47
by @mmnashfaq
93/94
***
Mukaci kaci muka k'oshi naje zan kwanta nayi bacci, Umar yace baisan wannan zancen ba, ya cire kayan sa ya cire mun nawa, ya fara kusanta ta abunka da sabin shiga Umar tunda yake bai tab'a kusantan yar kowa ba sai a kaina, jin shi a wani duniyan ya bud'e murya yana ta zafga ihu wanda ya hana mutan gidan bacci gaba d'aya, gashi bazasu iya hana shi ba dan duka gidan tsoron sa sukeji, ba k'aramun wahala nasha ba, da asuba Maman sa tazo ta d'auke ni ta wuni tana gasa ni, saida nayi kwana uku a d'akin ta kafin na dawo d'akin Umar, tunda Umar yasan dad'in kusan tan mace ya fara neman Mata a b'oye ban sani ba, da kud'in sadaki na muke cin abinci yana k'arewa muka shiga damuwa Umar ya fara bin y'an uwansa akan su taimaka masa da abunda zaici, amma suka rufe Ido su suka koresa, sukace suma karatun da sukayi nutsu sukayi ne ya kaisu wannan matakin da suke, gashi cikin gidan su ba'a zuba mana abinci, Abbah kuma ya hanani shiga gidan sa, sai Aisha ne take taimako na watarana ta kawo mun abinci naci a sace, saiya dawo duk gidan mu bamai sona sai Aisha, kullun ana gama abinci zata saci idon Umma tazo muci tare, tunda Umar ya fahinci haka yace yafi k'arfin gidan mak'iyan sa su ciyar da Matan sa, dan haka ya fara dako yana kawo mun abinci naci, a haka nima na samu wanke wanke da shara a gidan masu kud'i, kullun saina dawo mana da abincin da zamuci, idan wata yayi suka biyani albashi ina zuwa gida na damk'a wa Umar duka, shi zamuyi ta tattali ya kaimu wani lokaci kuma dashi yake siyan abun shaye shayen sa dan ya kasa dainawa duka, tunda na fara aiki Umar ya daina futa ko ina kullun a gida yake wuni, idan kunga ya futa to anyi mana salary yaje siya mana nama da abun shaye shayen sa, kuma hakan bai tab'a damuna ba tunda muna zaman lafiya, iyaye na da y'an uwana nabisu sunce duk ranan dana sake zuwa kusa dasu saisun kashe ni duk cikin su Aisha ce kawai maisona, nima ita kad'e nake gani naji dad'i, daga farko ina aikina cikin kwanciyan hankali, tun ranan da mai gidan ya d'aura Ido a kaina ya kwallafa ransa akan sai yayi sex dani, dan nafi duka matan sa kyau da diri had'i da sura maikyau duk talaucin da muke ciki baisa jikina ya lalace koya nuna talauci ba, ranan daya fad'a mun buk'atan sa akaina hankali na yayi mungun tashi nace masa ni Matar aure ce, yace mun ya sani ai hark'a da Matan aure yafi dad'i, suna bani kud'in aikina na gudu nabar aiki a gidan, da Umar ya tambaye ni dalilin barina aikin nace masa sun tashi a garin ne, baiyi wani dogon bincike ba ya amince da abunda na fad'a, sabon talauci ya sake zuwa mana yayunsa suna da kud'i amma sunk'i taimakon mu, ga laulayin ciki daya sakani a gaba, muna cikin wannan mawuyacin halin wani abokin cin mushen sa ya dawo daga Abuja, ganin yadda yayi kud'i lokaci guda abun yayi mungun d'agawa Umar hankali, ya kasa hak'uri saida yaje ya tambaye sa wani aiki yakeyi da yayi kud'i lokaci guda, bai b'oye masa ba yace "Umar bazaka iya aikin da nakeyi ba, domin nima hanyan arzikin aka mun lokacin da naje Abuja, na had'u da wani bawan Allah daya ciro rayuwa ta a k'angin talauci, saidai hanyan ba kowa bane yake yarda yayi bishi"
Umar yace masa wani irin hanya ne?
Yace "k'ungiyan mafiya ya sakani, saidai na basu y'an uwana guda biyu da wani mak'oci na, shikenan iya abunda na basu suka bani dukiya irin wannan"
Umar yace "dan Allah shima ya sakashi a hanyan komai suka buk'ata zai basu, koda kuwa ran Maman sane" Haladu yace ya shirya su koma tare, Umar yace masa bazai iya tafiya yabar Matan sa ba, dariya Haladu yayi yace ai dama bance kabar Matar kaba, tare zamu tafi dukan mu.
Lokacin da Umar yazo ya sanar dani ya samu aikin yi ba k'aramun tsoro naji daga farko ba, saida yayita kwantar mun da hankali ya gwada mun ai aikin bayi da matsala, idan ya shiga k'ungiyan bazai bada kowa nasa ba, kawai akwai aikin da zasu na turasa yayi ne, nidai na amince ne kawai dan bani da katangan dafawa, muka tattara muka koma Abuja ba tare da mun ma kowa sallamah ba, sai wayan gari akayi akaga bamu nan, koda mukaje Abuja a gidan Haladu muka fara zama, a daren da mukaje a daren haladu ya tafi da Umar wajen meeting d'insu ya gabatar dashi, awun farko aka bashi jinin mutum ya sha bai musu musu ba ya karb'a ya sha, Shugaban su ya dube sa yace "ina maka murnan shigowa cikin mu, sannan sharad'in mu na farko zaka bamu jinin d'an uwanka guda d'aya, na biyu kuma zaka bamu ya'yan ka gudu biyu, idan kuma kana son dukiya mai yawa wanda duniya zasu san dakai zaka bamu ya'yan ka guda hud'u, muna sonsu duka guda hud'un rayayyu, idan ka amince da sharad'in mu shikenan idan kuma baka amince ba zaka biya mu jinin daka sha yanzu kayi tafiyan ka"
Umar jin ance zaiyi dukiyan da duniya zata san dashi yasa yace "na amince zan muku duk abunda kukeso saidai Matana bata aihu ba jikine na wata bakwai a jikin ta, sukace karya damu duk ranan data aihu zasu fad'a masa inda zasu kai y'ayan saidai bazasu karb'a ya'yan ba harsai da amincewan Matan sa, Umar yace "ba komai kuma ya bada k'anin sa mai suna Yusuf wanda ya mutu ta hanyan accident kowa ya zaci mutuwan Allah yayi ba wanda ya gane Umar ne ya bada shi, lokacin daya dawo ya kasa mun bayani, sai bayan sati d'aya lokacin ya siya mana gida mun koma harya nema mun y'an aiki, a sati d'ayan rayuwa ta canja mana muka manta da wani abu waishi talauci, lokacin da cikina ya shiga wata takwas ya bani kyautan million uku da mota babba, kafin ya sanar dani abunda k'ungiya take buk'ata, ina gamaji na watsa masa kud'in sa da key motan sa nace rayuwar ya'yana ya fiye mun komai a duniya idan ya bani kud'i da mota dan toshiyar baki ne ya kwashe abunsa banaso, hankalin sa ba k'aramun tashi yayi ba, yayita lallab'i na amma fur nak'i amincewa daga k'arshe na tattara kayana nace ya sakeni zan bar mishi gidan sa, ganin haka yasa yace ya fasa na rik'e ya'yana amma zamu koma k'angin talauci, nace masa na amince ai da damuke talaucin ba mutuwa mukayi ba, ganin bazan amince ba yaje ya sanarwa Haladu halin da yake ciki Haladu yace ya bari idan sukaje meeting da daddare sai yayi bayani.
Da sukaje meeting bayan an gama gabatar da komai Umar ya kawo k'orafin sa akaina k'ungiya tace idan baisan hanyan da zaibi ya shawo kan Matar sa ba ya biyasu duka dukiyan da suka bashi yayi gaba, kuma basu yarda yayi amfani da magic d'in da suka bashi ba wajen shawo kaina, hankalin Umar ya sake tashi yasan ko abunda dangin sa suka mallaka ya kawo musu baikai kud'in da suka bashi ba, daya dawo ba irin lallab'in da baimun ba amma nak'i fur nace mishi ni na gaji da auran sa ya sake ni kawai na tafi gidan mu bazanyi zaman auran ba.
Ganin da gaske zan tafi yasa yayita bani hak'uri yace mun k'ungiya tace mishi ta hak'ura da karb'an ya'yan sa, saidai zai koma talauci, nace masa na amince ai talauci ba uban daya kashe, bayan kwana hud'u da yin maganan mu muna kwance yace "Zainab yanzu kinfi zab'an d'anki akan dukiya ko? tun kafin ki aihu kin fifita abunda zaki aifa fiye dani, shifa d'a idan suka karb'a zamu sake aifan wani dukiya kuma idan ya wuce mun shikenan, amma tunda ban isa nace miki ki bada abu ki bayar ba ki tashi kibar mun gidana yanzu"
Jikina ne ya fara b'ari nace "dan Allah Umar kayi hak'uri kasan bazan iya rabuwa dakai ba, amma tunda kace kana son abasu abasun kawai na hak'ura" na k'arasa magana cikin kuka.
Yace "karna basu wataran kizo kina cewa nina ba da ya'yan ki fa"
Tace "ai kaima ya'yan kane yadda nake sonsu haka kaima kake sonsu"
Yace "ba d'a d'aya zaki basu ba ya'ya hud'u zasu karb'a, amma zamuyi dukiya fiye da tunanin ki" nace ba komai duk yadda kakeso haka za'ayi na amince.
Yaje ya nasarwa k'ungiya akan na amince, ranan dana aihu aka mana umarnin damu kai abunda na aifa bakin ruwa dan a gaban mu za'a yanka abunda na aifa, tun ina nak'uda yaje ya mana booking d'in jirgi dan wajen da zamu kai yaran ea nisa, ina aihuwa muka bar Abuja zuwa bakin ruwan da zamu ajiye jinjirin nida Umar, inaji ina gani aka janye mun abunda na aifa ta cikin ruwa, bayan mun koma na rufe kaina a d'aki nayita kuka, ina ganin Umar nake saurin share hawaye na, na wanke fuska na gudun kar yayiyta mun fad'a, ranan da muka kai y'ar mu k'ungiya yama Umar kyautan mak'udan kud'in daya rikita shi, shine ya gina mana gida a Maitama muka koma, kowa rayuwar sa yakeyi a unguwar, anan na had'u da Hanifa, saidai ita bata da aure zaman kanta takeyi dan maneman tane ma suka gina Mata gidan, k'awance mukeyi sosai dukan mu bamu b'oyewa junan mu sirrin mu, saidai ban tab'a fad'a Mata Umar d'an mafiya bane, ban jima da aihuwa ba na sake samun wani cikin, shima ina aihuwa muka sake kai abunda na aifa wannan bakin ruwan, a shekara biyar na aifa yara hud'u, mata uku namiji d'aya duka ana yankasu a gaban idona, tun abun yana damuna har na cire a raina na zauna zaman jiran Allah ya kawo mun wanda zan goyasu a bayana tunda na gama bawa k'ungiya ya'yan su, dangin Umar suna ganin munyi kud'i suka dawo jikin mu kowa so yake yace Umar d'an uwansa sane, shi kuma ya daina zuwa wajen su, duk wanda ya nemi yaje wajen sa kuma zaisha wulak'anci, haka kowa ya hak'ura ya zuba masa Ido, nima ranan daya ganni muna waya da Aisha ba k'aramun fad'a nasha ba yace duk ranan da muka sake waya a bakin aure na, haka inaji ina gani ya rabani da Aisha, dan lokacin ba k'aramun tsoran sa nakeji ba, duk abunda yace nayi shi nake aikatawa ban isa na musan ta masa ba, bayan k'ungiya ta karb'a y'aya na hud'u, na fara murnan zan fara rik'e d'a, kwatsam Umar yace mun k'ungiya tace mishi ya'yan da muka basu basu ishe suba dan haka zasuna dauk'an duk cikin dana samu, haka dole na amince dan ban isa na mishi musu ba, tun lokacin daga zaran nasamu ciki yana wata biyar zan nemeshi na rasa, bansan iya adadin cikin da k'ungiya suka d'auka a jiki na ba, ranan da Umar ya futo yaga inata kuka yace mun k'ungiya tace bazata sake dauk'an cikina ba yanzu zan iya aihu, ba k'aramun farin ciki nayi ba ranan, saidai kuma a ranan daya fad'a mun a ranan yabar garin, saida ya jima kafin ya dawo, daya dawo kuma komai nashi ya canja, kullun yana d'akin sirrin sa, saidaga baya nakeji a bakin Inna Turai ashe yara uku ya ajiye a d'akin yana sex dasu k'ungiya na dauk'an cikin jikin su, saina nuna masa kaman bansan abunda yakeyi ba gudun karya bincika yagane Inna Turai ne ta fad'a mun ya koreta, labarin yadda yayi aure da ce Mata da yayi k'ungiya ta cire ma'aifan ta da kuma yadda akayi har ta kamu da ciwon zuciya k'arshe ya saketa da zaman da tayi a gidan doctor Mansur duk ta fad'a musu"
Falon ne ya d'auki salati kowa yana Allah wadar da halin ta, Abba yace ban tab'a ganin wawiyan yarinyan shashasha irin kiba, amma Zainab kinyi asaran rayuwa duniya da lahira" dakyar Daddy ya lallab'a sa yayi shuru dan ganin yana k'ok'arin Mata baki, yace ya barta taji da rashin d'a da ma'aifan da k'ungiya ta cire ma kawai ya isheta.
Amna da take kuka kaman idonta zai futa tace "dama akwai uwa irin ki a duniyan nan? Wallahi tunda nake ban tab'a ganin uwa mara Imani da tausayi irin kiba, ashe gwanda uwar mu k'in shayar damu kawai tayi ta d'anka wa ma'aifin mu mu, tace ya rik'e abun sa, ke kuma dakan ki kike kai y'ayan ki ga gunki, kai Allah yayi wadaran rayuwar ki, ai baki ga komai bama kijira sakayan ya'yan da kika wulak'an ta" kukan da Inna Turai takeyi ne yasa kowa mayar da hankali kanta Daddy yace..............
***
Mmn Ashfaq