50
by @mmnashfaq
99/100
***
Umma tace "ai kunya bazai barta ta zauna ba, nasan yanzu haka ta d'auki hanyan garin su, Allah ya shirya masu hali irin nata" suka amsa da amin.
Amna tace "karku damu da abunda tayi, wasu ma sunayin abunda yafi nata ma wanda suka yarda dasu, mukan a wajen mu abunda tayi alkairi ya dawo mana, dan ba k'aramun taimakon rayuwar mu tayi ba, nasan ko mun tashi a gidan uban mu baza mu mutu ba, tunda Allah yayi baza'a kashe mu ta wannan hanyan ba, saidai zamuci haram musha haram mu saka haram, karatun mu haram daidai da nunfashin da zamu shak'a a gidan sa haram ne, sai Allah ya kub'utar damu ko iskan gidan sa bamu tab'a shak'a ba daga asibiti aka wucewa damu bakin ruwa, kunga kamata yayi mu gode wa Allah daya wurga mu wajen da aka ciyar damu aka shayar damu da halak, ita kuma duniya ce bakayi bama aka maka ballan tana kayi, nasan ma'aifiyar mu bata tab'a zaluntan wani ba ballan tana ace hakkin wani ne ya bita, saidai ace hakkin iyayen tane na bijire musu da tayi shiya jawo Mata ta shiga wannan halin, duk da Abba ma yana da nashi laifin a ciki"
Daddy yace "tabbas Abbah yafi kowa ma laifin domin zan iya cewa kusan shine ma ya jawo komai ya faru duk da Allah ya k'adarci sai aure ya kasance a tsakanin su, a lokacin da mukaga yaran mu sun mana ba daidai ba ko kuma suna shirin aikata abunda zai cutar da rayuwar su, ba fushi ya kamata muyi dasu ba, k'ok'arin jawo su jikin mu zamuyi mu fahintar dasu illan abunda suke shirin aikatawa, amma kai kuma ka kasa aikata hakan duk da kana ikirarin duk cikin ya'yan ka tafi maka biyayya, Zainab daga farko bata kula Umar ba duk abunda ya Mata saitazo ta sanar dakai, maimakon kayi k'ok'arin dauk'an matakin hanyan da zaka raba y'arka dashi sai kuma kafara ma y'arka hukunci akan laifin da ba nata ba, ka kuma daina kulata, wannan abunda kayi shiya jawo ta fara kulasa domin taga ana dukan ta akan abunda batayi ba zuciyar ta zai raya Mata ai gwanda tayi laifin a daketa da tushe akan ana dukan ta batare datayi komai ba, ya kamata wannan abun ya ishe duk mai shirin aikata irin abunda kayi ishara, ita kuma Zainab Allah ya saka Mata ga duk wanda ya zalince rayuwar ta, shi kuma Umar idan mai shiryuwa ne Allah ya ganar dash ya dawo hanya madaidaiciya idan kuma bamai shiryuwa bane Allah ya mana maganin sa, Alhamdulillah ma da Allah yasa yanzu ba auran sa akanta, Zainab ki dage da addu'an neman tsari daga sharrin sa, dan idan ya farga ya gane ya'yan sa sun dawo zaiyi ta kawo muku hari, Allah ya d'aura ku akansa.
Duka wajen suka amsa da amin Abbah yace "nima sai bayan auran na gane kuskure na, lokacin da naso jawota jikina a lokacin muka wayi gari da labarin barin su garin, kuma ba wanda yasan inda suka nufa, lokacin da labarin irin azzikin da sukayi da kuma yawan mutuwan ya'yan Zainab yazo mana, abun ba k'aramun firgita ni yayi ba, tun daga nan muka du'ufa Mata addu'a, da neman kariya daga sharrin sa, duk wanda yazo wajena saina saka sun Mata addu'a, kwatsam watarana yazo nan yana neman ta, na mishi barazanan kartazo gida nane kawai amma ba haka bane a zuciya ta, kullun idona yana kan hanyan ganin dawowan ta tunda yace tagudu bata gidan sa, dan muyi addu'an Allah ya farrak'a ta da gidan shi, kuma Alhamdulillah Allah ya karb'a addu'an mu, dan kaman yadda ta fad'a mana haka kawai ya saketa batare data mishi laifin komai ba, saidai mu cigaba da addu'an neman tsari" kowa a wajen saida ya furta albarkacin bakin sa, doctor Mansur ne ya fara mik'ewa yace zai tafi, Kabiru yace "ai ko cin mutane mukeyi a gidan nan bazaka tafi ba sai gobe, ka duba lokaci mana dare yayi, dukan ku hak'uri zakuyi idan Allah ya kaimu gobe saiku tafi"
Daddy yace "Allah ya nuna mana goben amma da ya'yana zan tafi"
Zainab ta zare ido tare da dafe k'irji tace "wasu ya'yan?
Yadda tayi maganan ba k'aramun dariya taba mutanen wajen ba, ai tana ganin sun fara Mata dariya ta futa da gudu itama tana dariya, Amna tabi bayan ta da kallo tana murmushi dan wani sabon soyayyan tane taji ya dad'a shiga zuciyar ta, Abbas kan kasa zama yayi yabi bayan ta, yana zuwa ya kwanta a cinyan ta yana cewa nayi missing komai naki Momma, shafa kansa tayi tace "karka damu har yanzu kai jinjiri ne, ko goyo kakeso yanzu zan maka, inaso nabiya bashin abunda banyi ba"
Rungume ta yayi yace "Momma ina sonki" bata iya mishi magana ba saboda kukan daya taso Mata, Amna itama kasa zama tayi ta biyo su tana zuwa ta ture sa a cinyan ta tace "nafika yinwan cinyan ta, dan nice abun tausayi kaifa tun kana jinjiri kakejin d'umi na ni kuma na Baffa na kawai naji" Zainab rungume ya'yan ta tayi tanajin soyayyan su a zuciyar ta, da daddare bayan kowa yaci abinci sun kwanta Amna tana manne da Malama Aisha, Zainab tana gefen ta, sun sakata a tsakiya ta kama hanun Zainab tana wasa da yatsun ta hawaye na gangarowa a idon ta Malama Aisha tace "a zato na kukan ki ya k'are, tunda kin rabu da duk wani TSANANIN rayuwa, yanzu zaki fara rayuwar farin ciki"
Kuka ne ya kub'uce Mata saida tayi mai isarta kafin tace "ban tab'a tunanin akwai ranan dazaizo nayi farin ciki irin na yau ba, wai yau nice a kwance a tsakiyan iyayena ina jin d'umin ma'aifiya ta, Allah mai yadda yaso da bawan sa, inama Goggo zatazo taga kyautar da Allah yamun yau, yau Allah ya had'a ni da dangi na farin cikin rayuwa ta, a kullun idan naganta tana hira da ya'yan ta sai abun ya bani sha'awa, ashe nima wannnan ranan zatazo mun, nasha wahalan rayuwa na shiga hatsari kala kala, labarin rayuwar ta tafara basu tun daga kan wahalan data sha da kuma lalata ta da Ilu Sama'ila da headmaster sukaso suyi Allah ya kub'utar da ita, sai kuma na k'arshe Saifuddeen, ta d'aura da cewa abunda yake damuna yanzu, Saifuddeen shiya fara taimakon mu lokacin da muka bar gidan Ummi na, shiya ciro rayuwar mu daga bayi ya bamu y'anci, saidai da manufa yayi, bayan ya tafi Spain ya barmu a hanun Ammar shi kuma Ammar yana mun soyayyan tsakani da Allah badan jikina ba, duk sta nace masa maza sun lalata mun rayuwa ciki kuwa harda abokin sa, amma yace yana sona haka, sai kuma Saifuddeen daya dawo shima yace yana sona da aure, amma bai daina neman Mata ba, ranan dazan bar gidan daya kama mun da k'awata na kamasa suna sex akan gadon da nake kwanciya, shine Daddy ya dawo dani gidan sa, yanzu na rasa wa zan aura a cikin su, na bar muku zab'i, ku zab'a mun duk wanda yafi dacewa da rayuwa ta"
Dukan su ba k'aramun kuka sukaci ba da tausayin rayuwar da ya'yan su suka shiga, Zainab tace "nagode wa Allah daya kub'utar mun dake batare da d'aya daga cikin su yayi nasaran lalata ki ba, Allah zai saka miki Amna, bani da abun cewa tunda Ummi ki tana wajen.
Malama Aisha taji dad'in karan da y'ar uwarta ta Mata tace "gaskiya Amna bazan baki shawaran auran Saifuddeen ba, dan auran mazinacin namiji abune mai wahalan gaske, amma zamuyi ta miki addu'an Allah ya zab'a miki mafi alkairi, idan Ammar alkairi ne a gareki Allah ya tabbatar mana, idan kuma ba mijin ki a cikin su Allah ya kawo miki nagari, amma gaskiya duk wanda yayi yunk'urin b'ata miki rayuwa bazan barshi ba dukan su sai nayi Sharia dasu"
Amna tayi murmushi tace "ai Allah ya nuna musu sakamakon duk abunda suka mun tun kafin su mutu, yau da mukaje Tilde danaga Sama'ila ba k'aramun tausayi ya bani ba dan ya dawo kaman wani almajiri, na d'auki kud'in sa da yayita bani na basa nayi gaba, shi kuma headmaster tun ba'aje ko inaba yaga sakamako, labarin yadda komai ya kasance ta basu, da jinyan da yayita yi, ba k'aramun dariya sukayi ba Malama Aisha tace "dama kece silan ciwon da yayi tayi kai amma naji dad'i, da haka yana faruwa da masu son lalata ya'yan mutane da abun yayi sauk'i" sun jima suna tattaunawa kafin bacci ya d'auke su.
Da safe bayan sun karya Daddy suka tashi zasu tafi, Ammar ne ya fara futa kafin Amna tabi bayan shi kallon ta yakeyi kaman zaiyi kuka saiya bata tausayi, a hankali ya bud'e bakin sa yace "Amna nasan zan tafine da d'unbin soyayyan ki a zuciya ta, lokacin da kikaga na daina kulaki, banyi haka danna kuntata miki ba sai dan na gujewa kawo matsala tsakani na da Saifu, saboda banaso Saifu yace naci amanan sa, dan ban tab'a tunanin akwai soyayya a tsakanin ku ba, amma yanzu ko bazaki aure niba bana miki sha'awan auran Saifu, saidai zanyi addu'an Allah ya zab'a mana mafi alkairi a tsakanin mu, zanso ace nine wanda zanyi nasara akanki, amma idan hakan bai faru ba, nasan Allah bai nufi ke Mata na bane, saidai ina rok'on karki manta dani a rayuwar ki" futowan su Mommy ne ya yanke musu maganan da sukeyi, Mommy ta rungume ta tace "zamuyi kewan ki Amna, nasan Aleesa idan sukaga bamu dawo tare ba zasuyi kuka, amma nasan kinyi kusan zuwa, sannan kar ganin Momman ki yasa ki mance da karatun ki kinga kina daf da had'a karatun ki karki bari kiyi asaran wannan daman.
Tace "insha Allahu Mommy zamuzo saidai dan Allah ku nemawa Abbas transfer ya dawo kusa da Momma zatafi jin dad'i, dan nasan idan muka tafi dukan mu bazata ji dad'i a ranta ba, zatayi ta tunanin wani abu zai faru damu, kuma masu irin ciwon su ba'a son suna yawan tunani, amma idan d'aya daga cikin mu yana kusa da ita abun zaizo Mata da sauk'i"
Daddy yace zamuyi k'ok'arin yin hakan insha Allahu"
Ammar tunda ya shiga mota ya saita mirror yana kallon Amna yana jin kaman ya d'auke ta su tafi tare, lokacin da motan su ya tashi Amna ta juyo suka had'a Ido sai taga idonsa yayi jajazur, itama ji tayi kaman zatayi kuka Malama Aisha tace "ai aji kunyan idona tunda ina wajen" rufe Idon ta tayi gida da gudu su Umma suka kwashe da dariya sunajin wani irin farin ciki mara musaltuwa a zuciyar su.
Bayan tafiyan su doctor Mansur shima ya musu sallamah yace duk lokacin da yasamu nutsuwa zaizo ya sake duba ta, sun mishi godiya sosai kafin ya tafi suka had'a masa talatin da takwas na arziki, Amna sosai suke samun kulawa da soyayyan agun kowa, Malama Aisha jinsu takeyi tamkar ya'yan data aifa a cikin ta dan jin son su take mara musaltuwa a zuciyar ta, Zainab ma tana nuna musu nata soyayyan da gata, saidai wani lokacin tana ma Malama Aisha kawaici, Amna rayuwa ya dawo Mata sabo idan ta tuna rayuwar ta na baya ta tuna na yanzu saita dad'a godewa Ubangiji na irin ni'imomin daya musu yanzu, daidai da rana d'aya basu tab'a tunanin Baban su ba ko kuma suyi maganan sa sun rungume iyayen su Mata, danko gidan su Umar basu tab'a shiga ba, Amna watan ta d'aya ta fara shirin komawa Bauchi domin karatun ta, Zainab har ranta batason nesa da y'arta saidai kuma ba yadda ta iya, saidai wannan karan Abba yace bazata zauna a gidan su Ammar ba akwai k'anin sa da yake Bauchi a gidan sa zata zauna, da kanshi ya kaita bauchi, a gidan k'anin sa suka sauk'a ya musu bayanin komai, sun nuna farin cikin su sosai na zuwan ta gidan haka ya'yan sama sun karb'e ta hanu hur hud'u, tare sukaje gidan su Ammar suka musu bayani, daga farko Daddy ya nuna rashin jin dad'in sa, amma dayaji tana gidan k'anin Abbah ne uwa d'aya uba d'aya, saiya hak'ura, amma yace shi zai cigaba da dauk'an nauyin karatun ta, Ammar ma yayi farin ciki da dawowan ta bauchi yasan koba komai zai samu daman dasa sabon soyayyan sa a zuciyar ta, Abbah basu bar garin ba saida suka karb'a transfer Abbas.
Umar zuwa yanzu hankalin sa ya fara mungun tashi na rashin sanin inda Zainab take ga k'ungiya ta sakashi a gaba akan lokacin amfani ma'aifar ta yayi, yaje duk inda take ya nemo ta dan suna buk'atan ganin ta a gaban su, dodon tsafin yace yanaso yasha jinin ta yaci namanta da ranta, Umar yace "saidai ayi hak'uri a canja mun ta wani hanya, ina da wata Matan yanzu haka nabar ta tana gida idan dodon tsafi ya yarda nakawo masa ita da abunda ta aifa duka.
Tsawa aka daka Masa kafin akace............
***
Mmn Ashfaq