49
by @mmnashfaq
97/98
***
Wata rana d'an uwana ya futo zai zaga sai yaga wata bak'ar mota a gefen rigan mu, kuma kowa yasan fulani ko keke basu mallaka nasu na kansu ballan tana mota, hakan yasa ya fara duba motan yaga ba kowa saiyayi tunanin ko masu satan shanu ne, saiya gangara bakin ruwa a hankali ganin wasu mutane guda biyu Mace da namiji sun ajiye yarinya a bakin ruwa yasa ya shiga cikin ruwan ta k'asan ruwan yake tafiya harya gangara wajen da yarinyan take suna tsaye a wajen ya ciro hanun sa ta cikin ruwa ya d'auki jinjiran ya fara tafiya da ita hanun sa yana waje jikin sa yana cikin ruwa ganin haka yasa mutanen suka juya suka tafi da gudu dankar mutanen rigan suzo su gansu, yana ganin sun shiga motan su sun tafi ya futo ya shiga gida da ita da gudu ya d'auko rigansa ya kanannad'e ta dan tsirara take ba kayan ajikin ta, a zuciyar shi yana mamakin rashin imani irin na mutanen nan, lokacin da Matar sa taga jinjiran ba k'aramun tashin hankali sukayi da ita akan yarinyan ba, ba yadda baiyi da ita akan ta shayar da ita ba amma tak'i yarda, k'arshe haka d'an uwana yayi ta fama da raino, ranan data cika sati d'aya a wajen sa ya saka Mata suna Amina, dalilin dayasa ake kiran ta da Amna kenan ya yanka Mata rago, haka abubuwa suka masa yawa ga kiwo ga reno, duk inda zaije da ita yake zuwa, yayi rigan sak'i mai k'aton aljihu a gaba, sai ya zama na duk inda zaije da ita yake zuwa daidai da kiwo tare suke zuwa, hakan yasa shak'uwa mai k'arfi irin shak'uwan da uwa takeyi d'an ta ya shiga tsakanin su, wanda yafi sonta fiye da ya'yan daya aifa a cikin sa, a haka rayuwa tayi taja har Amna takai shekara biyar kuma ta tashi da kwarjini kowa ya ganta saiya sota, gata fara kyakykyawa kana ganin ta kaga fulanin usul, ranan data cika shekara biyar ranan wasu mutane suka sake dawowa da daddare suka ajiye jariri, kuma ranan ma anyi sa'a Baffa Salihu yana wajen yaje iban ruwa, basu lura dashi ba suna ajiyewa Matan ta juya tana kuka, mijin shima ya juya yana ta Mata fad'a, Baffa Salihu yana ganin haka ya lallab'o ya d'auki jinjirin a garin dauk'an sa wani k'aramun iccen da yake wajen ya soki hanun shi a take jini ya b'alle, bai damu da ciwon dayaji ba, ya koma gefe ya lab'e yasawa jinjirin hancin sa a baki da yake da yunwa a jikin jinjiri yayi saurin cafkewa yana tsotsa, yana gani suka juyo Matan taje ta tab'a jinin tace shikenan shima harsu yanka sa sai kuma ta saka kuka, ya Allah ka dube zuciya ta kasan bada nufi nakeba da ya'yana ba saidan bin umarnin mijina, fusgan hanun ta namijin yayi sukaje suka shiga mota yana ta Mata masifa, duk da d'an uwana yaga laifin mace amma furucin ta na k'arshe yasa shi saurin tashi ya dubata, anan ya gane akwai mungun asiri a jikin ta, kallon fuskan mijin yayi ya ganshi bak'i k'irin yayi saurin tsuguna dan ya zaci hukuma ne kuma kowa yasan mu fulani akwai tsoron hukuma, shima yaran randa ya cika sati Baffa Salihu yacewa Amna wani suna takeso a saka mishi "bugun farko tace "Abbas" Baffa Salihu yace da naso asaka mishi Adamu amma tunda kinfi son Abbas shikenan Allah ya raya da imana, tun daga lokacin Amna ta dawo uwar Abbas, itake rainon sa idan Baffan su baya nan, idan ya dawo kuma ya karb'e ta, kasancewan Baffa bayida d'a namiji yasa ya d'auki son duniyan nan ya d'aura wa Abbas dukda yafi son Amna amma shima Abbas d'in yana ganin gata, wanda haka ya jawo sanadin rashin zaman lafiya a gidan sa harya koma ga Allah, wannan shine tarihin rayuwar ku Amna da Abbas, daidai da Baffan ku baisan asalin kuba"
Amna tashiga mummunan tashin hankali ta taso tazo gaban Baffa Sule cikin kuka daya bayyana tashin hankalin ta tace "Baffa Sule dan Allah kace ba daidai naji ba, mun yarda mun yafe ma'aifiyar mu basai mun santa ba, amma dan Allah kace Baffa na shine ma'aifin mu, Baffa Sule bakaga irin shak'uwan mu bane kowa yasan irin shak'uwan da yake tsakinin d'a da iyayen sane, ka tuna irin soyayyan da yake tsakanin mun da Baffa na Baffa yaso fiye da y'ayan Goggo dan Allah Baffa Sule kace mun ba haka bane" kuka takeyi da iya k'arfin ta Baffa Sule ya rasa maizai ce Mata dan iya gaskiyan abunda ya sani ya fad'a musu, Abbas kan ya dawo kaman gunki dan ya nemi magana ya rasa a bakin sa dakyar ya iya had'a kalmomi yace "wato bayan rashin uwa harda rashin uba ma, ashe mu shegune iyayen mun sunyi abun kunya ne suka yar damu? Koda yake nikam ina da uwa da uba, Adda Amna ce uwata Baffa na kuma ubana dan ba wanda ya isa yamun gorin rashin asali" sai lokacin yaji kuka yazo masa falon yayi tsit kaman ba mutane a cikin ta, bakajin motsin komai sai kukan Amna dana Abbas, dukkan su ba wanda ya lura da halin da Zainab take ciki, magana ta farayi da k'arfi cikin fusgan nunfashi tace "K'ARAMAN HUKUMAN TILDE A KOGIN RIGAN LARRO? tana gama fad'a idon ta ya k'arasa kafewa bakin ta yana futar da yawu mai kumfa, Amna ce ta taso dagudu tana cewa karkiyi haka karkiyi haka dan Allah, kafin su doctor Mansur su k'araso harta sume a hanun Amna Abbas dauk'an ta yayi cak yace "inane asibitin garin nan ya fuce da gudu yana sake tambayan su, doctor Mansur sanin bayi da kayan aikin da zai iya ceto rayuwar ta yasa shima ya rufa masa baya, saidai kafin ya futa har Ammar ya bud'e motan da sukazo dashi Abbas ya sakata, wani privet hospital suka kaita, suna zuwa doctor Mansur ya nuna musu Idcard d'insa, ba musu suka barshi ya shiga ya fara dubata sauran likitotin suna taya shi, kowa yayi tagumi a waje yana jiran sakamakon dazai futo, Abbas da Amna sai kuka sukeyi ana basu hak'uri, cikin ikon Allah anyi nasaran ceton rai ta, amma sunsha wahala alluran bacci aka Mata kowa yaje yayi sallah, Amna da Abbas sun kasa gotawa a wajen dakyar ka lallab'a su akan suje suyi sallah, sukace saidai suyi a k'ofan d'akin, alola sukaje sukayi suka tada sallah a wajen, suna zaune suna Mata addu'an samun sauk'i har aka kira mangrib, saidai kowa yaje yayi sallah ya dawo kafin suka ta da nasu, suna cikin sallah wata Norse ta futo tana cewa patient d'in ku ta farka sai kiran sunan yara biyu takeyi wai Abbas da Amna idan suna wajen nan su shigo, dakyar Amna suka iya k'arasa sallah, ko addu'a basu samu daman tofawa ba suka tashi da sauri suka shiga d'akin da suka tabbatar anan Zainab take, suna shiga suka k'arasa jikin gadon Abbas ya rik'e hanun ta d'aya Amna ta haura saman gadon ta d'aura kan Zainab a cinyan ta tace "sannu Momma kiyi hak'uri kowa da tasa kalan jarabawan, kiyi addu'a Allah ya baki ikon cikin jarabawan ki, idan zaki yarda zamu maye miki gurbin ya'yan ki da kika rasa, tunda mu bamu san inda zamu samo namu iyayen ba"
Zainab rumtse idonta tayi tanajin wani farin ciki a zuciyar ta mara musaltuwa, a take lafiya ya zamo Mata kaman ba ita bane take nunfashi dakyar d'azu, tace "Abbas karb'o mun waya na a hanun doctor Mansur" ba musu yaje ya karb'o Mata wayan ta da tun zuwan su yake aljihun doctor Mansur, rabonta da kunna wayan tun ranan da Umar ya sake ta, hotunan wayan ta shiga ta dubo hoton kogin Larro tace "kunsan wannan ruwan?
Amna ta karb'a ta kalli ruwan murmushi tayi tace "kinga nan wajen kullun a nan muke zama da Baffa na yana bani labari wasu mutane da ban fahinci labarin rayuwar mu yake bani ba sai d'azu, ta sake nuna wani waje tace nan kuma a wajen muke zama da ni da Abbas da Baffan mu shima labarin wajen daban kullun, ashe labarin Abbas ne, murmushi taga Zainab tanayi tace "Momma a ina kika samu wannan photon?
Wani photo Zainab ta nuna Mata tace "kinsan wannan Matan?
K'urawa photon Ido tayi tace "amma Allah yayi kama anan da ina da irin kayan saina d'auka nice, Momma dan Allah ki nuna mun ita, saboda kaman mu ya b'aci" Abbas yana karb'a yace kece mana Adda Amna duba photon dakyau ki gani, murmushi Amna tayi tace bani bace Abbas bani da irin kayan, agarin kallon photon hanun sa ya danna masa photon Umar tashi yayi da sauri ya kalli Amna yace Adda Amna duba wannan photon ki gani! Amna itama cikin fad'uwan gaba tace kodai shine Baban ka duba kaga yadda kukayi kama?
Zainab tace "ku kashe wayan na baku wani labari" ajiye wayan sukayi suka mayar da hankali kanta, Daddy dasu Abbah ganin shuru shuru basu futo ba, yasa suka shiga d'akin dan su duba abunda ya rik'e su, suna shiga suka tadda Zainab zaune a tsakiyan su Amna kaman ba ita bane aka kawo rai a hanun Allah, dukan su basu lura da shigowan su ba, Amna tace "Momma kinyi shuru sai murmushi kikeyi bayan kinsan ke muke sauraro?
Zainab murmushi ta sakeyi tace "Amna ko yau na fad'i na mutu zan mutu ina farin cikin ganin ku a rayuwa ta, labarin da Baffan ku ya bayar duka nasan dashi, mune mutanen da mukaje muka ajiye ki a bakin ruwan Larro, a zaton mu hanun dodon tsafin sune ya d'auke ki ashe bashi bane, lokacin da nayi aihuwa na biyu dana uku a ruwan Lagos mukaje mu ajiye yaran, kuma a gabana aka yanke kan yaran kafin gangan jikin su ya b'ace a hanuna, aihuwa na na hud'u Umar yace ance mu sake kai jinjirin bakin ruwan Larro, aka mishi gargad'i da mu lura dakyau kuma karmu bar wajen harsai mun goga jikin jinjirin a hanun mu da goshin mu, da mukaje na kasa kallon abunda za'a ma d'ana na juya baya, Umar ya juyo shima yana mun masifa akan na juyo naga kashe d'an da idona dan haka Shugaban su ya fad'a, kafin na juyo sai jini nagani a wajen ashe ba jinin d'ana bane jikin Baffan kune, bayan mun koma gida, cikin dare bayan Umar ya dawo daga meeting yayita zagina akan wai nayi kuskure ban aikata abunda k'ungiya tace ba, dan haka duk lokacin dana samu ciki zasuna cirewa da zaran yakai wata biyar, hankali na ba k'aramun tashi yayi ba, sai nayi saurin dannewa dankar Umar yayita mun fad'a, nasan dai banyi kuskure ba wajen ajiye yaro, sai nazaci dama haka ya musu alk'awari tun farko ya fake da wai nai , ta damk'e hanun Amna tace "Amna ke y'ata ce ke nafara aifa son zuciya yasa muka kaiki bakin kogi, kuma da Allah ba azzalumin bawan sa bane saiya kare mun ke ya kaiki hanu maikyau kuma kikaci sunan Umma na, ta dawo da hankalin ta kan Abbas tace "Baba Abbas kaine d'ana na hud'u, kuma sunan kakan ka ma'aifin Umar kaci, da Amna ta yarda ansaka maka Adamu da sunan Abba na kaci, nasan ba soyayya ta a zuciyar ku, nasan na muku abunda ban cancanci ku kirani da suna Mama ba, amma dan Allah ku yafe mun nima bada san raina nayi ba, gusar mun da tunani na akayi" ta rungume hannun su a k'irjin ta tace "dan Allah kar kuce zaku gujeni nasan idan na sake rasa ku a karo na biyu rayuwa ta zata shiga mawuyacin hali" Amna da take jin maganan kaman a mafarki wai yau itace a gaban ma'aifiyar ta? Ta rungume ta tace "ina sonki Momma na ina sonki fiye da tunanin mutum, ashe Allah zai nuna mun wannan ranan, Momma ki daina tunanin zamu guje ki, mun dawo gareki kenan har k'arshen rayuwar mu" ta sauk'a a gadon taje da gudu ta rungume Malama Aisha tace "ashe soyayyan y'a da uwarta kike mun, shiyasa tun ranan da kika gammu kikaji kina sonmu tare da tausayin rayuwar mu, ashe ke uwar muce bamu sani ba?
Abbas shima yazo ya rungume ta yace "shiyasa kika shiga wani hali da kika rasamu, tabbas soyayyan uwa gaskiya ne akan d'anta, sai yau na dad'a tabbatar wa jini ya wuci wasa, muma tun ranan da muka tafi kike ranmu, tabbas Baffan mu yayi gaskiya kafin ya rasu yacewa Adda Amna akwai wata rana da sabin mutane zasuzo rayuwar mu, dan Allah karmu gujesu, mu karb'e su hanu bibbiyu, tabbas Baffa mun karb'e su hanu hamsin hamsin ma, saidai Baffa bamu buk'atan d'ayan bak'on, dan duk duniya bani da wanda na tsana sama dashi" duk wajen ba wanda baiyi farin ciki ba, ba kaman Baffa Sule ma da yakeji inama d'an uwansa yana raye yaga wannan ranan"
Doctor Mansur yace "kar kace haka Abbas shima duk lokacin da shiriya yazo mishi ku karb'e sa hanu bibbiyu domin ko ba komai uban kune"
Amna tace "doctor dan Allah ka daina kwatan tasa a matsayin uba a gare mu, inba haka ba zan furta kalman la'ana akansa, Malama Aisha tayi saurin toshe Mata baki tace karna sake jin haka a bakin ki"
Tashi Amna tayi tazo gaban Zainab ta sunkuya tace "hauna goyaki Momma na mu tafi gida tunda kin samu sauk'i, kuma insha Allahu har abada bazaki sake ciwo ba"
Zainab tayi murmushin farin ciki tace "bazaki iya goyani ba Amna"
Dariya Amna ta kwashe dashi tace " Baffa Sule kaji wai bazan iya goyata ba, Momma kin manta ni baffulatanan riga ne, jiki na ya ginu da noma da daka dacin tuwon dawa dana gero, tunda Baffa na ya rasu na nemi gata na rasa, kinga da wannan hanun nake daka masara dawa da gero ya dawo gari, da hanun nake zuwa ice na ibo ruwa a kogin da kika ajiye mu nayi girki kowa yaci a gidan, har kike tunanin akwai abunda bazan iya yinshi ba a duniyan nan?
Zainab da tausayi ta kalli y'arta hawaye wani nayin wani a idon ta, Amna ta share Mata tace "meye kuma na kuka Momma keda ya kamata kiyi farin ciki, Allah nefa ya duba zaluntan ki da akayi ya barki da ya'yan ki biyu, amma Momma kin tabbatar da an yanka sauran k'anne na a gaban idonki ko kuma suma irin namu ne ya faru dasu"
Zainab cikin kuka tace "tabbas sukan basu doran k'asa, dan tun suna hanuna ake cire musu kansu, kafin gangan jikin su ya b'ace a hanuna"
Baffa Sule yace "muma rigan mu tunda muka lura matsafa suna son wajen domin sunce akwai wani babban nasara da yake tattare dawajen yasa muka kafe ruwan ta yadda duk wani mungu bazai taba haurawa ruwan ba, inaga sun zaci zasu iyane yasa sukace ku kawo su wajen.
Doctors ne suka shigo dansu dubata sai suka ganta a zaune anata hira da ita, abun ba k'aramun mamaki ya basu ba, Abbas yace zamu tafi ku bamu sallama, a take suka bata sallama, Amna ta dage Zainab bazata taka da k'afan ta zuwa wajen mota ba, dole Zainab ta hak'ura Amna ta goyata, Abbas ya bud'e musu mota ta ajiyeta tace "Momma ko nauyi baki dashi" suna isa gida Mommy ta taso da sauri tana tambayan su ya jikin Zainab d'in? Dan dama ita bata bisu ba, Amna tace "ta warke da taga ya'yan ta"
Mommy tace "Alhamdulillah a ina taga ya'yan tan? Dariya Amna tayi wannan karan tace "Mommy ashe mu ya'yan tane da Allah ya kub'utar Mata damu, labarin komai taba Mommy" ba k'aramun murna Mommy tayi ba ta musu addu'an alkairi da neman tsarin Allah" Abbas yace "ina azzaluman tsohuwan nan take tazo taga Allah ya kub'utar Mata damu bamu mutu ba"
Mommy tace "ai tare kuka futa bata biku asibitin bane?
***
Mmn Ashfaq