ta kalleta tace "nikam bakiyi kewa na ba ko? Dariya Malama Aisha tayi ta sake rungume Amna a jikin ta kaman mai tsoron karta sake guduwa ta barta tace "bazaki gane yadda nake jinta a raina bane, kema nayi kewan ki sosai, amma nafi kewan su Amna saboda su bansan inda suka shiga ba ke kuma nasan duk inda kike kina cikin kwanciyan hankali"
Amna tace "kai Ummi itama kice kinyi kewan ta sosai fiye damu, kodan ciwon da yake damun ta, wallahi Ummi Yayar ki taban tausayi duk da bansan abunda tayi ba, naga sai kuka takeyi kuma gashi ance tana da ciwon zuciya" Abbas yace "ni karo na farko kenan da mutum ya bani tausayi, ya kalli Zainab yace Yayan Ummin mu Allah ya baki lafiya ya yafe miki zunuban ki" kowa a wajen yace amin.
Doctor Mansur ya tashi yace "Zainab ni zan koma Abuja kar dare yamun, Allah ya baki ikon cin jarabawan ki, sai wani lokacin idan Allah ya sake had'amu"
Itama tashi tayi tace "ai bazaka tafi ba sai na baka tarihin rayuwa ta kaman yadda nayi maka alk'awari"
Yace "ba za'ayi haka ba keda baki da lafiya mai zai kaiki bada tarihin rayuwar ki"
Tace "inaso na dawo mutum mai cika alk'awari a rayuwa ta, zan baku tarihin rayuwa ta koda kuwa hakan zaiyi sanadiyar d'aukewan nunfashi na, nasan idan na fad'a muku kaifin dana aikata ko bayan mutuwa na zaku tayani rok'on Allah ya yafe mun zunubai na, kuma bana so sai bayan mutuwa ta kuji abunda na aikata nafison kuji daga baki na"
Abbah yace "tunda ita tace zata baka ka barta ta futar da abunda yake damun ta a zuciyar ta, sannan kuma ko muma muna son muji wani irin rayuwa tayi da mijin ta bayan barin su Birnin Kudu, sannan kuma taya sukayi dukiya a lokaci k'ank'ani alhalin da su talakawa ne wanda abunda zasuci watarana ma gagaran su yakeyi, dan haka Zainab bissimillah muna jinki.
Komawa yayi ya zauna kafin kowa ya gyara zaman sa danjin abunda zai futo daga bakin ta.
Zainab ta futo tsakiyan falon ta zauna ta dubi mutanen falon d'aya bayan d'aya ta sauk'e ajiyan zuciya hawaye ya fara tsiyaya a fuskan ta tun kafin ta fara bada labarin kanta gyaran murya tayi tace "..............
***
Mmn Ashfaq