48
by @mmnashfaq
95/96
***
Yaya Kabiru yace "baiwar Allah wannan wani irin kuka ne haka, idan bazaki iyayin shuru ba ki futa kibamu waje muji da bak'in cikin labarin da mukaji kawai ya ishe mu"
Doctor Mansur yace "ku barta tayi kukan ta nasan kukan bak'in cikin zaman da tayi tana cin kud'in haram ne yake damun ta, ya kalli Zainab yace amma Zainab kin bani mamaki, da har inajin bak'in cikin abunda mijin ki ya miki ashe kin cancanci fiye da haka ma, wallahi dana san abunda kika aikata kenan da ko tab'a jikin ki ban tab'a yiba, Allah ya isa lokaci na da kika b'ata mun bazan tab'a yafe miki ba" kowa a wajen da abunda yake fad'a na Allah wadar da halin ta, Malama Aisha ce kawai ta rungume ta tana kuka tace "karki damu da abunda kowa zai fad'a y'ar uwata Allah gafurun rahim ne mai yawan gafara ne ga bayin sa, idan kika tuba domin shi zai yafe miki kura kuran ki, ki toshe kunne ki daga jin duk wani mungun abunda mutane zasu fad'a akanki, ki du'ufa istingifari da neman gafaran ubangijin ki"
Muryan Inna Turai sukaji tana cewa batama Allah laifin komai ba idan ma akwai masu laifi to nida mijin tane, domin duk abunda ta aikata bada son ranta tayi ba anfi k'arfin tane kawai, sannnan nice silan komai a karo na biyu na cutar da rayuwar Zainab"
Abbah yace "bamu fahinci abunda kike nufi ba, ko zaki iya mana bayani"
Zainab tace "Inna Turai karki d'aura wa kanki laifi alhalin bakisan duk abunda muke aikatawa ba a b'oye, dan Allah na rok'e ki karkima kanki k'azafi domin ki wanke ni a idon y'an uwana, domin ni nawa rayuwar ya k'are nasan ko y'an uwana sun karb'e ni sun yafe mun abunda na aikata ni bazan tab'a yafewa kaina ba, dan zuciya ta daf take da fashewa na mutu kowa ya huta, nasan kin soni kin zauna dani tamkar y'arda kika aifa a cikin ki, kin mun abunda uwar data aifeni bata mun ba, na rok'eki da girman Allah kiyi shuru da bakin ki, dan bana buk'atan kowa ya wanke ni daga munanan aiyukan dana aikata" ta k'arasa maganan cikin matsanancin kuka, saidai duk kukan da takeyi ba wanda yaji tausayin ta a wajen sai ma ganin ta cika musu kunne sukayi, Yaya Kabiru tasowa yayi zai daketa akan ta cika musu kunne, Abbas ya taso rai a b'ace yace "bawan Allah wakai tama laifi ne da kake k'ok'arin hukunta ta?
Da mamaki Yaya Kabiru ya kallesa yace "baka da tarbiyya ko? Ka b'ace mun anan kafin na had'a da kai"
Abbas shima cikin b'acin rai yace "kai ai tarbiyyan ne ya maka yawa shiyasa naga kana k'ok'arin shiga tsakanin Allah da bawan sa, wallahi kunji na rantse muku duk wanda yayi yunk'urin fad'a Mata maganan dazai d'aga Mata ciwo sai nayi shari'a dashi, dan ba ruwana da girman mutum, akwai wanda ya jawo Mata shiga wannan halin da take ciki daya wuce kune, dakun jata a jiki da wannan k'addaran bata fad'a Mata ba kuma ku bud'e kunnen ku dakyau ku saurare ni wlh.....ganin irin kallon da Amna take masa yasa ya kama bakin sa yayi shuru yazo kusa da Zainab ya zauna dan haka kawai yakejin soyayyan ta a ransa.
Inna Turai tace "Zainab ba sharri zanyi wa kaina danna wanke ki ba, abunda ya faru zan fad'a, inama yadda kika d'auke ni nima haka na d'auke ki da irin wannan ranan baizo mun ba, ban cancanci zama uwa ko y'ar aiki a gareki ba, domin nama rayuwar ki mungun illan da ba kowa bane zaiji ya yafe mun, idan baki manta ba tunda mijin ki ya siya gida aka kawo muku ni daga k'auyen Kano a matsayin y'ar aiki, ganin yadda kike wasa da dukiya yasa tunani na ya fara canjawa, naji inama jikata ne a gidan nan dan ina bak'in cikin ganin irin dukiyan da kike watsawa duk da baki rageni da komai ba kina girmama ni fiye da mijin ki, kina yawan mun kyautan kud'i da sutura hakan baisa naji ina sonki ba a zuciya ta, bani da wani tunanin daya wuce ta wani hanya zanbi jikata ta shigo gidan ki, saidai a fili ina kiyaye b'acin ranki kaman yadda kike kuje na duk wanda kike tare dasu, kwatsam na fahinci akwai matsalan da take faruwa tsakanin ki da mijin ki hakan yasa watarana zai futa naje na samesa akan na bashi shawaran idan bazaki bashi kwanciyan hankali ba yayi aure zakifi girmama shi, daga farko na gaishe shi cikin kirsa nace masa "Alhaji kayi hak'uri da abunda zan fad'a maka, naga kaman ba jituwa tsakanin ka da matar ka, ya kamata ku zauna lafiya ka daina d'aga maka hankali tana kuka kodan cikin da yake jikin ta" anan yake sheda mun wai tun kafin ya aure ki dama baki sonsa dakyar kika amince kukayi aure bayan kunyi aure, yace miki zakuzo garin nan a karan farko kikak'i amincewa saida yaje gun wani malami a garin ku ya bashi abunda ya rufe miki baki kafin kika amince, amma maganin baiyi tasiri akanki ba, kuna zuwa ya b'aci, dan akwai wani buk'atan dayazo miki dashi kikak'i amincewa, daga k'arshe kikace ya sake ki, yace mun yanzu ma kukan danaga kinayi kwana biyu akan wai saiya sake kine ke bazaki zauna dashi ba, shiyasa duk ya shiga damuwa gashi Allah ya jarabe shi da sonki, kuma y'an uwan ki sunce idan kika kashe auran ki karki koma gare su, ma'aifin ki yace zai tsine miki idan kikak'i zaman aure, ke kuma kince ya sakeki ki tafi yawon duniya, yanzu baisan ya zaiyi ba dan Allah idan akwai Malamin dana sani wanda aikin sa yakeci kaman yankan wuk'a dan Allah na kaishi.
Nace indai akan wannan ne ya kwantar da hankalin sa ina da wanda zansa ya mishi aiki a k'auyen mu wanda duk abunda ya fad'a bazaki iya mishi musu ba, a take Umar ya bani kyautan dubu d'ari biyar yace idan kuma aikin yayi zai bani kud'in da ban tab'a rik'ewa a rayuwa ta ba, washe gari muka tafi k'auyen mu da yake Albasu cikin k'araman hukuman Kano, muna zuwa na shiga na samu Malamin nace masa dan Allah yamun abunda Umar zaiji yana son jikata daya buga k'asa yace mun na bari sai zuwa gaba kad'an tukunna, na futo nama Umar iso yana shiga suka gaisa kafin yace yana so ya kafe masa Matan sa kuma asa Mata tsoran sa a zuciyar ta, ta inda duk abunda ya fad'a Mata bazata iya mishi musu ba, Malamin yace bazai mishi duka wannan aikin ba harsai yaga yawan abun sadakan sa, mak'udan kud'i Umar ya zuba masa a gaban sa wanda ya rud'a sa, yace idan kana da wasu buk'atan ka fad'a ni kuma namaka alk'awarin maka, Umar najin haka yayita lissafo masa abunda yakeso ya masa akan Zainab da kuma ya cire Mata son y'an uwan ta gaba d'aya a zuciyar ta, ta inda bazata na tunawa da kowa ba, ina gefe ina jinsu a lokacin abun bai dameni ba saboda Umar ya gama siyeni da kud'i, wani ruwan magani Malamin ya bashi yace yaje ya had'a da ruwan maniyin sa ya had'awa Zainab tea tasha, ya bashi wani garin magani yace ya hura Mata a fuskan ta, sauran aikin kuma zaiyi daga inda yake, kud'i Umar ya dad'a masa muka dawo gida, muna zuwa Umar ya aiwatar da abunda Malam ya sakashi zuwa kwana uku Zainab ta canja, kukan da takeyi ta daina, duk abunda Umar yace Mata baya so a take zata daina yin sa, sai naji dad'i a raina, ganin burin Umar ya cika saura nawa, bayan lokaci kad'an Zainab ta aihu saidai bata dawo gida da abunda ta aifa ba, sukace mun abun baizo da raiba, haka tayita aihuwa ba ya'yan sai na sake samun Umar na shigar masa da tallan jikata, yace mun bayi da ra'ayin k'ara aure na tashi na bashi waje, nace masa bawai inaso ya auri jikata bane dan kwad'ayin dukiyan sa, saidan ganin matanshi wabi ne da ita duk ya'yan da ta aifa suna mutuwa, kuma bana so ya mutu bayi da magaji, amma idan ya auri jikata zatayi ta aifa masa yara danmu duk zuri'an mu ba mai wabi, a lokacin ya nuna yayi na'am da magana ta, yace idan aka kwana biyu zamuje k'auyen sai a d'aura auran kawai gaba d'aya, ba k'aramun farin ciki nayi ba ganin muma zamu faso gari jikata zata auri mai dukiya, bamufi wata biyu dayin magana ba kwatsam naji labarin Umar yayi aure ya auri Hanifa k'awar Zainab hakan ba k'aramun k'ona mun rai yayi ba, nasamu labarin ne a wajen driver sa, naso sanarwa Zainab cin amanan da Umar da Hanifa suka Mata sai kuma nayi shuru, na bari taji da kanta, wallahi Zainab ban tab'a tunanin Umar d'an mafiya bane, kuma ban zaci ya'yan ki yakeso ki mallaka mishi ba, dan Allah Zainab ki yafe mun, ban miki wannan abunda da mungun nufi ba, saidan ganin kin zauna lafiya keda mijin ki, kinji dalilin dayasa nace miki ba laifin ki bane laifi nane dan nice nakai Umar wajen da aka canja miki tunani zuwa na Umar kika dawo sai......bata k'arasa ba taji ankai Mata naushi a baki kafin ta d'ago ya rufeta da duka ta ko ina, duk yadda akayi dashi ya barta amma yak'i saida Amna tace "Abbas irin tarbiyyan da muka baka nida Baffa kenan? Abbas har ka kai munzalin da manya zasuna maka magana kana banza dasu? Saita fashe da kuka, zuwa yayi da gudu ya rungume ta yace "dan Allah Adda Amna kiyi hak'uri ki yafe mun wallahi ta b'ata mun raine, kijifa abunda ta aikata wa baiwar Allah da bataji ba bata gani ba, baiwar Allah tana son ya'yan ta amma saida tabi hanyan datasa aka kwace Mata ya'yan ta daga k'arshe aka rabata da duk abunda zata aifa a duniya, wallahi ko Goggo ban tsaneta ba kaman yadda na tsani wannan Matan, waya sani ma ko muma abunda akama ma'aifiyar mu kenan yasa ta tsane mu"
Zainab da zuciyar ta ya bushe ta kasa kuka sai nuna Inna Turai da yatsan ta takeyi tace Inna kece silan rabani da Ya'yana, duk inda nak'i amincewa da mungun nufin Umar amma saida kika kaishi wajen da aka juya mun ra'ayi? Bazance miki Allah ya isa ba dan nasan Allah zai isar mun, shi kad'e zai iya mun sakayya a tsakani na dake, gwanda ni naga k'arshe na ke kuma kijira zuwan naki k'arshen dan bazaki bar duniya ba harsai kin fara girb'an abunda kika shuka, idan kina son na zauna da mijina lafiya meyasa ni baki tun k'areni kin mun nasiha ba, kije na barki da Allah"
A take zuciyar kowa yayi rauni a wajen wanda suke ganin laifin Zainab na biyewa zuciyar ta suka daina kowa ya fara ganin bak'in Inna Turai, sukayi ta lallab'in Zainab suna bata hak'uri"
Doctor Mansur yace "kiyi hak'uri Zainab nayi gaggawan yanke miki hukunci ba tare danaji k'arshen labarinn ba, dan Allah ki samu kiyi kuka kar kibar abun a zuciyar ki dan ba k'aramun illa zai iya miki ba, rik'e wan zai iya fasa miki zuciya ki mutu"
Murmushi Zainab tayi yace ai da zuciyar zata fashe na mutu yanzu da nafi kowa farin ciki, meye amfanin rayuwa ta yanzu dani da gawa duk d'aya muke a halin da nake ciki"
Baffa daya k'ura Mata Ido tunda aka fara maganan baiyi magana ba yana ayyana abubuwa a ransa"
Daddy ya tab'a sa ganin irin kallon da yake Mata ya zaci zallan k'auyanci ne yace "bawan Allah tunda mun had'u dukan mu, kuma munsan yaran nan tunda suka had'u da Malama Aisha bazasu yarda su bimu yau ba, idan ba matsala ka fad'a mana inda uwar yaran take inso idan sun kwana biyu anan sai Aisha ta kaisu wajen ta suga juna.
Baffa Sule ya jinjina kai yace "mai ake cewa idan mutum zai godewa wa Allah daya bashi ikon fad'an magana?
Daddy yayi murmushi yace "kace Alhamdulillah ka godewa Allah daya baka ikon kaiwa wannan lokacin"
Baffa Sule yace yawwa nagode kafin yayi gyaran murya yace "Alhamdulillah nagodewa Allah dabani ikon ganin ranan dazan sauk'e nauyin da d'an uwana ya d'aura mun, saidai bansan ta inda zan muku bayani ba saidai duk abunda zan fad'a nasan Amna tasan dashi, dan Baffan ta ya sanar da ita komai saidai bai Mata bayani ta sigan da zata fahinta bane..........
***
Mmn Ashfaq